MyDugsiStart learning

Surah Az-Zumar in Hausa: translation and audio

Surah 39 · الزمر · The Troops · 75 verses

Surah Az-Zumar verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Az-Zumar word by word in English.

Verse 1

تَنزِيلُ ٱلْكِتَـٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَكِيمِ

Transliteration tanzīlu l-kitābi mina l-lahi l-ʿazīzi l-ḥakīmi

Hausa Saukar da Littãfin daga Allah ne, Mabuwãyi, Mai hikima.

Verse 2

إِنَّآ أَنزَلْنَآ إِلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ بِٱلْحَقِّ فَٱعْبُدِ ٱللَّهَ مُخْلِصًا لَّهُ ٱلدِّينَ

Transliteration innā anzalnā ilayka l-kitāba bil-ḥaqi fa-uʿ'budi l-laha mukh'liṣan lahu l-dīna

Hausa Mun saukar da littafi a gareka da Gaskiya ka bautawa Allah kana mai tsarkake Addini a gare shi

Verse 3

أَلَا لِلَّهِ ٱلدِّينُ ٱلْخَالِصُ ۚ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُوا۟ مِن دُونِهِۦٓ أَوْلِيَآءَ مَا نَعْبُدُهُمْ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلْفَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ فِى مَا هُمْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى مَنْ هُوَ كَـٰذِبٌ كَفَّارٌ

Transliteration alā lillahi l-dīnu l-khāliṣu wa-alladhīna ittakhadhū min dūnihi awliyāa mā naʿbuduhum illā liyuqarribūnā ilā l-lahi zul'fā inna l-laha yaḥkumu baynahum fī mā hum fīhi yakhtalifūna inna l-laha lā yahdī man huwa kādhibun kaffārun

Hausa To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci.

Verse 4

لَّوْ أَرَادَ ٱللَّهُ أَن يَتَّخِذَ وَلَدًا لَّٱصْطَفَىٰ مِمَّا يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ ۚ سُبْحَـٰنَهُۥ ۖ هُوَ ٱللَّهُ ٱلْوَٰحِدُ ٱلْقَهَّارُ

Transliteration law arāda l-lahu an yattakhidha waladan la-iṣ'ṭafā mimmā yakhluqu mā yashāu sub'ḥānahu huwa l-lahu l-wāḥidu l-qahāru

Hausa Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.

Verse 5

خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ بِٱلْحَقِّ ۖ يُكَوِّرُ ٱلَّيْلَ عَلَى ٱلنَّهَارِ وَيُكَوِّرُ ٱلنَّهَارَ عَلَى ٱلَّيْلِ ۖ وَسَخَّرَ ٱلشَّمْسَ وَٱلْقَمَرَ ۖ كُلٌّ يَجْرِى لِأَجَلٍ مُّسَمًّى ۗ أَلَا هُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْغَفَّـٰرُ

Transliteration khalaqa l-samāwāti wal-arḍa bil-ḥaqi yukawwiru al-layla ʿalā l-nahāri wayukawwiru l-nahāra ʿalā al-layli wasakhara l-shamsa wal-qamara kullun yajrī li-ajalin musamman alā huwa l-ʿazīzu l-ghafāru

Hausa Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara.

Verse 6

خَلَقَكُم مِّن نَّفْسٍ وَٰحِدَةٍ ثُمَّ جَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ ٱلْأَنْعَـٰمِ ثَمَـٰنِيَةَ أَزْوَٰجٍ ۚ يَخْلُقُكُمْ فِى بُطُونِ أُمَّهَـٰتِكُمْ خَلْقًا مِّنۢ بَعْدِ خَلْقٍ فِى ظُلُمَـٰتٍ ثَلَـٰثٍ ۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمْ لَهُ ٱلْمُلْكُ ۖ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ فَأَنَّىٰ تُصْرَفُونَ

Transliteration khalaqakum min nafsin wāḥidatin thumma jaʿala min'hā zawjahā wa-anzala lakum mina l-anʿāmi thamāniyata azwājin yakhluqukum fī buṭūni ummahātikum khalqan min baʿdi khalqin fī ẓulumātin thalāthin dhālikumu l-lahu rabbukum lahu l-mul'ku lā ilāha illā huwa fa-annā tuṣ'rafūna

Hausa Yã halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma ya saukar muku daga dabbõbin gida nau'i takwas Yanã halitta ku a cikin cikunnan uwayenku, halitta a bãyan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shĩ ne Allah Ubangijin ku. Mulki a gare shi yake. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?

Verse 7

إِن تَكْفُرُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِىٌّ عَنكُمْ ۖ وَلَا يَرْضَىٰ لِعِبَادِهِ ٱلْكُفْرَ ۖ وَإِن تَشْكُرُوا۟ يَرْضَهُ لَكُمْ ۗ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ ۗ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرْجِعُكُمْ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ ۚ إِنَّهُۥ عَلِيمٌۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Transliteration in takfurū fa-inna l-laha ghaniyyun ʿankum walā yarḍā liʿibādihi l-kuf'ra wa-in tashkurū yarḍahu lakum walā taziru wāziratun wiz'ra ukh'rā thumma ilā rabbikum marjiʿukum fayunabbi-ukum bimā kuntum taʿmalūna innahu ʿalīmun bidhāti l-ṣudūri

Hausa Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da kãfirci ga bãyin Sa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar) a gare ku, kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma makõmarku zuwa ga Ubangijinku take, dõmin Ya bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. Lalle Shĩ, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata.

Verse 8

۞ وَإِذَا مَسَّ ٱلْإِنسَـٰنَ ضُرٌّ دَعَا رَبَّهُۥ مُنِيبًا إِلَيْهِ ثُمَّ إِذَا خَوَّلَهُۥ نِعْمَةً مِّنْهُ نَسِىَ مَا كَانَ يَدْعُوٓا۟ إِلَيْهِ مِن قَبْلُ وَجَعَلَ لِلَّهِ أَندَادًا لِّيُضِلَّ عَن سَبِيلِهِۦ ۚ قُلْ تَمَتَّعْ بِكُفْرِكَ قَلِيلًا ۖ إِنَّكَ مِنْ أَصْحَـٰبِ ٱلنَّارِ

Transliteration wa-idhā massa l-insāna ḍurrun daʿā rabbahu munīban ilayhi thumma idhā khawwalahu niʿ'matan min'hu nasiya mā kāna yadʿū ilayhi min qablu wajaʿala lillahi andādan liyuḍilla ʿan sabīlihi qul tamattaʿ bikuf'rika qalīlan innaka min aṣḥābi l-nāri

Hausa Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga 'yan wutã ne."

Verse 9

أَمَّنْ هُوَ قَـٰنِتٌ ءَانَآءَ ٱلَّيْلِ سَاجِدًا وَقَآئِمًا يَحْذَرُ ٱلْـَٔاخِرَةَ وَيَرْجُوا۟ رَحْمَةَ رَبِّهِۦ ۗ قُلْ هَلْ يَسْتَوِى ٱلَّذِينَ يَعْلَمُونَ وَٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ ۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُو۟لُوا۟ ٱلْأَلْبَـٰبِ

Transliteration amman huwa qānitun ānāa al-layli sājidan waqāiman yaḥdharu l-ākhirata wayarjū raḥmata rabbihi qul hal yastawī alladhīna yaʿlamūna wa-alladhīna lā yaʿlamūna innamā yatadhakkaru ulū l-albābi

Hausa Shin, wanda yake mai tawãli'u sã'õ'in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai da waninsa?) Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba?" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni.

Verse 10

قُلْ يَـٰعِبَادِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ رَبَّكُمْ ۚ لِلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ فِى هَـٰذِهِ ٱلدُّنْيَا حَسَنَةٌ ۗ وَأَرْضُ ٱللَّهِ وَٰسِعَةٌ ۗ إِنَّمَا يُوَفَّى ٱلصَّـٰبِرُونَ أَجْرَهُم بِغَيْرِ حِسَابٍ

Transliteration qul yāʿibādi alladhīna āmanū ittaqū rabbakum lilladhīna aḥsanū fī hādhihi l-dun'yā ḥasanatun wa-arḍu l-lahi wāsiʿatun innamā yuwaffā l-ṣābirūna ajrahum bighayri ḥisābin

Hausa Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩ Na waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai fãɗi ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani lissãfi ba.

Verse 11

قُلْ إِنِّىٓ أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ ٱللَّهَ مُخْلِصًا لَّهُ ٱلدِّينَ

Transliteration qul innī umir'tu an aʿbuda l-laha mukh'liṣan lahu l-dīna

Hausa Ka ce: "Lalle nĩ, an umurce ni da in bauta wa Allah, inã tsarkake addini a gare Shi.

Verse 12

وَأُمِرْتُ لِأَنْ أَكُونَ أَوَّلَ ٱلْمُسْلِمِينَ

Transliteration wa-umir'tu li-an akūna awwala l-mus'limīna

Hausa "Kuma an umurce ni da in kasance farkon mãsu miƙa wuya (ga umurnin Allah)."

Verse 13

قُلْ إِنِّىٓ أَخَافُ إِنْ عَصَيْتُ رَبِّى عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ

Transliteration qul innī akhāfu in ʿaṣaytu rabbī ʿadhāba yawmin ʿaẓīmin

Hausa Ka ce: "Lalle nĩ inã tsõro, idan na sãɓã wa Ubangijĩna, ga azãbar yini mai girma."

Verse 14

قُلِ ٱللَّهَ أَعْبُدُ مُخْلِصًا لَّهُۥ دِينِى

Transliteration quli l-laha aʿbudu mukh'liṣan lahu dīnī

Hausa Ka ce: "Allah nake bautã wa, inã mai tsarkake addinĩna a gare Shi.

Verse 15

فَٱعْبُدُوا۟ مَا شِئْتُم مِّن دُونِهِۦ ۗ قُلْ إِنَّ ٱلْخَـٰسِرِينَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ وَأَهْلِيهِمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۗ أَلَا ذَٰلِكَ هُوَ ٱلْخُسْرَانُ ٱلْمُبِينُ

Transliteration fa-uʿ'budū mā shi'tum min dūnihi qul inna l-khāsirīna alladhīna khasirū anfusahum wa-ahlīhim yawma l-qiyāmati alā dhālika huwa l-khus'rānu l-mubīnu

Hausa "To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa." Ka ce: "Lalle mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa, ita ce hasãra bayyananna."

Verse 16

لَهُم مِّن فَوْقِهِمْ ظُلَلٌ مِّنَ ٱلنَّارِ وَمِن تَحْتِهِمْ ظُلَلٌ ۚ ذَٰلِكَ يُخَوِّفُ ٱللَّهُ بِهِۦ عِبَادَهُۥ ۚ يَـٰعِبَادِ فَٱتَّقُونِ

Transliteration lahum min fawqihim ẓulalun mina l-nāri wamin taḥtihim ẓulalun dhālika yukhawwifu l-lahu bihi ʿibādahu yāʿibādi fa-ittaqūni

Hausa Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyin Sa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa.

Verse 17

وَٱلَّذِينَ ٱجْتَنَبُوا۟ ٱلطَّـٰغُوتَ أَن يَعْبُدُوهَا وَأَنَابُوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ لَهُمُ ٱلْبُشْرَىٰ ۚ فَبَشِّرْ عِبَادِ

Transliteration wa-alladhīna ij'tanabū l-ṭāghūta an yaʿbudūhā wa-anābū ilā l-lahi lahumu l-bush'rā fabashir ʿibādi

Hausa Kuma waɗanda suka nĩsanci Shaiɗannu ga bauta musu, kuma suka mai da al'amari ga Allah, sunã da bushãra. To, ka bãyar da bushãra ga bãyiNa.

Verse 18

ٱلَّذِينَ يَسْتَمِعُونَ ٱلْقَوْلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحْسَنَهُۥٓ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ هَدَىٰهُمُ ٱللَّهُ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمْ أُو۟لُوا۟ ٱلْأَلْبَـٰبِ

Transliteration alladhīna yastamiʿūna l-qawla fayattabiʿūna aḥsanahu ulāika alladhīna hadāhumu l-lahu wa-ulāika hum ulū l-albābi

Hausa Waɗanda ke sauraren magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali,

Verse 19

أَفَمَنْ حَقَّ عَلَيْهِ كَلِمَةُ ٱلْعَذَابِ أَفَأَنتَ تُنقِذُ مَن فِى ٱلنَّارِ

Transliteration afaman ḥaqqa ʿalayhi kalimatu l-ʿadhābi afa-anta tunqidhu man fī l-nāri

Hausa Shin fa, wanda kalmar azãba ta wajaba a kansa? Shin fa, kanã iya tsãmar da wanda ke a cikin wutã?

Verse 20

لَـٰكِنِ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوْا۟ رَبَّهُمْ لَهُمْ غُرَفٌ مِّن فَوْقِهَا غُرَفٌ مَّبْنِيَّةٌ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۖ وَعْدَ ٱللَّهِ ۖ لَا يُخْلِفُ ٱللَّهُ ٱلْمِيعَادَ

Transliteration lākini alladhīna ittaqaw rabbahum lahum ghurafun min fawqihā ghurafun mabniyyatun tajrī min taḥtihā l-anhāru waʿda l-lahi lā yukh'lifu l-lahu l-mīʿāda

Hausa Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah. Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa.

Verse 21

أَلَمْ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَسَلَكَهُۥ يَنَـٰبِيعَ فِى ٱلْأَرْضِ ثُمَّ يُخْرِجُ بِهِۦ زَرْعًا مُّخْتَلِفًا أَلْوَٰنُهُۥ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَىٰهُ مُصْفَرًّا ثُمَّ يَجْعَلُهُۥ حُطَـٰمًا ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَذِكْرَىٰ لِأُو۟لِى ٱلْأَلْبَـٰبِ

Transliteration alam tara anna l-laha anzala mina l-samāi māan fasalakahu yanābīʿa fī l-arḍi thumma yukh'riju bihi zarʿan mukh'talifan alwānuhu thumma yahīju fatarāhu muṣ'farran thumma yajʿaluhu ḥuṭāman inna fī dhālika ladhik'rā li-ulī l-albābi

Hausa Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna).

Verse 22

أَفَمَن شَرَحَ ٱللَّهُ صَدْرَهُۥ لِلْإِسْلَـٰمِ فَهُوَ عَلَىٰ نُورٍ مِّن رَّبِّهِۦ ۚ فَوَيْلٌ لِّلْقَـٰسِيَةِ قُلُوبُهُم مِّن ذِكْرِ ٱللَّهِ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ

Transliteration afaman sharaḥa l-lahu ṣadrahu lil'is'lāmi fahuwa ʿalā nūrin min rabbihi fawaylun lil'qāsiyati qulūbuhum min dhik'ri l-lahi ulāika fī ḍalālin mubīnin

Hausa Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa'an nan shi yanã a kan haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata bayyananna.

Verse 23

ٱللَّهُ نَزَّلَ أَحْسَنَ ٱلْحَدِيثِ كِتَـٰبًا مُّتَشَـٰبِهًا مَّثَانِىَ تَقْشَعِرُّ مِنْهُ جُلُودُ ٱلَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُمْ ثُمَّ تَلِينُ جُلُودُهُمْ وَقُلُوبُهُمْ إِلَىٰ ذِكْرِ ٱللَّهِ ۚ ذَٰلِكَ هُدَى ٱللَّهِ يَهْدِى بِهِۦ مَن يَشَآءُ ۚ وَمَن يُضْلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنْ هَادٍ

Transliteration al-lahu nazzala aḥsana l-ḥadīthi kitāban mutashābihan mathāniya taqshaʿirru min'hu julūdu alladhīna yakhshawna rabbahum thumma talīnu julūduhum waqulūbuhum ilā dhik'ri l-lahi dhālika hudā l-lahi yahdī bihi man yashāu waman yuḍ'lili l-lahu famā lahu min hādin

Hausa Allah Ya sassaukar da mafi kyaun lãbãri, Littãfi mai kama da jũna, wanda ake konkoma karãtunsa fãtun waɗanda ke tsõron Ubangijinsu, sunã tãƙura sabõda Shi, sa'an nan fãtunsu da zukãtansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa.

Verse 24

أَفَمَن يَتَّقِى بِوَجْهِهِۦ سُوٓءَ ٱلْعَذَابِ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ وَقِيلَ لِلظَّـٰلِمِينَ ذُوقُوا۟ مَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ

Transliteration afaman yattaqī biwajhihi sūa l-ʿadhābi yawma l-qiyāmati waqīla lilẓẓālimīna dhūqū mā kuntum taksibūna

Hausa Shin fa, wanda ke kãre mũguwar azãba da fuskarsa (yanã zama kamar waninsa) a Rãnar ƙiyãma? Kuma a ce wa azzãlumai, "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Verse 25

كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَأَتَىٰهُمُ ٱلْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لَا يَشْعُرُونَ

Transliteration kadhaba alladhīna min qablihim fa-atāhumu l-ʿadhābu min ḥaythu lā yashʿurūna

Hausa Waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata, sai azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba.

Verse 26

فَأَذَاقَهُمُ ٱللَّهُ ٱلْخِزْىَ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۖ وَلَعَذَابُ ٱلْـَٔاخِرَةِ أَكْبَرُ ۚ لَوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ

Transliteration fa-adhāqahumu l-lahu l-khiz'ya fī l-ḥayati l-dun'yā walaʿadhābu l-ākhirati akbaru law kānū yaʿlamūna

Hausa Sai Allah Ya ɗanɗana musu azãbar wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi girma, dã sun kasance sunã da sani.

Verse 27

وَلَقَدْ ضَرَبْنَا لِلنَّاسِ فِى هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٍ لَّعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ

Transliteration walaqad ḍarabnā lilnnāsi fī hādhā l-qur'āni min kulli mathalin laʿallahum yatadhakkarūna

Hausa Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun buga wa mutãne a, cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli, ɗammãninsu su yi tunãni.

Verse 28

قُرْءَانًا عَرَبِيًّا غَيْرَ ذِى عِوَجٍ لَّعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ

Transliteration qur'ānan ʿarabiyyan ghayra dhī ʿiwajin laʿallahum yattaqūna

Hausa Abin karantãwa ne na Lãrabci, ba mai wata karkata ba, ɗammãninsu, su yi taƙawa.

Verse 29

ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا رَّجُلًا فِيهِ شُرَكَآءُ مُتَشَـٰكِسُونَ وَرَجُلًا سَلَمًا لِّرَجُلٍ هَلْ يَسْتَوِيَانِ مَثَلًا ۚ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration ḍaraba l-lahu mathalan rajulan fīhi shurakāu mutashākisūna warajulan salaman lirajulin hal yastawiyāni mathalan l-ḥamdu lillahi bal aktharuhum lā yaʿlamūna

Hausa Allah Yã buga misãli; wani mutum (bãwa) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun hãlin jãyayya, da wani mutum (bãwa) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah (a kan bayãni). Ã'a, mafi yawan mutãne ba su sani ba.

Verse 30

إِنَّكَ مَيِّتٌ وَإِنَّهُم مَّيِّتُونَ

Transliteration innaka mayyitun wa-innahum mayyitūna

Hausa Lalle kai mai mutuwa ne, kuma su mã lalle mãsu mutuwa ne.

Verse 31

ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ عِندَ رَبِّكُمْ تَخْتَصِمُونَ

Transliteration thumma innakum yawma l-qiyāmati ʿinda rabbikum takhtaṣimūna

Hausa Sa'an nan, lalle kũ, a Rãnar ¡iyãma, a wurin Ubangijinku, zã ku yi ta yin husũma.

Verse 32

۞ فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن كَذَبَ عَلَى ٱللَّهِ وَكَذَّبَ بِٱلصِّدْقِ إِذْ جَآءَهُۥٓ ۚ أَلَيْسَ فِى جَهَنَّمَ مَثْوًى لِّلْكَـٰفِرِينَ

Transliteration faman aẓlamu mimman kadhaba ʿalā l-lahi wakadhaba bil-ṣid'qi idh jāahu alaysa fī jahannama mathwan lil'kāfirīna

Hausa To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta jẽ masa? Shin bãbu mazauni a cikin Jahannama ga kãfirai?

Verse 33

وَٱلَّذِى جَآءَ بِٱلصِّدْقِ وَصَدَّقَ بِهِۦٓ ۙ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُتَّقُونَ

Transliteration wa-alladhī jāa bil-ṣid'qi waṣaddaqa bihi ulāika humu l-mutaqūna

Hausa Kuma wanda ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata a game da ita, waɗancan sũ ne mãsu taƙawa.

Verse 34

لَهُم مَّا يَشَآءُونَ عِندَ رَبِّهِمْ ۚ ذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلْمُحْسِنِينَ

Transliteration lahum mā yashāūna ʿinda rabbihim dhālika jazāu l-muḥ'sinīna

Hausa Sunã da abin da suke so wajen Ubangijinsu. Wancan shĩ ne sakamakon mãsu kyautatãwa.

Verse 35

لِيُكَفِّرَ ٱللَّهُ عَنْهُمْ أَسْوَأَ ٱلَّذِى عَمِلُوا۟ وَيَجْزِيَهُمْ أَجْرَهُم بِأَحْسَنِ ٱلَّذِى كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Transliteration liyukaffira l-lahu ʿanhum aswa-a alladhī ʿamilū wayajziyahum ajrahum bi-aḥsani alladhī kānū yaʿmalūna

Hausa Dõmin Allah Ya kankare musu mafi mũnin abin da suka aikata, kuma Ya sãkã musu ijãrarsu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Verse 36

أَلَيْسَ ٱللَّهُ بِكَافٍ عَبْدَهُۥ ۖ وَيُخَوِّفُونَكَ بِٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦ ۚ وَمَن يُضْلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنْ هَادٍ

Transliteration alaysa l-lahu bikāfin ʿabdahu wayukhawwifūnaka bi-alladhīna min dūnihi waman yuḍ'lili l-lahu famā lahu min hādin

Hausa Ashe Allah bai zama Mai isa ga BãwanSa ba? Kuma sunã tsõratar da kai ga waɗanda suke wanin Sa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bã, shi da mai shiryarwa.

Verse 37

وَمَن يَهْدِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن مُّضِلٍّ ۗ أَلَيْسَ ٱللَّهُ بِعَزِيزٍ ذِى ٱنتِقَامٍ

Transliteration waman yahdi l-lahu famā lahu min muḍillin alaysa l-lahu biʿazīzin dhī intiqāmin

Hausa Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, bã shi da mai ɓatarwa. Ashe, Allah bai zama Mabuwãyi ba, Mai azãbar rãmuwa?

Verse 38

وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ ۚ قُلْ أَفَرَءَيْتُم مَّا تَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ إِنْ أَرَادَنِىَ ٱللَّهُ بِضُرٍّ هَلْ هُنَّ كَـٰشِفَـٰتُ ضُرِّهِۦٓ أَوْ أَرَادَنِى بِرَحْمَةٍ هَلْ هُنَّ مُمْسِكَـٰتُ رَحْمَتِهِۦ ۚ قُلْ حَسْبِىَ ٱللَّهُ ۖ عَلَيْهِ يَتَوَكَّلُ ٱلْمُتَوَكِّلُونَ

Transliteration wala-in sa-altahum man khalaqa l-samāwāti wal-arḍa layaqūlunna l-lahu qul afara-aytum mā tadʿūna min dūni l-lahi in arādaniya l-lahu biḍurrin hal hunna kāshifātu ḍurrihi aw arādanī biraḥmatin hal hunna mum'sikātu raḥmatihi qul ḥasbiya l-lahu ʿalayhi yatawakkalu l-mutawakilūna

Hausa Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?" Haƙĩƙa, zã su ce, "Allah ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan mãsu kãme rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke dõgara."

Verse 39

قُلْ يَـٰقَوْمِ ٱعْمَلُوا۟ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمْ إِنِّى عَـٰمِلٌ ۖ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ

Transliteration qul yāqawmi iʿ'malū ʿalā makānatikum innī ʿāmilun fasawfa taʿlamūna

Hausa Ka ce: "Yã mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle nĩ, inã aiki a kan hãlĩna. Sa'an nan zã ku sani."

Verse 40

مَن يَأْتِيهِ عَذَابٌ يُخْزِيهِ وَيَحِلُّ عَلَيْهِ عَذَابٌ مُّقِيمٌ

Transliteration man yatīhi ʿadhābun yukh'zīhi wayaḥillu ʿalayhi ʿadhābun muqīmun

Hausa "Wanda azãba ta je masa, zã ta wulãkanta shi, kuma wata azãba mai dawwama za ta sauka a kansa."

Verse 41

إِنَّآ أَنزَلْنَا عَلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ لِلنَّاسِ بِٱلْحَقِّ ۖ فَمَنِ ٱهْتَدَىٰ فَلِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا ۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيْهِم بِوَكِيلٍ

Transliteration innā anzalnā ʿalayka l-kitāba lilnnāsi bil-ḥaqi famani ih'tadā falinafsihi waman ḍalla fa-innamā yaḍillu ʿalayhā wamā anta ʿalayhim biwakīlin

Hausa Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa'an nan wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba.

Verse 42

ٱللَّهُ يَتَوَفَّى ٱلْأَنفُسَ حِينَ مَوْتِهَا وَٱلَّتِى لَمْ تَمُتْ فِى مَنَامِهَا ۖ فَيُمْسِكُ ٱلَّتِى قَضَىٰ عَلَيْهَا ٱلْمَوْتَ وَيُرْسِلُ ٱلْأُخْرَىٰٓ إِلَىٰٓ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ

Transliteration al-lahu yatawaffā l-anfusa ḥīna mawtihā wa-allatī lam tamut fī manāmihā fayum'siku allatī qaḍā ʿalayhā l-mawta wayur'silu l-ukh'rā ilā ajalin musamman inna fī dhālika laāyātin liqawmin yatafakkarūna

Hausa Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.

Verse 43

أَمِ ٱتَّخَذُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ شُفَعَآءَ ۚ قُلْ أَوَلَوْ كَانُوا۟ لَا يَمْلِكُونَ شَيْـًٔا وَلَا يَعْقِلُونَ

Transliteration ami ittakhadhū min dūni l-lahi shufaʿāa qul awalaw kānū lā yamlikūna shayan walā yaʿqilūna

Hausa Kõ kuma sun riƙi mãsu cẽto ne, waɗansun Allah? Ka ce: "Shin, kuma kõ dã sun kasance bã su da mallakar kõme, kuma bã su hankalta?"

Verse 44

قُل لِّلَّهِ ٱلشَّفَـٰعَةُ جَمِيعًا ۖ لَّهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Transliteration qul lillahi l-shafāʿatu jamīʿan lahu mul'ku l-samāwāti wal-arḍi thumma ilayhi tur'jaʿūna

Hausa Ka ce: "Cẽto gabã ɗaya ga Allah yake. Mulkin sammai da ƙasã Nãsa ne. Sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku."

Verse 45

وَإِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَحْدَهُ ٱشْمَأَزَّتْ قُلُوبُ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ ۖ وَإِذَا ذُكِرَ ٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦٓ إِذَا هُمْ يَسْتَبْشِرُونَ

Transliteration wa-idhā dhukira l-lahu waḥdahu ish'ma-azzat qulūbu alladhīna lā yu'minūna bil-ākhirati wa-idhā dhukira alladhīna min dūnihi idhā hum yastabshirūna

Hausa Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasun Sa, sai gãsu sunã yin bushãrar farin ciki.

Verse 46

قُلِ ٱللَّهُمَّ فَاطِرَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ عَـٰلِمَ ٱلْغَيْبِ وَٱلشَّهَـٰدَةِ أَنتَ تَحْكُمُ بَيْنَ عِبَادِكَ فِى مَا كَانُوا۟ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ

Transliteration quli l-lahuma fāṭira l-samāwāti wal-arḍi ʿālima l-ghaybi wal-shahādati anta taḥkumu bayna ʿibādika fī mā kānū fīhi yakhtalifūna

Hausa Ka ce: "Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane! Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa."

Verse 47

وَلَوْ أَنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مَا فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا وَمِثْلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفْتَدَوْا۟ بِهِۦ مِن سُوٓءِ ٱلْعَذَابِ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ وَبَدَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مَا لَمْ يَكُونُوا۟ يَحْتَسِبُونَ

Transliteration walaw anna lilladhīna ẓalamū mā fī l-arḍi jamīʿan wamith'lahu maʿahu la-if'tadaw bihi min sūi l-ʿadhābi yawma l-qiyāmati wabadā lahum mina l-lahi mā lam yakūnū yaḥtasibūna

Hausa Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a Rãnar ¡iyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a gare su.

Verse 48

وَبَدَا لَهُمْ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُوا۟ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ

Transliteration wabadā lahum sayyiātu mā kasabū waḥāqa bihim mā kānū bihi yastahziūna

Hausa Mũnãnan ayyuka da suka aikata, suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi, na izgili, ya wajaba a kansu.

Verse 49

فَإِذَا مَسَّ ٱلْإِنسَـٰنَ ضُرٌّ دَعَانَا ثُمَّ إِذَا خَوَّلْنَـٰهُ نِعْمَةً مِّنَّا قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلْمٍۭ ۚ بَلْ هِىَ فِتْنَةٌ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration fa-idhā massa l-insāna ḍurrun daʿānā thumma idhā khawwalnāhu niʿ'matan minnā qāla innamā ūtītuhu ʿalā ʿil'min bal hiya fit'natun walākinna aktharahum lā yaʿlamūna

Hausa To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa'an nan idan Muka canza masa ita, ya sãmi ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: "An bã ni ita ne a kan wani ilmi nãwa kawai." Ã'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba su sani ba.

Verse 50

قَدْ قَالَهَا ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَمَآ أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ

Transliteration qad qālahā alladhīna min qablihim famā aghnā ʿanhum mā kānū yaksibūna

Hausa Lalle waɗanda ke a gabãninsu, sun faɗe ta, sabõda haka abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su da kõme ba.

Verse 51

فَأَصَابَهُمْ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُوا۟ ۚ وَٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مِنْ هَـٰٓؤُلَآءِ سَيُصِيبُهُمْ سَيِّـَٔاتُ مَا كَسَبُوا۟ وَمَا هُم بِمُعْجِزِينَ

Transliteration fa-aṣābahum sayyiātu mā kasabū wa-alladhīna ẓalamū min hāulāi sayuṣībuhum sayyiātu mā kasabū wamā hum bimuʿ'jizīna

Hausa Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma ba su zama mabuwãya ba.

Verse 52

أَوَلَمْ يَعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

Transliteration awalam yaʿlamū anna l-laha yabsuṭu l-riz'qa liman yashāu wayaqdiru inna fī dhālika laāyātin liqawmin yu'minūna

Hausa Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni.

Verse 53

۞ قُلْ يَـٰعِبَادِىَ ٱلَّذِينَ أَسْرَفُوا۟ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا۟ مِن رَّحْمَةِ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَغْفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration qul yāʿibādiya alladhīna asrafū ʿalā anfusihim lā taqnaṭū min raḥmati l-lahi inna l-laha yaghfiru l-dhunūba jamīʿan innahu huwa l-ghafūru l-raḥīmu

Hausa Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩ Na waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."

Verse 54

وَأَنِيبُوٓا۟ إِلَىٰ رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا۟ لَهُۥ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَكُمُ ٱلْعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ

Transliteration wa-anībū ilā rabbikum wa-aslimū lahu min qabli an yatiyakumu l-ʿadhābu thumma lā tunṣarūna

Hausa "Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin azãba ta zo muku, sa'an nan kuwa bã zã a taimake ku ba."

Verse 55

وَٱتَّبِعُوٓا۟ أَحْسَنَ مَآ أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِيَكُمُ ٱلْعَذَابُ بَغْتَةً وَأَنتُمْ لَا تَشْعُرُونَ

Transliteration wa-ittabiʿū aḥsana mā unzila ilaykum min rabbikum min qabli an yatiyakumu l-ʿadhābu baghtatan wa-antum lā tashʿurūna

Hausa "Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba."

Verse 56

أَن تَقُولَ نَفْسٌ يَـٰحَسْرَتَىٰ عَلَىٰ مَا فَرَّطتُ فِى جَنۢبِ ٱللَّهِ وَإِن كُنتُ لَمِنَ ٱلسَّـٰخِرِينَ

Transliteration an taqūla nafsun yāḥasratā ʿalā mā farraṭtu fī janbi l-lahi wa-in kuntu lamina l-sākhirīna

Hausa "Kada wani rai ya ce: 'Yã nadãmãta a kan abin da na yi sakaci a cikin sãshen Allah' kuma lalle na kasance, haƙĩƙa, daga mãsu izgili!"'

Verse 57

أَوْ تَقُولَ لَوْ أَنَّ ٱللَّهَ هَدَىٰنِى لَكُنتُ مِنَ ٱلْمُتَّقِينَ

Transliteration aw taqūla law anna l-laha hadānī lakuntu mina l-mutaqīna

Hausa "Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa.'"

Verse 58

أَوْ تَقُولَ حِينَ تَرَى ٱلْعَذَابَ لَوْ أَنَّ لِى كَرَّةً فَأَكُونَ مِنَ ٱلْمُحْسِنِينَ

Transliteration aw taqūla ḥīna tarā l-ʿadhāba law anna lī karratan fa-akūna mina l-muḥ'sinīna

Hausa "Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba, 'Dã lalle a ce inã da wata kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa.'"

Verse 59

بَلَىٰ قَدْ جَآءَتْكَ ءَايَـٰتِى فَكَذَّبْتَ بِهَا وَٱسْتَكْبَرْتَ وَكُنتَ مِنَ ٱلْكَـٰفِرِينَ

Transliteration balā qad jāatka āyātī fakadhabta bihā wa-is'takbarta wakunta mina l-kāfirīna

Hausa "Na'am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai."

Verse 60

وَيَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ تَرَى ٱلَّذِينَ كَذَبُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ وُجُوهُهُم مُّسْوَدَّةٌ ۚ أَلَيْسَ فِى جَهَنَّمَ مَثْوًى لِّلْمُتَكَبِّرِينَ

Transliteration wayawma l-qiyāmati tarā alladhīna kadhabū ʿalā l-lahi wujūhuhum mus'waddatun alaysa fī jahannama mathwan lil'mutakabbirīna

Hausa Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai?

Verse 61

وَيُنَجِّى ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوْا۟ بِمَفَازَتِهِمْ لَا يَمَسُّهُمُ ٱلسُّوٓءُ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ

Transliteration wayunajjī l-lahu alladhīna ittaqaw bimafāzatihim lā yamassuhumu l-sūu walā hum yaḥzanūna

Hausa Kuma Allah na tsĩrar da waɗanda suka yi taƙawa a game da wurin sãmun babban rabonsu, cũta bã zã tashãfe su ba, kuma ba su zama sunã baƙin ciki ba.

Verse 62

ٱللَّهُ خَـٰلِقُ كُلِّ شَىْءٍ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ وَكِيلٌ

Transliteration al-lahu khāliqu kulli shayin wahuwa ʿalā kulli shayin wakīlun

Hausa Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme.

Verse 63

لَّهُۥ مَقَالِيدُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۗ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ

Transliteration lahu maqālīdu l-samāwāti wal-arḍi wa-alladhīna kafarū biāyāti l-lahi ulāika humu l-khāsirūna

Hausa Shĩ ke da mabũɗan sammai da ƙasã. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra.

Verse 64

قُلْ أَفَغَيْرَ ٱللَّهِ تَأْمُرُوٓنِّىٓ أَعْبُدُ أَيُّهَا ٱلْجَـٰهِلُونَ

Transliteration qul afaghayra l-lahi tamurūnnī aʿbudu ayyuhā l-jāhilūna

Hausa Ka ce: "Shin, wanin Allah kuke umurni na da in bauta wa? Yã ku jãhilai!"

Verse 65

وَلَقَدْ أُوحِىَ إِلَيْكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْخَـٰسِرِينَ

Transliteration walaqad ūḥiya ilayka wa-ilā alladhīna min qablika la-in ashrakta layaḥbaṭanna ʿamaluka walatakūnanna mina l-khāsirīna

Hausa Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra."

Verse 66

بَلِ ٱللَّهَ فَٱعْبُدْ وَكُن مِّنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ

Transliteration bali l-laha fa-uʿ'bud wakun mina l-shākirīna

Hausa Ã'aha! Ka bauta wa Allah kaɗai, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya.

Verse 67

وَمَا قَدَرُوا۟ ٱللَّهَ حَقَّ قَدْرِهِۦ وَٱلْأَرْضُ جَمِيعًا قَبْضَتُهُۥ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ وَٱلسَّمَـٰوَٰتُ مَطْوِيَّـٰتٌۢ بِيَمِينِهِۦ ۚ سُبْحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ

Transliteration wamā qadarū l-laha ḥaqqa qadrihi wal-arḍu jamīʿan qabḍatuhu yawma l-qiyāmati wal-samāwātu maṭwiyyātun biyamīnihi sub'ḥānahu wataʿālā ʿammā yush'rikūna

Hausa Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi.

Verse 68

وَنُفِخَ فِى ٱلصُّورِ فَصَعِقَ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ إِلَّا مَن شَآءَ ٱللَّهُ ۖ ثُمَّ نُفِخَ فِيهِ أُخْرَىٰ فَإِذَا هُمْ قِيَامٌ يَنظُرُونَ

Transliteration wanufikha fī l-ṣūri faṣaʿiqa man fī l-samāwāti waman fī l-arḍi illā man shāa l-lahu thumma nufikha fīhi ukh'rā fa-idhā hum qiyāmun yanẓurūna

Hausa Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo.

Verse 69

وَأَشْرَقَتِ ٱلْأَرْضُ بِنُورِ رَبِّهَا وَوُضِعَ ٱلْكِتَـٰبُ وَجِا۟ىٓءَ بِٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَقُضِىَ بَيْنَهُم بِٱلْحَقِّ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ

Transliteration wa-ashraqati l-arḍu binūri rabbihā wawuḍiʿa l-kitābu wajīa bil-nabiyīna wal-shuhadāi waquḍiya baynahum bil-ḥaqi wahum lā yuẓ'lamūna

Hausa Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba.

Verse 70

وَوُفِّيَتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّا عَمِلَتْ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَا يَفْعَلُونَ

Transliteration wawuffiyat kullu nafsin mā ʿamilat wahuwa aʿlamu bimā yafʿalūna

Hausa Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani game da abin da suke aikatãwa.

Verse 71

وَسِيقَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ إِلَىٰ جَهَنَّمَ زُمَرًا ۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوهَا فُتِحَتْ أَبْوَٰبُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَآ أَلَمْ يَأْتِكُمْ رُسُلٌ مِّنكُمْ يَتْلُونَ عَلَيْكُمْ ءَايَـٰتِ رَبِّكُمْ وَيُنذِرُونَكُمْ لِقَآءَ يَوْمِكُمْ هَـٰذَا ۚ قَالُوا۟ بَلَىٰ وَلَـٰكِنْ حَقَّتْ كَلِمَةُ ٱلْعَذَابِ عَلَى ٱلْكَـٰفِرِينَ

Transliteration wasīqa alladhīna kafarū ilā jahannama zumaran ḥattā idhā jāūhā futiḥat abwābuhā waqāla lahum khazanatuhā alam yatikum rusulun minkum yatlūna ʿalaykum āyāti rabbikum wayundhirūnakum liqāa yawmikum hādhā qālū balā walākin ḥaqqat kalimatu l-ʿadhābi ʿalā l-kāfirīna

Hausa Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am, "kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!"

Verse 72

قِيلَ ٱدْخُلُوٓا۟ أَبْوَٰبَ جَهَنَّمَ خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۖ فَبِئْسَ مَثْوَى ٱلْمُتَكَبِّرِينَ

Transliteration qīla ud'khulū abwāba jahannama khālidīna fīhā fabi'sa mathwā l-mutakabirīna

Hausa Aka ce, "Ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kaunã madawwama a cikinta. Sa'an nan mazaunin makangara yã munana."

Verse 73

وَسِيقَ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوْا۟ رَبَّهُمْ إِلَى ٱلْجَنَّةِ زُمَرًا ۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوهَا وَفُتِحَتْ أَبْوَٰبُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَا سَلَـٰمٌ عَلَيْكُمْ طِبْتُمْ فَٱدْخُلُوهَا خَـٰلِدِينَ

Transliteration wasīqa alladhīna ittaqaw rabbahum ilā l-janati zumaran ḥattā idhā jāūhā wafutiḥat abwābuhā waqāla lahum khazanatuhā salāmun ʿalaykum ṭib'tum fa-ud'khulūhā khālidīna

Hausa Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama (a cikinta)."

Verse 74

وَقَالُوا۟ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ٱلَّذِى صَدَقَنَا وَعْدَهُۥ وَأَوْرَثَنَا ٱلْأَرْضَ نَتَبَوَّأُ مِنَ ٱلْجَنَّةِ حَيْثُ نَشَآءُ ۖ فَنِعْمَ أَجْرُ ٱلْعَـٰمِلِينَ

Transliteration waqālū l-ḥamdu lillahi alladhī ṣadaqanā waʿdahu wa-awrathanā l-arḍa natabawwa-u mina l-janati ḥaythu nashāu faniʿ'ma ajru l-ʿāmilīna

Hausa Kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa, kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla da ijãrar ma'aikata.

Verse 75

وَتَرَى ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ حَآفِّينَ مِنْ حَوْلِ ٱلْعَرْشِ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ ۖ وَقُضِىَ بَيْنَهُم بِٱلْحَقِّ وَقِيلَ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration watarā l-malāikata ḥāffīna min ḥawli l-ʿarshi yusabbiḥūna biḥamdi rabbihim waquḍiya baynahum bil-ḥaqi waqīla l-ḥamdu lillahi rabbi l-ʿālamīna

Hausa Kuma kanã ganin malã'iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga kẽwayen Al'arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce, "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu."

Read Surah Az-Zumar in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.