Surah An-Najm in Hausa: translation and audio
Surah 53 · النجم · The Star · 62 verses
Surah An-Najm verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah An-Najm word by word in English.
Verse 1
وَٱلنَّجْمِ إِذَا هَوَىٰ
Transliteration wal-najmi idhā hawā
Hausa Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.
Verse 2
مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَىٰ
Transliteration mā ḍalla ṣāḥibukum wamā ghawā
Hausa Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.
Verse 3
وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلْهَوَىٰٓ
Transliteration wamā yanṭiqu ʿani l-hawā
Hausa Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
Verse 4
إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْىٌ يُوحَىٰ
Transliteration in huwa illā waḥyun yūḥā
Hausa (Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.
Verse 5
عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلْقُوَىٰ
Transliteration ʿallamahu shadīdu l-quwā
Hausa (Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.
Verse 6
ذُو مِرَّةٍ فَٱسْتَوَىٰ
Transliteration dhū mirratin fa-is'tawā
Hausa Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.
Verse 7
وَهُوَ بِٱلْأُفُقِ ٱلْأَعْلَىٰ
Transliteration wahuwa bil-ufuqi l-aʿlā
Hausa Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi daukaka.
Verse 8
ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ
Transliteration thumma danā fatadallā
Hausa Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.
Verse 9
فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَىٰ
Transliteration fakāna qāba qawsayni aw adnā
Hausa Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.
Verse 10
فَأَوْحَىٰٓ إِلَىٰ عَبْدِهِۦ مَآ أَوْحَىٰ
Transliteration fa-awḥā ilā ʿabdihi mā awḥā
Hausa Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).
Verse 11
مَا كَذَبَ ٱلْفُؤَادُ مَا رَأَىٰٓ
Transliteration mā kadhaba l-fuādu mā raā
Hausa Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.
Verse 12
أَفَتُمَـٰرُونَهُۥ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ
Transliteration afatumārūnahu ʿalā mā yarā
Hausa Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?
Verse 13
وَلَقَدْ رَءَاهُ نَزْلَةً أُخْرَىٰ
Transliteration walaqad raāhu nazlatan ukh'rā
Hausa Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.
Verse 14
عِندَ سِدْرَةِ ٱلْمُنتَهَىٰ
Transliteration ʿinda sid'rati l-muntahā
Hausa A wurin da magaryar tuƙẽwa take.
Verse 15
عِندَهَا جَنَّةُ ٱلْمَأْوَىٰٓ
Transliteration ʿindahā jannatu l-mawā
Hausa A inda taken, nan Aljannar makoma take.
Verse 16
إِذْ يَغْشَى ٱلسِّدْرَةَ مَا يَغْشَىٰ
Transliteration idh yaghshā l-sid'rata mā yaghshā
Hausa Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.
Verse 17
مَا زَاغَ ٱلْبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ
Transliteration mā zāgha l-baṣaru wamā ṭaghā
Hausa Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
Verse 18
لَقَدْ رَأَىٰ مِنْ ءَايَـٰتِ رَبِّهِ ٱلْكُبْرَىٰٓ
Transliteration laqad raā min āyāti rabbihi l-kub'rā
Hausa Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.
Verse 19
أَفَرَءَيْتُمُ ٱللَّـٰتَ وَٱلْعُزَّىٰ
Transliteration afara-aytumu l-lāta wal-ʿuzā
Hausa Shin, kun ga Lãta da uzza?
Verse 20
وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلْأُخْرَىٰٓ
Transliteration wamanata l-thālithata l-ukh'rā
Hausa Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?
Verse 21
أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلْأُنثَىٰ
Transliteration alakumu l-dhakaru walahu l-unthā
Hausa Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?
Verse 22
تِلْكَ إِذًا قِسْمَةٌ ضِيزَىٰٓ
Transliteration til'ka idhan qis'matun ḍīzā
Hausa Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.
Verse 23
إِنْ هِىَ إِلَّآ أَسْمَآءٌ سَمَّيْتُمُوهَآ أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلْطَـٰنٍ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهْوَى ٱلْأَنفُسُ ۖ وَلَقَدْ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلْهُدَىٰٓ
Transliteration in hiya illā asmāon sammaytumūhā antum waābāukum mā anzala l-lahu bihā min sul'ṭānin in yattabiʿūna illā l-ẓana wamā tahwā l-anfusu walaqad jāahum min rabbihimu l-hudā
Hausa Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).
Verse 24
أَمْ لِلْإِنسَـٰنِ مَا تَمَنَّىٰ
Transliteration am lil'insāni mā tamannā
Hausa Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?
Verse 25
فَلِلَّهِ ٱلْـَٔاخِرَةُ وَٱلْأُولَىٰ
Transliteration falillahi l-ākhiratu wal-ūlā
Hausa To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).
Verse 26
۞ وَكَم مِّن مَّلَكٍ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ لَا تُغْنِى شَفَـٰعَتُهُمْ شَيْـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعْدِ أَن يَأْذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرْضَىٰٓ
Transliteration wakam min malakin fī l-samāwāti lā tugh'nī shafāʿatuhum shayan illā min baʿdi an yadhana l-lahu liman yashāu wayarḍā
Hausa Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.
Verse 27
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ لَيُسَمُّونَ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ تَسْمِيَةَ ٱلْأُنثَىٰ
Transliteration inna alladhīna lā yu'minūna bil-ākhirati layusammūna l-malāikata tasmiyata l-unthā
Hausa Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.
Verse 28
وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ ۖ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغْنِى مِنَ ٱلْحَقِّ شَيْـًٔا
Transliteration wamā lahum bihi min ʿil'min in yattabiʿūna illā l-ẓana wa-inna l-ẓana lā yugh'nī mina l-ḥaqi shayan
Hausa Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.
Verse 29
فَأَعْرِضْ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكْرِنَا وَلَمْ يُرِدْ إِلَّا ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا
Transliteration fa-aʿriḍ ʿan man tawallā ʿan dhik'rinā walam yurid illā l-ḥayata l-dun'yā
Hausa Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).
Verse 30
ذَٰلِكَ مَبْلَغُهُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ ٱهْتَدَىٰ
Transliteration dhālika mablaghuhum mina l-ʿil'mi inna rabbaka huwa aʿlamu biman ḍalla ʿan sabīlihi wahuwa aʿlamu bimani ih'tadā
Hausa Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.
Verse 31
وَلِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ لِيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔوا۟ بِمَا عَمِلُوا۟ وَيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ بِٱلْحُسْنَى
Transliteration walillahi mā fī l-samāwāti wamā fī l-arḍi liyajziya alladhīna asāū bimā ʿamilū wayajziya alladhīna aḥsanū bil-ḥus'nā
Hausa Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.
Verse 32
ٱلَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلْإِثْمِ وَٱلْفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلْمَغْفِرَةِ ۚ هُوَ أَعْلَمُ بِكُمْ إِذْ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ وَإِذْ أَنتُمْ أَجِنَّةٌ فِى بُطُونِ أُمَّهَـٰتِكُمْ ۖ فَلَا تُزَكُّوٓا۟ أَنفُسَكُمْ ۖ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ
Transliteration alladhīna yajtanibūna kabāira l-ith'mi wal-fawāḥisha illā l-lamama inna rabbaka wāsiʿu l-maghfirati huwa aʿlamu bikum idh ansha-akum mina l-arḍi wa-idh antum ajinnatun fī buṭūni ummahātikum falā tuzakkū anfusakum huwa aʿlamu bimani ittaqā
Hausa Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.
Verse 33
أَفَرَءَيْتَ ٱلَّذِى تَوَلَّىٰ
Transliteration afara-ayta alladhī tawallā
Hausa Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?
Verse 34
وَأَعْطَىٰ قَلِيلًا وَأَكْدَىٰٓ
Transliteration wa-aʿṭā qalīlan wa-akdā
Hausa Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?
Verse 35
أَعِندَهُۥ عِلْمُ ٱلْغَيْبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ
Transliteration aʿindahu ʿil'mu l-ghaybi fahuwa yarā
Hausa Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?
Verse 36
أَمْ لَمْ يُنَبَّأْ بِمَا فِى صُحُفِ مُوسَىٰ
Transliteration am lam yunabba bimā fī ṣuḥufi mūsā
Hausa Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?
Verse 37
وَإِبْرَٰهِيمَ ٱلَّذِى وَفَّىٰٓ
Transliteration wa-ib'rāhīma alladhī waffā
Hausa Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?
Verse 38
أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ
Transliteration allā taziru wāziratun wiz'ra ukh'rā
Hausa Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.
Verse 39
وَأَن لَّيْسَ لِلْإِنسَـٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ
Transliteration wa-an laysa lil'insāni illā mā saʿā
Hausa Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.
Verse 40
وَأَنَّ سَعْيَهُۥ سَوْفَ يُرَىٰ
Transliteration wa-anna saʿyahu sawfa yurā
Hausa Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi.
Verse 41
ثُمَّ يُجْزَىٰهُ ٱلْجَزَآءَ ٱلْأَوْفَىٰ
Transliteration thumma yuj'zāhu l-jazāa l-awfā
Hausa Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?
Verse 42
وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلْمُنتَهَىٰ
Transliteration wa-anna ilā rabbika l-muntahā
Hausa Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?
Verse 43
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰ
Transliteration wa-annahu huwa aḍḥaka wa-abkā
Hausa Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.
Verse 44
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحْيَا
Transliteration wa-annahu huwa amāta wa-aḥyā
Hausa Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.
Verse 45
وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰ
Transliteration wa-annahu khalaqa l-zawjayni l-dhakara wal-unthā
Hausa Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
Verse 46
مِن نُّطْفَةٍ إِذَا تُمْنَىٰ
Transliteration min nuṭ'fatin idhā tum'nā
Hausa Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
Verse 47
وَأَنَّ عَلَيْهِ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْأُخْرَىٰ
Transliteration wa-anna ʿalayhi l-nashata l-ukh'rā
Hausa Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
Verse 48
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغْنَىٰ وَأَقْنَىٰ
Transliteration wa-annahu huwa aghnā wa-aqnā
Hausa Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
Verse 49
وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعْرَىٰ
Transliteration wa-annahu huwa rabbu l-shiʿ'rā
Hausa Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.
Verse 50
وَأَنَّهُۥٓ أَهْلَكَ عَادًا ٱلْأُولَىٰ
Transliteration wa-annahu ahlaka ʿādan l-ūlā
Hausa Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.
Verse 51
وَثَمُودَا۟ فَمَآ أَبْقَىٰ
Transliteration wathamūdā famā abqā
Hausa Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
Verse 52
وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ هُمْ أَظْلَمَ وَأَطْغَىٰ
Transliteration waqawma nūḥin min qablu innahum kānū hum aẓlama wa-aṭghā
Hausa Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.
Verse 53
وَٱلْمُؤْتَفِكَةَ أَهْوَىٰ
Transliteration wal-mu'tafikata ahwā
Hausa Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.
Verse 54
فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ
Transliteration faghashāhā mā ghashā
Hausa Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
Verse 55
فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ
Transliteration fabi-ayyi ālāi rabbika tatamārā
Hausa To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka?
Verse 56
هَـٰذَا نَذِيرٌ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلْأُولَىٰٓ
Transliteration hādhā nadhīrun mina l-nudhuri l-ūlā
Hausa wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
Verse 57
أَزِفَتِ ٱلْـَٔازِفَةُ
Transliteration azifati l-āzifatu
Hausa Makusanciya fa, tã yi kusa.
Verse 58
لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ
Transliteration laysa lahā min dūni l-lahi kāshifatun
Hausa Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
Verse 59
أَفَمِنْ هَـٰذَا ٱلْحَدِيثِ تَعْجَبُونَ
Transliteration afamin hādhā l-ḥadīthi taʿjabūna
Hausa Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki?
Verse 60
وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَ
Transliteration wataḍḥakūna walā tabkūna
Hausa Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
Verse 61
وَأَنتُمْ سَـٰمِدُونَ
Transliteration wa-antum sāmidūna
Hausa Alhãli kunã mãsu wãsã?
Verse 62
فَٱسْجُدُوا۟ لِلَّهِ وَٱعْبُدُوا۟ ۩
Transliteration fa-us'judū lillahi wa-uʿ'budū
Hausa To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa).
Read Surah An-Najm in another language
- English (word by word)
- Albanian
- Amazigh
- Amharic
- Assamese
- Azerbaijani
- Bambara
- Bangla
- Bosnian
- Bulgarian
- Chechen
- Chinese
- Czech
- Dari
- Dhivehi
- Dutch
- Finnish
- French
- German
- Gujarati
- Hebrew
- Hindi
- Indonesian
- Italian
- Japanese
- Kannada
- Kazakh
- Khmer
- Kinyarwanda
- Korean
- Kurdish
- Luganda
- Malay
- Malayalam
- Maranao
- Marathi
- Nepali
- Norwegian
- Oromo
- Pashto
- Persian
- Polish
- Portuguese
- Romanian
- Russian
- Sindhi
- Sinhala
- Somali
- Spanish
- Swahili
- Swedish
- Tagalog
- Tajik
- Tamil
- Tatar
- Telugu
- Thai
- Turkish
- Ukrainian
- Urdu
- Uyghur
- Uzbek
- Vietnamese
- Yao
- Yoruba
All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.
Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.