MyDugsiStart learning

Surah Al-Waqi'ah in Hausa: translation and audio

Surah 56 · الواقعة · The Inevitable · 96 verses

Surah Al-Waqi'ah verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Waqi'ah word by word in English.

Verse 1

إِذَا وَقَعَتِ ٱلْوَاقِعَةُ

Transliteration idhā waqaʿati l-wāqiʿatu

Hausa Idan mai aukuwa ta auku.

Verse 2

لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌ

Transliteration laysa liwaqʿatihā kādhibatun

Hausa Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.

Verse 3

خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ

Transliteration khāfiḍatun rāfiʿatun

Hausa (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.

Verse 4

إِذَا رُجَّتِ ٱلْأَرْضُ رَجًّا

Transliteration idhā rujjati l-arḍu rajjan

Hausa Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.

Verse 5

وَبُسَّتِ ٱلْجِبَالُ بَسًّا

Transliteration wabussati l-jibālu bassan

Hausa Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.

Verse 6

فَكَانَتْ هَبَآءً مُّنۢبَثًّا

Transliteration fakānat habāan munbathan

Hausa Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.

Verse 7

وَكُنتُمْ أَزْوَٰجًا ثَلَـٰثَةً

Transliteration wakuntum azwājan thalāthatan

Hausa Kuma kun kasance nau'i uku.

Verse 8

فَأَصْحَـٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ

Transliteration fa-aṣḥābu l-maymanati mā aṣḥābu l-maymanati

Hausa Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?

Verse 9

وَأَصْحَـٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ

Transliteration wa-aṣḥābu l-mashamati mā aṣḥābu l-mashamati

Hausa Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?

Verse 10

وَٱلسَّـٰبِقُونَ ٱلسَّـٰبِقُونَ

Transliteration wal-sābiqūna l-sābiqūna

Hausa Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,

Verse 11

أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلْمُقَرَّبُونَ

Transliteration ulāika l-muqarabūna

Hausa Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.

Verse 12

فِى جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ

Transliteration fī jannāti l-naʿīmi

Hausa A ckin Aljannar ni'ima.

Verse 13

ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration thullatun mina l-awalīna

Hausa Jama'a ne daga mutãnen farko.

Verse 14

وَقَلِيلٌ مِّنَ ٱلْـَٔاخِرِينَ

Transliteration waqalīlun mina l-ākhirīna

Hausa Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.

Verse 15

عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوْضُونَةٍ

Transliteration ʿalā sururin mawḍūnatin

Hausa (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu.

Verse 16

مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيْهَا مُتَقَـٰبِلِينَ

Transliteration muttakiīna ʿalayhā mutaqābilīna

Hausa Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.

Verse 17

يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَٰنٌ مُّخَلَّدُونَ

Transliteration yaṭūfu ʿalayhim wil'dānun mukhalladūna

Hausa Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.

Verse 18

بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ

Transliteration bi-akwābin wa-abārīqa wakasin min maʿīnin

Hausa Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.

Verse 19

لَّا يُصَدَّعُونَ عَنْهَا وَلَا يُنزِفُونَ

Transliteration lā yuṣaddaʿūna ʿanhā walā yunzifūna

Hausa Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.

Verse 20

وَفَـٰكِهَةٍ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ

Transliteration wafākihatin mimmā yatakhayyarūna

Hausa Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.

Verse 21

وَلَحْمِ طَيْرٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ

Transliteration walaḥmi ṭayrin mimmā yashtahūna

Hausa Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.

Verse 22

وَحُورٌ عِينٌ

Transliteration waḥūrun ʿīnun

Hausa Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.

Verse 23

كَأَمْثَـٰلِ ٱللُّؤْلُؤِ ٱلْمَكْنُونِ

Transliteration ka-amthāli l-lu'lu-i l-maknūni

Hausa Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.

Verse 24

جَزَآءًۢ بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Transliteration jazāan bimā kānū yaʿmalūna

Hausa A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Verse 25

لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا تَأْثِيمًا

Transliteration lā yasmaʿūna fīhā laghwan walā tathīman

Hausa Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.

Verse 26

إِلَّا قِيلًا سَلَـٰمًا سَلَـٰمًا

Transliteration illā qīlan salāman salāman

Hausa Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.

Verse 27

وَأَصْحَـٰبُ ٱلْيَمِينِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلْيَمِينِ

Transliteration wa-aṣḥābu l-yamīni mā aṣḥābu l-yamīni

Hausa Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?

Verse 28

فِى سِدْرٍ مَّخْضُودٍ

Transliteration fī sid'rin makhḍūdin

Hausa (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.

Verse 29

وَطَلْحٍ مَّنضُودٍ

Transliteration waṭalḥin manḍūdin

Hausa Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.

Verse 30

وَظِلٍّ مَّمْدُودٍ

Transliteration waẓillin mamdūdin

Hausa Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.

Verse 31

وَمَآءٍ مَّسْكُوبٍ

Transliteration wamāin maskūbin

Hausa Da wani ruwa mai gudãna.

Verse 32

وَفَـٰكِهَةٍ كَثِيرَةٍ

Transliteration wafākihatin kathīratin

Hausa Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.

Verse 33

لَّا مَقْطُوعَةٍ وَلَا مَمْنُوعَةٍ

Transliteration lā maqṭūʿatin walā mamnūʿatin

Hausa Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.

Verse 34

وَفُرُشٍ مَّرْفُوعَةٍ

Transliteration wafurushin marfūʿatin

Hausa Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.

Verse 35

إِنَّآ أَنشَأْنَـٰهُنَّ إِنشَآءً

Transliteration innā anshanāhunna inshāan

Hausa Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.

Verse 36

فَجَعَلْنَـٰهُنَّ أَبْكَارًا

Transliteration fajaʿalnāhunna abkāran

Hausa Sa'an nan Muka sanya su budurwai.

Verse 37

عُرُبًا أَتْرَابًا

Transliteration ʿuruban atrāban

Hausa Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.

Verse 38

لِّأَصْحَـٰبِ ٱلْيَمِينِ

Transliteration li-aṣḥābi l-yamīni

Hausa Ga mazõwa dãma.

Verse 39

ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration thullatun mina l-awalīna

Hausa Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.

Verse 40

وَثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْـَٔاخِرِينَ

Transliteration wathullatun mina l-ākhirīna

Hausa Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.

Verse 41

وَأَصْحَـٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلشِّمَالِ

Transliteration wa-aṣḥābu l-shimāli mā aṣḥābu l-shimāli

Hausa Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?

Verse 42

فِى سَمُومٍ وَحَمِيمٍ

Transliteration fī samūmin waḥamīmin

Hausa Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.

Verse 43

وَظِلٍّ مِّن يَحْمُومٍ

Transliteration waẓillin min yaḥmūmin

Hausa Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.

Verse 44

لَّا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍ

Transliteration lā bāridin walā karīmin

Hausa Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.

Verse 45

إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَبْلَ ذَٰلِكَ مُتْرَفِينَ

Transliteration innahum kānū qabla dhālika mut'rafīna

Hausa Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.

Verse 46

وَكَانُوا۟ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلْحِنثِ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration wakānū yuṣirrūna ʿalā l-ḥinthi l-ʿaẓīmi

Hausa Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.

Verse 47

وَكَانُوا۟ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَـٰمًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ

Transliteration wakānū yaqūlūna a-idhā mit'nā wakunnā turāban waʿiẓāman a-innā lamabʿūthūna

Hausa Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"

Verse 48

أَوَءَابَآؤُنَا ٱلْأَوَّلُونَ

Transliteration awaābāunā l-awalūna

Hausa "Shin, kuma da ubanninmu na farko?"

Verse 49

قُلْ إِنَّ ٱلْأَوَّلِينَ وَٱلْـَٔاخِرِينَ

Transliteration qul inna l-awalīna wal-ākhirīna

Hausa Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."

Verse 50

لَمَجْمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَـٰتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ

Transliteration lamajmūʿūna ilā mīqāti yawmin maʿlūmin

Hausa "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."

Verse 51

ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلْمُكَذِّبُونَ

Transliteration thumma innakum ayyuhā l-ḍālūna l-mukadhibūna

Hausa "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"

Verse 52

لَـَٔاكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ

Transliteration laākilūna min shajarin min zaqqūmin

Hausa "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."

Verse 53

فَمَالِـُٔونَ مِنْهَا ٱلْبُطُونَ

Transliteration famāliūna min'hā l-buṭūna

Hausa "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."

Verse 54

فَشَـٰرِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ ٱلْحَمِيمِ

Transliteration fashāribūna ʿalayhi mina l-ḥamīmi

Hausa "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."

Verse 55

فَشَـٰرِبُونَ شُرْبَ ٱلْهِيمِ

Transliteration fashāribūna shur'ba l-hīmi

Hausa "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."

Verse 56

هَـٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ ٱلدِّينِ

Transliteration hādhā nuzuluhum yawma l-dīni

Hausa Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.

Verse 57

نَحْنُ خَلَقْنَـٰكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَ

Transliteration naḥnu khalaqnākum falawlā tuṣaddiqūna

Hausa Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?

Verse 58

أَفَرَءَيْتُم مَّا تُمْنُونَ

Transliteration afara-aytum mā tum'nūna

Hausa Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?

Verse 59

ءَأَنتُمْ تَخْلُقُونَهُۥٓ أَمْ نَحْنُ ٱلْخَـٰلِقُونَ

Transliteration a-antum takhluqūnahu am naḥnu l-khāliqūna

Hausa Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?

Verse 60

نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ ٱلْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ

Transliteration naḥnu qaddarnā baynakumu l-mawta wamā naḥnu bimasbūqīna

Hausa Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,

Verse 61

عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمْثَـٰلَكُمْ وَنُنشِئَكُمْ فِى مَا لَا تَعْلَمُونَ

Transliteration ʿalā an nubaddila amthālakum wanunshi-akum fī mā lā taʿlamūna

Hausa A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.

Verse 62

وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَ

Transliteration walaqad ʿalim'tumu l-nashata l-ūlā falawlā tadhakkarūna

Hausa Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?

Verse 63

أَفَرَءَيْتُم مَّا تَحْرُثُونَ

Transliteration afara-aytum mā taḥruthūna

Hausa Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?

Verse 64

ءَأَنتُمْ تَزْرَعُونَهُۥٓ أَمْ نَحْنُ ٱلزَّٰرِعُونَ

Transliteration a-antum tazraʿūnahu am naḥnu l-zāriʿūna

Hausa Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?

Verse 65

لَوْ نَشَآءُ لَجَعَلْنَـٰهُ حُطَـٰمًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَ

Transliteration law nashāu lajaʿalnāhu ḥuṭāman faẓaltum tafakkahūna

Hausa Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.

Verse 66

إِنَّا لَمُغْرَمُونَ

Transliteration innā lamugh'ramūna

Hausa (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"

Verse 67

بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ

Transliteration bal naḥnu maḥrūmūna

Hausa "Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"

Verse 68

أَفَرَءَيْتُمُ ٱلْمَآءَ ٱلَّذِى تَشْرَبُونَ

Transliteration afara-aytumu l-māa alladhī tashrabūna

Hausa Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?

Verse 69

ءَأَنتُمْ أَنزَلْتُمُوهُ مِنَ ٱلْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ ٱلْمُنزِلُونَ

Transliteration a-antum anzaltumūhu mina l-muz'ni am naḥnu l-munzilūna

Hausa Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?

Verse 70

لَوْ نَشَآءُ جَعَلْنَـٰهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَ

Transliteration law nashāu jaʿalnāhu ujājan falawlā tashkurūna

Hausa Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?

Verse 71

أَفَرَءَيْتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِى تُورُونَ

Transliteration afara-aytumu l-nāra allatī tūrūna

Hausa Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?

Verse 72

ءَأَنتُمْ أَنشَأْتُمْ شَجَرَتَهَآ أَمْ نَحْنُ ٱلْمُنشِـُٔونَ

Transliteration a-antum anshatum shajaratahā am naḥnu l-munshiūna

Hausa Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?

Verse 73

نَحْنُ جَعَلْنَـٰهَا تَذْكِرَةً وَمَتَـٰعًا لِّلْمُقْوِينَ

Transliteration naḥnu jaʿalnāhā tadhkiratan wamatāʿan lil'muq'wīna

Hausa Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.

Verse 74

فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration fasabbiḥ bi-is'mi rabbika l-ʿaẓīmi

Hausa Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.

Verse 75

۞ فَلَآ أُقْسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ

Transliteration falā uq'simu bimawāqiʿi l-nujūmi

Hausa To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.

Verse 76

وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٌ لَّوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌ

Transliteration wa-innahu laqasamun law taʿlamūna ʿaẓīmun

Hausa Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.

Verse 77

إِنَّهُۥ لَقُرْءَانٌ كَرِيمٌ

Transliteration innahu laqur'ānun karīmun

Hausa Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.

Verse 78

فِى كِتَـٰبٍ مَّكْنُونٍ

Transliteration fī kitābin maknūnin

Hausa A cikin wani littafi tsararre.

Verse 79

لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلْمُطَهَّرُونَ

Transliteration lā yamassuhu illā l-muṭaharūna

Hausa Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.

Verse 80

تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration tanzīlun min rabbi l-ʿālamīna

Hausa Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.

Verse 81

أَفَبِهَـٰذَا ٱلْحَدِيثِ أَنتُم مُّدْهِنُونَ

Transliteration afabihādhā l-ḥadīthi antum mud'hinūna

Hausa Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?

Verse 82

وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَ

Transliteration watajʿalūna riz'qakum annakum tukadhibūna

Hausa Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?

Verse 83

فَلَوْلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلْحُلْقُومَ

Transliteration falawlā idhā balaghati l-ḥul'qūma

Hausa To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).

Verse 84

وَأَنتُمْ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَ

Transliteration wa-antum ḥīna-idhin tanẓurūna

Hausa Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.

Verse 85

وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنكُمْ وَلَـٰكِن لَّا تُبْصِرُونَ

Transliteration wanaḥnu aqrabu ilayhi minkum walākin lā tub'ṣirūna

Hausa Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.

Verse 86

فَلَوْلَآ إِن كُنتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَ

Transliteration falawlā in kuntum ghayra madīnīna

Hausa To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?

Verse 87

تَرْجِعُونَهَآ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ

Transliteration tarjiʿūnahā in kuntum ṣādiqīna

Hausa Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.

Verse 88

فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ

Transliteration fa-ammā in kāna mina l-muqarabīna

Hausa To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,

Verse 89

فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ

Transliteration farawḥun warayḥānun wajannatu naʿīmin

Hausa Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.

Verse 90

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنْ أَصْحَـٰبِ ٱلْيَمِينِ

Transliteration wa-ammā in kāna min aṣḥābi l-yamīni

Hausa Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,

Verse 91

فَسَلَـٰمٌ لَّكَ مِنْ أَصْحَـٰبِ ٱلْيَمِينِ

Transliteration fasalāmun laka min aṣḥābi l-yamīni

Hausa Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.

Verse 92

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلْمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ

Transliteration wa-ammā in kāna mina l-mukadhibīna l-ḍālīna

Hausa Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,

Verse 93

فَنُزُلٌ مِّنْ حَمِيمٍ

Transliteration fanuzulun min ḥamīmin

Hausa Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.

Verse 94

وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍ

Transliteration wataṣliyatu jaḥīmin

Hausa Da ƙõnuwa da Jahĩm,

Verse 95

إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلْيَقِينِ

Transliteration inna hādhā lahuwa ḥaqqu l-yaqīni

Hausa Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.

Verse 96

فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration fasabbiḥ bi-is'mi rabbika l-ʿaẓīmi

Hausa Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.

Read Surah Al-Waqi'ah in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.