MyDugsiStart learning

Surah As-Saffat in Hausa: translation and audio

Surah 37 · الصافات · Those who set the Ranks · 182 verses

Surah As-Saffat verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah As-Saffat word by word in English.

Verse 1

وَٱلصَّـٰٓفَّـٰتِ صَفًّا

Transliteration wal-ṣāfāti ṣaffan

Hausa Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).

Verse 2

فَٱلزَّٰجِرَٰتِ زَجْرًا

Transliteration fal-zājirāti zajran

Hausa Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.

Verse 3

فَٱلتَّـٰلِيَـٰتِ ذِكْرًا

Transliteration fal-tāliyāti dhik'ran

Hausa Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.

Verse 4

إِنَّ إِلَـٰهَكُمْ لَوَٰحِدٌ

Transliteration inna ilāhakum lawāḥidun

Hausa Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.

Verse 5

رَّبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ ٱلْمَشَـٰرِقِ

Transliteration rabbu l-samāwāti wal-arḍi wamā baynahumā warabbu l-mashāriqi

Hausa Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.

Verse 6

إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنْيَا بِزِينَةٍ ٱلْكَوَاكِبِ

Transliteration innā zayyannā l-samāa l-dun'yā bizīnatin l-kawākibi

Hausa Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.

Verse 7

وَحِفْظًا مِّن كُلِّ شَيْطَـٰنٍ مَّارِدٍ

Transliteration waḥif'ẓan min kulli shayṭānin māridin

Hausa Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.

Verse 8

لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلْمَلَإِ ٱلْأَعْلَىٰ وَيُقْذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍ

Transliteration lā yassammaʿūna ilā l-mala-i l-aʿlā wayuq'dhafūna min kulli jānibin

Hausa Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.

Verse 9

دُحُورًا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ وَاصِبٌ

Transliteration duḥūran walahum ʿadhābun wāṣibun

Hausa Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.

Verse 10

إِلَّا مَنْ خَطِفَ ٱلْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَهُۥ شِهَابٌ ثَاقِبٌ

Transliteration illā man khaṭifa l-khaṭfata fa-atbaʿahu shihābun thāqibun

Hausa Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.

Verse 11

فَٱسْتَفْتِهِمْ أَهُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَم مَّنْ خَلَقْنَآ ۚ إِنَّا خَلَقْنَـٰهُم مِّن طِينٍ لَّازِبٍۭ

Transliteration fa-is'taftihim ahum ashaddu khalqan am man khalaqnā innā khalaqnāhum min ṭīnin lāzibin

Hausa Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.

Verse 12

بَلْ عَجِبْتَ وَيَسْخَرُونَ

Transliteration bal ʿajib'ta wayaskharūna

Hausa Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.

Verse 13

وَإِذَا ذُكِّرُوا۟ لَا يَذْكُرُونَ

Transliteration wa-idhā dhukkirū lā yadhkurūna

Hausa Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.

Verse 14

وَإِذَا رَأَوْا۟ ءَايَةً يَسْتَسْخِرُونَ

Transliteration wa-idhā ra-aw āyatan yastaskhirūna

Hausa Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.

Verse 15

وَقَالُوٓا۟ إِنْ هَـٰذَآ إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ

Transliteration waqālū in hādhā illā siḥ'run mubīnun

Hausa Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."

Verse 16

أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَـٰمًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ

Transliteration a-idhā mit'nā wakunnā turāban waʿiẓāman a-innā lamabʿūthūna

Hausa "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?

Verse 17

أَوَءَابَآؤُنَا ٱلْأَوَّلُونَ

Transliteration awaābāunā l-awalūna

Hausa "Ashe kõ da ubanninmu na farko?"

Verse 18

قُلْ نَعَمْ وَأَنتُمْ دَٰخِرُونَ

Transliteration qul naʿam wa-antum dākhirūna

Hausa Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."

Verse 19

فَإِنَّمَا هِىَ زَجْرَةٌ وَٰحِدَةٌ فَإِذَا هُمْ يَنظُرُونَ

Transliteration fa-innamā hiya zajratun wāḥidatun fa-idhā hum yanẓurūna

Hausa Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.

Verse 20

وَقَالُوا۟ يَـٰوَيْلَنَا هَـٰذَا يَوْمُ ٱلدِّينِ

Transliteration waqālū yāwaylanā hādhā yawmu l-dīni

Hausa Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."

Verse 21

هَـٰذَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ

Transliteration hādhā yawmu l-faṣli alladhī kuntum bihi tukadhibūna

Hausa Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.

Verse 22

۞ ٱحْشُرُوا۟ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ وَأَزْوَٰجَهُمْ وَمَا كَانُوا۟ يَعْبُدُونَ

Transliteration uḥ'shurū alladhīna ẓalamū wa-azwājahum wamā kānū yaʿbudūna

Hausa Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.

Verse 23

مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهْدُوهُمْ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلْجَحِيمِ

Transliteration min dūni l-lahi fa-ih'dūhum ilā ṣirāṭi l-jaḥīmi

Hausa Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.

Verse 24

وَقِفُوهُمْ ۖ إِنَّهُم مَّسْـُٔولُونَ

Transliteration waqifūhum innahum masūlūna

Hausa Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.

Verse 25

مَا لَكُمْ لَا تَنَاصَرُونَ

Transliteration mā lakum lā tanāṣarūna

Hausa Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?

Verse 26

بَلْ هُمُ ٱلْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَ

Transliteration bal humu l-yawma mus'taslimūna

Hausa Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.

Verse 27

وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَآءَلُونَ

Transliteration wa-aqbala baʿḍuhum ʿalā baʿḍin yatasāalūna

Hausa Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.

Verse 28

قَالُوٓا۟ إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ ٱلْيَمِينِ

Transliteration qālū innakum kuntum tatūnanā ʿani l-yamīni

Hausa Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."

Verse 29

قَالُوا۟ بَل لَّمْ تَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ

Transliteration qālū bal lam takūnū mu'minīna

Hausa Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.

Verse 30

وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُم مِّن سُلْطَـٰنٍۭ ۖ بَلْ كُنتُمْ قَوْمًا طَـٰغِينَ

Transliteration wamā kāna lanā ʿalaykum min sul'ṭānin bal kuntum qawman ṭāghīna

Hausa "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."

Verse 31

فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَآ ۖ إِنَّا لَذَآئِقُونَ

Transliteration faḥaqqa ʿalaynā qawlu rabbinā innā ladhāiqūna

Hausa "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."

Verse 32

فَأَغْوَيْنَـٰكُمْ إِنَّا كُنَّا غَـٰوِينَ

Transliteration fa-aghwaynākum innā kunnā ghāwīna

Hausa "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."

Verse 33

فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذٍ فِى ٱلْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ

Transliteration fa-innahum yawma-idhin fī l-ʿadhābi mush'tarikūna

Hausa To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.

Verse 34

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِٱلْمُجْرِمِينَ

Transliteration innā kadhālika nafʿalu bil-muj'rimīna

Hausa Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.

Verse 35

إِنَّهُمْ كَانُوٓا۟ إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ

Transliteration innahum kānū idhā qīla lahum lā ilāha illā l-lahu yastakbirūna

Hausa Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.

Verse 36

وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوٓا۟ ءَالِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجْنُونٍۭ

Transliteration wayaqūlūna a-innā latārikū ālihatinā lishāʿirin majnūnin

Hausa Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?

Verse 37

بَلْ جَآءَ بِٱلْحَقِّ وَصَدَّقَ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration bal jāa bil-ḥaqi waṣaddaqa l-mur'salīna

Hausa Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.

Verse 38

إِنَّكُمْ لَذَآئِقُوا۟ ٱلْعَذَابِ ٱلْأَلِيمِ

Transliteration innakum ladhāiqū l-ʿadhābi l-alīmi

Hausa Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.

Verse 39

وَمَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Transliteration wamā tuj'zawna illā mā kuntum taʿmalūna

Hausa Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

Verse 40

إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ

Transliteration illā ʿibāda l-lahi l-mukh'laṣīna

Hausa Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

Verse 41

أُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ رِزْقٌ مَّعْلُومٌ

Transliteration ulāika lahum riz'qun maʿlūmun

Hausa Waɗannan sunã da abinci sananne.

Verse 42

فَوَٰكِهُ ۖ وَهُم مُّكْرَمُونَ

Transliteration fawākihu wahum muk'ramūna

Hausa Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.

Verse 43

فِى جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ

Transliteration fī jannāti l-naʿīmi

Hausa A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.

Verse 44

عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَـٰبِلِينَ

Transliteration ʿalā sururin mutaqābilīna

Hausa A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.

Verse 45

يُطَافُ عَلَيْهِم بِكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍۭ

Transliteration yuṭāfu ʿalayhim bikasin min maʿīnin

Hausa Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.

Verse 46

بَيْضَآءَ لَذَّةٍ لِّلشَّـٰرِبِينَ

Transliteration bayḍāa ladhatin lilshāribīna

Hausa Farã mai dãɗi ga mashãyan.

Verse 47

لَا فِيهَا غَوْلٌ وَلَا هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَ

Transliteration lā fīhā ghawlun walā hum ʿanhā yunzafūna

Hausa A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,

Verse 48

وَعِندَهُمْ قَـٰصِرَٰتُ ٱلطَّرْفِ عِينٌ

Transliteration waʿindahum qāṣirātu l-ṭarfi ʿīnun

Hausa Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.

Verse 49

كَأَنَّهُنَّ بَيْضٌ مَّكْنُونٌ

Transliteration ka-annahunna bayḍun maknūnun

Hausa Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.

Verse 50

فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَآءَلُونَ

Transliteration fa-aqbala baʿḍuhum ʿalā baʿḍin yatasāalūna

Hausa Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.

Verse 51

قَالَ قَآئِلٌ مِّنْهُمْ إِنِّى كَانَ لِى قَرِينٌ

Transliteration qāla qāilun min'hum innī kāna lī qarīnun

Hausa Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."

Verse 52

يَقُولُ أَءِنَّكَ لَمِنَ ٱلْمُصَدِّقِينَ

Transliteration yaqūlu a-innaka lamina l-muṣadiqīna

Hausa Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"

Verse 53

أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَـٰمًا أَءِنَّا لَمَدِينُونَ

Transliteration a-idhā mit'nā wakunnā turāban waʿiẓāman a-innā lamadīnūna

Hausa "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"

Verse 54

قَالَ هَلْ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ

Transliteration qāla hal antum muṭṭaliʿūna

Hausa (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"

Verse 55

فَٱطَّلَعَ فَرَءَاهُ فِى سَوَآءِ ٱلْجَحِيمِ

Transliteration fa-iṭṭalaʿa faraāhu fī sawāi l-jaḥīmi

Hausa Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.

Verse 56

قَالَ تَٱللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرْدِينِ

Transliteration qāla tal-lahi in kidtta latur'dīni

Hausa Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."

Verse 57

وَلَوْلَا نِعْمَةُ رَبِّى لَكُنتُ مِنَ ٱلْمُحْضَرِينَ

Transliteration walawlā niʿ'matu rabbī lakuntu mina l-muḥ'ḍarīna

Hausa "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."

Verse 58

أَفَمَا نَحْنُ بِمَيِّتِينَ

Transliteration afamā naḥnu bimayyitīna

Hausa "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."

Verse 59

إِلَّا مَوْتَتَنَا ٱلْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ

Transliteration illā mawtatanā l-ūlā wamā naḥnu bimuʿadhabīna

Hausa "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"

Verse 60

إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ

Transliteration inna hādhā lahuwa l-fawzu l-ʿaẓīmu

Hausa Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.

Verse 61

لِمِثْلِ هَـٰذَا فَلْيَعْمَلِ ٱلْعَـٰمِلُونَ

Transliteration limith'li hādhā falyaʿmali l-ʿāmilūna

Hausa Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.

Verse 62

أَذَٰلِكَ خَيْرٌ نُّزُلًا أَمْ شَجَرَةُ ٱلزَّقُّومِ

Transliteration adhālika khayrun nuzulan am shajaratu l-zaqūmi

Hausa Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?

Verse 63

إِنَّا جَعَلْنَـٰهَا فِتْنَةً لِّلظَّـٰلِمِينَ

Transliteration innā jaʿalnāhā fit'natan lilẓẓālimīna

Hausa Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.

Verse 64

إِنَّهَا شَجَرَةٌ تَخْرُجُ فِىٓ أَصْلِ ٱلْجَحِيمِ

Transliteration innahā shajaratun takhruju fī aṣli l-jaḥīmi

Hausa Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.

Verse 65

طَلْعُهَا كَأَنَّهُۥ رُءُوسُ ٱلشَّيَـٰطِينِ

Transliteration ṭalʿuhā ka-annahu ruūsu l-shayāṭīni

Hausa Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.

Verse 66

فَإِنَّهُمْ لَـَٔاكِلُونَ مِنْهَا فَمَالِـُٔونَ مِنْهَا ٱلْبُطُونَ

Transliteration fa-innahum laākilūna min'hā famāliūna min'hā l-buṭūna

Hausa To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.

Verse 67

ثُمَّ إِنَّ لَهُمْ عَلَيْهَا لَشَوْبًا مِّنْ حَمِيمٍ

Transliteration thumma inna lahum ʿalayhā lashawban min ḥamīmin

Hausa Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.

Verse 68

ثُمَّ إِنَّ مَرْجِعَهُمْ لَإِلَى ٱلْجَحِيمِ

Transliteration thumma inna marjiʿahum la-ilā l-jaḥīmi

Hausa Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.

Verse 69

إِنَّهُمْ أَلْفَوْا۟ ءَابَآءَهُمْ ضَآلِّينَ

Transliteration innahum alfaw ābāahum ḍāllīna

Hausa Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.

Verse 70

فَهُمْ عَلَىٰٓ ءَاثَـٰرِهِمْ يُهْرَعُونَ

Transliteration fahum ʿalā āthārihim yuh'raʿūna

Hausa Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.

Verse 71

وَلَقَدْ ضَلَّ قَبْلَهُمْ أَكْثَرُ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration walaqad ḍalla qablahum aktharu l-awalīna

Hausa Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.

Verse 72

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ

Transliteration walaqad arsalnā fīhim mundhirīna

Hausa Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.

Verse 73

فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُنذَرِينَ

Transliteration fa-unẓur kayfa kāna ʿāqibatu l-mundharīna

Hausa Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.

Verse 74

إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ

Transliteration illā ʿibāda l-lahi l-mukh'laṣīna

Hausa Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

Verse 75

وَلَقَدْ نَادَىٰنَا نُوحٌ فَلَنِعْمَ ٱلْمُجِيبُونَ

Transliteration walaqad nādānā nūḥun falaniʿ'ma l-mujībūna

Hausa Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.

Verse 76

وَنَجَّيْنَـٰهُ وَأَهْلَهُۥ مِنَ ٱلْكَرْبِ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration wanajjaynāhu wa-ahlahu mina l-karbi l-ʿaẓīmi

Hausa Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.

Verse 77

وَجَعَلْنَا ذُرِّيَّتَهُۥ هُمُ ٱلْبَاقِينَ

Transliteration wajaʿalnā dhurriyyatahu humu l-bāqīna

Hausa Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.

Verse 78

وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ

Transliteration wataraknā ʿalayhi fī l-ākhirīna

Hausa Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.

Verse 79

سَلَـٰمٌ عَلَىٰ نُوحٍ فِى ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration salāmun ʿalā nūḥin fī l-ʿālamīna

Hausa Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.

Verse 80

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ

Transliteration innā kadhālika najzī l-muḥ'sinīna

Hausa Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Verse 81

إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration innahu min ʿibādinā l-mu'minīna

Hausa Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai.

Verse 82

ثُمَّ أَغْرَقْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ

Transliteration thumma aghraqnā l-ākharīna

Hausa Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.

Verse 83

۞ وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِۦ لَإِبْرَٰهِيمَ

Transliteration wa-inna min shīʿatihi la-ib'rāhīma

Hausa Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.

Verse 84

إِذْ جَآءَ رَبَّهُۥ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ

Transliteration idh jāa rabbahu biqalbin salīmin

Hausa A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya.

Verse 85

إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦ مَاذَا تَعْبُدُونَ

Transliteration idh qāla li-abīhi waqawmihi mādhā taʿbudūna

Hausa A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"

Verse 86

أَئِفْكًا ءَالِهَةً دُونَ ٱللَّهِ تُرِيدُونَ

Transliteration a-if'kan ālihatan dūna l-lahi turīdūna

Hausa "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"

Verse 87

فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration famā ẓannukum birabbi l-ʿālamīna

Hausa "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"

Verse 88

فَنَظَرَ نَظْرَةً فِى ٱلنُّجُومِ

Transliteration fanaẓara naẓratan fī l-nujūmi

Hausa Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.

Verse 89

فَقَالَ إِنِّى سَقِيمٌ

Transliteration faqāla innī saqīmun

Hausa Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."

Verse 90

فَتَوَلَّوْا۟ عَنْهُ مُدْبِرِينَ

Transliteration fatawallaw ʿanhu mud'birīna

Hausa Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.

Verse 91

فَرَاغَ إِلَىٰٓ ءَالِهَتِهِمْ فَقَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ

Transliteration farāgha ilā ālihatihim faqāla alā takulūna

Hausa Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?

Verse 92

مَا لَكُمْ لَا تَنطِقُونَ

Transliteration mā lakum lā tanṭiqūna

Hausa "Me ya sãme ku, bã ku magana?"

Verse 93

فَرَاغَ عَلَيْهِمْ ضَرْبًۢا بِٱلْيَمِينِ

Transliteration farāgha ʿalayhim ḍarban bil-yamīni

Hausa Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.

Verse 94

فَأَقْبَلُوٓا۟ إِلَيْهِ يَزِفُّونَ

Transliteration fa-aqbalū ilayhi yaziffūna

Hausa Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.

Verse 95

قَالَ أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَ

Transliteration qāla ataʿbudūna mā tanḥitūna

Hausa Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,

Verse 96

وَٱللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ

Transliteration wal-lahu khalaqakum wamā taʿmalūna

Hausa "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"

Verse 97

قَالُوا۟ ٱبْنُوا۟ لَهُۥ بُنْيَـٰنًا فَأَلْقُوهُ فِى ٱلْجَحِيمِ

Transliteration qālū ib'nū lahu bun'yānan fa-alqūhu fī l-jaḥīmi

Hausa Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."

Verse 98

فَأَرَادُوا۟ بِهِۦ كَيْدًا فَجَعَلْنَـٰهُمُ ٱلْأَسْفَلِينَ

Transliteration fa-arādū bihi kaydan fajaʿalnāhumu l-asfalīna

Hausa Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.

Verse 99

وَقَالَ إِنِّى ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّى سَيَهْدِينِ

Transliteration waqāla innī dhāhibun ilā rabbī sayahdīni

Hausa Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."

Verse 100

رَبِّ هَبْ لِى مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Transliteration rabbi hab lī mina l-ṣāliḥīna

Hausa "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."

Verse 101

فَبَشَّرْنَـٰهُ بِغُلَـٰمٍ حَلِيمٍ

Transliteration fabasharnāhu bighulāmin ḥalīmin

Hausa Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.

Verse 102

فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعْىَ قَالَ يَـٰبُنَىَّ إِنِّىٓ أَرَىٰ فِى ٱلْمَنَامِ أَنِّىٓ أَذْبَحُكَ فَٱنظُرْ مَاذَا تَرَىٰ ۚ قَالَ يَـٰٓأَبَتِ ٱفْعَلْ مَا تُؤْمَرُ ۖ سَتَجِدُنِىٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

Transliteration falammā balagha maʿahu l-saʿya qāla yābunayya innī arā fī l-manāmi annī adhbaḥuka fa-unẓur mādhā tarā qāla yāabati if'ʿal mā tu'maru satajidunī in shāa l-lahu mina l-ṣābirīna

Hausa To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."

Verse 103

فَلَمَّآ أَسْلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلْجَبِينِ

Transliteration falammā aslamā watallahu lil'jabīni

Hausa Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago

Verse 104

وَنَـٰدَيْنَـٰهُ أَن يَـٰٓإِبْرَٰهِيمُ

Transliteration wanādaynāhu an yāib'rāhīmu

Hausa Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"

Verse 105

قَدْ صَدَّقْتَ ٱلرُّءْيَآ ۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ

Transliteration qad ṣaddaqta l-ru'yā innā kadhālika najzī l-muḥ'sinīna

Hausa "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Verse 106

إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ ٱلْبَلَـٰٓؤُا۟ ٱلْمُبِينُ

Transliteration inna hādhā lahuwa l-balāu l-mubīnu

Hausa Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.

Verse 107

وَفَدَيْنَـٰهُ بِذِبْحٍ عَظِيمٍ

Transliteration wafadaynāhu bidhib'ḥin ʿaẓīmin

Hausa Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.

Verse 108

وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ

Transliteration wataraknā ʿalayhi fī l-ākhirīna

Hausa Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.

Verse 109

سَلَـٰمٌ عَلَىٰٓ إِبْرَٰهِيمَ

Transliteration salāmun ʿalā ib'rāhīma

Hausa Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.

Verse 110

كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ

Transliteration kadhālika najzī l-muḥ'sinīna

Hausa Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Verse 111

إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration innahu min ʿibādinā l-mu'minīna

Hausa Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.

Verse 112

وَبَشَّرْنَـٰهُ بِإِسْحَـٰقَ نَبِيًّا مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Transliteration wabasharnāhu bi-is'ḥāqa nabiyyan mina l-ṣāliḥīna

Hausa Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.

Verse 113

وَبَـٰرَكْنَا عَلَيْهِ وَعَلَىٰٓ إِسْحَـٰقَ ۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحْسِنٌ وَظَالِمٌ لِّنَفْسِهِۦ مُبِينٌ

Transliteration wabāraknā ʿalayhi waʿalā is'ḥāqa wamin dhurriyyatihimā muḥ'sinun waẓālimun linafsihi mubīnun

Hausa Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).

Verse 114

وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَـٰرُونَ

Transliteration walaqad manannā ʿalā mūsā wahārūna

Hausa Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.

Verse 115

وَنَجَّيْنَـٰهُمَا وَقَوْمَهُمَا مِنَ ٱلْكَرْبِ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration wanajjaynāhumā waqawmahumā mina l-karbi l-ʿaẓīmi

Hausa Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.

Verse 116

وَنَصَرْنَـٰهُمْ فَكَانُوا۟ هُمُ ٱلْغَـٰلِبِينَ

Transliteration wanaṣarnāhum fakānū humu l-ghālibīna

Hausa Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.

Verse 117

وَءَاتَيْنَـٰهُمَا ٱلْكِتَـٰبَ ٱلْمُسْتَبِينَ

Transliteration waātaynāhumā l-kitāba l-mus'tabīna

Hausa Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.

Verse 118

وَهَدَيْنَـٰهُمَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلْمُسْتَقِيمَ

Transliteration wahadaynāhumā l-ṣirāṭa l-mus'taqīma

Hausa Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.

Verse 119

وَتَرَكْنَا عَلَيْهِمَا فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ

Transliteration wataraknā ʿalayhimā fī l-ākhirīna

Hausa Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.

Verse 120

سَلَـٰمٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَـٰرُونَ

Transliteration salāmun ʿalā mūsā wahārūna

Hausa Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.

Verse 121

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ

Transliteration innā kadhālika najzī l-muḥ'sinīna

Hausa Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Verse 122

إِنَّهُمَا مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration innahumā min ʿibādinā l-mu'minīna

Hausa Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai.

Verse 123

وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration wa-inna il'yāsa lamina l-mur'salīna

Hausa Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

Verse 124

إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ

Transliteration idh qāla liqawmihi alā tattaqūna

Hausa A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"

Verse 125

أَتَدْعُونَ بَعْلًا وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ ٱلْخَـٰلِقِينَ

Transliteration atadʿūna baʿlan watadharūna aḥsana l-khāliqīna

Hausa "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"

Verse 126

ٱللَّهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration al-laha rabbakum warabba ābāikumu l-awalīna

Hausa "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"

Verse 127

فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ

Transliteration fakadhabūhu fa-innahum lamuḥ'ḍarūna

Hausa Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).

Verse 128

إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ

Transliteration illā ʿibāda l-lahi l-mukh'laṣīna

Hausa Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

Verse 129

وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ

Transliteration wataraknā ʿalayhi fī l-ākhirīna

Hausa Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.

Verse 130

سَلَـٰمٌ عَلَىٰٓ إِلْ يَاسِينَ

Transliteration salāmun ʿalā il yāsīna

Hausa Aminci ya tabbata ga Ilyãs.

Verse 131

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ

Transliteration innā kadhālika najzī l-muḥ'sinīna

Hausa Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Verse 132

إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration innahu min ʿibādinā l-mu'minīna

Hausa Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai.

Verse 133

وَإِنَّ لُوطًا لَّمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration wa-inna lūṭan lamina l-mur'salīna

Hausa Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

Verse 134

إِذْ نَجَّيْنَـٰهُ وَأَهْلَهُۥٓ أَجْمَعِينَ

Transliteration idh najjaynāhu wa-ahlahu ajmaʿīna

Hausa A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.

Verse 135

إِلَّا عَجُوزًا فِى ٱلْغَـٰبِرِينَ

Transliteration illā ʿajūzan fī l-ghābirīna

Hausa Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).

Verse 136

ثُمَّ دَمَّرْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ

Transliteration thumma dammarnā l-ākharīna

Hausa Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.

Verse 137

وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِم مُّصْبِحِينَ

Transliteration wa-innakum latamurrūna ʿalayhim muṣ'biḥīna

Hausa Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.

Verse 138

وَبِٱلَّيْلِ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ

Transliteration wabi-al-layli afalā taʿqilūna

Hausa Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?

Verse 139

وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration wa-inna yūnusa lamina l-mur'salīna

Hausa Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

Verse 140

إِذْ أَبَقَ إِلَى ٱلْفُلْكِ ٱلْمَشْحُونِ

Transliteration idh abaqa ilā l-ful'ki l-mashḥūni

Hausa A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.

Verse 141

فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلْمُدْحَضِينَ

Transliteration fasāhama fakāna mina l-mud'ḥaḍīna

Hausa Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.

Verse 142

فَٱلْتَقَمَهُ ٱلْحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌ

Transliteration fal-taqamahu l-ḥūtu wahuwa mulīmun

Hausa Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.

Verse 143

فَلَوْلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلْمُسَبِّحِينَ

Transliteration falawlā annahu kāna mina l-musabiḥīna

Hausa To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,

Verse 144

لَلَبِثَ فِى بَطْنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ

Transliteration lalabitha fī baṭnihi ilā yawmi yub'ʿathūna

Hausa Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.

Verse 145

۞ فَنَبَذْنَـٰهُ بِٱلْعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٌ

Transliteration fanabadhnāhu bil-ʿarāi wahuwa saqīmun

Hausa Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.

Verse 146

وَأَنۢبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَةً مِّن يَقْطِينٍ

Transliteration wa-anbatnā ʿalayhi shajaratan min yaqṭīnin

Hausa Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.

Verse 147

وَأَرْسَلْنَـٰهُ إِلَىٰ مِا۟ئَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَ

Transliteration wa-arsalnāhu ilā mi-ati alfin aw yazīdūna

Hausa Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).

Verse 148

فَـَٔامَنُوا۟ فَمَتَّعْنَـٰهُمْ إِلَىٰ حِينٍ

Transliteration faāmanū famattaʿnāhum ilā ḥīnin

Hausa Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.

Verse 149

فَٱسْتَفْتِهِمْ أَلِرَبِّكَ ٱلْبَنَاتُ وَلَهُمُ ٱلْبَنُونَ

Transliteration fa-is'taftihim alirabbika l-banātu walahumu l-banūna

Hausa Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"

Verse 150

أَمْ خَلَقْنَا ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ إِنَـٰثًا وَهُمْ شَـٰهِدُونَ

Transliteration am khalaqnā l-malāikata ināthan wahum shāhidūna

Hausa Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?

Verse 151

أَلَآ إِنَّهُم مِّنْ إِفْكِهِمْ لَيَقُولُونَ

Transliteration alā innahum min if'kihim layaqūlūna

Hausa To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.

Verse 152

وَلَدَ ٱللَّهُ وَإِنَّهُمْ لَكَـٰذِبُونَ

Transliteration walada l-lahu wa-innahum lakādhibūna

Hausa "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.

Verse 153

أَصْطَفَى ٱلْبَنَاتِ عَلَى ٱلْبَنِينَ

Transliteration aṣṭafā l-banāti ʿalā l-banīna

Hausa Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?

Verse 154

مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ

Transliteration mā lakum kayfa taḥkumūna

Hausa Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci)?

Verse 155

أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Transliteration afalā tadhakkarūna

Hausa Shin, bã ku tunãni?

Verse 156

أَمْ لَكُمْ سُلْطَـٰنٌ مُّبِينٌ

Transliteration am lakum sul'ṭānun mubīnun

Hausa Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?

Verse 157

فَأْتُوا۟ بِكِتَـٰبِكُمْ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ

Transliteration fatū bikitābikum in kuntum ṣādiqīna

Hausa To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.

Verse 158

وَجَعَلُوا۟ بَيْنَهُۥ وَبَيْنَ ٱلْجِنَّةِ نَسَبًا ۚ وَلَقَدْ عَلِمَتِ ٱلْجِنَّةُ إِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ

Transliteration wajaʿalū baynahu wabayna l-jinati nasaban walaqad ʿalimati l-jinatu innahum lamuḥ'ḍarūna

Hausa Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"

Verse 159

سُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ

Transliteration sub'ḥāna l-lahi ʿammā yaṣifūna

Hausa Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.

Verse 160

إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ

Transliteration illā ʿibāda l-lahi l-mukh'laṣīna

Hausa Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

Verse 161

فَإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ

Transliteration fa-innakum wamā taʿbudūna

Hausa To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,

Verse 162

مَآ أَنتُمْ عَلَيْهِ بِفَـٰتِنِينَ

Transliteration mā antum ʿalayhi bifātinīna

Hausa Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.

Verse 163

إِلَّا مَنْ هُوَ صَالِ ٱلْجَحِيمِ

Transliteration illā man huwa ṣāli l-jaḥīmi

Hausa Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.

Verse 164

وَمَا مِنَّآ إِلَّا لَهُۥ مَقَامٌ مَّعْلُومٌ

Transliteration wamā minnā illā lahu maqāmun maʿlūmun

Hausa "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne."

Verse 165

وَإِنَّا لَنَحْنُ ٱلصَّآفُّونَ

Transliteration wa-innā lanaḥnu l-ṣāfūna

Hausa "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."

Verse 166

وَإِنَّا لَنَحْنُ ٱلْمُسَبِّحُونَ

Transliteration wa-innā lanaḥnu l-musabiḥūna

Hausa "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."

Verse 167

وَإِن كَانُوا۟ لَيَقُولُونَ

Transliteration wa-in kānū layaqūlūna

Hausa Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,

Verse 168

لَوْ أَنَّ عِندَنَا ذِكْرًا مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration law anna ʿindanā dhik'ran mina l-awalīna

Hausa "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."

Verse 169

لَكُنَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ

Transliteration lakunnā ʿibāda l-lahi l-mukh'laṣīna

Hausa "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."

Verse 170

فَكَفَرُوا۟ بِهِۦ ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ

Transliteration fakafarū bihi fasawfa yaʿlamūna

Hausa Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.

Verse 171

وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration walaqad sabaqat kalimatunā liʿibādinā l-mur'salīna

Hausa Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.

Verse 172

إِنَّهُمْ لَهُمُ ٱلْمَنصُورُونَ

Transliteration innahum lahumu l-manṣūrūna

Hausa Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.

Verse 173

وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ ٱلْغَـٰلِبُونَ

Transliteration wa-inna jundanā lahumu l-ghālibūna

Hausa Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.

Verse 174

فَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ

Transliteration fatawalla ʿanhum ḥattā ḥīnin

Hausa Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.

Verse 175

وَأَبْصِرْهُمْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ

Transliteration wa-abṣir'hum fasawfa yub'ṣirūna

Hausa Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.

Verse 176

أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ

Transliteration afabiʿadhābinā yastaʿjilūna

Hausa Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?

Verse 177

فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمْ فَسَآءَ صَبَاحُ ٱلْمُنذَرِينَ

Transliteration fa-idhā nazala bisāḥatihim fasāa ṣabāḥu l-mundharīna

Hausa To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.

Verse 178

وَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ

Transliteration watawalla ʿanhum ḥattā ḥīnin

Hausa Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.

Verse 179

وَأَبْصِرْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ

Transliteration wa-abṣir fasawfa yub'ṣirūna

Hausa Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.

Verse 180

سُبْحَـٰنَ رَبِّكَ رَبِّ ٱلْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ

Transliteration sub'ḥāna rabbika rabbi l-ʿizati ʿammā yaṣifūna

Hausa Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.

Verse 181

وَسَلَـٰمٌ عَلَى ٱلْمُرْسَلِينَ

Transliteration wasalāmun ʿalā l-mur'salīna

Hausa Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.

Verse 182

وَٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration wal-ḥamdu lillahi rabbi l-ʿālamīna

Hausa Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.

Read Surah As-Saffat in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.