MyDugsiStart learning

Surah Al-Haqqah in Hausa: translation and audio

Surah 69 · الحاقة · The Reality · 52 verses

Surah Al-Haqqah verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Haqqah word by word in English.

Verse 1

ٱلْحَآقَّةُ

Transliteration al-ḥāqatu

Hausa Kiran gaskiya!

Verse 2

مَا ٱلْحَآقَّةُ

Transliteration mā l-ḥāqatu

Hausa Mẽne ne kiran gaskiya?

Verse 3

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْحَآقَّةُ

Transliteration wamā adrāka mā l-ḥāqatu

Hausa Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?

Verse 4

كَذَّبَتْ ثَمُودُ وَعَادٌۢ بِٱلْقَارِعَةِ

Transliteration kadhabat thamūdu waʿādun bil-qāriʿati

Hausa Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!

Verse 5

فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهْلِكُوا۟ بِٱلطَّاغِيَةِ

Transliteration fa-ammā thamūdu fa-uh'likū bil-ṭāghiyati

Hausa To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.

Verse 6

وَأَمَّا عَادٌ فَأُهْلِكُوا۟ بِرِيحٍ صَرْصَرٍ عَاتِيَةٍ

Transliteration wa-ammā ʿādun fa-uh'likū birīḥin ṣarṣarin ʿātiyatin

Hausa Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.

Verse 7

سَخَّرَهَا عَلَيْهِمْ سَبْعَ لَيَالٍ وَثَمَـٰنِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومًا فَتَرَى ٱلْقَوْمَ فِيهَا صَرْعَىٰ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ خَاوِيَةٍ

Transliteration sakharahā ʿalayhim sabʿa layālin wathamāniyata ayyāmin ḥusūman fatarā l-qawma fīhā ṣarʿā ka-annahum aʿjāzu nakhlin khāwiyatin

Hausa (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.

Verse 8

فَهَلْ تَرَىٰ لَهُم مِّنۢ بَاقِيَةٍ

Transliteration fahal tarā lahum min bāqiyatin

Hausa To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?

Verse 9

وَجَآءَ فِرْعَوْنُ وَمَن قَبْلَهُۥ وَٱلْمُؤْتَفِكَـٰتُ بِٱلْخَاطِئَةِ

Transliteration wajāa fir'ʿawnu waman qablahu wal-mu'tafikātu bil-khāṭi-ati

Hausa Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.

Verse 10

فَعَصَوْا۟ رَسُولَ رَبِّهِمْ فَأَخَذَهُمْ أَخْذَةً رَّابِيَةً

Transliteration faʿaṣaw rasūla rabbihim fa-akhadhahum akhdhatan rābiyatan

Hausa Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).

Verse 11

إِنَّا لَمَّا طَغَا ٱلْمَآءُ حَمَلْنَـٰكُمْ فِى ٱلْجَارِيَةِ

Transliteration innā lammā ṭaghā l-māu ḥamalnākum fī l-jāriyati

Hausa Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.

Verse 12

لِنَجْعَلَهَا لَكُمْ تَذْكِرَةً وَتَعِيَهَآ أُذُنٌ وَٰعِيَةٌ

Transliteration linajʿalahā lakum tadhkiratan wataʿiyahā udhunun wāʿiyatun

Hausa Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).

Verse 13

فَإِذَا نُفِخَ فِى ٱلصُّورِ نَفْخَةٌ وَٰحِدَةٌ

Transliteration fa-idhā nufikha fī l-ṣūri nafkhatun wāḥidatun

Hausa To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.

Verse 14

وَحُمِلَتِ ٱلْأَرْضُ وَٱلْجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةً وَٰحِدَةً

Transliteration waḥumilati l-arḍu wal-jibālu fadukkatā dakkatan wāḥidatan

Hausa Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.

Verse 15

فَيَوْمَئِذٍ وَقَعَتِ ٱلْوَاقِعَةُ

Transliteration fayawma-idhin waqaʿati l-wāqiʿatu

Hausa A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.

Verse 16

وَٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَهِىَ يَوْمَئِذٍ وَاهِيَةٌ

Transliteration wa-inshaqqati l-samāu fahiya yawma-idhin wāhiyatun

Hausa Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.

Verse 17

وَٱلْمَلَكُ عَلَىٰٓ أَرْجَآئِهَا ۚ وَيَحْمِلُ عَرْشَ رَبِّكَ فَوْقَهُمْ يَوْمَئِذٍ ثَمَـٰنِيَةٌ

Transliteration wal-malaku ʿalā arjāihā wayaḥmilu ʿarsha rabbika fawqahum yawma-idhin thamāniyatun

Hausa Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.

Verse 18

يَوْمَئِذٍ تُعْرَضُونَ لَا تَخْفَىٰ مِنكُمْ خَافِيَةٌ

Transliteration yawma-idhin tuʿ'raḍūna lā takhfā minkum khāfiyatun

Hausa A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.

Verse 19

فَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَيَقُولُ هَآؤُمُ ٱقْرَءُوا۟ كِتَـٰبِيَهْ

Transliteration fa-ammā man ūtiya kitābahu biyamīnihi fayaqūlu hāumu iq'raū kitābiyah

Hausa To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina."

Verse 20

إِنِّى ظَنَنتُ أَنِّى مُلَـٰقٍ حِسَابِيَهْ

Transliteration innī ẓanantu annī mulāqin ḥisābiyah

Hausa "Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."

Verse 21

فَهُوَ فِى عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ

Transliteration fahuwa fī ʿīshatin rāḍiyatin

Hausa Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.

Verse 22

فِى جَنَّةٍ عَالِيَةٍ

Transliteration fī jannatin ʿāliyatin

Hausa A cikin Aljanna maɗaukakiya.

Verse 23

قُطُوفُهَا دَانِيَةٌ

Transliteration quṭūfuhā dāniyatun

Hausa Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),

Verse 24

كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَآ أَسْلَفْتُمْ فِى ٱلْأَيَّامِ ٱلْخَالِيَةِ

Transliteration kulū wa-ish'rabū hanīan bimā aslaftum fī l-ayāmi l-khāliyati

Hausa (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige."

Verse 25

وَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ بِشِمَالِهِۦ فَيَقُولُ يَـٰلَيْتَنِى لَمْ أُوتَ كِتَـٰبِيَهْ

Transliteration wa-ammā man ūtiya kitābahu bishimālihi fayaqūlu yālaytanī lam ūta kitābiyah

Hausa Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!"

Verse 26

وَلَمْ أَدْرِ مَا حِسَابِيَهْ

Transliteration walam adri mā ḥisābiyah

Hausa "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!"

Verse 27

يَـٰلَيْتَهَا كَانَتِ ٱلْقَاضِيَةَ

Transliteration yālaytahā kānati l-qāḍiyata

Hausa "In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!

Verse 28

مَآ أَغْنَىٰ عَنِّى مَالِيَهْ ۜ

Transliteration mā aghnā ʿannī māliyah

Hausa "Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!"

Verse 29

هَلَكَ عَنِّى سُلْطَـٰنِيَهْ

Transliteration halaka ʿannī sul'ṭāniyah

Hausa "Ĩkona ya ɓace mini!"

Verse 30

خُذُوهُ فَغُلُّوهُ

Transliteration khudhūhu faghullūhu

Hausa (Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi."

Verse 31

ثُمَّ ٱلْجَحِيمَ صَلُّوهُ

Transliteration thumma l-jaḥīma ṣallūhu

Hausa "Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi."

Verse 32

ثُمَّ فِى سِلْسِلَةٍ ذَرْعُهَا سَبْعُونَ ذِرَاعًا فَٱسْلُكُوهُ

Transliteration thumma fī sil'silatin dharʿuhā sabʿūna dhirāʿan fa-us'lukūhu

Hausa "Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi."

Verse 33

إِنَّهُۥ كَانَ لَا يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration innahu kāna lā yu'minu bil-lahi l-ʿaẓīmi

Hausa "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!"

Verse 34

وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ

Transliteration walā yaḥuḍḍu ʿalā ṭaʿāmi l-mis'kīni

Hausa "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!"

Verse 35

فَلَيْسَ لَهُ ٱلْيَوْمَ هَـٰهُنَا حَمِيمٌ

Transliteration falaysa lahu l-yawma hāhunā ḥamīmun

Hausa "Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi."

Verse 36

وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنْ غِسْلِينٍ

Transliteration walā ṭaʿāmun illā min ghis'līnin

Hausa "Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."

Verse 37

لَّا يَأْكُلُهُۥٓ إِلَّا ٱلْخَـٰطِـُٔونَ

Transliteration lā yakuluhu illā l-khāṭiūna

Hausa "Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci."

Verse 38

فَلَآ أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ

Transliteration falā uq'simu bimā tub'ṣirūna

Hausa To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,

Verse 39

وَمَا لَا تُبْصِرُونَ

Transliteration wamā lā tub'ṣirūna

Hausa Da abin da bã ku iya gani.

Verse 40

إِنَّهُۥ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ

Transliteration innahu laqawlu rasūlin karīmin

Hausa Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.

Verse 41

وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَاعِرٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تُؤْمِنُونَ

Transliteration wamā huwa biqawli shāʿirin qalīlan mā tu'minūna

Hausa Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.

Verse 42

وَلَا بِقَوْلِ كَاهِنٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ

Transliteration walā biqawli kāhinin qalīlan mā tadhakkarūna

Hausa Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.

Verse 43

تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration tanzīlun min rabbi l-ʿālamīna

Hausa Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.

Verse 44

وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ ٱلْأَقَاوِيلِ

Transliteration walaw taqawwala ʿalaynā baʿḍa l-aqāwīli

Hausa Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.

Verse 45

لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِٱلْيَمِينِ

Transliteration la-akhadhnā min'hu bil-yamīni

Hausa Dã Mun kãma shi da dãma.

Verse 46

ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ ٱلْوَتِينَ

Transliteration thumma laqaṭaʿnā min'hu l-watīna

Hausa sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.

Verse 47

فَمَا مِنكُم مِّنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَـٰجِزِينَ

Transliteration famā minkum min aḥadin ʿanhu ḥājizīna

Hausa Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbar Mu) daga gare shi.

Verse 48

وَإِنَّهُۥ لَتَذْكِرَةٌ لِّلْمُتَّقِينَ

Transliteration wa-innahu latadhkiratun lil'muttaqīna

Hausa Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.

Verse 49

وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ

Transliteration wa-innā lanaʿlamu anna minkum mukadhibīna

Hausa Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.

Verse 50

وَإِنَّهُۥ لَحَسْرَةٌ عَلَى ٱلْكَـٰفِرِينَ

Transliteration wa-innahu laḥasratun ʿalā l-kāfirīna

Hausa Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.

Verse 51

وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلْيَقِينِ

Transliteration wa-innahu laḥaqqu l-yaqīni

Hausa Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙini.

Verse 52

فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration fasabbiḥ bi-is'mi rabbika l-ʿaẓīmi

Hausa Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.

Read Surah Al-Haqqah in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.