MyDugsiStart learning

Surah An-Nazi'at in Hausa: translation and audio

Surah 79 · النازعات · Those who drag forth · 46 verses

Surah An-Nazi'at verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah An-Nazi'at word by word in English.

Verse 1

وَٱلنَّـٰزِعَـٰتِ غَرْقًا

Transliteration wal-nāziʿāti gharqan

Hausa Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.

Verse 2

وَٱلنَّـٰشِطَـٰتِ نَشْطًا

Transliteration wal-nāshiṭāti nashṭan

Hausa Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.

Verse 3

وَٱلسَّـٰبِحَـٰتِ سَبْحًا

Transliteration wal-sābiḥāti sabḥan

Hausa Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.

Verse 4

فَٱلسَّـٰبِقَـٰتِ سَبْقًا

Transliteration fal-sābiqāti sabqan

Hausa Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre.

Verse 5

فَٱلْمُدَبِّرَٰتِ أَمْرًا

Transliteration fal-mudabirāti amran

Hausa Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni.

Verse 6

يَوْمَ تَرْجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ

Transliteration yawma tarjufu l-rājifatu

Hausa Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.

Verse 7

تَتْبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ

Transliteration tatbaʿuhā l-rādifatu

Hausa Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.

Verse 8

قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ

Transliteration qulūbun yawma-idhin wājifatun

Hausa Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.

Verse 9

أَبْصَـٰرُهَا خَـٰشِعَةٌ

Transliteration abṣāruhā khāshiʿatun

Hausa Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.

Verse 10

يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِى ٱلْحَافِرَةِ

Transliteration yaqūlūna a-innā lamardūdūna fī l-ḥāfirati

Hausa Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?

Verse 11

أَءِذَا كُنَّا عِظَـٰمًا نَّخِرَةً

Transliteration a-idhā kunnā ʿiẓāman nakhiratan

Hausa "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"

Verse 12

قَالُوا۟ تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ

Transliteration qālū til'ka idhan karratun khāsiratun

Hausa Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"

Verse 13

فَإِنَّمَا هِىَ زَجْرَةٌ وَٰحِدَةٌ

Transliteration fa-innamā hiya zajratun wāḥidatun

Hausa To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.

Verse 14

فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ

Transliteration fa-idhā hum bil-sāhirati

Hausa Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.

Verse 15

هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ

Transliteration hal atāka ḥadīthu mūsā

Hausa Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?

Verse 16

إِذْ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلْوَادِ ٱلْمُقَدَّسِ طُوًى

Transliteration idh nādāhu rabbuhu bil-wādi l-muqadasi ṭuwan

Hausa A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?

Verse 17

ٱذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ

Transliteration idh'hab ilā fir'ʿawna innahu ṭaghā

Hausa Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.

Verse 18

فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ

Transliteration faqul hal laka ilā an tazakkā

Hausa "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.

Verse 19

وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ

Transliteration wa-ahdiyaka ilā rabbika fatakhshā

Hausa "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa?"

Verse 20

فَأَرَىٰهُ ٱلْـَٔايَةَ ٱلْكُبْرَىٰ

Transliteration fa-arāhu l-āyata l-kub'rā

Hausa Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.

Verse 21

فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ

Transliteration fakadhaba waʿaṣā

Hausa Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),

Verse 22

ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰ

Transliteration thumma adbara yasʿā

Hausa Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.

Verse 23

فَحَشَرَ فَنَادَىٰ

Transliteration faḥashara fanādā

Hausa Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.

Verse 24

فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلْأَعْلَىٰ

Transliteration faqāla anā rabbukumu l-aʿlā

Hausa Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."

Verse 25

فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلْـَٔاخِرَةِ وَٱلْأُولَىٰٓ

Transliteration fa-akhadhahu l-lahu nakāla l-ākhirati wal-ūlā

Hausa Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.

Verse 26

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَىٰٓ

Transliteration inna fī dhālika laʿib'ratan liman yakhshā

Hausa Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.

Verse 27

ءَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُ ۚ بَنَىٰهَا

Transliteration a-antum ashaddu khalqan ami l-samāu banāhā

Hausa Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.

Verse 28

رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّىٰهَا

Transliteration rafaʿa samkahā fasawwāhā

Hausa Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.

Verse 29

وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَىٰهَا

Transliteration wa-aghṭasha laylahā wa-akhraja ḍuḥāhā

Hausa Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.

Verse 30

وَٱلْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ

Transliteration wal-arḍa baʿda dhālika daḥāhā

Hausa Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.

Verse 31

أَخْرَجَ مِنْهَا مَآءَهَا وَمَرْعَىٰهَا

Transliteration akhraja min'hā māahā wamarʿāhā

Hausa Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.

Verse 32

وَٱلْجِبَالَ أَرْسَىٰهَا

Transliteration wal-jibāla arsāhā

Hausa Da duwatsu, Yã kafe ta.

Verse 33

مَتَـٰعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَـٰمِكُمْ

Transliteration matāʿan lakum wali-anʿāmikum

Hausa Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.

Verse 34

فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلْكُبْرَىٰ

Transliteration fa-idhā jāati l-ṭāmatu l-kub'rā

Hausa To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.

Verse 35

يَوْمَ يَتَذَكَّرُ ٱلْإِنسَـٰنُ مَا سَعَىٰ

Transliteration yawma yatadhakkaru l-insānu mā saʿā

Hausa Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.

Verse 36

وَبُرِّزَتِ ٱلْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ

Transliteration waburrizati l-jaḥīmu liman yarā

Hausa Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.

Verse 37

فَأَمَّا مَن طَغَىٰ

Transliteration fa-ammā man ṭaghā

Hausa To, amma wanda ya yi girman kai.

Verse 38

وَءَاثَرَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا

Transliteration waāthara l-ḥayata l-dun'yā

Hausa Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).

Verse 39

فَإِنَّ ٱلْجَحِيمَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ

Transliteration fa-inna l-jaḥīma hiya l-mawā

Hausa To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.

Verse 40

وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفْسَ عَنِ ٱلْهَوَىٰ

Transliteration wa-ammā man khāfa maqāma rabbihi wanahā l-nafsa ʿani l-hawā

Hausa Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.

Verse 41

فَإِنَّ ٱلْجَنَّةَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ

Transliteration fa-inna l-janata hiya l-mawā

Hausa To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.

Verse 42

يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَىٰهَا

Transliteration yasalūnaka ʿani l-sāʿati ayyāna mur'sāhā

Hausa Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?

Verse 43

فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَىٰهَآ

Transliteration fīma anta min dhik'rāhā

Hausa Me ya haɗã ka da ambatonta?

Verse 44

إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ

Transliteration ilā rabbika muntahāhā

Hausa Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.

Verse 45

إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَىٰهَا

Transliteration innamā anta mundhiru man yakhshāhā

Hausa Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.

Verse 46

كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوٓا۟ إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَىٰهَا

Transliteration ka-annahum yawma yarawnahā lam yalbathū illā ʿashiyyatan aw ḍuḥāhā

Hausa Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.

Read Surah An-Nazi'at in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.