Surah Al-Mursalat in Hausa: translation and audio
Surah 77 · المرسلات · The Emissaries · 50 verses
Surah Al-Mursalat verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Mursalat word by word in English.
Verse 1
وَٱلْمُرْسَلَـٰتِ عُرْفًا
Transliteration wal-mur'salāti ʿur'fan
Hausa Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
Verse 2
فَٱلْعَـٰصِفَـٰتِ عَصْفًا
Transliteration fal-ʿāṣifāti ʿaṣfan
Hausa Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
Verse 3
وَٱلنَّـٰشِرَٰتِ نَشْرًا
Transliteration wal-nāshirāti nashran
Hausa Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
Verse 4
فَٱلْفَـٰرِقَـٰتِ فَرْقًا
Transliteration fal-fāriqāti farqan
Hausa sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
Verse 5
فَٱلْمُلْقِيَـٰتِ ذِكْرًا
Transliteration fal-mul'qiyāti dhik'ran
Hausa Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
Verse 6
عُذْرًا أَوْ نُذْرًا
Transliteration ʿudh'ran aw nudh'ran
Hausa Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
Verse 7
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٌ
Transliteration innamā tūʿadūna lawāqiʿun
Hausa Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
Verse 8
فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتْ
Transliteration fa-idhā l-nujūmu ṭumisat
Hausa To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
Verse 9
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتْ
Transliteration wa-idhā l-samāu furijat
Hausa Kuma, idan sama aka tsãge ta.
Verse 10
وَإِذَا ٱلْجِبَالُ نُسِفَتْ
Transliteration wa-idhā l-jibālu nusifat
Hausa Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
Verse 11
وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتْ
Transliteration wa-idhā l-rusulu uqqitat
Hausa Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
Verse 12
لِأَىِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ
Transliteration li-ayyi yawmin ujjilat
Hausa Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
Verse 13
لِيَوْمِ ٱلْفَصْلِ
Transliteration liyawmi l-faṣli
Hausa Domin rãnar rarrabẽwa.
Verse 14
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ
Transliteration wamā adrāka mā yawmu l-faṣli
Hausa Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
Verse 15
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 16
أَلَمْ نُهْلِكِ ٱلْأَوَّلِينَ
Transliteration alam nuh'liki l-awalīna
Hausa Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
Verse 17
ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ ٱلْـَٔاخِرِينَ
Transliteration thumma nut'biʿuhumu l-ākhirīna
Hausa Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
Verse 18
كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِٱلْمُجْرِمِينَ
Transliteration kadhālika nafʿalu bil-muj'rimīna
Hausa Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
Verse 19
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 20
أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّآءٍ مَّهِينٍ
Transliteration alam nakhluqkkum min māin mahīnin
Hausa Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
Verse 21
فَجَعَلْنَـٰهُ فِى قَرَارٍ مَّكِينٍ
Transliteration fajaʿalnāhu fī qarārin makīnin
Hausa Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
Verse 22
إِلَىٰ قَدَرٍ مَّعْلُومٍ
Transliteration ilā qadarin maʿlūmin
Hausa Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
Verse 23
فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ ٱلْقَـٰدِرُونَ
Transliteration faqadarnā faniʿ'ma l-qādirūna
Hausa Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
Verse 24
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 25
أَلَمْ نَجْعَلِ ٱلْأَرْضَ كِفَاتًا
Transliteration alam najʿali l-arḍa kifātan
Hausa Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
Verse 26
أَحْيَآءً وَأَمْوَٰتًا
Transliteration aḥyāan wa-amwātan
Hausa Ga rãyayyu da matattu,
Verse 27
وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ شَـٰمِخَـٰتٍ وَأَسْقَيْنَـٰكُم مَّآءً فُرَاتًا
Transliteration wajaʿalnā fīhā rawāsiya shāmikhātin wa-asqaynākum māan furātan
Hausa Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
Verse 28
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 29
ٱنطَلِقُوٓا۟ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Transliteration inṭaliqū ilā mā kuntum bihi tukadhibūna
Hausa Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
Verse 30
ٱنطَلِقُوٓا۟ إِلَىٰ ظِلٍّ ذِى ثَلَـٰثِ شُعَبٍ
Transliteration inṭaliqū ilā ẓillin dhī thalāthi shuʿabin
Hausa Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
Verse 31
لَّا ظَلِيلٍ وَلَا يُغْنِى مِنَ ٱللَّهَبِ
Transliteration lā ẓalīlin walā yugh'nī mina l-lahabi
Hausa Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
Verse 32
إِنَّهَا تَرْمِى بِشَرَرٍ كَٱلْقَصْرِ
Transliteration innahā tarmī bishararin kal-qaṣri
Hausa Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
Verse 33
كَأَنَّهُۥ جِمَـٰلَتٌ صُفْرٌ
Transliteration ka-annahu jimālatun ṣuf'run
Hausa Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
Verse 34
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 35
هَـٰذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ
Transliteration hādhā yawmu lā yanṭiqūna
Hausa Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
Verse 36
وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ
Transliteration walā yu'dhanu lahum fayaʿtadhirūna
Hausa Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
Verse 37
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 38
هَـٰذَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ ۖ جَمَعْنَـٰكُمْ وَٱلْأَوَّلِينَ
Transliteration hādhā yawmu l-faṣli jamaʿnākum wal-awalīna
Hausa Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
Verse 39
فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌ فَكِيدُونِ
Transliteration fa-in kāna lakum kaydun fakīdūni
Hausa To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
Verse 40
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 41
إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى ظِلَـٰلٍ وَعُيُونٍ
Transliteration inna l-mutaqīna fī ẓilālin waʿuyūnin
Hausa Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
Verse 42
وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ
Transliteration wafawākiha mimmā yashtahūna
Hausa Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
Verse 43
كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Transliteration kulū wa-ish'rabū hanīan bimā kuntum taʿmalūna
Hausa (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
Verse 44
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
Transliteration innā kadhālika najzī l-muḥ'sinīna
Hausa Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Verse 45
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 46
كُلُوا۟ وَتَمَتَّعُوا۟ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ
Transliteration kulū watamattaʿū qalīlan innakum muj'rimūna
Hausa (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
Verse 47
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 48
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرْكَعُوا۟ لَا يَرْكَعُونَ
Transliteration wa-idhā qīla lahumu ir'kaʿū lā yarkaʿūna
Hausa Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."
Verse 49
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration waylun yawma-idhin lil'mukadhibīna
Hausa Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Verse 50
فَبِأَىِّ حَدِيثٍۭ بَعْدَهُۥ يُؤْمِنُونَ
Transliteration fabi-ayyi ḥadīthin baʿdahu yu'minūna
Hausa To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni
Read Surah Al-Mursalat in another language
- English (word by word)
- Albanian
- Amazigh
- Amharic
- Assamese
- Azerbaijani
- Bambara
- Bangla
- Bosnian
- Bulgarian
- Chechen
- Chinese
- Czech
- Dari
- Dhivehi
- Dutch
- Finnish
- French
- German
- Gujarati
- Hebrew
- Hindi
- Indonesian
- Italian
- Japanese
- Kannada
- Kazakh
- Khmer
- Kinyarwanda
- Korean
- Kurdish
- Luganda
- Malay
- Malayalam
- Maranao
- Marathi
- Nepali
- Norwegian
- Oromo
- Pashto
- Persian
- Polish
- Portuguese
- Romanian
- Russian
- Sindhi
- Sinhala
- Somali
- Spanish
- Swahili
- Swedish
- Tagalog
- Tajik
- Tamil
- Tatar
- Telugu
- Thai
- Turkish
- Ukrainian
- Urdu
- Uyghur
- Uzbek
- Vietnamese
- Yao
- Yoruba
All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.
Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.