Surah Adh-Dhariyat in Hausa: translation and audio
Surah 51 · الذاريات · The Winnowing Winds · 60 verses
Surah Adh-Dhariyat verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Adh-Dhariyat word by word in English.
Verse 1
وَٱلذَّٰرِيَـٰتِ ذَرْوًا
Transliteration wal-dhāriyāti dharwan
Hausa Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.
Verse 2
فَٱلْحَـٰمِلَـٰتِ وِقْرًا
Transliteration fal-ḥāmilāti wiq'ran
Hausa Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).
Verse 3
فَٱلْجَـٰرِيَـٰتِ يُسْرًا
Transliteration fal-jāriyāti yus'ran
Hausa Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.
Verse 4
فَٱلْمُقَسِّمَـٰتِ أَمْرًا
Transliteration fal-muqasimāti amran
Hausa Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).
Verse 5
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَصَادِقٌ
Transliteration innamā tūʿadūna laṣādiqun
Hausa Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.
Verse 6
وَإِنَّ ٱلدِّينَ لَوَٰقِعٌ
Transliteration wa-inna l-dīna lawāqiʿun
Hausa Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne
Verse 7
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلْحُبُكِ
Transliteration wal-samāi dhāti l-ḥubuki
Hausa Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo).
Verse 8
إِنَّكُمْ لَفِى قَوْلٍ مُّخْتَلِفٍ
Transliteration innakum lafī qawlin mukh'talifin
Hausa Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani).
Verse 9
يُؤْفَكُ عَنْهُ مَنْ أُفِكَ
Transliteration yu'faku ʿanhu man ufika
Hausa Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).
Verse 10
قُتِلَ ٱلْخَرَّٰصُونَ
Transliteration qutila l-kharāṣūna
Hausa An la'ani mãsu ƙiri-faɗi.
Verse 11
ٱلَّذِينَ هُمْ فِى غَمْرَةٍ سَاهُونَ
Transliteration alladhīna hum fī ghamratin sāhūna
Hausa Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.
Verse 12
يَسْـَٔلُونَ أَيَّانَ يَوْمُ ٱلدِّينِ
Transliteration yasalūna ayyāna yawmu l-dīni
Hausa Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?"
Verse 13
يَوْمَ هُمْ عَلَى ٱلنَّارِ يُفْتَنُونَ
Transliteration yawma hum ʿalā l-nāri yuf'tanūna
Hausa Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.
Verse 14
ذُوقُوا۟ فِتْنَتَكُمْ هَـٰذَا ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تَسْتَعْجِلُونَ
Transliteration dhūqū fit'natakum hādhā alladhī kuntum bihi tastaʿjilūna
Hausa (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa."
Verse 15
إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ
Transliteration inna l-mutaqīna fī jannātin waʿuyūnin
Hausa Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.
Verse 16
ءَاخِذِينَ مَآ ءَاتَىٰهُمْ رَبُّهُمْ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَبْلَ ذَٰلِكَ مُحْسِنِينَ
Transliteration ākhidhīna mā ātāhum rabbuhum innahum kānū qabla dhālika muḥ'sinīna
Hausa Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).
Verse 17
كَانُوا۟ قَلِيلًا مِّنَ ٱلَّيْلِ مَا يَهْجَعُونَ
Transliteration kānū qalīlan mina al-layli mā yahjaʿūna
Hausa Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.
Verse 18
وَبِٱلْأَسْحَارِ هُمْ يَسْتَغْفِرُونَ
Transliteration wabil-asḥāri hum yastaghfirūna
Hausa Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.
Verse 19
وَفِىٓ أَمْوَٰلِهِمْ حَقٌّ لِّلسَّآئِلِ وَٱلْمَحْرُومِ
Transliteration wafī amwālihim ḥaqqun lilssāili wal-maḥrūmi
Hausa Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.
Verse 20
وَفِى ٱلْأَرْضِ ءَايَـٰتٌ لِّلْمُوقِنِينَ
Transliteration wafī l-arḍi āyātun lil'mūqinīna
Hausa Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.
Verse 21
وَفِىٓ أَنفُسِكُمْ ۚ أَفَلَا تُبْصِرُونَ
Transliteration wafī anfusikum afalā tub'ṣirūna
Hausa Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?
Verse 22
وَفِى ٱلسَّمَآءِ رِزْقُكُمْ وَمَا تُوعَدُونَ
Transliteration wafī l-samāi riz'qukum wamā tūʿadūna
Hausa Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.
Verse 23
فَوَرَبِّ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ إِنَّهُۥ لَحَقٌّ مِّثْلَ مَآ أَنَّكُمْ تَنطِقُونَ
Transliteration fawarabbi l-samāi wal-arḍi innahu laḥaqqun mith'la mā annakum tanṭiqūna
Hausa To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,
Verse 24
هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ضَيْفِ إِبْرَٰهِيمَ ٱلْمُكْرَمِينَ
Transliteration hal atāka ḥadīthu ḍayfi ib'rāhīma l-muk'ramīna
Hausa Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?
Verse 25
إِذْ دَخَلُوا۟ عَلَيْهِ فَقَالُوا۟ سَلَـٰمًا ۖ قَالَ سَلَـٰمٌ قَوْمٌ مُّنكَرُونَ
Transliteration idh dakhalū ʿalayhi faqālū salāman qāla salāmun qawmun munkarūna
Hausa A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!"
Verse 26
فَرَاغَ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ فَجَآءَ بِعِجْلٍ سَمِينٍ
Transliteration farāgha ilā ahlihi fajāa biʿij'lin samīnin
Hausa Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,
Verse 27
فَقَرَّبَهُۥٓ إِلَيْهِمْ قَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ
Transliteration faqarrabahu ilayhim qāla alā takulūna
Hausa Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?"
Verse 28
فَأَوْجَسَ مِنْهُمْ خِيفَةً ۖ قَالُوا۟ لَا تَخَفْ ۖ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَـٰمٍ عَلِيمٍ
Transliteration fa-awjasa min'hum khīfatan qālū lā takhaf wabasharūhu bighulāmin ʿalīmin
Hausa Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.
Verse 29
فَأَقْبَلَتِ ٱمْرَأَتُهُۥ فِى صَرَّةٍ فَصَكَّتْ وَجْهَهَا وَقَالَتْ عَجُوزٌ عَقِيمٌ
Transliteration fa-aqbalati im'ra-atuhu fī ṣarratin faṣakkat wajhahā waqālat ʿajūzun ʿaqīmun
Hausa Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!"
Verse 30
قَالُوا۟ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ ۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْحَكِيمُ ٱلْعَلِيمُ
Transliteration qālū kadhāliki qāla rabbuki innahu huwa l-ḥakīmu l-ʿalīmu
Hausa Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi."
Verse 31
۞ قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا ٱلْمُرْسَلُونَ
Transliteration qāla famā khaṭbukum ayyuhā l-mur'salūna
Hausa (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"
Verse 32
قَالُوٓا۟ إِنَّآ أُرْسِلْنَآ إِلَىٰ قَوْمٍ مُّجْرِمِينَ
Transliteration qālū innā ur'sil'nā ilā qawmin muj'rimīna
Hausa Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.
Verse 33
لِنُرْسِلَ عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن طِينٍ
Transliteration linur'sila ʿalayhim ḥijāratan min ṭīnin
Hausa "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).
Verse 34
مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلْمُسْرِفِينَ
Transliteration musawwamatan ʿinda rabbika lil'mus'rifīna
Hausa "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."
Verse 35
فَأَخْرَجْنَا مَن كَانَ فِيهَا مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Transliteration fa-akhrajnā man kāna fīhā mina l-mu'minīna
Hausa Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
Verse 36
فَمَا وَجَدْنَا فِيهَا غَيْرَ بَيْتٍ مِّنَ ٱلْمُسْلِمِينَ
Transliteration famā wajadnā fīhā ghayra baytin mina l-mus'limīna
Hausa Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.
Verse 37
وَتَرَكْنَا فِيهَآ ءَايَةً لِّلَّذِينَ يَخَافُونَ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ
Transliteration wataraknā fīhā āyatan lilladhīna yakhāfūna l-ʿadhāba l-alīma
Hausa Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.
Verse 38
وَفِى مُوسَىٰٓ إِذْ أَرْسَلْنَـٰهُ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ بِسُلْطَـٰنٍ مُّبِينٍ
Transliteration wafī mūsā idh arsalnāhu ilā fir'ʿawna bisul'ṭānin mubīnin
Hausa Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.
Verse 39
فَتَوَلَّىٰ بِرُكْنِهِۦ وَقَالَ سَـٰحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌ
Transliteration fatawallā biruk'nihi waqāla sāḥirun aw majnūnun
Hausa Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"
Verse 40
فَأَخَذْنَـٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذْنَـٰهُمْ فِى ٱلْيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٌ
Transliteration fa-akhadhnāhu wajunūdahu fanabadhnāhum fī l-yami wahuwa mulīmun
Hausa Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
Verse 41
وَفِى عَادٍ إِذْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ ٱلرِّيحَ ٱلْعَقِيمَ
Transliteration wafī ʿādin idh arsalnā ʿalayhimu l-rīḥa l-ʿaqīma
Hausa Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.
Verse 42
مَا تَذَرُ مِن شَىْءٍ أَتَتْ عَلَيْهِ إِلَّا جَعَلَتْهُ كَٱلرَّمِيمِ
Transliteration mā tadharu min shayin atat ʿalayhi illā jaʿalathu kal-ramīmi
Hausa Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.
Verse 43
وَفِى ثَمُودَ إِذْ قِيلَ لَهُمْ تَمَتَّعُوا۟ حَتَّىٰ حِينٍ
Transliteration wafī thamūda idh qīla lahum tamattaʿū ḥattā ḥīnin
Hausa Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"
Verse 44
فَعَتَوْا۟ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ فَأَخَذَتْهُمُ ٱلصَّـٰعِقَةُ وَهُمْ يَنظُرُونَ
Transliteration faʿataw ʿan amri rabbihim fa-akhadhathumu l-ṣāʿiqatu wahum yanẓurūna
Hausa Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.
Verse 45
فَمَا ٱسْتَطَـٰعُوا۟ مِن قِيَامٍ وَمَا كَانُوا۟ مُنتَصِرِينَ
Transliteration famā is'taṭāʿū min qiyāmin wamā kānū muntaṣirīna
Hausa Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.
Verse 46
وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَوْمًا فَـٰسِقِينَ
Transliteration waqawma nūḥin min qablu innahum kānū qawman fāsiqīna
Hausa Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
Verse 47
وَٱلسَّمَآءَ بَنَيْنَـٰهَا بِأَيْي۟دٍ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَ
Transliteration wal-samāa banaynāhā bi-aydin wa-innā lamūsiʿūna
Hausa Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.
Verse 48
وَٱلْأَرْضَ فَرَشْنَـٰهَا فَنِعْمَ ٱلْمَـٰهِدُونَ
Transliteration wal-arḍa farashnāhā faniʿ'ma l-māhidūna
Hausa Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,
Verse 49
وَمِن كُلِّ شَىْءٍ خَلَقْنَا زَوْجَيْنِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Transliteration wamin kulli shayin khalaqnā zawjayni laʿallakum tadhakkarūna
Hausa Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.
Verse 50
فَفِرُّوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ ۖ إِنِّى لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Transliteration fafirrū ilā l-lahi innī lakum min'hu nadhīrun mubīnun
Hausa Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
Verse 51
وَلَا تَجْعَلُوا۟ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ ۖ إِنِّى لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Transliteration walā tajʿalū maʿa l-lahi ilāhan ākhara innī lakum min'hu nadhīrun mubīnun
Hausa Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
Verse 52
كَذَٰلِكَ مَآ أَتَى ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُوا۟ سَاحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌ
Transliteration kadhālika mā atā alladhīna min qablihim min rasūlin illā qālū sāḥirun aw majnūnun
Hausa Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."
Verse 53
أَتَوَاصَوْا۟ بِهِۦ ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ
Transliteration atawāṣaw bihi bal hum qawmun ṭāghūna
Hausa shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
Verse 54
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ فَمَآ أَنتَ بِمَلُومٍ
Transliteration fatawalla ʿanhum famā anta bimalūmin
Hausa Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
Verse 55
وَذَكِّرْ فَإِنَّ ٱلذِّكْرَىٰ تَنفَعُ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Transliteration wadhakkir fa-inna l-dhik'rā tanfaʿu l-mu'minīna
Hausa Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
Verse 56
وَمَا خَلَقْتُ ٱلْجِنَّ وَٱلْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ
Transliteration wamā khalaqtu l-jina wal-insa illā liyaʿbudūni
Hausa Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
Verse 57
مَآ أُرِيدُ مِنْهُم مِّن رِّزْقٍ وَمَآ أُرِيدُ أَن يُطْعِمُونِ
Transliteration mā urīdu min'hum min riz'qin wamā urīdu an yuṭ'ʿimūni
Hausa Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.
Verse 58
إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلْقُوَّةِ ٱلْمَتِينُ
Transliteration inna l-laha huwa l-razāqu dhū l-quwati l-matīnu
Hausa Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
Verse 59
فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ ذَنُوبًا مِّثْلَ ذَنُوبِ أَصْحَـٰبِهِمْ فَلَا يَسْتَعْجِلُونِ
Transliteration fa-inna lilladhīna ẓalamū dhanūban mith'la dhanūbi aṣḥābihim falā yastaʿjilūni
Hausa To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
Verse 60
فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِن يَوْمِهِمُ ٱلَّذِى يُوعَدُونَ
Transliteration fawaylun lilladhīna kafarū min yawmihimu alladhī yūʿadūna
Hausa Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.
Read Surah Adh-Dhariyat in another language
- English (word by word)
- Albanian
- Amazigh
- Amharic
- Assamese
- Azerbaijani
- Bambara
- Bangla
- Bosnian
- Bulgarian
- Chechen
- Chinese
- Czech
- Dari
- Dhivehi
- Dutch
- Finnish
- French
- German
- Gujarati
- Hebrew
- Hindi
- Indonesian
- Italian
- Japanese
- Kannada
- Kazakh
- Khmer
- Kinyarwanda
- Korean
- Kurdish
- Luganda
- Malay
- Malayalam
- Maranao
- Marathi
- Nepali
- Norwegian
- Oromo
- Pashto
- Persian
- Polish
- Portuguese
- Romanian
- Russian
- Sindhi
- Sinhala
- Somali
- Spanish
- Swahili
- Swedish
- Tagalog
- Tajik
- Tamil
- Tatar
- Telugu
- Thai
- Turkish
- Ukrainian
- Urdu
- Uyghur
- Uzbek
- Vietnamese
- Yao
- Yoruba
All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.
Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.