Surah Al-'Ankabut in Hausa: translation and audio
Surah 29 · العنكبوت · The Spider · 69 verses
Surah Al-'Ankabut verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-'Ankabut word by word in English.
Verse 1
الٓمٓ
Transliteration alif-lam-meem
Hausa A. L̃. M̃.
Verse 2
أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتْرَكُوٓا۟ أَن يَقُولُوٓا۟ ءَامَنَّا وَهُمْ لَا يُفْتَنُونَ
Transliteration aḥasiba l-nāsu an yut'rakū an yaqūlū āmannā wahum lā yuf'tanūna
Hausa Ashe, mutãne sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi ĩmãni," alhãli kuwa bã zã a Jarrabe su ba?"
Verse 3
وَلَقَدْ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۖ فَلَيَعْلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُوا۟ وَلَيَعْلَمَنَّ ٱلْكَـٰذِبِينَ
Transliteration walaqad fatannā alladhīna min qablihim falayaʿlamanna l-lahu alladhīna ṣadaqū walayaʿlamanna l-kādhibīna
Hausa Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabãninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata.
Verse 4
أَمْ حَسِبَ ٱلَّذِينَ يَعْمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن يَسْبِقُونَا ۚ سَآءَ مَا يَحْكُمُونَ
Transliteration am ḥasiba alladhīna yaʿmalūna l-sayiāti an yasbiqūnā sāa mā yaḥkumūna
Hausa Kõ waɗanda ke aikata miyãgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke hukuntãwa ya mũnana.
Verse 5
مَن كَانَ يَرْجُوا۟ لِقَآءَ ٱللَّهِ فَإِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ لَـَٔاتٍ ۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ
Transliteration man kāna yarjū liqāa l-lahi fa-inna ajala l-lahi laātin wahuwa l-samīʿu l-ʿalīmu
Hausa Wanda ya kasance yanã fãtan gamuwa da Alah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne, kuma (Allah) Shĩ ne Mai ji, Masani.
Verse 6
وَمَن جَـٰهَدَ فَإِنَّمَا يُجَـٰهِدُ لِنَفْسِهِۦٓ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَغَنِىٌّ عَنِ ٱلْعَـٰلَمِينَ
Transliteration waman jāhada fa-innamā yujāhidu linafsihi inna l-laha laghaniyyun ʿani l-ʿālamīna
Hausa Kuma wanda ya yi jihãdi, to, yanã yin jihãdin ne dõmin kansa. lalle Allah haƙĩƙa waɗatacce ne daga barin tãlikai.
Verse 7
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَنُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّـَٔاتِهِمْ وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَحْسَنَ ٱلَّذِى كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
Transliteration wa-alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti lanukaffiranna ʿanhum sayyiātihim walanajziyannahum aḥsana alladhī kānū yaʿmalūna
Hausa Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã kankare musu miyãgun ayyukansu, kuma lalle Munã sãka musu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Verse 8
وَوَصَّيْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ بِوَٰلِدَيْهِ حُسْنًا ۖ وَإِن جَـٰهَدَاكَ لِتُشْرِكَ بِى مَا لَيْسَ لَكَ بِهِۦ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَآ ۚ إِلَىَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Transliteration wawaṣṣaynā l-insāna biwālidayhi ḥus'nan wa-in jāhadāka litush'rika bī mā laysa laka bihi ʿil'mun falā tuṭiʿ'humā ilayya marjiʿukum fa-unabbi-ukum bimā kuntum taʿmalūna
Hausa Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatãwa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta maka dõmin ka yi shirki da Ni game da abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'ã. Zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Verse 9
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَنُدْخِلَنَّهُمْ فِى ٱلصَّـٰلِحِينَ
Transliteration wa-alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti lanud'khilannahum fī l-ṣāliḥīna
Hausa Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã shigar da su a cikin mutãnen kirki.
Verse 10
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ فَإِذَآ أُوذِىَ فِى ٱللَّهِ جَعَلَ فِتْنَةَ ٱلنَّاسِ كَعَذَابِ ٱللَّهِ وَلَئِن جَآءَ نَصْرٌ مِّن رَّبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمْ ۚ أَوَلَيْسَ ٱللَّهُ بِأَعْلَمَ بِمَا فِى صُدُورِ ٱلْعَـٰلَمِينَ
Transliteration wamina l-nāsi man yaqūlu āmannā bil-lahi fa-idhā ūdhiya fī l-lahi jaʿala fit'nata l-nāsi kaʿadhābi l-lahi wala-in jāa naṣrun min rabbika layaqūlunna innā kunnā maʿakum awalaysa l-lahu bi-aʿlama bimā fī ṣudūri l-ʿālamīna
Hausa Kuma daga cikin mutãne akwai mai cẽwa, 'Mun yi ĩmãni da Allah" sa'an nan idan aka cũce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutãne kamar azãbar Allah kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙĩƙa, ya kan ce: "Lalle mũ mun kasance tãre da ku." shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin ƙirãzan halittun Sa?
Verse 11
وَلَيَعْلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَلَيَعْلَمَنَّ ٱلْمُنَـٰفِقِينَ
Transliteration walayaʿlamanna l-lahu alladhīna āmanū walayaʿlamanna l-munāfiqīna
Hausa Kuma lalle Allah na sanin waɗanda suka yi ĩmãni kuma lalle Yanã sanin munafukai.
Verse 12
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لِلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّبِعُوا۟ سَبِيلَنَا وَلْنَحْمِلْ خَطَـٰيَـٰكُمْ وَمَا هُم بِحَـٰمِلِينَ مِنْ خَطَـٰيَـٰهُم مِّن شَىْءٍ ۖ إِنَّهُمْ لَكَـٰذِبُونَ
Transliteration waqāla alladhīna kafarū lilladhīna āmanū ittabiʿū sabīlanā walnaḥmil khaṭāyākum wamā hum biḥāmilīna min khaṭāyāhum min shayin innahum lakādhibūna
Hausa Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Ku bi hanyarmu, kuma Mu ɗauki laifuffukanku," alhãli kõwa ba su zamo mãsu ɗauka da a kõme ba daga laifuffukansu. Lalle sũ maƙaryata ne.
Verse 13
وَلَيَحْمِلُنَّ أَثْقَالَهُمْ وَأَثْقَالًا مَّعَ أَثْقَالِهِمْ ۖ وَلَيُسْـَٔلُنَّ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ عَمَّا كَانُوا۟ يَفْتَرُونَ
Transliteration walayaḥmilunna athqālahum wa-athqālan maʿa athqālihim walayus'alunna yawma l-qiyāmati ʿammā kānū yaftarūna
Hausa Kuma lalle sunã ɗaukar kãyan nauyinsu da waɗansu nauyãyan kãya tãre da kãyan nauyinsu, kuma lalle zã a tambaye su a Rãnar ¡iyama game da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya.
Verse 14
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِۦ فَلَبِثَ فِيهِمْ أَلْفَ سَنَةٍ إِلَّا خَمْسِينَ عَامًا فَأَخَذَهُمُ ٱلطُّوفَانُ وَهُمْ ظَـٰلِمُونَ
Transliteration walaqad arsalnā nūḥan ilā qawmihi falabitha fīhim alfa sanatin illā khamsīna ʿāman fa-akhadhahumu l-ṭūfānu wahum ẓālimūna
Hausa Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu fãce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfãna) ta kãmã su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci.
Verse 15
فَأَنجَيْنَـٰهُ وَأَصْحَـٰبَ ٱلسَّفِينَةِ وَجَعَلْنَـٰهَآ ءَايَةً لِّلْعَـٰلَمِينَ
Transliteration fa-anjaynāhu wa-aṣḥāba l-safīnati wajaʿalnāhā āyatan lil'ʿālamīna
Hausa Sa'an nan Muka tsĩrar da shi da mutãnen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama wata ãyã ga tãlikai.
Verse 16
وَإِبْرَٰهِيمَ إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُ ۖ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Transliteration wa-ib'rāhīma idh qāla liqawmihi uʿ'budū l-laha wa-ittaqūhu dhālikum khayrun lakum in kuntum taʿlamūna
Hausa Da Ibrãhĩm a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ku bautã wa Allah ku bĩ Shi da taƙawa. Wannan Shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.
Verse 17
إِنَّمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوْثَـٰنًا وَتَخْلُقُونَ إِفْكًا ۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمْلِكُونَ لَكُمْ رِزْقًا فَٱبْتَغُوا۟ عِندَ ٱللَّهِ ٱلرِّزْقَ وَٱعْبُدُوهُ وَٱشْكُرُوا۟ لَهُۥٓ ۖ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Transliteration innamā taʿbudūna min dūni l-lahi awthānan watakhluqūna if'kan inna alladhīna taʿbudūna min dūni l-lahi lā yamlikūna lakum riz'qan fa-ib'taghū ʿinda l-lahi l-riz'qa wa-uʿ'budūhu wa-ush'kurū lahu ilayhi tur'jaʿūna
Hausa "Abin da dai kuke bautãwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya. Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bã su mallakã muku arziki. Sabõda haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gõdiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku.
Verse 18
وَإِن تُكَذِّبُوا۟ فَقَدْ كَذَّبَ أُمَمٌ مِّن قَبْلِكُمْ ۖ وَمَا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلْبَلَـٰغُ ٱلْمُبِينُ
Transliteration wa-in tukadhibū faqad kadhaba umamun min qablikum wamā ʿalā l-rasūli illā l-balāghu l-mubīnu
Hausa "Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummõmi a gabãninku sun ƙaryata, kuma bãbu abin da ke kan Manzo, fãce ayar da manzanci, iyarwa bayyananna."
Verse 19
أَوَلَمْ يَرَوْا۟ كَيْفَ يُبْدِئُ ٱللَّهُ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥٓ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٌ
Transliteration awalam yaraw kayfa yub'di-u l-lahu l-khalqa thumma yuʿīduhu inna dhālika ʿalā l-lahi yasīrun
Hausa Shin, ba su ga yadda Allah ke fãra yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah.
Verse 20
قُلْ سِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَٱنظُرُوا۟ كَيْفَ بَدَأَ ٱلْخَلْقَ ۚ ثُمَّ ٱللَّهُ يُنشِئُ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْـَٔاخِرَةَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ
Transliteration qul sīrū fī l-arḍi fa-unẓurū kayfa bada-a l-khalqa thumma l-lahu yunshi-u l-nashata l-ākhirata inna l-laha ʿalā kulli shayin qadīrun
Hausa Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin halitta, sa'an nan kuma Allah Yanã ƙãga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kõme.
Verse 21
يُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ وَيَرْحَمُ مَن يَشَآءُ ۖ وَإِلَيْهِ تُقْلَبُونَ
Transliteration yuʿadhibu man yashāu wayarḥamu man yashāu wa-ilayhi tuq'labūna
Hausa "Yanã azabta wanda Ya so, kuma Yanã jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake jũyaku."
Verse 22
وَمَآ أَنتُم بِمُعْجِزِينَ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا فِى ٱلسَّمَآءِ ۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِىٍّ وَلَا نَصِيرٍ
Transliteration wamā antum bimuʿ'jizīna fī l-arḍi walā fī l-samāi wamā lakum min dūni l-lahi min waliyyin walā naṣīrin
Hausa "Kuma ba ku zamo mãsu buwãya ba a cikin ƙasã, kuma haka a cikin sama kuma bã ku da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki."
Verse 23
وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ وَلِقَآئِهِۦٓ أُو۟لَـٰٓئِكَ يَئِسُوا۟ مِن رَّحْمَتِى وَأُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Transliteration wa-alladhīna kafarū biāyāti l-lahi waliqāihi ulāika ya-isū min raḥmatī wa-ulāika lahum ʿadhābun alīmun
Hausa Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan sunã da wata azãba mai raɗaɗi.
Verse 24
فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُوا۟ ٱقْتُلُوهُ أَوْ حَرِّقُوهُ فَأَنجَىٰهُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلنَّارِ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Transliteration famā kāna jawāba qawmihi illā an qālū uq'tulūhu aw ḥarriqūhu fa-anjāhu l-lahu mina l-nāri inna fī dhālika laāyātin liqawmin yu'minūna
Hausa Sa'an nan bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa (Ibrãhĩm) fãce dai suka ce: "Ku kashe shi kõ, ku ƙõnã shi," Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wutã. Lallea cikin wannan akwai ayõyi ga mutãnen da ke yin ĩmãni.
Verse 25
وَقَالَ إِنَّمَا ٱتَّخَذْتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَوْثَـٰنًا مَّوَدَّةَ بَيْنِكُمْ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۖ ثُمَّ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ يَكْفُرُ بَعْضُكُم بِبَعْضٍ وَيَلْعَنُ بَعْضُكُم بَعْضًا وَمَأْوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّـٰصِرِينَ
Transliteration waqāla innamā ittakhadhtum min dūni l-lahi awthānan mawaddata baynikum fī l-ḥayati l-dun'yā thumma yawma l-qiyāmati yakfuru baʿḍukum bibaʿḍin wayalʿanu baʿḍukum baʿḍan wamawākumu l-nāru wamā lakum min nāṣirīna
Hausa Kuma Ibrahĩm ya ce "Bãbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumãka sabõda sõyayyar tsakãninku a cikin rãyuwar dũniya, a'an nan a Rãnar ¡iyãma sãshinku zai kãfirce wa sãshi, kuma makõmarku ita ce wutã kuma bã ku da waɗansu mataimaka."
Verse 26
۞ فَـَٔامَنَ لَهُۥ لُوطٌ ۘ وَقَالَ إِنِّى مُهَاجِرٌ إِلَىٰ رَبِّىٓ ۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ
Transliteration faāmana lahu lūṭun waqāla innī muhājirun ilā rabbī innahu huwa l-ʿazīzu l-ḥakīmu
Hausa Sai Lũɗu ya yi ĩmãni da shi. Kuma Ibrãhĩm ya ce: "Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."
Verse 27
وَوَهَبْنَا لَهُۥٓ إِسْحَـٰقَ وَيَعْقُوبَ وَجَعَلْنَا فِى ذُرِّيَّتِهِ ٱلنُّبُوَّةَ وَٱلْكِتَـٰبَ وَءَاتَيْنَـٰهُ أَجْرَهُۥ فِى ٱلدُّنْيَا ۖ وَإِنَّهُۥ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Transliteration wawahabnā lahu is'ḥāqa wayaʿqūba wajaʿalnā fī dhurriyyatihi l-nubuwata wal-kitāba waātaynāhu ajrahu fī l-dun'yā wa-innahu fī l-ākhirati lamina l-ṣāliḥīna
Hausa Kuma Muka bã shi Ishãƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littãfi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun bã shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lãhira, tabbas, yanã a cikin sãlihai.
Verse 28
وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِۦٓ إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ ٱلْفَـٰحِشَةَ مَا سَبَقَكُم بِهَا مِنْ أَحَدٍ مِّنَ ٱلْعَـٰلَمِينَ
Transliteration walūṭan idh qāla liqawmihi innakum latatūna l-fāḥishata mā sabaqakum bihā min aḥadin mina l-ʿālamīna
Hausa Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa, "Lalle kũ, haƙĩƙa kunã jẽ wa alfãsha wadda wani mahalũƙi daga cikin dũniya bai riga ku gare ta ba.
Verse 29
أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ ٱلرِّجَالَ وَتَقْطَعُونَ ٱلسَّبِيلَ وَتَأْتُونَ فِى نَادِيكُمُ ٱلْمُنكَرَ ۖ فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُوا۟ ٱئْتِنَا بِعَذَابِ ٱللَّهِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
Transliteration a-innakum latatūna l-rijāla wataqṭaʿūna l-sabīla watatūna fī nādīkumu l-munkara famā kāna jawāba qawmihi illā an qālū i'tinā biʿadhābi l-lahi in kunta mina l-ṣādiqīna
Hausa "Ashe, lalle kũ kunã je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin majalisarku da abin da bã shi da kyau? To, jawãbin mutãnensa bai kasance ba fãce dai sun ce: 'Ka zo mana da azãbar Allah, idan ka kasance daga mãsu gaskiya.'"
Verse 30
قَالَ رَبِّ ٱنصُرْنِى عَلَى ٱلْقَوْمِ ٱلْمُفْسِدِينَ
Transliteration qāla rabbi unṣur'nī ʿalā l-qawmi l-muf'sidīna
Hausa Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni a kan mutãnen nan maɓarnata."
Verse 31
وَلَمَّا جَآءَتْ رُسُلُنَآ إِبْرَٰهِيمَ بِٱلْبُشْرَىٰ قَالُوٓا۟ إِنَّا مُهْلِكُوٓا۟ أَهْلِ هَـٰذِهِ ٱلْقَرْيَةِ ۖ إِنَّ أَهْلَهَا كَانُوا۟ ظَـٰلِمِينَ
Transliteration walammā jāat rusulunā ib'rāhīma bil-bush'rā qālū innā muh'likū ahli hādhihi l-qaryati inna ahlahā kānū ẓālimīna
Hausa Kuma a lõkacin da Manzannin Mu suka jẽ wa Ibrãhĩm da bushãra suka ce: "Lalle mu mãsu halaka mutãnen, wannan alƙarya ne. Lalle mutãnenta sun kasance mãsu zãlunci."
Verse 32
قَالَ إِنَّ فِيهَا لُوطًا ۚ قَالُوا۟ نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَن فِيهَا ۖ لَنُنَجِّيَنَّهُۥ وَأَهْلَهُۥٓ إِلَّا ٱمْرَأَتَهُۥ كَانَتْ مِنَ ٱلْغَـٰبِرِينَ
Transliteration qāla inna fīhā lūṭan qālū naḥnu aʿlamu biman fīhā lanunajjiyannahu wa-ahlahu illā im'ra-atahu kānat mina l-ghābirīna
Hausa Ya ce: "Lalle akwai Lũɗu a cikinta!" Suka ce: "Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke a cikinta, lalle munã tsĩrar da shi da mutãnensa, fãce fa mãtarsa ta kasance a cikin mãsu wanzuwa."
Verse 33
وَلَمَّآ أَن جَآءَتْ رُسُلُنَا لُوطًا سِىٓءَ بِهِمْ وَضَاقَ بِهِمْ ذَرْعًا وَقَالُوا۟ لَا تَخَفْ وَلَا تَحْزَنْ ۖ إِنَّا مُنَجُّوكَ وَأَهْلَكَ إِلَّا ٱمْرَأَتَكَ كَانَتْ مِنَ ٱلْغَـٰبِرِينَ
Transliteration walammā an jāat rusulunā lūṭan sīa bihim waḍāqa bihim dharʿan waqālū lā takhaf walā taḥzan innā munajjūka wa-ahlaka illā im'ra-ataka kānat mina l-ghābirīna
Hausa Kuma a lõkacin da Manzannin Mu suka je wa Lũɗu ya ɓãta rai sabõda su, kuma yã ƙuntata ga kirji sabõda su. Kuma suka ce: "Kada ka ji tsõro kuma kada ka yi baƙin ciki lalle mũ mãsu tsĩrar da kai ne da iyãlanka, fãce dai matarka ta kasance daga mãsu wanzuwa.
Verse 34
إِنَّا مُنزِلُونَ عَلَىٰٓ أَهْلِ هَـٰذِهِ ٱلْقَرْيَةِ رِجْزًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُوا۟ يَفْسُقُونَ
Transliteration innā munzilūna ʿalā ahli hādhihi l-qaryati rij'zan mina l-samāi bimā kānū yafsuqūna
Hausa "Lalle mũ, mãsu saukar da azãba ne daga sama a kan mutãnen wannan alƙarya sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci."
Verse 35
وَلَقَد تَّرَكْنَا مِنْهَآ ءَايَةًۢ بَيِّنَةً لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Transliteration walaqad taraknā min'hā āyatan bayyinatan liqawmin yaʿqilūna
Hausa Kuma lalle Mun bar wata ãyã bayyananna daga gare ta ga mutãne mãsu hankalta.
Verse 36
وَإِلَىٰ مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا فَقَالَ يَـٰقَوْمِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱرْجُوا۟ ٱلْيَوْمَ ٱلْـَٔاخِرَ وَلَا تَعْثَوْا۟ فِى ٱلْأَرْضِ مُفْسِدِينَ
Transliteration wa-ilā madyana akhāhum shuʿayban faqāla yāqawmi uʿ'budū l-laha wa-ir'jū l-yawma l-ākhira walā taʿthaw fī l-arḍi muf'sidīna
Hausa Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Rãnar Lãhira, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasã, alhãli kuwa kunã mãsu lãlãtarwa."
Verse 37
فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَتْهُمُ ٱلرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا۟ فِى دَارِهِمْ جَـٰثِمِينَ
Transliteration fakadhabūhu fa-akhadhathumu l-rajfatu fa-aṣbaḥū fī dārihim jāthimīna
Hausa Sai suka ƙaryata shi, sabõda haka tsãwa ta kãmã su, dõmin haka suka wãyi gari sunã guggurfãne.
Verse 38
وَعَادًا وَثَمُودَا۟ وَقَد تَّبَيَّنَ لَكُم مِّن مَّسَـٰكِنِهِمْ ۖ وَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ أَعْمَـٰلَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ ٱلسَّبِيلِ وَكَانُوا۟ مُسْتَبْصِرِينَ
Transliteration waʿādan wathamūdā waqad tabayyana lakum min masākinihim wazayyana lahumu l-shayṭānu aʿmālahum faṣaddahum ʿani l-sabīli wakānū mus'tabṣirīna
Hausa Da Ãdawa da Samũdãwa alhãli kuwa lalle alãmun azãba sun bayyana a gare su daga gidãjensu kuma Shaiɗan ya ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance mãsu basĩra!
Verse 39
وَقَـٰرُونَ وَفِرْعَوْنَ وَهَـٰمَـٰنَ ۖ وَلَقَدْ جَآءَهُم مُّوسَىٰ بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَٱسْتَكْبَرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا كَانُوا۟ سَـٰبِقِينَ
Transliteration waqārūna wafir'ʿawna wahāmāna walaqad jāahum mūsā bil-bayināti fa-is'takbarū fī l-arḍi wamā kānū sābiqīna
Hausa Kuma ¡ãrũna da Fir'auna da Hãmãna, kuma lalle Mũsaya je musu da hujjõji, sai suka yi girman kai a cikin ƙasã kuma ba su kasance mãsu tsẽrẽwa ba.
Verse 40
فَكُلًّا أَخَذْنَا بِذَنۢبِهِۦ ۖ فَمِنْهُم مَّنْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِ حَاصِبًا وَمِنْهُم مَّنْ أَخَذَتْهُ ٱلصَّيْحَةُ وَمِنْهُم مَّنْ خَسَفْنَا بِهِ ٱلْأَرْضَ وَمِنْهُم مَّنْ أَغْرَقْنَا ۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Transliteration fakullan akhadhnā bidhanbihi famin'hum man arsalnā ʿalayhi ḥāṣiban wamin'hum man akhadhathu l-ṣayḥatu wamin'hum man khasafnā bihi l-arḍa wamin'hum man aghraqnā wamā kāna l-lahu liyaẓlimahum walākin kānū anfusahum yaẓlimūna
Hausa Sabõda haka kõwanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsãwa ta kãmã, kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasã da shi kuma daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar. Bã ya yiwuwa ga Allah Ya zãlunce su, amma sun kasance kansu suke zãlunta.
Verse 41
مَثَلُ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوْلِيَآءَ كَمَثَلِ ٱلْعَنكَبُوتِ ٱتَّخَذَتْ بَيْتًا ۖ وَإِنَّ أَوْهَنَ ٱلْبُيُوتِ لَبَيْتُ ٱلْعَنكَبُوتِ ۖ لَوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ
Transliteration mathalu alladhīna ittakhadhū min dūni l-lahi awliyāa kamathali l-ʿankabūti ittakhadhat baytan wa-inna awhana l-buyūti labaytu l-ʿankabūti law kānū yaʿlamūna
Hausa Misãlin waɗanda suka riƙi waɗansu masõya waɗanda bã Allah ba, kamar misãlin gizõgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhãli kuwa lalle mafi raunin gidãje, shĩ ne gidan gizogizo, dã sun kasance sunã sane.
Verse 42
إِنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ مِن شَىْءٍ ۚ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ
Transliteration inna l-laha yaʿlamu mā yadʿūna min dūnihi min shayin wahuwa l-ʿazīzu l-ḥakīmu
Hausa Lalle Allah Yanã sane da abin da suke kira wanda bã Shi ba na wani abu duka kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
Verse 43
وَتِلْكَ ٱلْأَمْثَـٰلُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ ۖ وَمَا يَعْقِلُهَآ إِلَّا ٱلْعَـٰلِمُونَ
Transliteration watil'ka l-amthālu naḍribuhā lilnnāsi wamā yaʿqiluhā illā l-ʿālimūna
Hausa Kuma waɗancan misãlan Munã bayyana su ga mutãne kuma bãbu mai hankalta da su sai mãsu ilmi.
Verse 44
خَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ بِٱلْحَقِّ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّلْمُؤْمِنِينَ
Transliteration khalaqa l-lahu l-samāwāti wal-arḍa bil-ḥaqi inna fī dhālika laāyatan lil'mu'minīna
Hausa Allah Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle cikin wancan akwai ãyã ga mũminai.
Verse 45
ٱتْلُ مَآ أُوحِىَ إِلَيْكَ مِنَ ٱلْكِتَـٰبِ وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ ۖ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ تَنْهَىٰ عَنِ ٱلْفَحْشَآءِ وَٱلْمُنكَرِ ۗ وَلَذِكْرُ ٱللَّهِ أَكْبَرُ ۗ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَصْنَعُونَ
Transliteration ut'lu mā ūḥiya ilayka mina l-kitābi wa-aqimi l-ṣalata inna l-ṣalata tanhā ʿani l-faḥshāi wal-munkari waladhik'ru l-lahi akbaru wal-lahu yaʿlamu mā taṣnaʿūna
Hausa Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littãfi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abni ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah yafi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa.
Verse 46
۞ وَلَا تُجَـٰدِلُوٓا۟ أَهْلَ ٱلْكِتَـٰبِ إِلَّا بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ إِلَّا ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مِنْهُمْ ۖ وَقُولُوٓا۟ ءَامَنَّا بِٱلَّذِىٓ أُنزِلَ إِلَيْنَا وَأُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَإِلَـٰهُنَا وَإِلَـٰهُكُمْ وَٰحِدٌ وَنَحْنُ لَهُۥ مُسْلِمُونَ
Transliteration walā tujādilū ahla l-kitābi illā bi-allatī hiya aḥsanu illā alladhīna ẓalamū min'hum waqūlū āmannā bi-alladhī unzila ilaynā wa-unzila ilaykum wa-ilāhunā wa-ilāhukum wāḥidun wanaḥnu lahu mus'limūna
Hausa Kada ku yi jayayya da mazowa Littãfi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, kuma ku ce, "Mun yi ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautãwarmu da Abin bautãwarku Guda ne, kama mũ mãsu sallamãwa ne a gare shi."
Verse 47
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَآ إِلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ ۚ فَٱلَّذِينَ ءَاتَيْنَـٰهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ يُؤْمِنُونَ بِهِۦ ۖ وَمِنْ هَـٰٓؤُلَآءِ مَن يُؤْمِنُ بِهِۦ ۚ وَمَا يَجْحَدُ بِـَٔايَـٰتِنَآ إِلَّا ٱلْكَـٰفِرُونَ
Transliteration wakadhālika anzalnā ilayka l-kitāba fa-alladhīna ātaynāhumu l-kitāba yu'minūna bihi wamin hāulāi man yu'minu bihi wamā yajḥadu biāyātinā illā l-kāfirūna
Hausa Kuma kamar haka Muka saukar da Littafi a gare ka, to, waɗannan da Muka bai wa Littãfi sanã ĩmãni da shi, daga cikin wãɗannan akwai mai ĩmãni da shi, kuma bãbu mai musun ãyõyin Mu, fãce kãfirai.
Verse 48
وَمَا كُنتَ تَتْلُوا۟ مِن قَبْلِهِۦ مِن كِتَـٰبٍ وَلَا تَخُطُّهُۥ بِيَمِينِكَ ۖ إِذًا لَّٱرْتَابَ ٱلْمُبْطِلُونَ
Transliteration wamā kunta tatlū min qablihi min kitābin walā takhuṭṭuhu biyamīnika idhan la-ir'tāba l-mub'ṭilūna
Hausa Kuma ba ka kasance kana karãtun wani littãfi ba a gabãninsa, kuma bã ka rubũtunsa da dãmanka dã haka yã auku, dã mãsu ɓarnã sun yi shakka.
Verse 49
بَلْ هُوَ ءَايَـٰتٌۢ بَيِّنَـٰتٌ فِى صُدُورِ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ ۚ وَمَا يَجْحَدُ بِـَٔايَـٰتِنَآ إِلَّا ٱلظَّـٰلِمُونَ
Transliteration bal huwa āyātun bayyinātun fī ṣudūri alladhīna ūtū l-ʿil'ma wamā yajḥadu biāyātinā illā l-ẓālimūna
Hausa Ã'a, shĩ ãyõyi ne bayyanannu a cikin ƙirãzan waɗanda aka bai wa ilmi. Kuma bãbu mai musun ãyõyin Mu fãce azzãlumai.
Verse 50
وَقَالُوا۟ لَوْلَآ أُنزِلَ عَلَيْهِ ءَايَـٰتٌ مِّن رَّبِّهِۦ ۖ قُلْ إِنَّمَا ٱلْـَٔايَـٰتُ عِندَ ٱللَّهِ وَإِنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Transliteration waqālū lawlā unzila ʿalayhi āyātun min rabbihi qul innamā l-āyātu ʿinda l-lahi wa-innamā anā nadhīrun mubīnun
Hausa Kuma suka ce: "Don me ba a saukar masa da ãyõi ba daga Ubangijinsa? "Ka ce: "Su ãyõyi a wurin Allah kawai suke, kuma lalle ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa."
Verse 51
أَوَلَمْ يَكْفِهِمْ أَنَّآ أَنزَلْنَا عَلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ يُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَرَحْمَةً وَذِكْرَىٰ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Transliteration awalam yakfihim annā anzalnā ʿalayka l-kitāba yut'lā ʿalayhim inna fī dhālika laraḥmatan wadhik'rā liqawmin yu'minūna
Hausa Shin bai ishe su ba cẽwa lalle Mũ, Mun saukar da Littãfin akanka, anã karanta shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙĩƙa akwai rahama da tunãtawa ga mutanen da ke yin ĩmãni.
Verse 52
قُلْ كَفَىٰ بِٱللَّهِ بَيْنِى وَبَيْنَكُمْ شَهِيدًا ۖ يَعْلَمُ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۗ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِٱلْبَـٰطِلِ وَكَفَرُوا۟ بِٱللَّهِ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ
Transliteration qul kafā bil-lahi baynī wabaynakum shahīdan yaʿlamu mā fī l-samāwāti wal-arḍi wa-alladhīna āmanū bil-bāṭili wakafarū bil-lahi ulāika humu l-khāsirūna
Hausa Ka ce: "Allah Yã isa shaida a tsakãnĩna da tsakãnĩnku Yanã sane da abin da ke a cikin sammai da ƙasã, kuma waɗanda suka yi ĩmãni da ɗarya kuma suka kãfirta da Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra."
Verse 53
وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِٱلْعَذَابِ ۚ وَلَوْلَآ أَجَلٌ مُّسَمًّى لَّجَآءَهُمُ ٱلْعَذَابُ وَلَيَأْتِيَنَّهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
Transliteration wayastaʿjilūnaka bil-ʿadhābi walawlā ajalun musamman lajāahumu l-ʿadhābu walayatiyannahum baghtatan wahum lā yashʿurūna
Hausa Kuma suna nẽman ka da gaggauta azãba, to, bã dõmin ajali ƙayyadadde ba, dã azãba ta jẽ musu kuma lalle dã tanã iske su bisa ia abke, alhãli kuwa sũ ba su sani ba.
Verse 54
يَسْتَعْجِلُونَكَ بِٱلْعَذَابِ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةٌۢ بِٱلْكَـٰفِرِينَ
Transliteration yastaʿjilūnaka bil-ʿadhābi wa-inna jahannama lamuḥīṭatun bil-kāfirīna
Hausa Sunã nẽman ka da gaggauta azãba, kuma lalle Jahannama, tabbas, mai kẽwayewa ce gakãfirai.
Verse 55
يَوْمَ يَغْشَىٰهُمُ ٱلْعَذَابُ مِن فَوْقِهِمْ وَمِن تَحْتِ أَرْجُلِهِمْ وَيَقُولُ ذُوقُوا۟ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Transliteration yawma yaghshāhumu l-ʿadhābu min fawqihim wamin taḥti arjulihim wayaqūlu dhūqū mā kuntum taʿmalūna
Hausa Rãnar da azãba ke rufe su daga samansu da kuma ƙasan ƙafafunsu kuma Ya ce: "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
Verse 56
يَـٰعِبَادِىَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِنَّ أَرْضِى وَٰسِعَةٌ فَإِيَّـٰىَ فَٱعْبُدُونِ
Transliteration yāʿibādiya alladhīna āmanū inna arḍī wāsiʿatun fa-iyyāya fa-uʿ'budūni
Hausa Yã bãyiNa, waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle fa ƙasãTa mai yalwã ce, sabãda haka ku bauta Mini.
Verse 57
كُلُّ نَفْسٍ ذَآئِقَةُ ٱلْمَوْتِ ۖ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ
Transliteration kullu nafsin dhāiqatu l-mawti thumma ilaynā tur'jaʿūna
Hausa Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku.
Verse 58
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَنُبَوِّئَنَّهُم مِّنَ ٱلْجَنَّةِ غُرَفًا تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۚ نِعْمَ أَجْرُ ٱلْعَـٰمِلِينَ
Transliteration wa-alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti lanubawwi-annahum mina l-janati ghurafan tajrī min taḥtihā l-anhāru khālidīna fīhā niʿ'ma ajru l-ʿāmilīna
Hausa Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zã Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidãjen bẽne, ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon mãsu aikin ƙwarai.
Verse 59
ٱلَّذِينَ صَبَرُوا۟ وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Transliteration alladhīna ṣabarū waʿalā rabbihim yatawakkalūna
Hausa Waɗanda suka yi haƙuri, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu kawai.
Verse 60
وَكَأَيِّن مِّن دَآبَّةٍ لَّا تَحْمِلُ رِزْقَهَا ٱللَّهُ يَرْزُقُهَا وَإِيَّاكُمْ ۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ
Transliteration waka-ayyin min dābbatin lā taḥmilu riz'qahā l-lahu yarzuquhā wa-iyyākum wahuwa l-samīʿu l-ʿalīmu
Hausa Kuma da yawa dabba wadda bã ta ɗaukar abincinta Allah Yanã ciyar da ita tãre da ku, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai ilmi.
Verse 61
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَسَخَّرَ ٱلشَّمْسَ وَٱلْقَمَرَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ ۖ فَأَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ
Transliteration wala-in sa-altahum man khalaqa l-samāwāti wal-arḍa wasakhara l-shamsa wal-qamara layaqūlunna l-lahu fa-annā yu'fakūna
Hausa Lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasã kuma ya hõre rãnã da watã?" Lalle sunã cẽwa Allah ne. TO, yãya ake karkatar da su?
Verse 62
ٱللَّهُ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ وَيَقْدِرُ لَهُۥٓ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ
Transliteration al-lahu yabsuṭu l-riz'qa liman yashāu min ʿibādihi wayaqdiru lahu inna l-laha bikulli shayin ʿalīmun
Hausa Alah ne ke shimfiɗa arziki ga wanda Yake so daga cikin bãyinsa kuma Yanã ƙuntãtãwa ga (wanda, Yake so). Lalle Allah, Masani ne ga dukan kõme.
Verse 63
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّن نَّزَّلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَحْيَا بِهِ ٱلْأَرْضَ مِنۢ بَعْدِ مَوْتِهَا لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ ۚ قُلِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ
Transliteration wala-in sa-altahum man nazzala mina l-samāi māan fa-aḥyā bihi l-arḍa min baʿdi mawtihā layaqūlunna l-lahu quli l-ḥamdu lillahi bal aktharuhum lā yaʿqilūna
Hausa Kuma lalle idan ka tambaye su. "Wãne ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta?" Lalle sunã cẽwa, "Allah ne." Ka ce: "Gõdiya tã tabbata ga Allah." Ã'a, mafi yawansu bã su hankalta.
Verse 64
وَمَا هَـٰذِهِ ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَآ إِلَّا لَهْوٌ وَلَعِبٌ ۚ وَإِنَّ ٱلدَّارَ ٱلْـَٔاخِرَةَ لَهِىَ ٱلْحَيَوَانُ ۚ لَوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ
Transliteration wamā hādhihi l-ḥayatu l-dun'yā illā lahwun walaʿibun wa-inna l-dāra l-ākhirata lahiya l-ḥayawānu law kānū yaʿlamūna
Hausa Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani.
Verse 65
فَإِذَا رَكِبُوا۟ فِى ٱلْفُلْكِ دَعَوُا۟ ٱللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمْ إِلَى ٱلْبَرِّ إِذَا هُمْ يُشْرِكُونَ
Transliteration fa-idhā rakibū fī l-ful'ki daʿawū l-laha mukh'liṣīna lahu l-dīna falammā najjāhum ilā l-bari idhā hum yush'rikūna
Hausa To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki.
Verse 66
لِيَكْفُرُوا۟ بِمَآ ءَاتَيْنَـٰهُمْ وَلِيَتَمَتَّعُوا۟ ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
Transliteration liyakfurū bimā ātaynāhum waliyatamattaʿū fasawfa yaʿlamūna
Hausa Dõmin su kãfirce wa abin da Muka bã su kuma dõmin su ji dãɗi sa'an nan kuma zã su sani.
Verse 67
أَوَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّا جَعَلْنَا حَرَمًا ءَامِنًا وَيُتَخَطَّفُ ٱلنَّاسُ مِنْ حَوْلِهِمْ ۚ أَفَبِٱلْبَـٰطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَةِ ٱللَّهِ يَكْفُرُونَ
Transliteration awalam yaraw annā jaʿalnā ḥaraman āminan wayutakhaṭṭafu l-nāsu min ḥawlihim afabil-bāṭili yu'minūna wabiniʿ'mati l-lahi yakfurūna
Hausa Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhãli kuwa anã fisge mutãne a gẽfensu? Shin, da ɓãtaccen abu suke ĩmãni kuma da ni'imarAllah suka kãfirta?
Verse 68
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ ٱفْتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِٱلْحَقِّ لَمَّا جَآءَهُۥٓ ۚ أَلَيْسَ فِى جَهَنَّمَ مَثْوًى لِّلْكَـٰفِرِينَ
Transliteration waman aẓlamu mimmani if'tarā ʿalā l-lahi kadhiban aw kadhaba bil-ḥaqi lammā jāahu alaysa fī jahannama mathwan lil'kāfirīna
Hausa Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, kõ kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama bãbu mazauna ga kãfirai?
Verse 69
وَٱلَّذِينَ جَـٰهَدُوا۟ فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا ۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَمَعَ ٱلْمُحْسِنِينَ
Transliteration wa-alladhīna jāhadū fīnā lanahdiyannahum subulanā wa-inna l-laha lamaʿa l-muḥ'sinīna
Hausa Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa (ga addĩninsu).
Read Surah Al-'Ankabut in another language
- English (word by word)
- Albanian
- Amazigh
- Amharic
- Assamese
- Azerbaijani
- Bambara
- Bangla
- Bosnian
- Bulgarian
- Chechen
- Chinese
- Czech
- Dari
- Dhivehi
- Dutch
- Finnish
- French
- German
- Gujarati
- Hebrew
- Hindi
- Indonesian
- Italian
- Japanese
- Kannada
- Kazakh
- Khmer
- Kinyarwanda
- Korean
- Kurdish
- Luganda
- Malay
- Malayalam
- Maranao
- Marathi
- Nepali
- Norwegian
- Oromo
- Pashto
- Persian
- Polish
- Portuguese
- Romanian
- Russian
- Sindhi
- Sinhala
- Somali
- Spanish
- Swahili
- Swedish
- Tagalog
- Tajik
- Tamil
- Tatar
- Telugu
- Thai
- Turkish
- Ukrainian
- Urdu
- Uyghur
- Uzbek
- Vietnamese
- Yao
- Yoruba
All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.
Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.