MyDugsiStart learning

Surah Luqman in Hausa: translation and audio

Surah 31 · لقمان · Luqman · 34 verses

Surah Luqman verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Luqman word by word in English.

Verse 1

الٓمٓ

Transliteration alif-lam-meem

Hausa A. L̃. M̃.

Verse 2

تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ ٱلْحَكِيمِ

Transliteration til'ka āyātu l-kitābi l-ḥakīmi

Hausa Waɗancan ãyõyin Littãfin ne mai hikima.

Verse 3

هُدًى وَرَحْمَةً لِّلْمُحْسِنِينَ

Transliteration hudan waraḥmatan lil'muḥ'sinīna

Hausa Shiriya da rahama ne ga mãsu kyautatawa.

Verse 4

ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤْتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلْـَٔاخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ

Transliteration alladhīna yuqīmūna l-ṣalata wayu'tūna l-zakata wahum bil-ākhirati hum yūqinūna

Hausa Waɗanda ke tsai da salla kuma sunã bãyar da zakka kuma sũ, sunã yin ĩmãnin yaƙĩni, ga lãhira.

Verse 5

أُو۟لَـٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدًى مِّن رَّبِّهِمْ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ

Transliteration ulāika ʿalā hudan min rabbihim wa-ulāika humu l-muf'liḥūna

Hausa Waɗannan sunã a kan shiriya ta daga Ubangijinsu kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.

Verse 6

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَشْتَرِى لَهْوَ ٱلْحَدِيثِ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَيَتَّخِذَهَا هُزُوًا ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مُّهِينٌ

Transliteration wamina l-nāsi man yashtarī lahwa l-ḥadīthi liyuḍilla ʿan sabīli l-lahi bighayri ʿil'min wayattakhidhahā huzuwan ulāika lahum ʿadhābun muhīnun

Hausa Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.

Verse 7

وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ءَايَـٰتُنَا وَلَّىٰ مُسْتَكْبِرًا كَأَن لَّمْ يَسْمَعْهَا كَأَنَّ فِىٓ أُذُنَيْهِ وَقْرًا ۖ فَبَشِّرْهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Transliteration wa-idhā tut'lā ʿalayhi āyātunā wallā mus'takbiran ka-an lam yasmaʿhā ka-anna fī udhunayhi waqran fabashir'hu biʿadhābin alīmin

Hausa Kuma idan an karanta ãyõyin Mu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai, kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi.

Verse 8

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَهُمْ جَنَّـٰتُ ٱلنَّعِيمِ

Transliteration inna alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti lahum jannātu l-naʿīmi

Hausa Lalle, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljannar ni'ima.

Verse 9

خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۖ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقًّا ۚ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ

Transliteration khālidīna fīhā waʿda l-lahi ḥaqqan wahuwa l-ʿazīzu l-ḥakīmu

Hausa Sunã dawwama a cikinsu Allah Yã yi alkawarin, Ya tabbatar da shi. Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.

Verse 10

خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ بِغَيْرِ عَمَدٍ تَرَوْنَهَا ۖ وَأَلْقَىٰ فِى ٱلْأَرْضِ رَوَٰسِىَ أَن تَمِيدَ بِكُمْ وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٍ ۚ وَأَنزَلْنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ

Transliteration khalaqa l-samāwāti bighayri ʿamadin tarawnahā wa-alqā fī l-arḍi rawāsiya an tamīda bikum wabatha fīhā min kulli dābbatin wa-anzalnā mina l-samāi māan fa-anbatnā fīhā min kulli zawjin karīmin

Hausa (Allah) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa.

Verse 11

هَـٰذَا خَلْقُ ٱللَّهِ فَأَرُونِى مَاذَا خَلَقَ ٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦ ۚ بَلِ ٱلظَّـٰلِمُونَ فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ

Transliteration hādhā khalqu l-lahi fa-arūnī mādhā khalaqa alladhīna min dūnihi bali l-ẓālimūna fī ḍalālin mubīnin

Hausa Wannan shĩ ne halittar Allah. To ku nũna mini, "Mẽne ne waɗanan da ba Shi ba suka halitta? Ã'a, azzalumai sunã a cikin ɓata bayyananna."

Verse 12

وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا لُقْمَـٰنَ ٱلْحِكْمَةَ أَنِ ٱشْكُرْ لِلَّهِ ۚ وَمَن يَشْكُرْ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِىٌّ حَمِيدٌ

Transliteration walaqad ātaynā luq'māna l-ḥik'mata ani ush'kur lillahi waman yashkur fa-innamā yashkuru linafsihi waman kafara fa-inna l-laha ghaniyyun ḥamīdun

Hausa Kuma lalle haƙĩƙa Mun bai wa Luƙmãn hikima. (Muka ce masa) Ka gõde wa Allah, kuma wanda ya gõde, to yanã gõdẽwa ne dõmin kansa kawai kuma wanda ya kãfirta, to, lalle, Allah Mawadãci ne, Gõdadde.

Verse 13

وَإِذْ قَالَ لُقْمَـٰنُ لِٱبْنِهِۦ وَهُوَ يَعِظُهُۥ يَـٰبُنَىَّ لَا تُشْرِكْ بِٱللَّهِ ۖ إِنَّ ٱلشِّرْكَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ

Transliteration wa-idh qāla luq'mānu li-ib'nihi wahuwa yaʿiẓuhu yābunayya lā tush'rik bil-lahi inna l-shir'ka laẓul'mun ʿaẓīmun

Hausa Kuma a lõkacin da Luƙmãn ya ce wa ɗansa, alhãli kuwa yanã yi masa wa'azi, "Yã ƙaramin ɗãna! Kada ka yi shirki game da Allah. Lalle shirki wani zãlunci ne mai girma."

Verse 14

وَوَصَّيْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ بِوَٰلِدَيْهِ حَمَلَتْهُ أُمُّهُۥ وَهْنًا عَلَىٰ وَهْنٍ وَفِصَـٰلُهُۥ فِى عَامَيْنِ أَنِ ٱشْكُرْ لِى وَلِوَٰلِدَيْكَ إِلَىَّ ٱلْمَصِيرُ

Transliteration wawaṣṣaynā l-insāna biwālidayhi ḥamalathu ummuhu wahnan ʿalā wahnin wafiṣāluhu fī ʿāmayni ani ush'kur lī waliwālidayka ilayya l-maṣīru

Hausa Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa) "Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take."

Verse 15

وَإِن جَـٰهَدَاكَ عَلَىٰٓ أَن تُشْرِكَ بِى مَا لَيْسَ لَكَ بِهِۦ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا ۖ وَصَاحِبْهُمَا فِى ٱلدُّنْيَا مَعْرُوفًا ۖ وَٱتَّبِعْ سَبِيلَ مَنْ أَنَابَ إِلَىَّ ۚ ثُمَّ إِلَىَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Transliteration wa-in jāhadāka ʿalā an tush'rika bī mā laysa laka bihi ʿil'mun falā tuṭiʿ'humā waṣāḥib'humā fī l-dun'yā maʿrūfan wa-ittabiʿ sabīla man anāba ilayya thumma ilayya marjiʿukum fa-unabbi-ukum bimā kuntum taʿmalūna

Hausa "Kuma idan mahaifanka suka tsananta maka ga ka yi shirki game da Ni, ga abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'a. Kuma ka abũce su a cikin dũniya gwargwadon sharĩ'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa gare Ni, sa'an nan zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Verse 16

يَـٰبُنَىَّ إِنَّهَآ إِن تَكُ مِثْقَالَ حَبَّةٍ مِّنْ خَرْدَلٍ فَتَكُن فِى صَخْرَةٍ أَوْ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ أَوْ فِى ٱلْأَرْضِ يَأْتِ بِهَا ٱللَّهُ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٌ

Transliteration yābunayya innahā in taku mith'qāla ḥabbatin min khardalin fatakun fī ṣakhratin aw fī l-samāwāti aw fī l-arḍi yati bihā l-lahu inna l-laha laṭīfun khabīrun

Hausa "Yã ƙaramin ɗãna! Lalle ita idan gwargwadon ƙwãyar kõmayya ce ta kasance, to, ta kasance a cikin wani falalen dũtse, kõ a cikin sammai, kõ a cikin ƙasã, Allah zai kãwo ta Lalle Allah Mai tausasãwa ne, Masani."

Verse 17

يَـٰبُنَىَّ أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ وَأْمُرْ بِٱلْمَعْرُوفِ وَٱنْهَ عَنِ ٱلْمُنكَرِ وَٱصْبِرْ عَلَىٰ مَآ أَصَابَكَ ۖ إِنَّ ذَٰلِكَ مِنْ عَزْمِ ٱلْأُمُورِ

Transliteration yābunayya aqimi l-ṣalata wamur bil-maʿrūfi wa-in'ha ʿani l-munkari wa-iṣ'bir ʿalā mā aṣābaka inna dhālika min ʿazmi l-umūri

Hausa "Yã ƙaramin ɗãna! Ka tsai da salla, kuma ka yi umurni da abin da aka sani, kuma ka yi hani daga abin da ba a sani ba, kuma ka yi haƙuri a kan abin da ya sãme ka. Lalle, wancan yanã daga muhimman al'amura."

Verse 18

وَلَا تُصَعِّرْ خَدَّكَ لِلنَّاسِ وَلَا تَمْشِ فِى ٱلْأَرْضِ مَرَحًا ۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخْتَالٍ فَخُورٍ

Transliteration walā tuṣaʿʿir khaddaka lilnnāsi walā tamshi fī l-arḍi maraḥan inna l-laha lā yuḥibbu kulla mukh'tālin fakhūrin

Hausa "Kada ka karkatar da kundukukinka ga mutãne, kada ka yi tafiya a cikin ƙasã kanã mai nũna fãɗin rai. Lalle, Allah bã Ya son dukan mai tãƙama, mai alfahari."

Verse 19

وَٱقْصِدْ فِى مَشْيِكَ وَٱغْضُضْ مِن صَوْتِكَ ۚ إِنَّ أَنكَرَ ٱلْأَصْوَٰتِ لَصَوْتُ ٱلْحَمِيرِ

Transliteration wa-iq'ṣid fī mashyika wa-ugh'ḍuḍ min ṣawtika inna ankara l-aṣwāti laṣawtu l-ḥamīri

Hausa "Kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka runtse ga sautinka. Lalle mafi mũnin sautuka haƙĩƙa shĩ ne sautin jãkuna. "

Verse 20

أَلَمْ تَرَوْا۟ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ وَأَسْبَغَ عَلَيْكُمْ نِعَمَهُۥ ظَـٰهِرَةً وَبَاطِنَةً ۗ وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَـٰدِلُ فِى ٱللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَلَا هُدًى وَلَا كِتَـٰبٍ مُّنِيرٍ

Transliteration alam taraw anna l-laha sakhara lakum mā fī l-samāwāti wamā fī l-arḍi wa-asbagha ʿalaykum niʿamahu ẓāhiratan wabāṭinatan wamina l-nāsi man yujādilu fī l-lahi bighayri ʿil'min walā hudan walā kitābin munīrin

Hausa Ashe, ba ku gani ba, cẽwa Allah Yã hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasã, kuma Ya zuba ni'imõminsa a kanku, bayyanannu da ɓõyayyu? Kuma akwai daga mutãne wanda ke yin jidãli ga al'amarin Allah, bã da wani ilmi ba, kuma bã da wata shiriya ba, kumã ba da wani littãfi mai haskakãwa ba.

Verse 21

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُوا۟ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُوا۟ بَلْ نَتَّبِعُ مَا وَجَدْنَا عَلَيْهِ ءَابَآءَنَآ ۚ أَوَلَوْ كَانَ ٱلشَّيْطَـٰنُ يَدْعُوهُمْ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

Transliteration wa-idhā qīla lahumu ittabiʿū mā anzala l-lahu qālū bal nattabiʿu mā wajadnā ʿalayhi ābāanā awalaw kāna l-shayṭānu yadʿūhum ilā ʿadhābi l-saʿīri

Hausa Kuma idan aka ce musu, "Ku bi abin da Allah ya saukar," sai su ce: "Ã'a, munã bin abin da muka sãmi ubanninmu a kansa." shin kõ dã Shaiɗan nã kiran su ne zuwa ga azãbar sa'ir,

Verse 22

۞ وَمَن يُسْلِمْ وَجْهَهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ فَقَدِ ٱسْتَمْسَكَ بِٱلْعُرْوَةِ ٱلْوُثْقَىٰ ۗ وَإِلَى ٱللَّهِ عَـٰقِبَةُ ٱلْأُمُورِ

Transliteration waman yus'lim wajhahu ilā l-lahi wahuwa muḥ'sinun faqadi is'tamsaka bil-ʿur'wati l-wuth'qā wa-ilā l-lahi ʿāqibatu l-umūri

Hausa kuma wanda ya mĩka fuskarsa zuwa ga Allah, alhãli kuma yanã mai kyautatãwa, to, lalle ya yi riƙo ga igiya amintacciya. Kuma zuwa ga Allah ãƙibar al'amura take.

Verse 23

وَمَن كَفَرَ فَلَا يَحْزُنكَ كُفْرُهُۥٓ ۚ إِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ فَنُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوٓا۟ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Transliteration waman kafara falā yaḥzunka kuf'ruhu ilaynā marjiʿuhum fanunabbi-uhum bimā ʿamilū inna l-laha ʿalīmun bidhāti l-ṣudūri

Hausa Kuma wanda ya kãfirta, to, kada kãfircinsa ya baƙanta maka rai, zuwa gare Mu makõmarsu take, sa'an nan Mu bã su lãbari game da abin da suka aikata. Lalle Allah, Masani ne ga abin da ke a cikin ƙirãza.

Verse 24

نُمَتِّعُهُمْ قَلِيلًا ثُمَّ نَضْطَرُّهُمْ إِلَىٰ عَذَابٍ غَلِيظٍ

Transliteration numattiʿuhum qalīlan thumma naḍṭarruhum ilā ʿadhābin ghalīẓin

Hausa Munã jĩshe su dãdi kaɗan sa'an nan Mu tĩlasta su ga shiga zuwa azãba kakkaura.

Verse 25

وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ ۚ قُلِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration wala-in sa-altahum man khalaqa l-samāwāti wal-arḍa layaqūlunna l-lahu quli l-ḥamdu lillahi bal aktharuhum lā yaʿlamūna

Hausa Kuma lalle, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halĩtta sammai da kasa?" Lalle zã su ce: "Allah ne." Ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah" Ã'a, mafi yawansu ba su sani ba.

Verse 26

لِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْغَنِىُّ ٱلْحَمِيدُ

Transliteration lillahi mā fī l-samāwāti wal-arḍi inna l-laha huwa l-ghaniyu l-ḥamīdu

Hausa Abin da yake a cikin sammai da ƙasa duka na Allah kawai ne. Lalle, Allah Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde.

Verse 27

وَلَوْ أَنَّمَا فِى ٱلْأَرْضِ مِن شَجَرَةٍ أَقْلَـٰمٌ وَٱلْبَحْرُ يَمُدُّهُۥ مِنۢ بَعْدِهِۦ سَبْعَةُ أَبْحُرٍ مَّا نَفِدَتْ كَلِمَـٰتُ ٱللَّهِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ

Transliteration walaw annamā fī l-arḍi min shajaratin aqlāmun wal-baḥru yamudduhu min baʿdihi sabʿatu abḥurin mā nafidat kalimātu l-lahi inna l-laha ʿazīzun ḥakīmun

Hausa Kuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su ƙãre ba. Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.

Verse 28

مَّا خَلْقُكُمْ وَلَا بَعْثُكُمْ إِلَّا كَنَفْسٍ وَٰحِدَةٍ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌۢ بَصِيرٌ

Transliteration mā khalqukum walā baʿthukum illā kanafsin wāḥidatin inna l-laha samīʿun baṣīrun

Hausa Halittarku bã ta zama ba, kuma tãyar da ku bai zama ba, fãce kamar rai guda. Lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani.

Verse 29

أَلَمْ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يُولِجُ ٱلَّيْلَ فِى ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِى ٱلَّيْلِ وَسَخَّرَ ٱلشَّمْسَ وَٱلْقَمَرَ كُلٌّ يَجْرِىٓ إِلَىٰٓ أَجَلٍ مُّسَمًّى وَأَنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ

Transliteration alam tara anna l-laha yūliju al-layla fī l-nahāri wayūliju l-nahāra fī al-layli wasakhara l-shamsa wal-qamara kullun yajrī ilā ajalin musamman wa-anna l-laha bimā taʿmalūna khabīrun

Hausa Ashe, ba ku ga, lalle, Allah Yanã shigar da dare a cikin rãna ba, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare kuma Yã hõre rãnã da watã kõwane yanã gudãna zuwa a ajali ambatacce kuma lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa?

Verse 30

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِ ٱلْبَـٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْعَلِىُّ ٱلْكَبِيرُ

Transliteration dhālika bi-anna l-laha huwa l-ḥaqu wa-anna mā yadʿūna min dūnihi l-bāṭilu wa-anna l-laha huwa l-ʿaliyu l-kabīru

Hausa Wannan fa dõmin Allah Shĩ ne Gaskiya, kuma abin da suke kira wanda bã Shi ba, shi ne ƙaryã, kuma lalle, Alah shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.

Verse 31

أَلَمْ تَرَ أَنَّ ٱلْفُلْكَ تَجْرِى فِى ٱلْبَحْرِ بِنِعْمَتِ ٱللَّهِ لِيُرِيَكُم مِّنْ ءَايَـٰتِهِۦٓ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ

Transliteration alam tara anna l-ful'ka tajrī fī l-baḥri biniʿ'mati l-lahi liyuriyakum min āyātihi inna fī dhālika laāyātin likulli ṣabbārin shakūrin

Hausa Ashe, ba ka ga lalle jirgin ruwa nã gudãna ba a cikin tẽku da ni'imar Allah dõmin Ya nũna muku daga ãyõyinSa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, mai gõdiya.

Verse 32

وَإِذَا غَشِيَهُم مَّوْجٌ كَٱلظُّلَلِ دَعَوُا۟ ٱللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمْ إِلَى ٱلْبَرِّ فَمِنْهُم مُّقْتَصِدٌ ۚ وَمَا يَجْحَدُ بِـَٔايَـٰتِنَآ إِلَّا كُلُّ خَتَّارٍ كَفُورٍ

Transliteration wa-idhā ghashiyahum mawjun kal-ẓulali daʿawū l-laha mukh'liṣīna lahu l-dīna falammā najjāhum ilā l-bari famin'hum muq'taṣidun wamā yajḥadu biāyātinā illā kullu khattārin kafūrin

Hausa Kuma idan tãguwar ruwa, kamar duwatsu, ta rufe su, sai su kira Allah sunã tsarkakẽwar addini a gare shi. To, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudu, sai daga cikinsu akwai mai taƙaitãwa kuma bãbu mai musun ãyõyin Mu fãce dukkan mayaudari mai yawan kãfirci.

Verse 33

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُوا۟ رَبَّكُمْ وَٱخْشَوْا۟ يَوْمًا لَّا يَجْزِى وَالِدٌ عَن وَلَدِهِۦ وَلَا مَوْلُودٌ هُوَ جَازٍ عَن وَالِدِهِۦ شَيْـًٔا ۚ إِنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّ ۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا وَلَا يَغُرَّنَّكُم بِٱللَّهِ ٱلْغَرُورُ

Transliteration yāayyuhā l-nāsu ittaqū rabbakum wa-ikh'shaw yawman lā yajzī wālidun ʿan waladihi walā mawlūdun huwa jāzin ʿan wālidihi shayan inna waʿda l-lahi ḥaqqun falā taghurrannakumu l-ḥayatu l-dun'yā walā yaghurrannakum bil-lahi l-gharūru

Hausa Ya ku mutãne! Ku bauta wa Ubangijinku da taƙawa, kuma ku ji tsõron wani yini, rãnar da wani mahaifi bã ya sãka wa abin haifuwarsa da kõme kuma wani abin haifuwa bã ya sãka wa mahaifinsa da kõme. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Sabõda haka, kada wata rãyuwa ta kusa ta rũde ku, kuma kada marũɗin nan ya rũɗẽ ku game da Allah.

Verse 34

إِنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥ عِلْمُ ٱلسَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ ٱلْغَيْثَ وَيَعْلَمُ مَا فِى ٱلْأَرْحَامِ ۖ وَمَا تَدْرِى نَفْسٌ مَّاذَا تَكْسِبُ غَدًا ۖ وَمَا تَدْرِى نَفْسٌۢ بِأَىِّ أَرْضٍ تَمُوتُ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌۢ

Transliteration inna l-laha ʿindahu ʿil'mu l-sāʿati wayunazzilu l-ghaytha wayaʿlamu mā fī l-arḥāmi wamā tadrī nafsun mādhā taksibu ghadan wamā tadrī nafsun bi-ayyi arḍin tamūtu inna l-laha ʿalīmun khabīrun

Hausa Lalle, Allah a wurinsa kawai sanin sa'a yake, kuma Yanã saukar da girgije, kuma Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa.

Read Surah Luqman in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.