MyDugsiStart learning

Surah At-Tur in Hausa: translation and audio

Surah 52 · الطور · The Mount · 49 verses

Surah At-Tur verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah At-Tur word by word in English.

Verse 1

وَٱلطُّورِ

Transliteration wal-ṭūri

Hausa Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).

Verse 2

وَكِتَـٰبٍ مَّسْطُورٍ

Transliteration wakitābin masṭūrin

Hausa Da wani littãfi rubũtacce.

Verse 3

فِى رَقٍّ مَّنشُورٍ

Transliteration fī raqqin manshūrin

Hausa A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.

Verse 4

وَٱلْبَيْتِ ٱلْمَعْمُورِ

Transliteration wal-bayti l-maʿmūri

Hausa Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).

Verse 5

وَٱلسَّقْفِ ٱلْمَرْفُوعِ

Transliteration wal-saqfi l-marfūʿi

Hausa Da rufin nan da aka ɗaukaka.

Verse 6

وَٱلْبَحْرِ ٱلْمَسْجُورِ

Transliteration wal-baḥri l-masjūri

Hausa Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).

Verse 7

إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَٰقِعٌ

Transliteration inna ʿadhāba rabbika lawāqiʿun

Hausa Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.

Verse 8

مَّا لَهُۥ مِن دَافِعٍ

Transliteration mā lahu min dāfiʿin

Hausa Bã ta da mai tunkuɗẽwa.

Verse 9

يَوْمَ تَمُورُ ٱلسَّمَآءُ مَوْرًا

Transliteration yawma tamūru l-samāu mawran

Hausa Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.

Verse 10

وَتَسِيرُ ٱلْجِبَالُ سَيْرًا

Transliteration watasīru l-jibālu sayran

Hausa Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.

Verse 11

فَوَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ

Transliteration fawaylun yawma-idhin lil'mukadhibīna

Hausa To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

Verse 12

ٱلَّذِينَ هُمْ فِى خَوْضٍ يَلْعَبُونَ

Transliteration alladhīna hum fī khawḍin yalʿabūna

Hausa Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.

Verse 13

يَوْمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا

Transliteration yawma yudaʿʿūna ilā nāri jahannama daʿʿan

Hausa Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.

Verse 14

هَـٰذِهِ ٱلنَّارُ ٱلَّتِى كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ

Transliteration hādhihi l-nāru allatī kuntum bihā tukadhibūna

Hausa (A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."

Verse 15

أَفَسِحْرٌ هَـٰذَآ أَمْ أَنتُمْ لَا تُبْصِرُونَ

Transliteration afasiḥ'run hādhā am antum lā tub'ṣirūna

Hausa "To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?"

Verse 16

ٱصْلَوْهَا فَٱصْبِرُوٓا۟ أَوْ لَا تَصْبِرُوا۟ سَوَآءٌ عَلَيْكُمْ ۖ إِنَّمَا تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Transliteration iṣ'lawhā fa-iṣ'birū aw lā taṣbirū sawāon ʿalaykum innamā tuj'zawna mā kuntum taʿmalūna

Hausa "Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Verse 17

إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى جَنَّـٰتٍ وَنَعِيمٍ

Transliteration inna l-mutaqīna fī jannātin wanaʿīmin

Hausa Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima.

Verse 18

فَـٰكِهِينَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمْ رَبُّهُمْ وَوَقَىٰهُمْ رَبُّهُمْ عَذَابَ ٱلْجَحِيمِ

Transliteration fākihīna bimā ātāhum rabbuhum wawaqāhum rabbuhum ʿadhāba l-jaḥīmi

Hausa Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.

Verse 19

كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Transliteration kulū wa-ish'rabū hanīan bimā kuntum taʿmalūna

Hausa (A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Verse 20

مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ سُرُرٍ مَّصْفُوفَةٍ ۖ وَزَوَّجْنَـٰهُم بِحُورٍ عِينٍ

Transliteration muttakiīna ʿalā sururin maṣfūfatin wazawwajnāhum biḥūrin ʿīnin

Hausa Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.

Verse 21

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَٱتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَـٰنٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَمَآ أَلَتْنَـٰهُم مِّنْ عَمَلِهِم مِّن شَىْءٍ ۚ كُلُّ ٱمْرِئٍۭ بِمَا كَسَبَ رَهِينٌ

Transliteration wa-alladhīna āmanū wa-ittabaʿathum dhurriyyatuhum biīmānin alḥaqnā bihim dhurriyyatahum wamā alatnāhum min ʿamalihim min shayin kullu im'ri-in bimā kasaba rahīnun

Hausa Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.

Verse 22

وَأَمْدَدْنَـٰهُم بِفَـٰكِهَةٍ وَلَحْمٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ

Transliteration wa-amdadnāhum bifākihatin walaḥmin mimmā yashtahūna

Hausa Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari.

Verse 23

يَتَنَـٰزَعُونَ فِيهَا كَأْسًا لَّا لَغْوٌ فِيهَا وَلَا تَأْثِيمٌ

Transliteration yatanāzaʿūna fīhā kasan lā laghwun fīhā walā tathīmun

Hausa Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi.

Verse 24

۞ وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ غِلْمَانٌ لَّهُمْ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤٌ مَّكْنُونٌ

Transliteration wayaṭūfu ʿalayhim ghil'mānun lahum ka-annahum lu'lu-on maknūnun

Hausa Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.

Verse 25

وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَآءَلُونَ

Transliteration wa-aqbala baʿḍuhum ʿalā baʿḍin yatasāalūna

Hausa Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna.

Verse 26

قَالُوٓا۟ إِنَّا كُنَّا قَبْلُ فِىٓ أَهْلِنَا مُشْفِقِينَ

Transliteration qālū innā kunnā qablu fī ahlinā mush'fiqīna

Hausa Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro."

Verse 27

فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيْنَا وَوَقَىٰنَا عَذَابَ ٱلسَّمُومِ

Transliteration famanna l-lahu ʿalaynā wawaqānā ʿadhāba l-samūmi

Hausa "To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi."

Verse 28

إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلُ نَدْعُوهُ ۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْبَرُّ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration innā kunnā min qablu nadʿūhu innahu huwa l-baru l-raḥīmu

Hausa "Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama."

Verse 29

فَذَكِّرْ فَمَآ أَنتَ بِنِعْمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٍ وَلَا مَجْنُونٍ

Transliteration fadhakkir famā anta biniʿ'mati rabbika bikāhinin walā majnūnin

Hausa To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba.

Verse 30

أَمْ يَقُولُونَ شَاعِرٌ نَّتَرَبَّصُ بِهِۦ رَيْبَ ٱلْمَنُونِ

Transliteration am yaqūlūna shāʿirun natarabbaṣu bihi rayba l-manūni

Hausa Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?

Verse 31

قُلْ تَرَبَّصُوا۟ فَإِنِّى مَعَكُم مِّنَ ٱلْمُتَرَبِّصِينَ

Transliteration qul tarabbaṣū fa-innī maʿakum mina l-mutarabiṣīna

Hausa Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku."

Verse 32

أَمْ تَأْمُرُهُمْ أَحْلَـٰمُهُم بِهَـٰذَآ ۚ أَمْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ

Transliteration am tamuruhum aḥlāmuhum bihādhā am hum qawmun ṭāghūna

Hausa Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?

Verse 33

أَمْ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُۥ ۚ بَل لَّا يُؤْمِنُونَ

Transliteration am yaqūlūna taqawwalahu bal lā yu'minūna

Hausa Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba.

Verse 34

فَلْيَأْتُوا۟ بِحَدِيثٍ مِّثْلِهِۦٓ إِن كَانُوا۟ صَـٰدِقِينَ

Transliteration falyatū biḥadīthin mith'lihi in kānū ṣādiqīna

Hausa Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne.

Verse 35

أَمْ خُلِقُوا۟ مِنْ غَيْرِ شَىْءٍ أَمْ هُمُ ٱلْخَـٰلِقُونَ

Transliteration am khuliqū min ghayri shayin am humu l-khāliqūna

Hausa Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?

Verse 36

أَمْ خَلَقُوا۟ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ ۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ

Transliteration am khalaqū l-samāwāti wal-arḍa bal lā yūqinūna

Hausa Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba.

Verse 37

أَمْ عِندَهُمْ خَزَآئِنُ رَبِّكَ أَمْ هُمُ ٱلْمُصَۣيْطِرُونَ

Transliteration am ʿindahum khazāinu rabbika am humu l-muṣayṭirūna

Hausa Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?

Verse 38

أَمْ لَهُمْ سُلَّمٌ يَسْتَمِعُونَ فِيهِ ۖ فَلْيَأْتِ مُسْتَمِعُهُم بِسُلْطَـٰنٍ مُّبِينٍ

Transliteration am lahum sullamun yastamiʿūna fīhi falyati mus'tamiʿuhum bisul'ṭānin mubīnin

Hausa Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.

Verse 39

أَمْ لَهُ ٱلْبَنَـٰتُ وَلَكُمُ ٱلْبَنُونَ

Transliteration am lahu l-banātu walakumu l-banūna

Hausa Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?

Verse 40

أَمْ تَسْـَٔلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ

Transliteration am tasaluhum ajran fahum min maghramin muth'qalūna

Hausa Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?

Verse 41

أَمْ عِندَهُمُ ٱلْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ

Transliteration am ʿindahumu l-ghaybu fahum yaktubūna

Hausa Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?

Verse 42

أَمْ يُرِيدُونَ كَيْدًا ۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ هُمُ ٱلْمَكِيدُونَ

Transliteration am yurīdūna kaydan fa-alladhīna kafarū humu l-makīdūna

Hausa Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.

Verse 43

أَمْ لَهُمْ إِلَـٰهٌ غَيْرُ ٱللَّهِ ۚ سُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ

Transliteration am lahum ilāhun ghayru l-lahi sub'ḥāna l-lahi ʿammā yush'rikūna

Hausa Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!

Verse 44

وَإِن يَرَوْا۟ كِسْفًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ سَاقِطًا يَقُولُوا۟ سَحَابٌ مَّرْكُومٌ

Transliteration wa-in yaraw kis'fan mina l-samāi sāqiṭan yaqūlū saḥābun markūmun

Hausa Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.

Verse 45

فَذَرْهُمْ حَتَّىٰ يُلَـٰقُوا۟ يَوْمَهُمُ ٱلَّذِى فِيهِ يُصْعَقُونَ

Transliteration fadharhum ḥattā yulāqū yawmahumu alladhī fīhi yuṣ'ʿaqūna

Hausa To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.

Verse 46

يَوْمَ لَا يُغْنِى عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْـًٔا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ

Transliteration yawma lā yugh'nī ʿanhum kayduhum shayan walā hum yunṣarūna

Hausa Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su.

Verse 47

وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ عَذَابًا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration wa-inna lilladhīna ẓalamū ʿadhāban dūna dhālika walākinna aktharahum lā yaʿlamūna

Hausa Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.

Verse 48

وَٱصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعْيُنِنَا ۖ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ

Transliteration wa-iṣ'bir liḥuk'mi rabbika fa-innaka bi-aʿyuninā wasabbiḥ biḥamdi rabbika ḥīna taqūmu

Hausa Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnun Mu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).

Verse 49

وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَإِدْبَـٰرَ ٱلنُّجُومِ

Transliteration wamina al-layli fasabbiḥ'hu wa-id'bāra l-nujūmi

Hausa Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) da lõkacin jũyãwar taurãri.

Read Surah At-Tur in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.