MyDugsiStart learning

Surah Ghafir in Hausa: translation and audio

Surah 40 · غافر · The Forgiver · 85 verses

Surah Ghafir verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Ghafir word by word in English.

Verse 1

حمٓ

Transliteration hha-meem

Hausa Ḥ. M̃.

Verse 2

تَنزِيلُ ٱلْكِتَـٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْعَلِيمِ

Transliteration tanzīlu l-kitābi mina l-lahi l-ʿazīzi l-ʿalīmi

Hausa Saukar da Littãfi daga Allah ne, Mabuwãyi, Masani.

Verse 3

غَافِرِ ٱلذَّنۢبِ وَقَابِلِ ٱلتَّوْبِ شَدِيدِ ٱلْعِقَابِ ذِى ٱلطَّوْلِ ۖ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ إِلَيْهِ ٱلْمَصِيرُ

Transliteration ghāfiri l-dhanbi waqābili l-tawbi shadīdi l-ʿiqābi dhī l-ṭawli lā ilāha illā huwa ilayhi l-maṣīru

Hausa Mai gãfarta zunubi kuma Mai karɓar tũba Mai tsananin azãba, Mai wadãtarwa bãbu abin bautawa fãce Shi, zuwa gare Shi makõma take.

Verse 4

مَا يُجَـٰدِلُ فِىٓ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَلَا يَغْرُرْكَ تَقَلُّبُهُمْ فِى ٱلْبِلَـٰدِ

Transliteration mā yujādilu fī āyāti l-lahi illā alladhīna kafarū falā yaghrur'ka taqallubuhum fī l-bilādi

Hausa Bãbu mai jãyayya a cikin ãyõyin Allah, fãce waɗanda suka kãfirta. Sabõda haka kada jũyãwarsu a cikin garũruwa ta rũɗe ka

Verse 5

كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَٱلْأَحْزَابُ مِنۢ بَعْدِهِمْ ۖ وَهَمَّتْ كُلُّ أُمَّةٍۭ بِرَسُولِهِمْ لِيَأْخُذُوهُ ۖ وَجَـٰدَلُوا۟ بِٱلْبَـٰطِلِ لِيُدْحِضُوا۟ بِهِ ٱلْحَقَّ فَأَخَذْتُهُمْ ۖ فَكَيْفَ كَانَ عِقَابِ

Transliteration kadhabat qablahum qawmu nūḥin wal-aḥzābu min baʿdihim wahammat kullu ummatin birasūlihim liyakhudhūhu wajādalū bil-bāṭili liyud'ḥiḍū bihi l-ḥaqa fa-akhadhtuhum fakayfa kāna ʿiqābi

Hausa Mutãnen Nũhu sun ƙaryata a gabãninsu, da ƙungiyõyin da suke a bãyansu, kuma kõwace al'umma tã yi nufi game da Manzonsu, dõmin su kãmã shi. Kuma suka yi jãyayya da ƙarya dõmin su gusar da gaskiya da ita. Sai Na kãmã su. To, yãya azãbã Ta take?

Verse 6

وَكَذَٰلِكَ حَقَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَنَّهُمْ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ

Transliteration wakadhālika ḥaqqat kalimatu rabbika ʿalā alladhīna kafarū annahum aṣḥābu l-nāri

Hausa Kuma kamar haka kalmar Ubangijinka ta wajaba a kan waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ 'yan wutã ne.

Verse 7

ٱلَّذِينَ يَحْمِلُونَ ٱلْعَرْشَ وَمَنْ حَوْلَهُۥ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَيُؤْمِنُونَ بِهِۦ وَيَسْتَغْفِرُونَ لِلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ رَبَّنَا وَسِعْتَ كُلَّ شَىْءٍ رَّحْمَةً وَعِلْمًا فَٱغْفِرْ لِلَّذِينَ تَابُوا۟ وَٱتَّبَعُوا۟ سَبِيلَكَ وَقِهِمْ عَذَابَ ٱلْجَحِيمِ

Transliteration alladhīna yaḥmilūna l-ʿarsha waman ḥawlahu yusabbiḥūna biḥamdi rabbihim wayu'minūna bihi wayastaghfirūna lilladhīna āmanū rabbanā wasiʿ'ta kulla shayin raḥmatan waʿil'man fa-igh'fir lilladhīna tābū wa-ittabaʿū sabīlaka waqihim ʿadhāba l-jaḥīmi

Hausa Waɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kẽwayenta, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, kuma sunã yin ĩmãni da Shi, kuma sunã yin istigfãri dõmin waɗanda suka yi ĩmãni, (sunã cẽwa), "Yã Ubangijinmu! Kã yalwaci dukan kõme da rahama da ilmi to Ka yi gãfara ga waɗanda suka tũba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare musu azãbar Jahĩm."

Verse 8

رَبَّنَا وَأَدْخِلْهُمْ جَنَّـٰتِ عَدْنٍ ٱلَّتِى وَعَدتَّهُمْ وَمَن صَلَحَ مِنْ ءَابَآئِهِمْ وَأَزْوَٰجِهِمْ وَذُرِّيَّـٰتِهِمْ ۚ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ

Transliteration rabbanā wa-adkhil'hum jannāti ʿadnin allatī waʿadttahum waman ṣalaḥa min ābāihim wa-azwājihim wadhurriyyātihim innaka anta l-ʿazīzu l-ḥakīmu

Hausa "Ya Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su a gidãjen Aljannar zama, wannan da Ka yi musu wa'adi, sũ da wanda ya kyautatu daga ubanninsu da mãtan aurensu da zurriyarsu. Lalle Kai, Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima."

Verse 9

وَقِهِمُ ٱلسَّيِّـَٔاتِ ۚ وَمَن تَقِ ٱلسَّيِّـَٔاتِ يَوْمَئِذٍ فَقَدْ رَحِمْتَهُۥ ۚ وَذَٰلِكَ هُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ

Transliteration waqihimu l-sayiāti waman taqi l-sayiāti yawma-idhin faqad raḥim'tahu wadhālika huwa l-fawzu l-ʿaẓīmu

Hausa "Kuma Ka tsare su daga mũnãnan ayyuka, kuma wanda Ka tsare shi daga mũnãnan ayyuka a rãnarnan, to, lalle, Ka yi masa rahama kuma wancan shi ne babban rabo mai girma."

Verse 10

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يُنَادَوْنَ لَمَقْتُ ٱللَّهِ أَكْبَرُ مِن مَّقْتِكُمْ أَنفُسَكُمْ إِذْ تُدْعَوْنَ إِلَى ٱلْإِيمَـٰنِ فَتَكْفُرُونَ

Transliteration inna alladhīna kafarū yunādawna lamaqtu l-lahi akbaru min maqtikum anfusakum idh tud'ʿawna ilā l-īmāni fatakfurūna

Hausa Lalle waɗanda suka kãfirta, anã kiran su, "Haƙĩƙa, ƙin Allah (a gare ku) shĩ ne mafi girma daga ƙinku ga kanku a lõkacin da ake kiran ku zuwa ga ĩmãni, sai kunã ta kãfircẽwa."

Verse 11

قَالُوا۟ رَبَّنَآ أَمَتَّنَا ٱثْنَتَيْنِ وَأَحْيَيْتَنَا ٱثْنَتَيْنِ فَٱعْتَرَفْنَا بِذُنُوبِنَا فَهَلْ إِلَىٰ خُرُوجٍ مِّن سَبِيلٍ

Transliteration qālū rabbanā amattanā ith'natayni wa-aḥyaytanā ith'natayni fa-iʿ'tarafnā bidhunūbinā fahal ilā khurūjin min sabīlin

Hausa Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Kã matar da mu sau biyu, kuma Kã rãyar da mu sau biyu, sabõda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga fita?"

Verse 12

ذَٰلِكُم بِأَنَّهُۥٓ إِذَا دُعِىَ ٱللَّهُ وَحْدَهُۥ كَفَرْتُمْ ۖ وَإِن يُشْرَكْ بِهِۦ تُؤْمِنُوا۟ ۚ فَٱلْحُكْمُ لِلَّهِ ٱلْعَلِىِّ ٱلْكَبِيرِ

Transliteration dhālikum bi-annahu idhā duʿiya l-lahu waḥdahu kafartum wa-in yush'rak bihi tu'minū fal-ḥuk'mu lillahi l-ʿaliyi l-kabīri

Hausa Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirãyi Allah Shi kaɗai, sai ku kãfirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi ĩmãni. To, hukuncin fa, na Allah Maɗaukaki, Mai girma ne.

Verse 13

هُوَ ٱلَّذِى يُرِيكُمْ ءَايَـٰتِهِۦ وَيُنَزِّلُ لَكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ رِزْقًا ۚ وَمَا يَتَذَكَّرُ إِلَّا مَن يُنِيبُ

Transliteration huwa alladhī yurīkum āyātihi wayunazzilu lakum mina l-samāi riz'qan wamā yatadhakkaru illā man yunību

Hausa Shĩ ne Wanda ke nũna muku ãyõyin Sa, kuma Ya saukar da arziki daga sama sabõda ku, kuma bãbu mai yin tunãni fãce mai mayar da al'amari ga Allah.

Verse 14

فَٱدْعُوا۟ ٱللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ ٱلْكَـٰفِرُونَ

Transliteration fa-id'ʿū l-laha mukh'liṣīna lahu l-dīna walaw kariha l-kāfirūna

Hausa Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi.

Verse 15

رَفِيعُ ٱلدَّرَجَـٰتِ ذُو ٱلْعَرْشِ يُلْقِى ٱلرُّوحَ مِنْ أَمْرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ لِيُنذِرَ يَوْمَ ٱلتَّلَاقِ

Transliteration rafīʿu l-darajāti dhū l-ʿarshi yul'qī l-rūḥa min amrihi ʿalā man yashāu min ʿibādihi liyundhira yawma l-talāqi

Hausa Mai ɗaukaka darajõji (dõmin mũminai), Mai Al'arshi, Yanã jẽfa rũhi daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bãyinSa, dõmin ya yi gargaɗi kan rãnar gamuwa.

Verse 16

يَوْمَ هُم بَـٰرِزُونَ ۖ لَا يَخْفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِنْهُمْ شَىْءٌ ۚ لِّمَنِ ٱلْمُلْكُ ٱلْيَوْمَ ۖ لِلَّهِ ٱلْوَٰحِدِ ٱلْقَهَّارِ

Transliteration yawma hum bārizūna lā yakhfā ʿalā l-lahi min'hum shayon limani l-mul'ku l-yawma lillahi l-wāḥidi l-qahāri

Hausa Rãnar da suke bayyanannu, bãbu wani abu daga gare su wanda yake iya bõyuwa ga Allah. "Mulki ga wa ya ke a yau?" Yana ga Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.

Verse 17

ٱلْيَوْمَ تُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍۭ بِمَا كَسَبَتْ ۚ لَا ظُلْمَ ٱلْيَوْمَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلْحِسَابِ

Transliteration al-yawma tuj'zā kullu nafsin bimā kasabat lā ẓul'ma l-yawma inna l-laha sarīʿu l-ḥisābi

Hausa Yau anã sãka wa kõwane rai a game da abin da ya aikata, bãbu zãlunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisãbi ne.

Verse 18

وَأَنذِرْهُمْ يَوْمَ ٱلْـَٔازِفَةِ إِذِ ٱلْقُلُوبُ لَدَى ٱلْحَنَاجِرِ كَـٰظِمِينَ ۚ مَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنْ حَمِيمٍ وَلَا شَفِيعٍ يُطَاعُ

Transliteration wa-andhir'hum yawma l-āzifati idhi l-qulūbu ladā l-ḥanājiri kāẓimīna mā lilẓẓālimīna min ḥamīmin walā shafīʿin yuṭāʿu

Hausa Kuma ka yi musu gargaɗi kan rãnar (Sã'a) makusanciya, a lõkacin da zukãta suke mãsu cika da bakin ciki, ga maƙõsansu. Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a (ga cẽtonsu).

Verse 19

يَعْلَمُ خَآئِنَةَ ٱلْأَعْيُنِ وَمَا تُخْفِى ٱلصُّدُورُ

Transliteration yaʿlamu khāinata l-aʿyuni wamā tukh'fī l-ṣudūru

Hausa (Allah) Ya san yaudarar idãnu da abin da ƙirãza ke ɓõyẽwa.

Verse 20

وَٱللَّهُ يَقْضِى بِٱلْحَقِّ ۖ وَٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَقْضُونَ بِشَىْءٍ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْبَصِيرُ

Transliteration wal-lahu yaqḍī bil-ḥaqi wa-alladhīna yadʿūna min dūnihi lā yaqḍūna bishayin inna l-laha huwa l-samīʿu l-baṣīru

Hausa Kuma Allah Shĩ ke yin hukunci da gaskiya, waɗannan da kuke kira, wanin Sa, bã su yin hukunci da kõme. Lalle Allah, Shĩ ne Mai ji, Mai gani.

Verse 21

۞ أَوَلَمْ يَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَيَنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ كَانُوا۟ مِن قَبْلِهِمْ ۚ كَانُوا۟ هُمْ أَشَدَّ مِنْهُمْ قُوَّةً وَءَاثَارًا فِى ٱلْأَرْضِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمْ وَمَا كَانَ لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٍ

Transliteration awalam yasīrū fī l-arḍi fayanẓurū kayfa kāna ʿāqibatu alladhīna kānū min qablihim kānū hum ashadda min'hum quwwatan waāthāran fī l-arḍi fa-akhadhahumu l-lahu bidhunūbihim wamā kāna lahum mina l-lahi min wāqin

Hausa Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba ga yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninsu ta zama? Sun kasance sũ ne mafi tsananin ƙarfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasã, sai Allah Ya kãmã su da laifuffukansu. Kuma bã su da wani mai tsarẽwa daga Allah.

Verse 22

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَانَت تَّأْتِيهِمْ رُسُلُهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَكَفَرُوا۟ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ ۚ إِنَّهُۥ قَوِىٌّ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ

Transliteration dhālika bi-annahum kānat tatīhim rusuluhum bil-bayināti fakafarū fa-akhadhahumu l-lahu innahu qawiyyun shadīdu l-ʿiqābi

Hausa Wancan sababinsa, dõmin sũ Manzanninsu sun kasance sunã zuwa gare su da hujjõji bayyanannu, sai suka kãfirta, sai Allah Ya kãmã su. Lalle Shĩ Mai ƙarfi ne, Mai tsananin azãba.

Verse 23

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَـٰتِنَا وَسُلْطَـٰنٍ مُّبِينٍ

Transliteration walaqad arsalnā mūsā biāyātinā wasul'ṭānin mubīnin

Hausa Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã a game da ãyõyinMu da wani dalĩli bayyananne.

Verse 24

إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَهَـٰمَـٰنَ وَقَـٰرُونَ فَقَالُوا۟ سَـٰحِرٌ كَذَّابٌ

Transliteration ilā fir'ʿawna wahāmāna waqārūna faqālū sāḥirun kadhābun

Hausa Zuwa ga Fir'auna da Hãmãna da Kãrũna, sai suka ce: "Mai sihiri ne, maƙaryaci."

Verse 25

فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلْحَقِّ مِنْ عِندِنَا قَالُوا۟ ٱقْتُلُوٓا۟ أَبْنَآءَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَعَهُۥ وَٱسْتَحْيُوا۟ نِسَآءَهُمْ ۚ وَمَا كَيْدُ ٱلْكَـٰفِرِينَ إِلَّا فِى ضَلَـٰلٍ

Transliteration falammā jāahum bil-ḥaqi min ʿindinā qālū uq'tulū abnāa alladhīna āmanū maʿahu wa-is'taḥyū nisāahum wamā kaydu l-kāfirīna illā fī ḍalālin

Hausa Sa'an nan, a lõkacin da ya jẽ musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce: "Ku kashe ɗiyan waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, kuma ku rãyar da mãtansu." Kuma mugun shirin kãfirai, bai zama ba fãce a cikin bata.

Verse 26

وَقَالَ فِرْعَوْنُ ذَرُونِىٓ أَقْتُلْ مُوسَىٰ وَلْيَدْعُ رَبَّهُۥٓ ۖ إِنِّىٓ أَخَافُ أَن يُبَدِّلَ دِينَكُمْ أَوْ أَن يُظْهِرَ فِى ٱلْأَرْضِ ٱلْفَسَادَ

Transliteration waqāla fir'ʿawnu dharūnī aqtul mūsā walyadʿu rabbahu innī akhāfu an yubaddila dīnakum aw an yuẓ'hira fī l-arḍi l-fasāda

Hausa Kuma Fir'auna ya ce: "Ku bar ni in kashe Mũsã, kuma shĩ, ya kirãyi Ubangijinsa. Lalle ne nĩ, inã tsõron ya musanya addininku, kõ kuwa ya bayyana ɓarna a cikin kasã."

Verse 27

وَقَالَ مُوسَىٰٓ إِنِّى عُذْتُ بِرَبِّى وَرَبِّكُم مِّن كُلِّ مُتَكَبِّرٍ لَّا يُؤْمِنُ بِيَوْمِ ٱلْحِسَابِ

Transliteration waqāla mūsā innī ʿudh'tu birabbī warabbikum min kulli mutakabbirin lā yu'minu biyawmi l-ḥisābi

Hausa Kuma Mũsã ya ce: "Lalle nĩ, nã nẽmi tsari da Ubangijĩna kuma Ubangijinku, daga dukan makangari, wanda bã ya ĩmani da rãnar Hisãbi."

Verse 28

وَقَالَ رَجُلٌ مُّؤْمِنٌ مِّنْ ءَالِ فِرْعَوْنَ يَكْتُمُ إِيمَـٰنَهُۥٓ أَتَقْتُلُونَ رَجُلًا أَن يَقُولَ رَبِّىَ ٱللَّهُ وَقَدْ جَآءَكُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ مِن رَّبِّكُمْ ۖ وَإِن يَكُ كَـٰذِبًا فَعَلَيْهِ كَذِبُهُۥ ۖ وَإِن يَكُ صَادِقًا يُصِبْكُم بَعْضُ ٱلَّذِى يَعِدُكُمْ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى مَنْ هُوَ مُسْرِفٌ كَذَّابٌ

Transliteration waqāla rajulun mu'minun min āli fir'ʿawna yaktumu īmānahu ataqtulūna rajulan an yaqūla rabbiya l-lahu waqad jāakum bil-bayināti min rabbikum wa-in yaku kādhiban faʿalayhi kadhibuhu wa-in yaku ṣādiqan yuṣib'kum baʿḍu alladhī yaʿidukum inna l-laha lā yahdī man huwa mus'rifun kadhābun

Hausa Kuma wani namiji mũmini daga dangin Fir'auna, yanã bõye ĩmãninsa, ya ce: "Ashe, za ku kashe mutum dõmin ya ce Ubangijina Allah ne, alhãli kuwa haƙĩƙa ya zo muku da hujjõji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan yã kasance maƙaryaci ne, to, ƙaryarsa na kansa, kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, sãshen abin da yake yi muku wa'adi zai sãme ku. Lalle ne Allah bã Ya shiryar da wanda yake mai barna, mai yawan ƙarya."

Verse 29

يَـٰقَوْمِ لَكُمُ ٱلْمُلْكُ ٱلْيَوْمَ ظَـٰهِرِينَ فِى ٱلْأَرْضِ فَمَن يَنصُرُنَا مِنۢ بَأْسِ ٱللَّهِ إِن جَآءَنَا ۚ قَالَ فِرْعَوْنُ مَآ أُرِيكُمْ إِلَّا مَآ أَرَىٰ وَمَآ أَهْدِيكُمْ إِلَّا سَبِيلَ ٱلرَّشَادِ

Transliteration yāqawmi lakumu l-mul'ku l-yawma ẓāhirīna fī l-arḍi faman yanṣurunā min basi l-lahi in jāanā qāla fir'ʿawnu mā urīkum illā mā arā wamā ahdīkum illā sabīla l-rashādi

Hausa "Yã kũ mutãnẽna! Kunã da mulki a yau, kuma kũ ne marinjãya a cikin kasã to wãne ne zai taimake mu daga azãbar Allah idan ta zo mana?" Fir'auna ya ce: "Bã ni nũnamuku kõme face abin da na gani, kuma ba ni shiryar da ku, sai ga hanyar shiryuwa."

Verse 30

وَقَالَ ٱلَّذِىٓ ءَامَنَ يَـٰقَوْمِ إِنِّىٓ أَخَافُ عَلَيْكُم مِّثْلَ يَوْمِ ٱلْأَحْزَابِ

Transliteration waqāla alladhī āmana yāqawmi innī akhāfu ʿalaykum mith'la yawmi l-aḥzābi

Hausa Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: "Ya mutãnẽnã! Lallene, nĩ, inã yi muku tsõron kwatankwacin rãnar ƙungiyõyi."

Verse 31

مِثْلَ دَأْبِ قَوْمِ نُوحٍ وَعَادٍ وَثَمُودَ وَٱلَّذِينَ مِنۢ بَعْدِهِمْ ۚ وَمَا ٱللَّهُ يُرِيدُ ظُلْمًا لِّلْعِبَادِ

Transliteration mith'la dabi qawmi nūḥin waʿādin wathamūda wa-alladhīna min baʿdihim wamā l-lahu yurīdu ẓul'man lil'ʿibādi

Hausa "Kwatankwacin al'adar mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da waɗanda ke a bãyansu. Kuma Allah bã Ya nufin zãlunci ga bãyin Sa."

Verse 32

وَيَـٰقَوْمِ إِنِّىٓ أَخَافُ عَلَيْكُمْ يَوْمَ ٱلتَّنَادِ

Transliteration wayāqawmi innī akhāfu ʿalaykum yawma l-tanādi

Hausa "Kuma ya mutãnẽna! Lallenĩ, inã yi muku tsõron rãnar kiran jũna."

Verse 33

يَوْمَ تُوَلُّونَ مُدْبِرِينَ مَا لَكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنْ عَاصِمٍ ۗ وَمَن يُضْلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنْ هَادٍ

Transliteration yawma tuwallūna mud'birīna mā lakum mina l-lahi min ʿāṣimin waman yuḍ'lili l-lahu famā lahu min hādin

Hausa "A rãnar da zã ku jũya, kunã mãsu bãyar da bãya (gudãne) bã ku da wani mai tsaro daga Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa."

Verse 34

وَلَقَدْ جَآءَكُمْ يُوسُفُ مِن قَبْلُ بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَمَا زِلْتُمْ فِى شَكٍّ مِّمَّا جَآءَكُم بِهِۦ ۖ حَتَّىٰٓ إِذَا هَلَكَ قُلْتُمْ لَن يَبْعَثَ ٱللَّهُ مِنۢ بَعْدِهِۦ رَسُولًا ۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَنْ هُوَ مُسْرِفٌ مُّرْتَابٌ

Transliteration walaqad jāakum yūsufu min qablu bil-bayināti famā zil'tum fī shakkin mimmā jāakum bihi ḥattā idhā halaka qul'tum lan yabʿatha l-lahu min baʿdihi rasūlan kadhālika yuḍillu l-lahu man huwa mus'rifun mur'tābun

Hausa "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Yusufu ya zo muku daga gabãni, da hujjõji bayyanannu, ba ku gushe ba kunã a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lõkacin da ya halaka kuka ce, 'Allah bã zai aiko wani Manzo ba, a bãyansa.' Kamar haka Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka."

Verse 35

ٱلَّذِينَ يُجَـٰدِلُونَ فِىٓ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ بِغَيْرِ سُلْطَـٰنٍ أَتَىٰهُمْ ۖ كَبُرَ مَقْتًا عِندَ ٱللَّهِ وَعِندَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ۚ كَذَٰلِكَ يَطْبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ قَلْبِ مُتَكَبِّرٍ جَبَّارٍ

Transliteration alladhīna yujādilūna fī āyāti l-lahi bighayri sul'ṭānin atāhum kabura maqtan ʿinda l-lahi waʿinda alladhīna āmanū kadhālika yaṭbaʿu l-lahu ʿalā kulli qalbi mutakabbirin jabbārin

Hausa "Waɗanda kejayayya a cikin ãyõyin Allah, bã da wani dalĩli da ya zo musu ba. Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi ĩmãni. Kamar haka Allah ke bicẽwar haske a kan zũciyar dukan makangari, mai tĩlastãwa."

Verse 36

وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَـٰهَـٰمَـٰنُ ٱبْنِ لِى صَرْحًا لَّعَلِّىٓ أَبْلُغُ ٱلْأَسْبَـٰبَ

Transliteration waqāla fir'ʿawnu yāhāmānu ib'ni lī ṣarḥan laʿallī ablughu l-asbāba

Hausa Kuma Fir'auna ye ce, "Yã Hãmana! Ka gina mini bẽne, dammãnĩna zã ni isa ga ƙõfõfi."

Verse 37

أَسْبَـٰبَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ فَأَطَّلِعَ إِلَىٰٓ إِلَـٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّى لَأَظُنُّهُۥ كَـٰذِبًا ۚ وَكَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِفِرْعَوْنَ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ وَصُدَّ عَنِ ٱلسَّبِيلِ ۚ وَمَا كَيْدُ فِرْعَوْنَ إِلَّا فِى تَبَابٍ

Transliteration asbāba l-samāwāti fa-aṭṭaliʿa ilā ilāhi mūsā wa-innī la-aẓunnuhu kādhiban wakadhālika zuyyina lifir'ʿawna sūu ʿamalihi waṣudda ʿani l-sabīli wamā kaydu fir'ʿawna illā fī tabābin

Hausa "¡õfõfin sammai dõmin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautãwar Mũsã. Kuma lalle nĩ haƙĩƙa inã zaton sa maƙaryaci." Kuma haka dai aka ƙawãce wa Fir'auna mũnãnan aikinsa kuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir'auna bai zama ba fãce yanã a cikin hasãra."

Verse 38

وَقَالَ ٱلَّذِىٓ ءَامَنَ يَـٰقَوْمِ ٱتَّبِعُونِ أَهْدِكُمْ سَبِيلَ ٱلرَّشَادِ

Transliteration waqāla alladhī āmana yāqawmi ittabiʿūni ahdikum sabīla l-rashādi

Hausa Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bĩ ni, in shiryar da ku tafarkin shiryuwa."

Verse 39

يَـٰقَوْمِ إِنَّمَا هَـٰذِهِ ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا مَتَـٰعٌ وَإِنَّ ٱلْـَٔاخِرَةَ هِىَ دَارُ ٱلْقَرَارِ

Transliteration yāqawmi innamā hādhihi l-ḥayatu l-dun'yā matāʿun wa-inna l-ākhirata hiya dāru l-qarāri

Hausa "Kuma ya mutãnẽna! Wannan rãyuwa ta dũniya dan jin dãɗi ne kawai, kuma lalle Lãhira ita ce gidan tabbata."

Verse 40

مَنْ عَمِلَ سَيِّئَةً فَلَا يُجْزَىٰٓ إِلَّا مِثْلَهَا ۖ وَمَنْ عَمِلَ صَـٰلِحًا مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ يَدْخُلُونَ ٱلْجَنَّةَ يُرْزَقُونَ فِيهَا بِغَيْرِ حِسَابٍ

Transliteration man ʿamila sayyi-atan falā yuj'zā illā mith'lahā waman ʿamila ṣāliḥan min dhakarin aw unthā wahuwa mu'minun fa-ulāika yadkhulūna l-janata yur'zaqūna fīhā bighayri ḥisābin

Hausa "Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a sãka masa ba fãce da misãlinsa, kuma wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ mace alhãli kuwa shĩ mũmini ne, to, waɗannan sunã shiga Aljanna, anã ciyar da su a cikinta, bã da lissãfi ba."

Verse 41

۞ وَيَـٰقَوْمِ مَا لِىٓ أَدْعُوكُمْ إِلَى ٱلنَّجَوٰةِ وَتَدْعُونَنِىٓ إِلَى ٱلنَّارِ

Transliteration wayāqawmi mā lī adʿūkum ilā l-najati watadʿūnanī ilā l-nāri

Hausa "Kuma ya mutãnẽna! Me ya sãme ni, inã kiran ku zuwa ga tsĩra, kuma kunã kira na zuwa ga wutã?"

Verse 42

تَدْعُونَنِى لِأَكْفُرَ بِٱللَّهِ وَأُشْرِكَ بِهِۦ مَا لَيْسَ لِى بِهِۦ عِلْمٌ وَأَنَا۠ أَدْعُوكُمْ إِلَى ٱلْعَزِيزِ ٱلْغَفَّـٰرِ

Transliteration tadʿūnanī li-akfura bil-lahi wa-ush'rika bihi mā laysa lī bihi ʿil'mun wa-anā adʿūkum ilā l-ʿazīzi l-ghafāri

Hausa "Kuna kira na zuwa ga in kãfirta da Allah, kuma in yi shirki, game da Shi, da abin da bãbu wani ilmi game da shi gare ni, kuma ni inã kiran ku zuwa ga Mabuwãyi, Mai gãfara."

Verse 43

لَا جَرَمَ أَنَّمَا تَدْعُونَنِىٓ إِلَيْهِ لَيْسَ لَهُۥ دَعْوَةٌ فِى ٱلدُّنْيَا وَلَا فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ وَأَنَّ مَرَدَّنَآ إِلَى ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلْمُسْرِفِينَ هُمْ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ

Transliteration lā jarama annamā tadʿūnanī ilayhi laysa lahu daʿwatun fī l-dun'yā walā fī l-ākhirati wa-anna maraddanā ilā l-lahi wa-anna l-mus'rifīna hum aṣḥābu l-nāri

Hausa "Haƙƙan ne abin da kawai kuke kira na zuwa gare shi, bã ya da wani kira a cikin dũniya, kuma bã shi da shi a Lãhira kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah take, kuma lalle mabarnata sũ ne 'yan wutã."

Verse 44

فَسَتَذْكُرُونَ مَآ أَقُولُ لَكُمْ ۚ وَأُفَوِّضُ أَمْرِىٓ إِلَى ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَصِيرٌۢ بِٱلْعِبَادِ

Transliteration fasatadhkurūna mā aqūlu lakum wa-ufawwiḍu amrī ilā l-lahi inna l-laha baṣīrun bil-ʿibādi

Hausa "To zã ku ambaci abin da nake gaya muku, kuma inã fawwala al'amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai gani ne ga bãyin Sa."

Verse 45

فَوَقَىٰهُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِ مَا مَكَرُوا۟ ۖ وَحَاقَ بِـَٔالِ فِرْعَوْنَ سُوٓءُ ٱلْعَذَابِ

Transliteration fawaqāhu l-lahu sayyiāti mā makarū waḥāqa biāli fir'ʿawna sūu l-ʿadhābi

Hausa Sai Allah Ya tsare shi daga mũnãnan abũbuwa da suka yi na mãkirci, kuma mummunar azãba ta wajaba ga mutãnen Fir'auna.

Verse 46

ٱلنَّارُ يُعْرَضُونَ عَلَيْهَا غُدُوًّا وَعَشِيًّا ۖ وَيَوْمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ أَدْخِلُوٓا۟ ءَالَ فِرْعَوْنَ أَشَدَّ ٱلْعَذَابِ

Transliteration al-nāru yuʿ'raḍūna ʿalayhā ghuduwwan waʿashiyyan wayawma taqūmu l-sāʿatu adkhilū āla fir'ʿawna ashadda l-ʿadhābi

Hausa Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cẽwa, "Ku shigar da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba."

Verse 47

وَإِذْ يَتَحَآجُّونَ فِى ٱلنَّارِ فَيَقُولُ ٱلضُّعَفَـٰٓؤُا۟ لِلَّذِينَ ٱسْتَكْبَرُوٓا۟ إِنَّا كُنَّا لَكُمْ تَبَعًا فَهَلْ أَنتُم مُّغْنُونَ عَنَّا نَصِيبًا مِّنَ ٱلنَّارِ

Transliteration wa-idh yataḥājjūna fī l-nāri fayaqūlu l-ḍuʿafāu lilladhīna is'takbarū innā kunnā lakum tabaʿan fahal antum mugh'nūna ʿannā naṣīban mina l-nāri

Hausa Kuma a lõkacin da suke husũma a cikin wutã, sai raunãna (mabiya) su ce wa waɗanda suka kangara (shugabanni), "Lalle mũ, mun kasance mabiya gare ku, to, shin kũ mãsu wadãtar da mu ne daga barin wani rabo daga wutã?"

Verse 48

قَالَ ٱلَّذِينَ ٱسْتَكْبَرُوٓا۟ إِنَّا كُلٌّ فِيهَآ إِنَّ ٱللَّهَ قَدْ حَكَمَ بَيْنَ ٱلْعِبَادِ

Transliteration qāla alladhīna is'takbarū innā kullun fīhā inna l-laha qad ḥakama bayna l-ʿibādi

Hausa Waɗanda suka kangara suka ce: "Lalle mũ duka munã a cikinta. Lalle ne, Allah Ya yi hukunci a tsakãnin bãyin Sa."

Verse 49

وَقَالَ ٱلَّذِينَ فِى ٱلنَّارِ لِخَزَنَةِ جَهَنَّمَ ٱدْعُوا۟ رَبَّكُمْ يُخَفِّفْ عَنَّا يَوْمًا مِّنَ ٱلْعَذَابِ

Transliteration waqāla alladhīna fī l-nāri likhazanati jahannama id'ʿū rabbakum yukhaffif ʿannā yawman mina l-ʿadhābi

Hausa Kuma waɗanda suke a cikin wutã suka ce wa matsaran Jahannama, "Ku rõki Ubangijinku Ya sauƙaƙa mana, a yini ɗaya, daga azãba."

Verse 50

قَالُوٓا۟ أَوَلَمْ تَكُ تَأْتِيكُمْ رُسُلُكُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ ۖ قَالُوا۟ بَلَىٰ ۚ قَالُوا۟ فَٱدْعُوا۟ ۗ وَمَا دُعَـٰٓؤُا۟ ٱلْكَـٰفِرِينَ إِلَّا فِى ضَلَـٰلٍ

Transliteration qālū awalam taku tatīkum rusulukum bil-bayināti qālū balā qālū fa-id'ʿū wamā duʿāu l-kāfirīna illā fī ḍalālin

Hausa Suka ce: "Ashe, Manzanninku ba su jẽ muku da hujjõji bayyanannu ba?" Suka ce: "Na'am, sun jẽ!" Suka ce: "To, ku rõƙa." Kuma rõƙon kãfirai bai zamo ba fãce a cikin ɓata.

Verse 51

إِنَّا لَنَنصُرُ رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَيَوْمَ يَقُومُ ٱلْأَشْهَـٰدُ

Transliteration innā lananṣuru rusulanā wa-alladhīna āmanū fī l-ḥayati l-dun'yā wayawma yaqūmu l-ashhādu

Hausa Lalle Mũ, hakĩka, Munã taimakon ManzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, a cikin rãyuwar dũniya da rãnar da shaidu ke tsayãwa.

Verse 52

يَوْمَ لَا يَنفَعُ ٱلظَّـٰلِمِينَ مَعْذِرَتُهُمْ ۖ وَلَهُمُ ٱللَّعْنَةُ وَلَهُمْ سُوٓءُ ٱلدَّارِ

Transliteration yawma lā yanfaʿu l-ẓālimīna maʿdhiratuhum walahumu l-laʿnatu walahum sūu l-dāri

Hausa Rãnar da uzurin azzãlumai bã ya amfãninsu, kuma sunã da la'ana, kuma sunã da mũnin gida.

Verse 53

وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْهُدَىٰ وَأَوْرَثْنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱلْكِتَـٰبَ

Transliteration walaqad ātaynā mūsā l-hudā wa-awrathnā banī is'rāīla l-kitāba

Hausa Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã shiriya, kuma Mun gãdar da Banĩ Isrã'ĩla Littãfi.

Verse 54

هُدًى وَذِكْرَىٰ لِأُو۟لِى ٱلْأَلْبَـٰبِ

Transliteration hudan wadhik'rā li-ulī l-albābi

Hausa Shiryarwa da tunãwa ga ma'abũta hankali.

Verse 55

فَٱصْبِرْ إِنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّ وَٱسْتَغْفِرْ لِذَنۢبِكَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ بِٱلْعَشِىِّ وَٱلْإِبْكَـٰرِ

Transliteration fa-iṣ'bir inna waʿda l-lahi ḥaqqun wa-is'taghfir lidhanbika wasabbiḥ biḥamdi rabbika bil-ʿashiyi wal-ib'kāri

Hausa Sabõda haka, ka yi haƙuri, lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Kuma ka nẽmi gãfara ga zunubinka, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, maraice da kuma wãyẽwar sãfiya.

Verse 56

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُجَـٰدِلُونَ فِىٓ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ بِغَيْرِ سُلْطَـٰنٍ أَتَىٰهُمْ ۙ إِن فِى صُدُورِهِمْ إِلَّا كِبْرٌ مَّا هُم بِبَـٰلِغِيهِ ۚ فَٱسْتَعِذْ بِٱللَّهِ ۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْبَصِيرُ

Transliteration inna alladhīna yujādilūna fī āyāti l-lahi bighayri sul'ṭānin atāhum in fī ṣudūrihim illā kib'run mā hum bibālighīhi fa-is'taʿidh bil-lahi innahu huwa l-samīʿu l-baṣīru

Hausa Lalle waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, bã game da wani dalĩli wanda ya jẽ musu ba, bãbu kõme a cikin kirãzansu, fãce girman kai, ba su zama mãsu isa ga gũrinsu ba, sabõda haka ka nẽmi tsari daga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Mai gani.

Verse 57

لَخَلْقُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ أَكْبَرُ مِنْ خَلْقِ ٱلنَّاسِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration lakhalqu l-samāwāti wal-arḍi akbaru min khalqi l-nāsi walākinna akthara l-nāsi lā yaʿlamūna

Hausa Lalle halittar sammai da ƙasã, ita ce mafi girma daga halittar mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.

Verse 58

وَمَا يَسْتَوِى ٱلْأَعْمَىٰ وَٱلْبَصِيرُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَلَا ٱلْمُسِىٓءُ ۚ قَلِيلًا مَّا تَتَذَكَّرُونَ

Transliteration wamā yastawī l-aʿmā wal-baṣīru wa-alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti walā l-musīu qalīlan mā tatadhakkarūna

Hausa Kuma makãho da mai gani bã su daidaita kuma waɗanda suka yi ĩmãni suka, aikata ayyukan ƙwarai da mai mũnanãwa bã su daidaita. Kaɗan ƙwarai, kuke yin tunãni.

Verse 59

إِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَـَٔاتِيَةٌ لَّا رَيْبَ فِيهَا وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤْمِنُونَ

Transliteration inna l-sāʿata laātiyatun lā rayba fīhā walākinna akthara l-nāsi lā yu'minūna

Hausa Lalle Sa'a, haƙĩƙa mai zuwa ce, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni.

Verse 60

وَقَالَ رَبُّكُمُ ٱدْعُونِىٓ أَسْتَجِبْ لَكُمْ ۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِى سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ

Transliteration waqāla rabbukumu id'ʿūnī astajib lakum inna alladhīna yastakbirūna ʿan ʿibādatī sayadkhulūna jahannama dākhirīna

Hausa Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu."

Verse 61

ٱللَّهُ ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيْلَ لِتَسْكُنُوا۟ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبْصِرًا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشْكُرُونَ

Transliteration al-lahu alladhī jaʿala lakumu al-layla litaskunū fīhi wal-nahāra mub'ṣiran inna l-laha ladhū faḍlin ʿalā l-nāsi walākinna akthara l-nāsi lā yashkurūna

Hausa Allah ne Wanda Ya sanya muku dare dõmin ku natsu a cikinsa, da rãna mai gãnarwa. Lalle Allah, haƙĩƙa, Ma'abũcin falala ne a kan mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa.

Verse 62

ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمْ خَـٰلِقُ كُلِّ شَىْءٍ لَّآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ فَأَنَّىٰ تُؤْفَكُونَ

Transliteration dhālikumu l-lahu rabbukum khāliqu kulli shayin lā ilāha illā huwa fa-annā tu'fakūna

Hausa Wancan shine Allah Ubangijinku, Mahaliccin dukan kõme, bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?

Verse 63

كَذَٰلِكَ يُؤْفَكُ ٱلَّذِينَ كَانُوا۟ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ يَجْحَدُونَ

Transliteration kadhālika yu'faku alladhīna kānū biāyāti l-lahi yajḥadūna

Hausa Kamar haka ake karkatar da waɗanda suka kasance sunã jãyayya game da ãyõyin Allah.

Verse 64

ٱللَّهُ ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ قَرَارًا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءً وَصَوَّرَكُمْ فَأَحْسَنَ صُوَرَكُمْ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَـٰتِ ۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمْ ۖ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration al-lahu alladhī jaʿala lakumu l-arḍa qarāran wal-samāa bināan waṣawwarakum fa-aḥsana ṣuwarakum warazaqakum mina l-ṭayibāti dhālikumu l-lahu rabbukum fatabāraka l-lahu rabbu l-ʿālamīna

Hausa Allah ne Ya sanya muku kasã tabbatacciya, da sama ginanniya, kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku,, kuma Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana.

Verse 65

هُوَ ٱلْحَىُّ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱدْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ ۗ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration huwa l-ḥayu lā ilāha illā huwa fa-id'ʿūhu mukh'liṣīna lahu l-dīna l-ḥamdu lillahi rabbi l-ʿālamīna

Hausa Shĩ ne Mai rai, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Sabõda haka ku kira Shi, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi. Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.

Verse 66

۞ قُلْ إِنِّى نُهِيتُ أَنْ أَعْبُدَ ٱلَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَمَّا جَآءَنِىَ ٱلْبَيِّنَـٰتُ مِن رَّبِّى وَأُمِرْتُ أَنْ أُسْلِمَ لِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration qul innī nuhītu an aʿbuda alladhīna tadʿūna min dūni l-lahi lammā jāaniya l-bayinātu min rabbī wa-umir'tu an us'lima lirabbi l-ʿālamīna

Hausa Ka ce: "Lalle nĩ, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a lõkacin da hujjõji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in sallama ga Ubangijin halittu."

Verse 67

هُوَ ٱلَّذِى خَلَقَكُم مِّن تُرَابٍ ثُمَّ مِن نُّطْفَةٍ ثُمَّ مِنْ عَلَقَةٍ ثُمَّ يُخْرِجُكُمْ طِفْلًا ثُمَّ لِتَبْلُغُوٓا۟ أَشُدَّكُمْ ثُمَّ لِتَكُونُوا۟ شُيُوخًا ۚ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ مِن قَبْلُ ۖ وَلِتَبْلُغُوٓا۟ أَجَلًا مُّسَمًّى وَلَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ

Transliteration huwa alladhī khalaqakum min turābin thumma min nuṭ'fatin thumma min ʿalaqatin thumma yukh'rijukum ṭif'lan thumma litablughū ashuddakum thumma litakūnū shuyūkhan waminkum man yutawaffā min qablu walitablughū ajalan musamman walaʿallakum taʿqilūna

Hausa Shĩ ne Wanda Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga maniyyi, sa'an nan daga sãren jini, sa'an nan Ya fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan dõmin ku isa ga cikar ƙarfinku sa'an nan dõmin ku kasance tsõfaffi, kuma daga cikinku, akwai wanda ake karɓar ransa a gabãnin haka, kuma dõmin ku isa ga ajali ambatacce, kuma dammãninku ko zã ku hankalta.

Verse 68

هُوَ ٱلَّذِى يُحْىِۦ وَيُمِيتُ ۖ فَإِذَا قَضَىٰٓ أَمْرًا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

Transliteration huwa alladhī yuḥ'yī wayumītu fa-idhā qaḍā amran fa-innamā yaqūlu lahu kun fayakūnu

Hausa Shi ne Wanda ke rayarwa kuma Yana kashewa. To, idan Ya hukunta wani al'amari, to, Yana cewa kawai gare shi, ka kasance sai yana kasancewa (kamar yadda ake bukatar sa.)

Verse 69

أَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يُجَـٰدِلُونَ فِىٓ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ أَنَّىٰ يُصْرَفُونَ

Transliteration alam tara ilā alladhīna yujādilūna fī āyāti l-lahi annā yuṣ'rafūna

Hausa Ashe, ba ka gani ba ga waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, yadda ake karkatar da su?

Verse 70

ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِٱلْكِتَـٰبِ وَبِمَآ أَرْسَلْنَا بِهِۦ رُسُلَنَا ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ

Transliteration alladhīna kadhabū bil-kitābi wabimā arsalnā bihi rusulanā fasawfa yaʿlamūna

Hausa Waɗanda suka ƙaryata, game da Littãfin, kuma da abin da Muka aika Manzanninmu da shi. To, za su sani.

Verse 71

إِذِ ٱلْأَغْلَـٰلُ فِىٓ أَعْنَـٰقِهِمْ وَٱلسَّلَـٰسِلُ يُسْحَبُونَ

Transliteration idhi l-aghlālu fī aʿnāqihim wal-salāsilu yus'ḥabūna

Hausa A lõkacin da ƙuƙumma suke a cikin wuyõyinsu, da sarƙõƙi anã jan su.

Verse 72

فِى ٱلْحَمِيمِ ثُمَّ فِى ٱلنَّارِ يُسْجَرُونَ

Transliteration fī l-ḥamīmi thumma fī l-nāri yus'jarūna

Hausa A cikin ruwan zãfi, sa'an nan a cikin wutã anã babbaka su.

Verse 73

ثُمَّ قِيلَ لَهُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ تُشْرِكُونَ

Transliteration thumma qīla lahum ayna mā kuntum tush'rikūna

Hausa Sa'an nan a ce musu, "Ina abin da kuka kasance kunã shirki da shi"

Verse 74

مِن دُونِ ٱللَّهِ ۖ قَالُوا۟ ضَلُّوا۟ عَنَّا بَل لَّمْ نَكُن نَّدْعُوا۟ مِن قَبْلُ شَيْـًٔا ۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ ٱلْكَـٰفِرِينَ

Transliteration min dūni l-lahi qālū ḍallū ʿannā bal lam nakun nadʿū min qablu shayan kadhālika yuḍillu l-lahu l-kāfirīna

Hausa "Wanin Allah?" Suka ce: "Sun ɓace mana. Ã'a, ba mu kasance munã kiran kõme ba a gabani."Kamar wancan ne Allah Yake ɓatar da kãfirai.

Verse 75

ذَٰلِكُم بِمَا كُنتُمْ تَفْرَحُونَ فِى ٱلْأَرْضِ بِغَيْرِ ٱلْحَقِّ وَبِمَا كُنتُمْ تَمْرَحُونَ

Transliteration dhālikum bimā kuntum tafraḥūna fī l-arḍi bighayri l-ḥaqi wabimā kuntum tamraḥūna

Hausa Wancan dõmin abin da kuka kasance ne kunã farin ciki da shi, a cikin ƙasã, bã da hakki ba, kuma da abin da kuka kasance kunã yi na nishãɗi.

Verse 76

ٱدْخُلُوٓا۟ أَبْوَٰبَ جَهَنَّمَ خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۖ فَبِئْسَ مَثْوَى ٱلْمُتَكَبِّرِينَ

Transliteration ud'khulū abwāba jahannama khālidīna fīhā fabi'sa mathwā l-mutakabirīna

Hausa Ku shiga kofõfin Jahannama kunã madawwama a cikinta. To, mazaunin mãsu girman kai yã mũnana.

Verse 77

فَٱصْبِرْ إِنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّ ۚ فَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعْضَ ٱلَّذِى نَعِدُهُمْ أَوْ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيْنَا يُرْجَعُونَ

Transliteration fa-iṣ'bir inna waʿda l-lahi ḥaqqun fa-immā nuriyannaka baʿḍa alladhī naʿiduhum aw natawaffayannaka fa-ilaynā yur'jaʿūna

Hausa Sabõda haka ka yi haƙuri. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. To, kõ dai lalle Mu nũna maka sãshen abin da Muka yi musu wa'adi da shi kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu ake mayar da su.

Verse 78

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلًا مِّن قَبْلِكَ مِنْهُم مَّن قَصَصْنَا عَلَيْكَ وَمِنْهُم مَّن لَّمْ نَقْصُصْ عَلَيْكَ ۗ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأْتِىَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذْنِ ٱللَّهِ ۚ فَإِذَا جَآءَ أَمْرُ ٱللَّهِ قُضِىَ بِٱلْحَقِّ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلْمُبْطِلُونَ

Transliteration walaqad arsalnā rusulan min qablika min'hum man qaṣaṣnā ʿalayka wamin'hum man lam naqṣuṣ ʿalayka wamā kāna lirasūlin an yatiya biāyatin illā bi-idh'ni l-lahi fa-idhā jāa amru l-lahi quḍiya bil-ḥaqi wakhasira hunālika l-mub'ṭilūna

Hausa Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta lãbãrinsa ba a gare ka. Bã ya yiwuwa ga wani Manzo ya jẽ da wata ãyar mu'ujiza fãce da iznin Allah. Sa'an nan idan umurnin Allah ya jẽ, sai a yi hukunci da gaskiya, mãsu ɓãtãwa sun yi hasara a can.

Verse 79

ٱللَّهُ ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَنْعَـٰمَ لِتَرْكَبُوا۟ مِنْهَا وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ

Transliteration al-lahu alladhī jaʿala lakumu l-anʿāma litarkabū min'hā wamin'hā takulūna

Hausa Allah ne Wanda Ya sanya muku dabbõbi dõmin ku hau daga gare su, kuma daga gare su kuke ci.

Verse 80

وَلَكُمْ فِيهَا مَنَـٰفِعُ وَلِتَبْلُغُوا۟ عَلَيْهَا حَاجَةً فِى صُدُورِكُمْ وَعَلَيْهَا وَعَلَى ٱلْفُلْكِ تُحْمَلُونَ

Transliteration walakum fīhā manāfiʿu walitablughū ʿalayhā ḥājatan fī ṣudūrikum waʿalayhā waʿalā l-ful'ki tuḥ'malūna

Hausa Kuma kunã da abũbuwan amfãni a cikinsu, kuma dõmin ku isar da wata buƙãta, a cikin ƙirãzanku a kansu kuma a kansu da a kan jirãge ake, ɗaukar ku.

Verse 81

وَيُرِيكُمْ ءَايَـٰتِهِۦ فَأَىَّ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ تُنكِرُونَ

Transliteration wayurīkum āyātihi fa-ayya āyāti l-lahi tunkirūna

Hausa Kuma Ya nũna muku ayõyin Sa. To, wane ãyõyin Allah kuke musu?

Verse 82

أَفَلَمْ يَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَيَنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ كَانُوٓا۟ أَكْثَرَ مِنْهُمْ وَأَشَدَّ قُوَّةً وَءَاثَارًا فِى ٱلْأَرْضِ فَمَآ أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ

Transliteration afalam yasīrū fī l-arḍi fayanẓurū kayfa kāna ʿāqibatu alladhīna min qablihim kānū akthara min'hum wa-ashadda quwwatan waāthāran fī l-arḍi famā aghnā ʿanhum mā kānū yaksibūna

Hausa Ashe fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasã ba, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafi yawa daga gare su. Kuma sun fi tsananin ƙarfi, da (yawan) gurãbun sanã'õ'i a cikin ƙasã. To, abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su ba.

Verse 83

فَلَمَّا جَآءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَرِحُوا۟ بِمَا عِندَهُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ

Transliteration falammā jāathum rusuluhum bil-bayināti fariḥū bimā ʿindahum mina l-ʿil'mi waḥāqa bihim mā kānū bihi yastahziūna

Hausa A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi ya wajaba a kansu.

Verse 84

فَلَمَّا رَأَوْا۟ بَأْسَنَا قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَحْدَهُۥ وَكَفَرْنَا بِمَا كُنَّا بِهِۦ مُشْرِكِينَ

Transliteration falammā ra-aw basanā qālū āmannā bil-lahi waḥdahu wakafarnā bimā kunnā bihi mush'rikīna

Hausa Sa'an nan a lõkacin da suka ga azãbarMu, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, Shi kaɗai, kuma mun kãfirta da abin da muka kasance munã shirki da shi."

Verse 85

فَلَمْ يَكُ يَنفَعُهُمْ إِيمَـٰنُهُمْ لَمَّا رَأَوْا۟ بَأْسَنَا ۖ سُنَّتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِى قَدْ خَلَتْ فِى عِبَادِهِۦ ۖ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلْكَـٰفِرُونَ

Transliteration falam yaku yanfaʿuhum īmānuhum lammā ra-aw basanā sunnata l-lahi allatī qad khalat fī ʿibādihi wakhasira hunālika l-kāfirūna

Hausa To ĩmaninsu bai kasance yanã amfaninsu ba a lõkacin da suka ga azãbarMu. Hanyar Allah wadda ta gabãta a cikin bãyin Sa. Kuma kãfirai sun yi hasãra a can.

Read Surah Ghafir in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.