MyDugsiStart learning

Surah Ash-Shu'ara in Hausa: translation and audio

Surah 26 · الشعراء · The Poets · 227 verses

Surah Ash-Shu'ara verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Ash-Shu'ara word by word in English.

Verse 1

طسٓمٓ

Transliteration tta-seen-meem

Hausa T. S̃. M̃.

Verse 2

تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ ٱلْمُبِينِ

Transliteration til'ka āyātu l-kitābi l-mubīni

Hausa Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.

Verse 3

لَعَلَّكَ بَـٰخِعٌ نَّفْسَكَ أَلَّا يَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ

Transliteration laʿallaka bākhiʿun nafsaka allā yakūnū mu'minīna

Hausa Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba!

Verse 4

إِن نَّشَأْ نُنَزِّلْ عَلَيْهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةً فَظَلَّتْ أَعْنَـٰقُهُمْ لَهَا خَـٰضِعِينَ

Transliteration in nasha nunazzil ʿalayhim mina l-samāi āyatan faẓallat aʿnāquhum lahā khāḍiʿīna

Hausa Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.

Verse 5

وَمَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّنَ ٱلرَّحْمَـٰنِ مُحْدَثٍ إِلَّا كَانُوا۟ عَنْهُ مُعْرِضِينَ

Transliteration wamā yatīhim min dhik'rin mina l-raḥmāni muḥ'dathin illā kānū ʿanhu muʿ'riḍīna

Hausa Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.

Verse 6

فَقَدْ كَذَّبُوا۟ فَسَيَأْتِيهِمْ أَنۢبَـٰٓؤُا۟ مَا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ

Transliteration faqad kadhabū fasayatīhim anbāu mā kānū bihi yastahziūna

Hausa To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.

Verse 7

أَوَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَى ٱلْأَرْضِ كَمْ أَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ

Transliteration awalam yaraw ilā l-arḍi kam anbatnā fīhā min kulli zawjin karīmin

Hausa Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?

Verse 8

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ

Transliteration inna fī dhālika laāyatan wamā kāna aktharuhum mu'minīna

Hausa Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.

Verse 9

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration wa-inna rabbaka lahuwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.

Verse 10

وَإِذْ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئْتِ ٱلْقَوْمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Transliteration wa-idh nādā rabbuka mūsā ani i'ti l-qawma l-ẓālimīna

Hausa Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.

Verse 11

قَوْمَ فِرْعَوْنَ ۚ أَلَا يَتَّقُونَ

Transliteration qawma fir'ʿawna alā yattaqūna

Hausa "Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"

Verse 12

قَالَ رَبِّ إِنِّىٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ

Transliteration qāla rabbi innī akhāfu an yukadhibūni

Hausa Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.

Verse 13

وَيَضِيقُ صَدْرِى وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِى فَأَرْسِلْ إِلَىٰ هَـٰرُونَ

Transliteration wayaḍīqu ṣadrī walā yanṭaliqu lisānī fa-arsil ilā hārūna

Hausa "Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.

Verse 14

وَلَهُمْ عَلَىَّ ذَنۢبٌ فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ

Transliteration walahum ʿalayya dhanbun fa-akhāfu an yaqtulūni

Hausa "Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."

Verse 15

قَالَ كَلَّا ۖ فَٱذْهَبَا بِـَٔايَـٰتِنَآ ۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسْتَمِعُونَ

Transliteration qāla kallā fa-idh'habā biāyātinā innā maʿakum mus'tamiʿūna

Hausa Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."

Verse 16

فَأْتِيَا فِرْعَوْنَ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولُ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration fatiyā fir'ʿawna faqūlā innā rasūlu rabbi l-ʿālamīna

Hausa "Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne."

Verse 17

أَنْ أَرْسِلْ مَعَنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ

Transliteration an arsil maʿanā banī is'rāīla

Hausa "Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."

Verse 18

قَالَ أَلَمْ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدًا وَلَبِثْتَ فِينَا مِنْ عُمُرِكَ سِنِينَ

Transliteration qāla alam nurabbika fīnā walīdan walabith'ta fīnā min ʿumurika sinīna

Hausa Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"

Verse 19

وَفَعَلْتَ فَعْلَتَكَ ٱلَّتِى فَعَلْتَ وَأَنتَ مِنَ ٱلْكَـٰفِرِينَ

Transliteration wafaʿalta faʿlataka allatī faʿalta wa-anta mina l-kāfirīna

Hausa "Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"

Verse 20

قَالَ فَعَلْتُهَآ إِذًا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ

Transliteration qāla faʿaltuhā idhan wa-anā mina l-ḍālīna

Hausa Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi."

Verse 21

فَفَرَرْتُ مِنكُمْ لَمَّا خِفْتُكُمْ فَوَهَبَ لِى رَبِّى حُكْمًا وَجَعَلَنِى مِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration fafarartu minkum lammā khif'tukum fawahaba lī rabbī ḥuk'man wajaʿalanī mina l-mur'salīna

Hausa "Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."

Verse 22

وَتِلْكَ نِعْمَةٌ تَمُنُّهَا عَلَىَّ أَنْ عَبَّدتَّ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ

Transliteration watil'ka niʿ'matun tamunnuhā ʿalayya an ʿabbadtta banī is'rāīla

Hausa "Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."

Verse 23

قَالَ فِرْعَوْنُ وَمَا رَبُّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration qāla fir'ʿawnu wamā rabbu l-ʿālamīna

Hausa Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"

Verse 24

قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَآ ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ

Transliteration qāla rabbu l-samāwāti wal-arḍi wamā baynahumā in kuntum mūqinīna

Hausa Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni."

Verse 25

قَالَ لِمَنْ حَوْلَهُۥٓ أَلَا تَسْتَمِعُونَ

Transliteration qāla liman ḥawlahu alā tastamiʿūna

Hausa Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"

Verse 26

قَالَ رَبُّكُمْ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration qāla rabbukum warabbu ābāikumu l-awalīna

Hausa Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."

Verse 27

قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ ٱلَّذِىٓ أُرْسِلَ إِلَيْكُمْ لَمَجْنُونٌ

Transliteration qāla inna rasūlakumu alladhī ur'sila ilaykum lamajnūnun

Hausa Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."

Verse 28

قَالَ رَبُّ ٱلْمَشْرِقِ وَٱلْمَغْرِبِ وَمَا بَيْنَهُمَآ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْقِلُونَ

Transliteration qāla rabbu l-mashriqi wal-maghribi wamā baynahumā in kuntum taʿqilūna

Hausa Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta."

Verse 29

قَالَ لَئِنِ ٱتَّخَذْتَ إِلَـٰهًا غَيْرِى لَأَجْعَلَنَّكَ مِنَ ٱلْمَسْجُونِينَ

Transliteration qāla la-ini ittakhadhta ilāhan ghayrī la-ajʿalannaka mina l-masjūnīna

Hausa Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru."

Verse 30

قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكَ بِشَىْءٍ مُّبِينٍ

Transliteration qāla awalaw ji'tuka bishayin mubīnin

Hausa Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"

Verse 31

قَالَ فَأْتِ بِهِۦٓ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Transliteration qāla fati bihi in kunta mina l-ṣādiqīna

Hausa Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya."

Verse 32

فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِىَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ

Transliteration fa-alqā ʿaṣāhu fa-idhā hiya thuʿ'bānun mubīnun

Hausa Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.

Verse 33

وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِىَ بَيْضَآءُ لِلنَّـٰظِرِينَ

Transliteration wanazaʿa yadahu fa-idhā hiya bayḍāu lilnnāẓirīna

Hausa Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.

Verse 34

قَالَ لِلْمَلَإِ حَوْلَهُۥٓ إِنَّ هَـٰذَا لَسَـٰحِرٌ عَلِيمٌ

Transliteration qāla lil'mala-i ḥawlahu inna hādhā lasāḥirun ʿalīmun

Hausa (Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi!

Verse 35

يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُم بِسِحْرِهِۦ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ

Transliteration yurīdu an yukh'rijakum min arḍikum bisiḥ'rihi famādhā tamurūna

Hausa "Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?"

Verse 36

قَالُوٓا۟ أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَٱبْعَثْ فِى ٱلْمَدَآئِنِ حَـٰشِرِينَ

Transliteration qālū arjih wa-akhāhu wa-ib'ʿath fī l-madāini ḥāshirīna

Hausa Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne."

Verse 37

يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٍ

Transliteration yatūka bikulli saḥḥārin ʿalīmin

Hausa "Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani."

Verse 38

فَجُمِعَ ٱلسَّحَرَةُ لِمِيقَـٰتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ

Transliteration fajumiʿa l-saḥaratu limīqāti yawmin maʿlūmin

Hausa Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.

Verse 39

وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلْ أَنتُم مُّجْتَمِعُونَ

Transliteration waqīla lilnnāsi hal antum muj'tamiʿūna

Hausa Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne?

Verse 40

لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ ٱلسَّحَرَةَ إِن كَانُوا۟ هُمُ ٱلْغَـٰلِبِينَ

Transliteration laʿallanā nattabiʿu l-saḥarata in kānū humu l-ghālibīna

Hausa "Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya."

Verse 41

فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالُوا۟ لِفِرْعَوْنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن كُنَّا نَحْنُ ٱلْغَـٰلِبِينَ

Transliteration falammā jāa l-saḥaratu qālū lifir'ʿawna a-inna lanā la-ajran in kunnā naḥnu l-ghālibīna

Hausa To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?"

Verse 42

قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ إِذًا لَّمِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ

Transliteration qāla naʿam wa-innakum idhan lamina l-muqarabīna

Hausa Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai."

Verse 43

قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلْقُوا۟ مَآ أَنتُم مُّلْقُونَ

Transliteration qāla lahum mūsā alqū mā antum mul'qūna

Hausa Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa."

Verse 44

فَأَلْقَوْا۟ حِبَالَهُمْ وَعِصِيَّهُمْ وَقَالُوا۟ بِعِزَّةِ فِرْعَوْنَ إِنَّا لَنَحْنُ ٱلْغَـٰلِبُونَ

Transliteration fa-alqaw ḥibālahum waʿiṣiyyahum waqālū biʿizzati fir'ʿawna innā lanaḥnu l-ghālibūna

Hausa Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya."

Verse 45

فَأَلْقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِىَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ

Transliteration fa-alqā mūsā ʿaṣāhu fa-idhā hiya talqafu mā yafikūna

Hausa Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.

Verse 46

فَأُلْقِىَ ٱلسَّحَرَةُ سَـٰجِدِينَ

Transliteration fa-ul'qiya l-saḥaratu sājidīna

Hausa Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.

Verse 47

قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration qālū āmannā birabbi l-ʿālamīna

Hausa Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta."

Verse 48

رَبِّ مُوسَىٰ وَهَـٰرُونَ

Transliteration rabbi mūsā wahārūna

Hausa "Ubangijin Mũsa da Hãrũna."

Verse 49

قَالَ ءَامَنتُمْ لَهُۥ قَبْلَ أَنْ ءَاذَنَ لَكُمْ ۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِى عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحْرَ فَلَسَوْفَ تَعْلَمُونَ ۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَـٰفٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ

Transliteration qāla āmantum lahu qabla an ādhana lakum innahu lakabīrukumu alladhī ʿallamakumu l-siḥ'ra falasawfa taʿlamūna la-uqaṭṭiʿanna aydiyakum wa-arjulakum min khilāfin wala-uṣallibannakum ajmaʿīna

Hausa Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya."

Verse 50

قَالُوا۟ لَا ضَيْرَ ۖ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ

Transliteration qālū lā ḍayra innā ilā rabbinā munqalibūna

Hausa Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu."

Verse 51

إِنَّا نَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَـٰيَـٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration innā naṭmaʿu an yaghfira lanā rabbunā khaṭāyānā an kunnā awwala l-mu'minīna

Hausa "Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni."

Verse 52

۞ وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنْ أَسْرِ بِعِبَادِىٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ

Transliteration wa-awḥaynā ilā mūsā an asri biʿibādī innakum muttabaʿūna

Hausa Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã ne.

Verse 53

فَأَرْسَلَ فِرْعَوْنُ فِى ٱلْمَدَآئِنِ حَـٰشِرِينَ

Transliteration fa-arsala fir'ʿawnu fī l-madāini ḥāshirīna

Hausa Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.

Verse 54

إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَشِرْذِمَةٌ قَلِيلُونَ

Transliteration inna hāulāi lashir'dhimatun qalīlūna

Hausa "Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan."

Verse 55

وَإِنَّهُمْ لَنَا لَغَآئِظُونَ

Transliteration wa-innahum lanā laghāiẓūna

Hausa "Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne."

Verse 56

وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَـٰذِرُونَ

Transliteration wa-innā lajamīʿun ḥādhirūna

Hausa "Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne."

Verse 57

فَأَخْرَجْنَـٰهُم مِّن جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ

Transliteration fa-akhrajnāhum min jannātin waʿuyūnin

Hausa Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.

Verse 58

وَكُنُوزٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ

Transliteration wakunūzin wamaqāmin karīmin

Hausa Da taskõki da mazauni mai kyau.

Verse 59

كَذَٰلِكَ وَأَوْرَثْنَـٰهَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ

Transliteration kadhālika wa-awrathnāhā banī is'rāīla

Hausa Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.

Verse 60

فَأَتْبَعُوهُم مُّشْرِقِينَ

Transliteration fa-atbaʿūhum mush'riqīna

Hausa Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.

Verse 61

فَلَمَّا تَرَٰٓءَا ٱلْجَمْعَانِ قَالَ أَصْحَـٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدْرَكُونَ

Transliteration falammā tarāā l-jamʿāni qāla aṣḥābu mūsā innā lamud'rakūna

Hausa Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne."

Verse 62

قَالَ كَلَّآ ۖ إِنَّ مَعِىَ رَبِّى سَيَهْدِينِ

Transliteration qāla kallā inna maʿiya rabbī sayahdīni

Hausa Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."

Verse 63

فَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضْرِب بِّعَصَاكَ ٱلْبَحْرَ ۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرْقٍ كَٱلطَّوْدِ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration fa-awḥaynā ilā mūsā ani iḍ'rib biʿaṣāka l-baḥra fa-infalaqa fakāna kullu fir'qin kal-ṭawdi l-ʿaẓīmi

Hausa Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.

Verse 64

وَأَزْلَفْنَا ثَمَّ ٱلْـَٔاخَرِينَ

Transliteration wa-azlafnā thamma l-ākharīna

Hausa Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.

Verse 65

وَأَنجَيْنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجْمَعِينَ

Transliteration wa-anjaynā mūsā waman maʿahu ajmaʿīna

Hausa Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.

Verse 66

ثُمَّ أَغْرَقْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ

Transliteration thumma aghraqnā l-ākharīna

Hausa Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.

Verse 67

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ

Transliteration inna fī dhālika laāyatan wamā kāna aktharuhum mu'minīna

Hausa Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

Verse 68

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration wa-inna rabbaka lahuwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.

Verse 69

وَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ إِبْرَٰهِيمَ

Transliteration wa-ut'lu ʿalayhim naba-a ib'rāhīma

Hausa Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.

Verse 70

إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦ مَا تَعْبُدُونَ

Transliteration idh qāla li-abīhi waqawmihi mā taʿbudūna

Hausa A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?"

Verse 71

قَالُوا۟ نَعْبُدُ أَصْنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَـٰكِفِينَ

Transliteration qālū naʿbudu aṣnāman fanaẓallu lahā ʿākifīna

Hausa Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su."

Verse 72

قَالَ هَلْ يَسْمَعُونَكُمْ إِذْ تَدْعُونَ

Transliteration qāla hal yasmaʿūnakum idh tadʿūna

Hausa Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?"

Verse 73

أَوْ يَنفَعُونَكُمْ أَوْ يَضُرُّونَ

Transliteration aw yanfaʿūnakum aw yaḍurrūna

Hausa "Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?"

Verse 74

قَالُوا۟ بَلْ وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا كَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ

Transliteration qālū bal wajadnā ābāanā kadhālika yafʿalūna

Hausa Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa."

Verse 75

قَالَ أَفَرَءَيْتُم مَّا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ

Transliteration qāla afara-aytum mā kuntum taʿbudūna

Hausa Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?"

Verse 76

أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُمُ ٱلْأَقْدَمُونَ

Transliteration antum waābāukumu l-aqdamūna

Hausa "Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?"

Verse 77

فَإِنَّهُمْ عَدُوٌّ لِّىٓ إِلَّا رَبَّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration fa-innahum ʿaduwwun lī illā rabba l-ʿālamīna

Hausa "To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu."

Verse 78

ٱلَّذِى خَلَقَنِى فَهُوَ يَهْدِينِ

Transliteration alladhī khalaqanī fahuwa yahdīni

Hausa "Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni."

Verse 79

وَٱلَّذِى هُوَ يُطْعِمُنِى وَيَسْقِينِ

Transliteration wa-alladhī huwa yuṭ'ʿimunī wayasqīni

Hausa "Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni."

Verse 80

وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ

Transliteration wa-idhā mariḍ'tu fahuwa yashfīni

Hausa "Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni."

Verse 81

وَٱلَّذِى يُمِيتُنِى ثُمَّ يُحْيِينِ

Transliteration wa-alladhī yumītunī thumma yuḥ'yīni

Hausa "Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni."

Verse 82

وَٱلَّذِىٓ أَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لِى خَطِيٓـَٔتِى يَوْمَ ٱلدِّينِ

Transliteration wa-alladhī aṭmaʿu an yaghfira lī khaṭīatī yawma l-dīni

Hausa "Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako."

Verse 83

رَبِّ هَبْ لِى حُكْمًا وَأَلْحِقْنِى بِٱلصَّـٰلِحِينَ

Transliteration rabbi hab lī ḥuk'man wa-alḥiq'nī bil-ṣāliḥīna

Hausa "Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."

Verse 84

وَٱجْعَل لِّى لِسَانَ صِدْقٍ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ

Transliteration wa-ij'ʿal lī lisāna ṣid'qin fī l-ākhirīna

Hausa "Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya a cikin mutãnen ƙarshe."

Verse 85

وَٱجْعَلْنِى مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ ٱلنَّعِيمِ

Transliteration wa-ij'ʿalnī min warathati jannati l-naʿīmi

Hausa "Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima."

Verse 86

وَٱغْفِرْ لِأَبِىٓ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ

Transliteration wa-igh'fir li-abī innahu kāna mina l-ḍālīna

Hausa "Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu."

Verse 87

وَلَا تُخْزِنِى يَوْمَ يُبْعَثُونَ

Transliteration walā tukh'zinī yawma yub'ʿathūna

Hausa "Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su."

Verse 88

يَوْمَ لَا يَنفَعُ مَالٌ وَلَا بَنُونَ

Transliteration yawma lā yanfaʿu mālun walā banūna

Hausa "A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi."

Verse 89

إِلَّا مَنْ أَتَى ٱللَّهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ

Transliteration illā man atā l-laha biqalbin salīmin

Hausa "Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."

Verse 90

وَأُزْلِفَتِ ٱلْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ

Transliteration wa-uz'lifati l-janatu lil'muttaqīna

Hausa Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.

Verse 91

وَبُرِّزَتِ ٱلْجَحِيمُ لِلْغَاوِينَ

Transliteration waburrizati l-jaḥīmu lil'ghāwīna

Hausa Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.

Verse 92

وَقِيلَ لَهُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ

Transliteration waqīla lahum ayna mā kuntum taʿbudūna

Hausa Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?"

Verse 93

مِن دُونِ ٱللَّهِ هَلْ يَنصُرُونَكُمْ أَوْ يَنتَصِرُونَ

Transliteration min dūni l-lahi hal yanṣurūnakum aw yantaṣirūna

Hausa "Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?"

Verse 94

فَكُبْكِبُوا۟ فِيهَا هُمْ وَٱلْغَاوُۥنَ

Transliteration fakub'kibū fīhā hum wal-ghāwūna

Hausa Sai aka kikkife su a cikinta, su da halakakkun.

Verse 95

وَجُنُودُ إِبْلِيسَ أَجْمَعُونَ

Transliteration wajunūdu ib'līsa ajmaʿūna

Hausa Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.

Verse 96

قَالُوا۟ وَهُمْ فِيهَا يَخْتَصِمُونَ

Transliteration qālū wahum fīhā yakhtaṣimūna

Hausa Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,

Verse 97

تَٱللَّهِ إِن كُنَّا لَفِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ

Transliteration tal-lahi in kunnā lafī ḍalālin mubīnin

Hausa "Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna."

Verse 98

إِذْ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration idh nusawwīkum birabbi l-ʿālamīna

Hausa "A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu.

Verse 99

وَمَآ أَضَلَّنَآ إِلَّا ٱلْمُجْرِمُونَ

Transliteration wamā aḍallanā illā l-muj'rimūna

Hausa "Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi."

Verse 100

فَمَا لَنَا مِن شَـٰفِعِينَ

Transliteration famā lanā min shāfiʿīna

Hausa "Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta."

Verse 101

وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٍ

Transliteration walā ṣadīqin ḥamīmin

Hausa "Kuma bã mu da abõki, masõyi."

Verse 102

فَلَوْ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration falaw anna lanā karratan fanakūna mina l-mu'minīna

Hausa "Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!"

Verse 103

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ

Transliteration inna fī dhālika laāyatan wamā kāna aktharuhum mu'minīna

Hausa Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.

Verse 104

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration wa-inna rabbaka lahuwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Verse 105

كَذَّبَتْ قَوْمُ نُوحٍ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration kadhabat qawmu nūḥin l-mur'salīna

Hausa Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.

Verse 106

إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ

Transliteration idh qāla lahum akhūhum nūḥun alā tattaqūna

Hausa A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba?"

Verse 107

إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ

Transliteration innī lakum rasūlun amīnun

Hausa "Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce."

Verse 108

فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

Transliteration fa-ittaqū l-laha wa-aṭīʿūni

Hausa "To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

Verse 109

وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration wamā asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illā ʿalā rabbi l-ʿālamīna

Hausa "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."

Verse 110

فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

Transliteration fa-ittaqū l-laha wa-aṭīʿūni

Hausa "Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

Verse 111

۞ قَالُوٓا۟ أَنُؤْمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلْأَرْذَلُونَ

Transliteration qālū anu'minu laka wa-ittabaʿaka l-ardhalūna

Hausa Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?"

Verse 112

قَالَ وَمَا عِلْمِى بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Transliteration qāla wamā ʿil'mī bimā kānū yaʿmalūna

Hausa Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."

Verse 113

إِنْ حِسَابُهُمْ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّى ۖ لَوْ تَشْعُرُونَ

Transliteration in ḥisābuhum illā ʿalā rabbī law tashʿurūna

Hausa "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."

Verse 114

وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration wamā anā biṭāridi l-mu'minīna

Hausa "Ban zama mai kõre mũminai ba."

Verse 115

إِنْ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ

Transliteration in anā illā nadhīrun mubīnun

Hausa "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."

Verse 116

قَالُوا۟ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَـٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمَرْجُومِينَ

Transliteration qālū la-in lam tantahi yānūḥu latakūnanna mina l-marjūmīna

Hausa Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"

Verse 117

قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوْمِى كَذَّبُونِ

Transliteration qāla rabbi inna qawmī kadhabūni

Hausa Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."

Verse 118

فَٱفْتَحْ بَيْنِى وَبَيْنَهُمْ فَتْحًا وَنَجِّنِى وَمَن مَّعِىَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration fa-if'taḥ baynī wabaynahum fatḥan wanajjinī waman maʿiya mina l-mu'minīna

Hausa "Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai."

Verse 119

فَأَنجَيْنَـٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِى ٱلْفُلْكِ ٱلْمَشْحُونِ

Transliteration fa-anjaynāhu waman maʿahu fī l-ful'ki l-mashḥūni

Hausa Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.

Verse 120

ثُمَّ أَغْرَقْنَا بَعْدُ ٱلْبَاقِينَ

Transliteration thumma aghraqnā baʿdu l-bāqīna

Hausa Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.

Verse 121

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ

Transliteration inna fī dhālika laāyatan wamā kāna aktharuhum mu'minīna

Hausa Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

Verse 122

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration wa-inna rabbaka lahuwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.

Verse 123

كَذَّبَتْ عَادٌ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration kadhabat ʿādun l-mur'salīna

Hausa Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni.

Verse 124

إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ

Transliteration idh qāla lahum akhūhum hūdun alā tattaqūna

Hausa A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"

Verse 125

إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ

Transliteration innī lakum rasūlun amīnun

Hausa "Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce."

Verse 126

فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

Transliteration fa-ittaqū l-laha wa-aṭīʿūni

Hausa "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

Verse 127

وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration wamā asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illā ʿalā rabbi l-ʿālamīna

Hausa "Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu."

Verse 128

أَتَبْنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةً تَعْبَثُونَ

Transliteration atabnūna bikulli rīʿin āyatan taʿbathūna

Hausa "Shin, kunã yin ginin sitadiyo a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?"

Verse 129

وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمْ تَخْلُدُونَ

Transliteration watattakhidhūna maṣāniʿa laʿallakum takhludūna

Hausa "Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?"

Verse 130

وَإِذَا بَطَشْتُم بَطَشْتُمْ جَبَّارِينَ

Transliteration wa-idhā baṭashtum baṭashtum jabbārīna

Hausa "Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa."

Verse 131

فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

Transliteration fa-ittaqū l-laha wa-aṭīʿūni

Hausa "To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

Verse 132

وَٱتَّقُوا۟ ٱلَّذِىٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعْلَمُونَ

Transliteration wa-ittaqū alladhī amaddakum bimā taʿlamūna

Hausa "Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani."

Verse 133

أَمَدَّكُم بِأَنْعَـٰمٍ وَبَنِينَ

Transliteration amaddakum bi-anʿāmin wabanīna

Hausa "Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya."

Verse 134

وَجَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ

Transliteration wajannātin waʿuyūnin

Hausa "Da gõnaki da marẽmari."

Verse 135

إِنِّىٓ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ

Transliteration innī akhāfu ʿalaykum ʿadhāba yawmin ʿaẓīmin

Hausa "Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma."

Verse 136

قَالُوا۟ سَوَآءٌ عَلَيْنَآ أَوَعَظْتَ أَمْ لَمْ تَكُن مِّنَ ٱلْوَٰعِظِينَ

Transliteration qālū sawāon ʿalaynā awaʿaẓta am lam takun mina l-wāʿiẓīna

Hausa Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba."

Verse 137

إِنْ هَـٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration in hādhā illā khuluqu l-awalīna

Hausa "Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen mutãnen farko."

Verse 138

وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ

Transliteration wamā naḥnu bimuʿadhabīna

Hausa "Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba."

Verse 139

فَكَذَّبُوهُ فَأَهْلَكْنَـٰهُمْ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ

Transliteration fakadhabūhu fa-ahlaknāhum inna fī dhālika laāyatan wamā kāna aktharuhum mu'minīna

Hausa Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

Verse 140

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration wa-inna rabbaka lahuwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Verse 141

كَذَّبَتْ ثَمُودُ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration kadhabat thamūdu l-mur'salīna

Hausa Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni.

Verse 142

إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ صَـٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ

Transliteration idh qāla lahum akhūhum ṣāliḥun alā tattaqūna

Hausa A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?"

Verse 143

إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ

Transliteration innī lakum rasūlun amīnun

Hausa "Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce."

Verse 144

فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

Transliteration fa-ittaqū l-laha wa-aṭīʿūni

Hausa "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.

Verse 145

وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration wamā asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illā ʿalā rabbi l-ʿālamīna

Hausa "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu."

Verse 146

أَتُتْرَكُونَ فِى مَا هَـٰهُنَآ ءَامِنِينَ

Transliteration atut'rakūna fī mā hāhunā āminīna

Hausa "Shin, anã barin ku a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?"

Verse 147

فِى جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ

Transliteration fī jannātin waʿuyūnin

Hausa "A cikin gõnaki da marẽmari."

Verse 148

وَزُرُوعٍ وَنَخْلٍ طَلْعُهَا هَضِيمٌ

Transliteration wazurūʿin wanakhlin ṭalʿuhā haḍīmun

Hausa "Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi mãsu narkẽwa a ciki?"

Verse 149

وَتَنْحِتُونَ مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا فَـٰرِهِينَ

Transliteration watanḥitūna mina l-jibāli buyūtan fārihīna

Hausa "Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?"

Verse 150

فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

Transliteration fa-ittaqū l-laha wa-aṭīʿūni

Hausa "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

Verse 151

وَلَا تُطِيعُوٓا۟ أَمْرَ ٱلْمُسْرِفِينَ

Transliteration walā tuṭīʿū amra l-mus'rifīna

Hausa "Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata."

Verse 152

ٱلَّذِينَ يُفْسِدُونَ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا يُصْلِحُونَ

Transliteration alladhīna yuf'sidūna fī l-arḍi walā yuṣ'liḥūna

Hausa "Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa."

Verse 153

قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلْمُسَحَّرِينَ

Transliteration qālū innamā anta mina l-musaḥarīna

Hausa Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake."

Verse 154

مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا فَأْتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Transliteration mā anta illā basharun mith'lunā fati biāyatin in kunta mina l-ṣādiqīna

Hausa "Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya."

Verse 155

قَالَ هَـٰذِهِۦ نَاقَةٌ لَّهَا شِرْبٌ وَلَكُمْ شِرْبُ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ

Transliteration qāla hādhihi nāqatun lahā shir'bun walakum shir'bu yawmin maʿlūmin

Hausa Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan yini, kuma kunã da shan yini sasanne."

Verse 156

وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابُ يَوْمٍ عَظِيمٍ

Transliteration walā tamassūhā bisūin fayakhudhakum ʿadhābu yawmin ʿaẓīmin

Hausa "Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku."

Verse 157

فَعَقَرُوهَا فَأَصْبَحُوا۟ نَـٰدِمِينَ

Transliteration faʿaqarūhā fa-aṣbaḥū nādimīna

Hausa Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma.

Verse 158

فَأَخَذَهُمُ ٱلْعَذَابُ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ

Transliteration fa-akhadhahumu l-ʿadhābu inna fī dhālika laāyatan wamā kāna aktharuhum mu'minīna

Hausa Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

Verse 159

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration wa-inna rabbaka lahuwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai.

Verse 160

كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration kadhabat qawmu lūṭin l-mur'salīna

Hausa Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni.

Verse 161

إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ

Transliteration idh qāla lahum akhūhum lūṭun alā tattaqūna

Hausa A lõkacin da ɗan'uwansu, Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"

Verse 162

إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ

Transliteration innī lakum rasūlun amīnun

Hausa "Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce."

Verse 163

فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

Transliteration fa-ittaqū l-laha wa-aṭīʿūni

Hausa "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

Verse 164

وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration wamā asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illā ʿalā rabbi l-ʿālamīna

Hausa "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."

Verse 165

أَتَأْتُونَ ٱلذُّكْرَانَ مِنَ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration atatūna l-dhuk'rāna mina l-ʿālamīna

Hausa "Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"

Verse 166

وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمْ رَبُّكُم مِّنْ أَزْوَٰجِكُم ۚ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ عَادُونَ

Transliteration watadharūna mā khalaqa lakum rabbukum min azwājikum bal antum qawmun ʿādūna

Hausa "Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"

Verse 167

قَالُوا۟ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَـٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُخْرَجِينَ

Transliteration qālū la-in lam tantahi yālūṭu latakūnanna mina l-mukh'rajīna

Hausa Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."

Verse 168

قَالَ إِنِّى لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلْقَالِينَ

Transliteration qāla innī liʿamalikum mina l-qālīna

Hausa Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."

Verse 169

رَبِّ نَجِّنِى وَأَهْلِى مِمَّا يَعْمَلُونَ

Transliteration rabbi najjinī wa-ahlī mimmā yaʿmalūna

Hausa "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."

Verse 170

فَنَجَّيْنَـٰهُ وَأَهْلَهُۥٓ أَجْمَعِينَ

Transliteration fanajjaynāhu wa-ahlahu ajmaʿīna

Hausa Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya.

Verse 171

إِلَّا عَجُوزًا فِى ٱلْغَـٰبِرِينَ

Transliteration illā ʿajūzan fī l-ghābirīna

Hausa Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa.

Verse 172

ثُمَّ دَمَّرْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ

Transliteration thumma dammarnā l-ākharīna

Hausa Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu.

Verse 173

وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا ۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلْمُنذَرِينَ

Transliteration wa-amṭarnā ʿalayhim maṭaran fasāa maṭaru l-mundharīna

Hausa Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.

Verse 174

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ

Transliteration inna fī dhālika laāyatan wamā kāna aktharuhum mu'minīna

Hausa Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba.

Verse 175

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration wa-inna rabbaka lahuwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Verse 176

كَذَّبَ أَصْحَـٰبُ لْـَٔيْكَةِ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration kadhaba aṣḥābu al'aykati l-mur'salīna

Hausa Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni.

Verse 177

إِذْ قَالَ لَهُمْ شُعَيْبٌ أَلَا تَتَّقُونَ

Transliteration idh qāla lahum shuʿaybun alā tattaqūna

Hausa A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"

Verse 178

إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ

Transliteration innī lakum rasūlun amīnun

Hausa "Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce."

Verse 179

فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

Transliteration fa-ittaqū l-laha wa-aṭīʿūni

Hausa "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã."

Verse 180

وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration wamā asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illā ʿalā rabbi l-ʿālamīna

Hausa "Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."

Verse 181

۞ أَوْفُوا۟ ٱلْكَيْلَ وَلَا تَكُونُوا۟ مِنَ ٱلْمُخْسِرِينَ

Transliteration awfū l-kayla walā takūnū mina l-mukh'sirīna

Hausa "Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)."

Verse 182

وَزِنُوا۟ بِٱلْقِسْطَاسِ ٱلْمُسْتَقِيمِ

Transliteration wazinū bil-qis'ṭāsi l-mus'taqīmi

Hausa "Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce."

Verse 183

وَلَا تَبْخَسُوا۟ ٱلنَّاسَ أَشْيَآءَهُمْ وَلَا تَعْثَوْا۟ فِى ٱلْأَرْضِ مُفْسِدِينَ

Transliteration walā tabkhasū l-nāsa ashyāahum walā taʿthaw fī l-arḍi muf'sidīna

Hausa "Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna."

Verse 184

وَٱتَّقُوا۟ ٱلَّذِى خَلَقَكُمْ وَٱلْجِبِلَّةَ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration wa-ittaqū alladhī khalaqakum wal-jibilata l-awalīna

Hausa "Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko."

Verse 185

قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلْمُسَحَّرِينَ

Transliteration qālū innamā anta mina l-musaḥarīna

Hausa Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne."

Verse 186

وَمَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا وَإِن نَّظُنُّكَ لَمِنَ ٱلْكَـٰذِبِينَ

Transliteration wamā anta illā basharun mith'lunā wa-in naẓunnuka lamina l-kādhibīna

Hausa "Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata."

Verse 187

فَأَسْقِطْ عَلَيْنَا كِسَفًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Transliteration fa-asqiṭ ʿalaynā kisafan mina l-samāi in kunta mina l-ṣādiqīna

Hausa "To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya."

Verse 188

قَالَ رَبِّىٓ أَعْلَمُ بِمَا تَعْمَلُونَ

Transliteration qāla rabbī aʿlamu bimā taʿmalūna

Hausa Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa."

Verse 189

فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمْ عَذَابُ يَوْمِ ٱلظُّلَّةِ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ

Transliteration fakadhabūhu fa-akhadhahum ʿadhābu yawmi l-ẓulati innahu kāna ʿadhāba yawmin ʿaẓīmin

Hausa Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.

Verse 190

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ

Transliteration inna fī dhālika laāyatan wamā kāna aktharuhum mu'minīna

Hausa Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

Verse 191

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration wa-inna rabbaka lahuwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Verse 192

وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration wa-innahu latanzīlu rabbi l-ʿālamīna

Hausa Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne.

Verse 193

نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلْأَمِينُ

Transliteration nazala bihi l-rūḥu l-amīnu

Hausa Rũhi amintacce ne ya sauka da shi.

Verse 194

عَلَىٰ قَلْبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلْمُنذِرِينَ

Transliteration ʿalā qalbika litakūna mina l-mundhirīna

Hausa A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi.

Verse 195

بِلِسَانٍ عَرَبِىٍّ مُّبِينٍ

Transliteration bilisānin ʿarabiyyin mubīnin

Hausa Da harshe na Larabci mai bayãni.

Verse 196

وَإِنَّهُۥ لَفِى زُبُرِ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration wa-innahu lafī zuburi l-awalīna

Hausa Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko.

Verse 197

أَوَلَمْ يَكُن لَّهُمْ ءَايَةً أَن يَعْلَمَهُۥ عُلَمَـٰٓؤُا۟ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ

Transliteration awalam yakun lahum āyatan an yaʿlamahu ʿulamāu banī is'rāīla

Hausa Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi?

Verse 198

وَلَوْ نَزَّلْنَـٰهُ عَلَىٰ بَعْضِ ٱلْأَعْجَمِينَ

Transliteration walaw nazzalnāhu ʿalā baʿḍi l-aʿjamīna

Hausa Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa,

Verse 199

فَقَرَأَهُۥ عَلَيْهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ مُؤْمِنِينَ

Transliteration faqara-ahu ʿalayhim mā kānū bihi mu'minīna

Hausa Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba.

Verse 200

كَذَٰلِكَ سَلَكْنَـٰهُ فِى قُلُوبِ ٱلْمُجْرِمِينَ

Transliteration kadhālika salaknāhu fī qulūbi l-muj'rimīna

Hausa Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.

Verse 201

لَا يُؤْمِنُونَ بِهِۦ حَتَّىٰ يَرَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ

Transliteration lā yu'minūna bihi ḥattā yarawū l-ʿadhāba l-alīma

Hausa Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi.

Verse 202

فَيَأْتِيَهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ

Transliteration fayatiyahum baghtatan wahum lā yashʿurūna

Hausa Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba.

Verse 203

فَيَقُولُوا۟ هَلْ نَحْنُ مُنظَرُونَ

Transliteration fayaqūlū hal naḥnu munẓarūna

Hausa Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?"

Verse 204

أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ

Transliteration afabiʿadhābinā yastaʿjilūna

Hausa Ashe, to, da azãbar Mu suke nẽman gaggãwa?

Verse 205

أَفَرَءَيْتَ إِن مَّتَّعْنَـٰهُمْ سِنِينَ

Transliteration afara-ayta in mattaʿnāhum sinīna

Hausa Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru,

Verse 206

ثُمَّ جَآءَهُم مَّا كَانُوا۟ يُوعَدُونَ

Transliteration thumma jāahum mā kānū yūʿadūna

Hausa Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu,

Verse 207

مَآ أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يُمَتَّعُونَ

Transliteration mā aghnā ʿanhum mā kānū yumattaʿūna

Hausa Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare su.

Verse 208

وَمَآ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ

Transliteration wamā ahlaknā min qaryatin illā lahā mundhirūna

Hausa Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi.

Verse 209

ذِكْرَىٰ وَمَا كُنَّا ظَـٰلِمِينَ

Transliteration dhik'rā wamā kunnā ẓālimīna

Hausa Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba.

Verse 210

وَمَا تَنَزَّلَتْ بِهِ ٱلشَّيَـٰطِينُ

Transliteration wamā tanazzalat bihi l-shayāṭīnu

Hausa Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba.

Verse 211

وَمَا يَنۢبَغِى لَهُمْ وَمَا يَسْتَطِيعُونَ

Transliteration wamā yanbaghī lahum wamā yastaṭīʿūna

Hausa Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa.

Verse 212

إِنَّهُمْ عَنِ ٱلسَّمْعِ لَمَعْزُولُونَ

Transliteration innahum ʿani l-samʿi lamaʿzūlūna

Hausa Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne.

Verse 213

فَلَا تَدْعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلْمُعَذَّبِينَ

Transliteration falā tadʿu maʿa l-lahi ilāhan ākhara fatakūna mina l-muʿadhabīna

Hausa Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba.

Verse 214

وَأَنذِرْ عَشِيرَتَكَ ٱلْأَقْرَبِينَ

Transliteration wa-andhir ʿashīrataka l-aqrabīna

Hausa Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci.

Verse 215

وَٱخْفِضْ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration wa-ikh'fiḍ janāḥaka limani ittabaʿaka mina l-mu'minīna

Hausa Kuma ka sassauta fikãfikanka ga wanda ya bĩ ka daga mũminai.

Verse 216

فَإِنْ عَصَوْكَ فَقُلْ إِنِّى بَرِىٓءٌ مِّمَّا تَعْمَلُونَ

Transliteration fa-in ʿaṣawka faqul innī barīon mimmā taʿmalūna

Hausa Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa."

Verse 217

وَتَوَكَّلْ عَلَى ٱلْعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ

Transliteration watawakkal ʿalā l-ʿazīzi l-raḥīmi

Hausa Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Verse 218

ٱلَّذِى يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ

Transliteration alladhī yarāka ḥīna taqūmu

Hausa Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye.

Verse 219

وَتَقَلُّبَكَ فِى ٱلسَّـٰجِدِينَ

Transliteration wataqallubaka fī l-sājidīna

Hausa Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada.

Verse 220

إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ

Transliteration innahu huwa l-samīʿu l-ʿalīmu

Hausa Lalle Shi, Shi ne Mai ji, Masani.

Verse 221

هَلْ أُنَبِّئُكُمْ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَـٰطِينُ

Transliteration hal unabbi-ukum ʿalā man tanazzalu l-shayāṭīnu

Hausa Shin, (kunã so) in gaya muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?

Verse 222

تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ

Transliteration tanazzalu ʿalā kulli affākin athīmin

Hausa Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi.

Verse 223

يُلْقُونَ ٱلسَّمْعَ وَأَكْثَرُهُمْ كَـٰذِبُونَ

Transliteration yul'qūna l-samʿa wa-aktharuhum kādhibūna

Hausa Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne.

Verse 224

وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلْغَاوُۥنَ

Transliteration wal-shuʿarāu yattabiʿuhumu l-ghāwūna

Hausa Kuma mawãƙa halakakku ne ke bin su.

Verse 225

أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِى كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ

Transliteration alam tara annahum fī kulli wādin yahīmūna

Hausa Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba?

Verse 226

وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ

Transliteration wa-annahum yaqūlūna mā lā yafʿalūna

Hausa Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa?

Verse 227

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَذَكَرُوا۟ ٱللَّهَ كَثِيرًا وَٱنتَصَرُوا۟ مِنۢ بَعْدِ مَا ظُلِمُوا۟ ۗ وَسَيَعْلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓا۟ أَىَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ

Transliteration illā alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti wadhakarū l-laha kathīran wa-intaṣarū min baʿdi mā ẓulimū wasayaʿlamu alladhīna ẓalamū ayya munqalabin yanqalibūna

Hausa Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa.

Read Surah Ash-Shu'ara in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.