Surah Muhammad in Hausa: translation and audio
Surah 47 · محمد · Muhammad · 38 verses
Surah Muhammad verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Muhammad word by word in English.
Verse 1
ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ أَضَلَّ أَعْمَـٰلَهُمْ
Transliteration alladhīna kafarū waṣaddū ʿan sabīli l-lahi aḍalla aʿmālahum
Hausa Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange mutãne daga tafarkin Allah, (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu.
Verse 2
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَءَامَنُوا۟ بِمَا نُزِّلَ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَهُوَ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّهِمْ ۙ كَفَّرَ عَنْهُمْ سَيِّـَٔاتِهِمْ وَأَصْلَحَ بَالَهُمْ
Transliteration wa-alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti waāmanū bimā nuzzila ʿalā muḥammadin wahuwa l-ḥaqu min rabbihim kaffara ʿanhum sayyiātihim wa-aṣlaḥa bālahum
Hausa Kuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu.
Verse 3
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ٱتَّبَعُوا۟ ٱلْبَـٰطِلَ وَأَنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّبَعُوا۟ ٱلْحَقَّ مِن رَّبِّهِمْ ۚ كَذَٰلِكَ يَضْرِبُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ أَمْثَـٰلَهُمْ
Transliteration dhālika bi-anna alladhīna kafarū ittabaʿū l-bāṭila wa-anna alladhīna āmanū ittabaʿū l-ḥaqa min rabbihim kadhālika yaḍribu l-lahu lilnnāsi amthālahum
Hausa Wannan kuwa sabõda lalle, waɗanda suka kãfirta sun bi ƙarya, kumar lalle waɗanda suka yi ĩmãni, sun bi gaskiya daga Ubangijinsu. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana wa mutãne misãlansu.
Verse 4
فَإِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَضَرْبَ ٱلرِّقَابِ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَثْخَنتُمُوهُمْ فَشُدُّوا۟ ٱلْوَثَاقَ فَإِمَّا مَنًّۢا بَعْدُ وَإِمَّا فِدَآءً حَتَّىٰ تَضَعَ ٱلْحَرْبُ أَوْزَارَهَا ۚ ذَٰلِكَ وَلَوْ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَٱنتَصَرَ مِنْهُمْ وَلَـٰكِن لِّيَبْلُوَا۟ بَعْضَكُم بِبَعْضٍ ۗ وَٱلَّذِينَ قُتِلُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَن يُضِلَّ أَعْمَـٰلَهُمْ
Transliteration fa-idhā laqītumu alladhīna kafarū faḍarba l-riqābi ḥattā idhā athkhantumūhum fashuddū l-wathāqa fa-immā mannan baʿdu wa-immā fidāan ḥattā taḍaʿa l-ḥarbu awzārahā dhālika walaw yashāu l-lahu la-intaṣara min'hum walākin liyabluwā baʿḍakum bibaʿḍin wa-alladhīna qutilū fī sabīli l-lahi falan yuḍilla aʿmālahum
Hausa Sabõda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta, sai ku yi ta dũkan wuyõyinsu har a lõkacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma karimci a bãyan' haka kõ biyan fansa, har yãƙi ya saukar da kayansa mãsu nauyi. Wancan, dã Allah nã so da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaƙin ba) kuma amma (ya wajabta jihadi) dõmin Ya jarraba sãshenku da sãshe. Kuma waɗanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah, to, bã ai ɓatar da ayyukansu ba.
Verse 5
سَيَهْدِيهِمْ وَيُصْلِحُ بَالَهُمْ
Transliteration sayahdīhim wayuṣ'liḥu bālahum
Hausa Zai shiryar da su, kuma Ya kyautata hãlãyensu.
Verse 6
وَيُدْخِلُهُمُ ٱلْجَنَّةَ عَرَّفَهَا لَهُمْ
Transliteration wayud'khiluhumu l-janata ʿarrafahā lahum
Hausa Kuma Ya shigarda su Aljanna (wadda) Ya siffanta ta a gare su.
Verse 7
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِن تَنصُرُوا۟ ٱللَّهَ يَنصُرْكُمْ وَيُثَبِّتْ أَقْدَامَكُمْ
Transliteration yāayyuhā alladhīna āmanū in tanṣurū l-laha yanṣur'kum wayuthabbit aqdāmakum
Hausa Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku..
Verse 8
وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَتَعْسًا لَّهُمْ وَأَضَلَّ أَعْمَـٰلَهُمْ
Transliteration wa-alladhīna kafarū fataʿsan lahum wa-aḍalla aʿmālahum
Hausa Kuma waɗanda suka kãfirta, to, ruɓushi ya tabbata a gare su, kuma (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu.
Verse 9
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَرِهُوا۟ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأَحْبَطَ أَعْمَـٰلَهُمْ
Transliteration dhālika bi-annahum karihū mā anzala l-lahu fa-aḥbaṭa aʿmālahum
Hausa Wannan, sabõda lalle sũ, sun ƙi abin da Allah Ya saukar dõmin haka Ya ɓata ayyukansu.
Verse 10
۞ أَفَلَمْ يَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَيَنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ دَمَّرَ ٱللَّهُ عَلَيْهِمْ ۖ وَلِلْكَـٰفِرِينَ أَمْثَـٰلُهَا
Transliteration afalam yasīrū fī l-arḍi fayanẓurū kayfa kāna ʿāqibatu alladhīna min qablihim dammara l-lahu ʿalayhim walil'kāfirīna amthāluhā
Hausa Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai (na kõwane zãmani).
Verse 11
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ مَوْلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَأَنَّ ٱلْكَـٰفِرِينَ لَا مَوْلَىٰ لَهُمْ
Transliteration dhālika bi-anna l-laha mawlā alladhīna āmanū wa-anna l-kāfirīna lā mawlā lahum
Hausa Wancan! Sabõda lalle Allah ne Majiɓincin waɗanda suka yi ĩmãni, kuma lalle, kafirai bãbu wani majiɓinci a gare su.
Verse 12
إِنَّ ٱللَّهَ يُدْخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ جَنَّـٰتٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يَتَمَتَّعُونَ وَيَأْكُلُونَ كَمَا تَأْكُلُ ٱلْأَنْعَـٰمُ وَٱلنَّارُ مَثْوًى لَّهُمْ
Transliteration inna l-laha yud'khilu alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti jannātin tajrī min taḥtihā l-anhāru wa-alladhīna kafarū yatamattaʿūna wayakulūna kamā takulu l-anʿāmu wal-nāru mathwan lahum
Hausa Lalle ne, Allah nã shigar da waɗanda suka yi ĩmani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jin ɗan daɗi (adũniya) kuma sunã ci, kamar yadda dabbõbi ke ci, kuma wutã ita ce mazauni a gare su.
Verse 13
وَكَأَيِّن مِّن قَرْيَةٍ هِىَ أَشَدُّ قُوَّةً مِّن قَرْيَتِكَ ٱلَّتِىٓ أَخْرَجَتْكَ أَهْلَكْنَـٰهُمْ فَلَا نَاصِرَ لَهُمْ
Transliteration waka-ayyin min qaryatin hiya ashaddu quwwatan min qaryatika allatī akhrajatka ahlaknāhum falā nāṣira lahum
Hausa Kuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa bãbu wani mai taimako a gare su.
Verse 14
أَفَمَن كَانَ عَلَىٰ بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّهِۦ كَمَن زُيِّنَ لَهُۥ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ وَٱتَّبَعُوٓا۟ أَهْوَآءَهُم
Transliteration afaman kāna ʿalā bayyinatin min rabbihi kaman zuyyina lahu sūu ʿamalihi wa-ittabaʿū ahwāahum
Hausa Shin, wanda ya kasance a kan wata hujja daga Ubangijinsa, zai zama kamar wanda aka ƙawãce masa mugun aikinsa, kuma suka bibbiyi son zũciyõyinsu?
Verse 15
مَّثَلُ ٱلْجَنَّةِ ٱلَّتِى وُعِدَ ٱلْمُتَّقُونَ ۖ فِيهَآ أَنْهَـٰرٌ مِّن مَّآءٍ غَيْرِ ءَاسِنٍ وَأَنْهَـٰرٌ مِّن لَّبَنٍ لَّمْ يَتَغَيَّرْ طَعْمُهُۥ وَأَنْهَـٰرٌ مِّنْ خَمْرٍ لَّذَّةٍ لِّلشَّـٰرِبِينَ وَأَنْهَـٰرٌ مِّنْ عَسَلٍ مُّصَفًّى ۖ وَلَهُمْ فِيهَا مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ وَمَغْفِرَةٌ مِّن رَّبِّهِمْ ۖ كَمَنْ هُوَ خَـٰلِدٌ فِى ٱلنَّارِ وَسُقُوا۟ مَآءً حَمِيمًا فَقَطَّعَ أَمْعَآءَهُمْ
Transliteration mathalu l-janati allatī wuʿida l-mutaqūna fīhā anhārun min māin ghayri āsinin wa-anhārun min labanin lam yataghayyar ṭaʿmuhu wa-anhārun min khamrin ladhatin lilshāribīna wa-anhārun min ʿasalin muṣaffan walahum fīhā min kulli l-thamarāti wamaghfiratun min rabbihim kaman huwa khālidun fī l-nāri wasuqū māan ḥamīman faqaṭṭaʿa amʿāahum
Hausa Misãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata gãfara daga Ubangijinsu. (Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya kakkãtse hanjinsu?
Verse 16
وَمِنْهُم مَّن يَسْتَمِعُ إِلَيْكَ حَتَّىٰٓ إِذَا خَرَجُوا۟ مِنْ عِندِكَ قَالُوا۟ لِلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ مَاذَا قَالَ ءَانِفًا ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ وَٱتَّبَعُوٓا۟ أَهْوَآءَهُمْ
Transliteration wamin'hum man yastamiʿu ilayka ḥattā idhā kharajū min ʿindika qālū lilladhīna ūtū l-ʿil'ma mādhā qāla ānifan ulāika alladhīna ṭabaʿa l-lahu ʿalā qulūbihim wa-ittabaʿū ahwāahum
Hausa Kuma daga cikinsu akwai wanda ke saurare zuwa gare ka, har idan sun fita daga wurinka, su ce wa waɗanda aka bai wa ilmi "Mẽne ne (Muhammadu) ya fãɗa ɗazu?" Waɗannan ne waɗanda Allah Ya shãfe haske daga zukãtansu, kuma suka bi son zũciyõyinsu.
Verse 17
وَٱلَّذِينَ ٱهْتَدَوْا۟ زَادَهُمْ هُدًى وَءَاتَىٰهُمْ تَقْوَىٰهُمْ
Transliteration wa-alladhīna ih'tadaw zādahum hudan waātāhum taqwāhum
Hausa Kuma waɗannan da suka nẽmi shiryuwa (Allah) Ya ƙara musu shiryuwarsu, kuma Yã bã su (sakamakon) taƙawarsu.
Verse 18
فَهَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا ٱلسَّاعَةَ أَن تَأْتِيَهُم بَغْتَةً ۖ فَقَدْ جَآءَ أَشْرَاطُهَا ۚ فَأَنَّىٰ لَهُمْ إِذَا جَآءَتْهُمْ ذِكْرَىٰهُمْ
Transliteration fahal yanẓurūna illā l-sāʿata an tatiyahum baghtatan faqad jāa ashrāṭuhā fa-annā lahum idhā jāathum dhik'rāhum
Hausa To shin sunã jiran (wani abu)? Fãce Sa'a ta jẽ musu bisa abku. dõmin lalle sharuɗɗanta sun zo. To, yãya tunãwarsu take, idan har ta jẽ musu?
Verse 19
فَٱعْلَمْ أَنَّهُۥ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ وَٱسْتَغْفِرْ لِذَنۢبِكَ وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَـٰتِ ۗ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ مُتَقَلَّبَكُمْ وَمَثْوَىٰكُمْ
Transliteration fa-iʿ'lam annahu lā ilāha illā l-lahu wa-is'taghfir lidhanbika walil'mu'minīna wal-mu'mināti wal-lahu yaʿlamu mutaqallabakum wamathwākum
Hausa Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka, (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku.
Verse 20
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَوْلَا نُزِّلَتْ سُورَةٌ ۖ فَإِذَآ أُنزِلَتْ سُورَةٌ مُّحْكَمَةٌ وَذُكِرَ فِيهَا ٱلْقِتَالُ ۙ رَأَيْتَ ٱلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ نَظَرَ ٱلْمَغْشِىِّ عَلَيْهِ مِنَ ٱلْمَوْتِ ۖ فَأَوْلَىٰ لَهُمْ
Transliteration wayaqūlu alladhīna āmanū lawlā nuzzilat sūratun fa-idhā unzilat sūratun muḥ'kamatun wadhukira fīhā l-qitālu ra-ayta alladhīna fī qulūbihim maraḍun yanẓurūna ilayka naẓara l-maghshiyi ʿalayhi mina l-mawti fa-awlā lahum
Hausa Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: "Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba? "To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a gare su:
Verse 21
طَاعَةٌ وَقَوْلٌ مَّعْرُوفٌ ۚ فَإِذَا عَزَمَ ٱلْأَمْرُ فَلَوْ صَدَقُوا۟ ٱللَّهَ لَكَانَ خَيْرًا لَّهُمْ
Transliteration ṭāʿatun waqawlun maʿrūfun fa-idhā ʿazama l-amru falaw ṣadaqū l-laha lakāna khayran lahum
Hausa Yin ɗã'a da magana mai kyau. Sa'an nan idan al'marin ya ƙullu, to, dã sun yi wa Allah gaskiya, lalle dã ya kasance mafifi ci a gare su.
Verse 22
فَهَلْ عَسَيْتُمْ إِن تَوَلَّيْتُمْ أَن تُفْسِدُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ وَتُقَطِّعُوٓا۟ أَرْحَامَكُمْ
Transliteration fahal ʿasaytum in tawallaytum an tuf'sidū fī l-arḍi watuqaṭṭiʿū arḥāmakum
Hausa To, shin, kunã fãtan idan kun jũya (daga umurnin) zã ku yi ɓarna a cikin ƙasã, kuma ku yan yanke zumuntarku?
Verse 23
أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُ فَأَصَمَّهُمْ وَأَعْمَىٰٓ أَبْصَـٰرَهُمْ
Transliteration ulāika alladhīna laʿanahumu l-lahu fa-aṣammahum wa-aʿmā abṣārahum
Hausa Waɗannan sũ ne waɗanda Allah Ya la'anẽ su, sa'an nan Ya kurumtar da su, kuma Ya makantar da ganinsu.
Verse 24
أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلْقُرْءَانَ أَمْ عَلَىٰ قُلُوبٍ أَقْفَالُهَآ
Transliteration afalā yatadabbarūna l-qur'āna am ʿalā qulūbin aqfāluhā
Hausa Shin to, bã zã su, kula da Alƙur'ãni ba, kõ kuwa a bin zukã tansu akwai makullansu?
Verse 25
إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱرْتَدُّوا۟ عَلَىٰٓ أَدْبَـٰرِهِم مِّنۢ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلْهُدَى ۙ ٱلشَّيْطَـٰنُ سَوَّلَ لَهُمْ وَأَمْلَىٰ لَهُمْ
Transliteration inna alladhīna ir'taddū ʿalā adbārihim min baʿdi mā tabayyana lahumu l-hudā l-shayṭānu sawwala lahum wa-amlā lahum
Hausa lalle ne, waɗanda suka kõma bãya a kan dugãdugansu a bãyan shiryuwa tã bayyana a gare su, Shaiɗan ne ya ƙawãta musu (haka), kuma ya yi musu shibta.
Verse 26
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا۟ لِلَّذِينَ كَرِهُوا۟ مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ سَنُطِيعُكُمْ فِى بَعْضِ ٱلْأَمْرِ ۖ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ إِسْرَارَهُمْ
Transliteration dhālika bi-annahum qālū lilladhīna karihū mā nazzala l-lahu sanuṭīʿukum fī baʿḍi l-amri wal-lahu yaʿlamu is'rārahum
Hausa Wancan, dõmin lalle sũ sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: "Za mu yi muku ɗã'ã ga sãshen al'amarin," alhãli kuwa Allah Yanã sane da gãnawarsu ta asĩri.
Verse 27
فَكَيْفَ إِذَا تَوَفَّتْهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ يَضْرِبُونَ وُجُوهَهُمْ وَأَدْبَـٰرَهُمْ
Transliteration fakayfa idhā tawaffathumu l-malāikatu yaḍribūna wujūhahum wa-adbārahum
Hausa To, yãya hãlinsu yake a lõkacin da malã'iku ke karɓar rãyukansu, sunã dũkan fuskõkinsu da ɗuwaiwansu?
Verse 28
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱتَّبَعُوا۟ مَآ أَسْخَطَ ٱللَّهَ وَكَرِهُوا۟ رِضْوَٰنَهُۥ فَأَحْبَطَ أَعْمَـٰلَهُمْ
Transliteration dhālika bi-annahumu ittabaʿū mā askhaṭa l-laha wakarihū riḍ'wānahu fa-aḥbaṭa aʿmālahum
Hausa Wannan, dõmin lalle sũ sun bi abin da ya, fusãtar da Allah kuma sun ƙi yardarSa, sabõda haka Ya ɓãta ayyukansu.
Verse 29
أَمْ حَسِبَ ٱلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَن لَّن يُخْرِجَ ٱللَّهُ أَضْغَـٰنَهُمْ
Transliteration am ḥasiba alladhīna fī qulūbihim maraḍun an lan yukh'rija l-lahu aḍghānahum
Hausa Ko kuwa waɗanda ke da wata cũta a cikin zukatansu suna zaton cẽwa Allah ba zai fitar da mugun ƙulle-ƙullen su (ga Musulunci) ba?
Verse 30
وَلَوْ نَشَآءُ لَأَرَيْنَـٰكَهُمْ فَلَعَرَفْتَهُم بِسِيمَـٰهُمْ ۚ وَلَتَعْرِفَنَّهُمْ فِى لَحْنِ ٱلْقَوْلِ ۚ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ أَعْمَـٰلَكُمْ
Transliteration walaw nashāu la-araynākahum falaʿaraftahum bisīmāhum walataʿrifannahum fī laḥni l-qawli wal-lahu yaʿlamu aʿmālakum
Hausa Kuma dã Munã so, dã lalle Mun nũna maka su. To, lalle kanã sanin su game da alãmarsu. Kuma lalle kanã sanin su ga shaguɓen magana, alhali kuwa Allah Yanã sanin ayyukanku.
Verse 31
وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّىٰ نَعْلَمَ ٱلْمُجَـٰهِدِينَ مِنكُمْ وَٱلصَّـٰبِرِينَ وَنَبْلُوَا۟ أَخْبَارَكُمْ
Transliteration walanabluwannakum ḥattā naʿlama l-mujāhidīna minkum wal-ṣābirīna wanabluwā akhbārakum
Hausa Kuma lalle ne, Munã jarraba ku, har Mu san mãsu jihãdi daga cikinku da mãsu haƙuri kuma Muna jbrraba lãbãran ku.
Verse 32
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَشَآقُّوا۟ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلْهُدَىٰ لَن يَضُرُّوا۟ ٱللَّهَ شَيْـًٔا وَسَيُحْبِطُ أَعْمَـٰلَهُمْ
Transliteration inna alladhīna kafarū waṣaddū ʿan sabīli l-lahi washāqqū l-rasūla min baʿdi mā tabayyana lahumu l-hudā lan yaḍurrū l-laha shayan wasayuḥ'biṭu aʿmālahum
Hausa Lalle ne, waɗanda suka kãfirta, kuma suka kange daga tafarkin Allah, kuma suka saɓa wa Manzon sa a bãyan shiriyar ta bayyana a gare su, bã za su cũci Allah da kõme ba, kuma zã Ya ɓãta ayyukansu.
Verse 33
۞ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَطِيعُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُوا۟ ٱلرَّسُولَ وَلَا تُبْطِلُوٓا۟ أَعْمَـٰلَكُمْ
Transliteration yāayyuhā alladhīna āmanū aṭīʿū l-laha wa-aṭīʿū l-rasūla walā tub'ṭilū aʿmālakum
Hausa Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗa'a ga Manzon Sa, kuma kada ku ɓãta ayyukanku.
Verse 34
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ مَاتُوا۟ وَهُمْ كُفَّارٌ فَلَن يَغْفِرَ ٱللَّهُ لَهُمْ
Transliteration inna alladhīna kafarū waṣaddū ʿan sabīli l-lahi thumma mātū wahum kuffārun falan yaghfira l-lahu lahum
Hausa Lalle ne waɗanda suka kãfirta sa'an nan kuma suka kange (mutãne) daga tafarkin Allah, sa'an nan suka mutu, alhãli kuwa sunã kãfirai, to, Allah bã zai yi gãfara ba a gare su.
Verse 35
فَلَا تَهِنُوا۟ وَتَدْعُوٓا۟ إِلَى ٱلسَّلْمِ وَأَنتُمُ ٱلْأَعْلَوْنَ وَٱللَّهُ مَعَكُمْ وَلَن يَتِرَكُمْ أَعْمَـٰلَكُمْ
Transliteration falā tahinū watadʿū ilā l-salmi wa-antumu l-aʿlawna wal-lahu maʿakum walan yatirakum aʿmālakum
Hausa Sabõda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zũwaga sulhi alhãli kuwa kũ ne mafiɗaukaka kuma Allah na tãre da ku, kuma bã, zai naƙasa muku ayyukanku ba.
Verse 36
إِنَّمَا ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا لَعِبٌ وَلَهْوٌ ۚ وَإِن تُؤْمِنُوا۟ وَتَتَّقُوا۟ يُؤْتِكُمْ أُجُورَكُمْ وَلَا يَسْـَٔلْكُمْ أَمْوَٰلَكُمْ
Transliteration innamā l-ḥayatu l-dun'yā laʿibun walahwun wa-in tu'minū watattaqū yu'tikum ujūrakum walā yasalkum amwālakum
Hausa Rãyuwar dũniya, wãsã da abin shagala kawai ce, kuma idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, Allah zai kãwo muku ijarõrinku, kuma bã zai tambaye ku dũkiyarku ba.
Verse 37
إِن يَسْـَٔلْكُمُوهَا فَيُحْفِكُمْ تَبْخَلُوا۟ وَيُخْرِجْ أَضْغَـٰنَكُمْ
Transliteration in yasalkumūhā fayuḥ'fikum tabkhalū wayukh'rij aḍghānakum
Hausa Dã Allah zai tambaye ku su (dũkiyõyin) har Ya wajabta muku bãyarwa, zã ku yi rõwa kuma Ya fitar da miyãgun ƙulle-ƙullenku.
Verse 38
هَـٰٓأَنتُمْ هَـٰٓؤُلَآءِ تُدْعَوْنَ لِتُنفِقُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ فَمِنكُم مَّن يَبْخَلُ ۖ وَمَن يَبْخَلْ فَإِنَّمَا يَبْخَلُ عَن نَّفْسِهِۦ ۚ وَٱللَّهُ ٱلْغَنِىُّ وَأَنتُمُ ٱلْفُقَرَآءُ ۚ وَإِن تَتَوَلَّوْا۟ يَسْتَبْدِلْ قَوْمًا غَيْرَكُمْ ثُمَّ لَا يَكُونُوٓا۟ أَمْثَـٰلَكُم
Transliteration hāantum hāulāi tud'ʿawna litunfiqū fī sabīli l-lahi faminkum man yabkhalu waman yabkhal fa-innamā yabkhalu ʿan nafsihi wal-lahu l-ghaniyu wa-antumu l-fuqarāu wa-in tatawallaw yastabdil qawman ghayrakum thumma lā yakūnū amthālakum
Hausa Ga ku, ya ku waɗannan! Anã kiran ku dõmin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa'an nan daga cikinku akwai mai yin rõwa. Kuma wanda ke yin rõwa, to, yanã yin rõwar ne ga kansa. Kuma Allah ne wadãtacce alhãli kuwa kũ fãƙĩrai ne. Kuma idan kuka jũya (daga yi Masa ɗã'a), zai musanya waɗansu mutãne waɗansunku sa'an nan bã zã su kasance kwatankwacinku ba.
Read Surah Muhammad in another language
- English (word by word)
- Albanian
- Amazigh
- Amharic
- Assamese
- Azerbaijani
- Bambara
- Bangla
- Bosnian
- Bulgarian
- Chechen
- Chinese
- Czech
- Dari
- Dhivehi
- Dutch
- Finnish
- French
- German
- Gujarati
- Hebrew
- Hindi
- Indonesian
- Italian
- Japanese
- Kannada
- Kazakh
- Khmer
- Kinyarwanda
- Korean
- Kurdish
- Luganda
- Malay
- Malayalam
- Maranao
- Marathi
- Nepali
- Norwegian
- Oromo
- Pashto
- Persian
- Polish
- Portuguese
- Romanian
- Russian
- Sindhi
- Sinhala
- Somali
- Spanish
- Swahili
- Swedish
- Tagalog
- Tajik
- Tamil
- Tatar
- Telugu
- Thai
- Turkish
- Ukrainian
- Urdu
- Uyghur
- Uzbek
- Vietnamese
- Yao
- Yoruba
All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.
Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.