MyDugsiStart learning

Surah Ar-Rum in Hausa: translation and audio

Surah 30 · الروم · The Romans · 60 verses

Surah Ar-Rum verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Ar-Rum word by word in English.

Verse 1

الٓمٓ

Transliteration alif-lam-meem

Hausa A. L̃. M̃.

Verse 2

غُلِبَتِ ٱلرُّومُ

Transliteration ghulibati l-rūmu

Hausa An rinjãyi Rũmawa.

Verse 3

فِىٓ أَدْنَى ٱلْأَرْضِ وَهُم مِّنۢ بَعْدِ غَلَبِهِمْ سَيَغْلِبُونَ

Transliteration fī adnā l-arḍi wahum min baʿdi ghalabihim sayaghlibūna

Hausa A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya.

Verse 4

فِى بِضْعِ سِنِينَ ۗ لِلَّهِ ٱلْأَمْرُ مِن قَبْلُ وَمِنۢ بَعْدُ ۚ وَيَوْمَئِذٍ يَفْرَحُ ٱلْمُؤْمِنُونَ

Transliteration fī biḍ'ʿi sinīna lillahi l-amru min qablu wamin baʿdu wayawma-idhin yafraḥu l-mu'minūna

Hausa A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki.

Verse 5

بِنَصْرِ ٱللَّهِ ۚ يَنصُرُ مَن يَشَآءُ ۖ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration binaṣri l-lahi yanṣuru man yashāu wahuwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Verse 6

وَعْدَ ٱللَّهِ ۖ لَا يُخْلِفُ ٱللَّهُ وَعْدَهُۥ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration waʿda l-lahi lā yukh'lifu l-lahu waʿdahu walākinna akthara l-nāsi lā yaʿlamūna

Hausa Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.

Verse 7

يَعْلَمُونَ ظَـٰهِرًا مِّنَ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَهُمْ عَنِ ٱلْـَٔاخِرَةِ هُمْ غَـٰفِلُونَ

Transliteration yaʿlamūna ẓāhiran mina l-ḥayati l-dun'yā wahum ʿani l-ākhirati hum ghāfilūna

Hausa Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar Lãhira.

Verse 8

أَوَلَمْ يَتَفَكَّرُوا۟ فِىٓ أَنفُسِهِم ۗ مَّا خَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَآ إِلَّا بِٱلْحَقِّ وَأَجَلٍ مُّسَمًّى ۗ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ ٱلنَّاسِ بِلِقَآئِ رَبِّهِمْ لَكَـٰفِرُونَ

Transliteration awalam yatafakkarū fī anfusihim mā khalaqa l-lahu l-samāwāti wal-arḍa wamā baynahumā illā bil-ḥaqi wa-ajalin musamman wa-inna kathīran mina l-nāsi biliqāi rabbihim lakāfirūna

Hausa Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu?

Verse 9

أَوَلَمْ يَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَيَنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ كَانُوٓا۟ أَشَدَّ مِنْهُمْ قُوَّةً وَأَثَارُوا۟ ٱلْأَرْضَ وَعَمَرُوهَآ أَكْثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَآءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ ۖ فَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ

Transliteration awalam yasīrū fī l-arḍi fayanẓurū kayfa kāna ʿāqibatu alladhīna min qablihim kānū ashadda min'hum quwwatan wa-athārū l-arḍa waʿamarūhā akthara mimmā ʿamarūhā wajāathum rusuluhum bil-bayināti famā kāna l-lahu liyaẓlimahum walākin kānū anfusahum yaẓlimūna

Hausa Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.

Verse 10

ثُمَّ كَانَ عَـٰقِبَةَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔوا۟ ٱلسُّوٓأَىٰٓ أَن كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ وَكَانُوا۟ بِهَا يَسْتَهْزِءُونَ

Transliteration thumma kāna ʿāqibata alladhīna asāū l-sūā an kadhabū biāyāti l-lahi wakānū bihā yastahziūna

Hausa Sa'an nan ãƙibar waɗannan da suka aikata mũgun aiki ta kasance mafi muni, wãtau sun ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma suka kasance sunã izgili da su.

Verse 11

ٱللَّهُ يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Transliteration al-lahu yabda-u l-khalqa thumma yuʿīduhu thumma ilayhi tur'jaʿūna

Hausa Allah ne ke fãra yin halitta, sa'an nan Ya sãke ta sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku.

Verse 12

وَيَوْمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُبْلِسُ ٱلْمُجْرِمُونَ

Transliteration wayawma taqūmu l-sāʿatu yub'lisu l-muj'rimūna

Hausa Kuma a rãnar da sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi zã su kãsa magana.

Verse 13

وَلَمْ يَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَآئِهِمْ شُفَعَـٰٓؤُا۟ وَكَانُوا۟ بِشُرَكَآئِهِمْ كَـٰفِرِينَ

Transliteration walam yakun lahum min shurakāihim shufaʿāu wakānū bishurakāihim kāfirīna

Hausa Kuma bã su da mãsu cẽto daga abũbuwan shirkinsu, kuma snn kasance mãsu kãfircẽwa daga abũbuwan shirkinsu.

Verse 14

وَيَوْمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوْمَئِذٍ يَتَفَرَّقُونَ

Transliteration wayawma taqūmu l-sāʿatu yawma-idhin yatafarraqūna

Hausa kuma a rãnar tashin Alkiyama ranar ne suke rarrabuwa.

Verse 15

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ فَهُمْ فِى رَوْضَةٍ يُحْبَرُونَ

Transliteration fa-ammā alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti fahum fī rawḍatin yuḥ'barūna

Hausa To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã faranta musu rãyuka, a cikin wani lambu.

Verse 16

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَلِقَآئِ ٱلْـَٔاخِرَةِ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ فِى ٱلْعَذَابِ مُحْضَرُونَ

Transliteration wa-ammā alladhīna kafarū wakadhabū biāyātinā waliqāi l-ākhirati fa-ulāika fī l-ʿadhābi muḥ'ḍarūna

Hausa Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba.

Verse 17

فَسُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ حِينَ تُمْسُونَ وَحِينَ تُصْبِحُونَ

Transliteration fasub'ḥāna l-lahi ḥīna tum'sūna waḥīna tuṣ'biḥūna

Hausa Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da lõkacin da kuke shiga sãfiya.

Verse 18

وَلَهُ ٱلْحَمْدُ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَعَشِيًّا وَحِينَ تُظْهِرُونَ

Transliteration walahu l-ḥamdu fī l-samāwāti wal-arḍi waʿashiyyan waḥīna tuẓ'hirūna

Hausa Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin zawãli.

Verse 19

يُخْرِجُ ٱلْحَىَّ مِنَ ٱلْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ ٱلْمَيِّتَ مِنَ ٱلْحَىِّ وَيُحْىِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ وَكَذَٰلِكَ تُخْرَجُونَ

Transliteration yukh'riju l-ḥaya mina l-mayiti wayukh'riju l-mayita mina l-ḥayi wayuḥ'yī l-arḍa baʿda mawtihā wakadhālika tukh'rajūna

Hausa Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku.

Verse 20

وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦٓ أَنْ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٍ ثُمَّ إِذَآ أَنتُم بَشَرٌ تَنتَشِرُونَ

Transliteration wamin āyātihi an khalaqakum min turābin thumma idhā antum basharun tantashirūna

Hausa Kuma akwai daga ãyõyin Sa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum, kunã wãtsuwa.

Verse 21

وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦٓ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَٰجًا لِّتَسْكُنُوٓا۟ إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ

Transliteration wamin āyātihi an khalaqa lakum min anfusikum azwājan litaskunū ilayhā wajaʿala baynakum mawaddatan waraḥmatan inna fī dhālika laāyātin liqawmin yatafakkarūna

Hausa Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.

Verse 22

وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦ خَلْقُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَٱخْتِلَـٰفُ أَلْسِنَتِكُمْ وَأَلْوَٰنِكُمْ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّلْعَـٰلِمِينَ

Transliteration wamin āyātihi khalqu l-samāwāti wal-arḍi wa-ikh'tilāfu alsinatikum wa-alwānikum inna fī dhālika laāyātin lil'ʿālimīna

Hausa Kuma akwai daga ãyõyin Sa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi.

Verse 23

وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦ مَنَامُكُم بِٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱبْتِغَآؤُكُم مِّن فَضْلِهِۦٓ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ

Transliteration wamin āyātihi manāmukum bi-al-layli wal-nahāri wa-ib'tighāukum min faḍlihi inna fī dhālika laāyātin liqawmin yasmaʿūna

Hausa Kuma akwai daga cikin ãyõyin Sa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa.

Verse 24

وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦ يُرِيكُمُ ٱلْبَرْقَ خَوْفًا وَطَمَعًا وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَيُحْىِۦ بِهِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَآ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ

Transliteration wamin āyātihi yurīkumu l-barqa khawfan waṭamaʿan wayunazzilu mina l-samāi māan fayuḥ'yī bihi l-arḍa baʿda mawtihā inna fī dhālika laāyātin liqawmin yaʿqilūna

Hausa Kuma akwai daga cikin ãyõyin Sa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa.

Verse 25

وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦٓ أَن تَقُومَ ٱلسَّمَآءُ وَٱلْأَرْضُ بِأَمْرِهِۦ ۚ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمْ دَعْوَةً مِّنَ ٱلْأَرْضِ إِذَآ أَنتُمْ تَخْرُجُونَ

Transliteration wamin āyātihi an taqūma l-samāu wal-arḍu bi-amrihi thumma idhā daʿākum daʿwatan mina l-arḍi idhā antum takhrujūna

Hausa Kuma akwai daga ãyõyinsa, tsayuwar sama da asƙã bisa umurninsa, sa'an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasã, sai gã ku kunã fita.

Verse 26

وَلَهُۥ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ كُلٌّ لَّهُۥ قَـٰنِتُونَ

Transliteration walahu man fī l-samāwāti wal-arḍi kullun lahu qānitūna

Hausa Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasã Nãsa ne shi kaɗai. Dukansu mãsu tawãli'u ne a gare Shi.

Verse 27

وَهُوَ ٱلَّذِى يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ وَهُوَ أَهْوَنُ عَلَيْهِ ۚ وَلَهُ ٱلْمَثَلُ ٱلْأَعْلَىٰ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ

Transliteration wahuwa alladhī yabda-u l-khalqa thumma yuʿīduhu wahuwa ahwanu ʿalayhi walahu l-mathalu l-aʿlā fī l-samāwāti wal-arḍi wahuwa l-ʿazīzu l-ḥakīmu

Hausa Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Verse 28

ضَرَبَ لَكُم مَّثَلًا مِّنْ أَنفُسِكُمْ ۖ هَل لَّكُم مِّن مَّا مَلَكَتْ أَيْمَـٰنُكُم مِّن شُرَكَآءَ فِى مَا رَزَقْنَـٰكُمْ فَأَنتُمْ فِيهِ سَوَآءٌ تَخَافُونَهُمْ كَخِيفَتِكُمْ أَنفُسَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلْـَٔايَـٰتِ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ

Transliteration ḍaraba lakum mathalan min anfusikum hal lakum min mā malakat aymānukum min shurakāa fī mā razaqnākum fa-antum fīhi sawāon takhāfūnahum kakhīfatikum anfusakum kadhālika nufaṣṣilu l-āyāti liqawmin yaʿqilūna

Hausa Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltuwa.

Verse 29

بَلِ ٱتَّبَعَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓا۟ أَهْوَآءَهُم بِغَيْرِ عِلْمٍ ۖ فَمَن يَهْدِى مَنْ أَضَلَّ ٱللَّهُ ۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Transliteration bali ittabaʿa alladhīna ẓalamū ahwāahum bighayri ʿil'min faman yahdī man aḍalla l-lahu wamā lahum min nāṣirīna

Hausa Ã'aha! waɗanda suka yi zãunci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba. To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka?

Verse 30

فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا ۚ فِطْرَتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِى فَطَرَ ٱلنَّاسَ عَلَيْهَا ۚ لَا تَبْدِيلَ لِخَلْقِ ٱللَّهِ ۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلْقَيِّمُ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration fa-aqim wajhaka lilddīni ḥanīfan fiṭ'rata l-lahi allatī faṭara l-nāsa ʿalayhā lā tabdīla likhalqi l-lahi dhālika l-dīnu l-qayimu walākinna akthara l-nāsi lā yaʿlamūna

Hausa Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah, wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.

Verse 31

۞ مُنِيبِينَ إِلَيْهِ وَٱتَّقُوهُ وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَلَا تَكُونُوا۟ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ

Transliteration munībīna ilayhi wa-ittaqūhu wa-aqīmū l-ṣalata walā takūnū mina l-mush'rikīna

Hausa Kunã mãsu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bĩ Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai.

Verse 32

مِنَ ٱلَّذِينَ فَرَّقُوا۟ دِينَهُمْ وَكَانُوا۟ شِيَعًا ۖ كُلُّ حِزْبٍۭ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ

Transliteration mina alladhīna farraqū dīnahum wakānū shiyaʿan kullu ḥiz'bin bimā ladayhim fariḥūna

Hausa Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai.

Verse 33

وَإِذَا مَسَّ ٱلنَّاسَ ضُرٌّ دَعَوْا۟ رَبَّهُم مُّنِيبِينَ إِلَيْهِ ثُمَّ إِذَآ أَذَاقَهُم مِّنْهُ رَحْمَةً إِذَا فَرِيقٌ مِّنْهُم بِرَبِّهِمْ يُشْرِكُونَ

Transliteration wa-idhā massa l-nāsa ḍurrun daʿaw rabbahum munībīna ilayhi thumma idhā adhāqahum min'hu raḥmatan idhā farīqun min'hum birabbihim yush'rikūna

Hausa Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu.

Verse 34

لِيَكْفُرُوا۟ بِمَآ ءَاتَيْنَـٰهُمْ ۚ فَتَمَتَّعُوا۟ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ

Transliteration liyakfurū bimā ātaynāhum fatamattaʿū fasawfa taʿlamūna

Hausa Dõmin su kãfirta dl abin da Muka bã su. To ku ji dãɗi kaɗan Sa'an nan zã ku, sani.

Verse 35

أَمْ أَنزَلْنَا عَلَيْهِمْ سُلْطَـٰنًا فَهُوَ يَتَكَلَّمُ بِمَا كَانُوا۟ بِهِۦ يُشْرِكُونَ

Transliteration am anzalnā ʿalayhim sul'ṭānan fahuwa yatakallamu bimā kānū bihi yush'rikūna

Hausa Kõ Mun saukar da wani dalĩ li a gare su? Shi kuwa yanã magana da abin da suka kasance sunã shirkin da shi?

Verse 36

وَإِذَآ أَذَقْنَا ٱلنَّاسَ رَحْمَةً فَرِحُوا۟ بِهَا ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌۢ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ إِذَا هُمْ يَقْنَطُونَ

Transliteration wa-idhā adhaqnā l-nāsa raḥmatan fariḥū bihā wa-in tuṣib'hum sayyi-atun bimā qaddamat aydīhim idhā hum yaqnaṭūna

Hausa Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã yanke ƙauna,

Verse 37

أَوَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّ ٱللَّهَ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

Transliteration awalam yaraw anna l-laha yabsuṭu l-riz'qa liman yashāu wayaqdiru inna fī dhālika laāyātin liqawmin yu'minūna

Hausa Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni.

Verse 38

فَـَٔاتِ ذَا ٱلْقُرْبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلْمِسْكِينَ وَٱبْنَ ٱلسَّبِيلِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يُرِيدُونَ وَجْهَ ٱللَّهِ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ

Transliteration faāti dhā l-qur'bā ḥaqqahu wal-mis'kīna wa-ib'na l-sabīli dhālika khayrun lilladhīna yurīdūna wajha l-lahi wa-ulāika humu l-muf'liḥūna

Hausa Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban rabo.

Verse 39

وَمَآ ءَاتَيْتُم مِّن رِّبًا لِّيَرْبُوَا۟ فِىٓ أَمْوَٰلِ ٱلنَّاسِ فَلَا يَرْبُوا۟ عِندَ ٱللَّهِ ۖ وَمَآ ءَاتَيْتُم مِّن زَكَوٰةٍ تُرِيدُونَ وَجْهَ ٱللَّهِ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُضْعِفُونَ

Transliteration wamā ātaytum min riban liyarbuwā fī amwāli l-nāsi falā yarbū ʿinda l-lahi wamā ātaytum min zakatin turīdūna wajha l-lahi fa-ulāika humu l-muḍ'ʿifūna

Hausa Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar Allah to (mãsu yin haka) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa (ga dũkiyarsu).

Verse 40

ٱللَّهُ ٱلَّذِى خَلَقَكُمْ ثُمَّ رَزَقَكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ ۖ هَلْ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَفْعَلُ مِن ذَٰلِكُم مِّن شَىْءٍ ۚ سُبْحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ

Transliteration al-lahu alladhī khalaqakum thumma razaqakum thumma yumītukum thumma yuḥ'yīkum hal min shurakāikum man yafʿalu min dhālikum min shayin sub'ḥānahu wataʿālā ʿammā yush'rikūna

Hausa Allah ne Wanda Ya halicce ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki.

Verse 41

ظَهَرَ ٱلْفَسَادُ فِى ٱلْبَرِّ وَٱلْبَحْرِ بِمَا كَسَبَتْ أَيْدِى ٱلنَّاسِ لِيُذِيقَهُم بَعْضَ ٱلَّذِى عَمِلُوا۟ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ

Transliteration ẓahara l-fasādu fī l-bari wal-baḥri bimā kasabat aydī l-nāsi liyudhīqahum baʿḍa alladhī ʿamilū laʿallahum yarjiʿūna

Hausa ¥arnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su kõmo.

Verse 42

قُلْ سِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَٱنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلُ ۚ كَانَ أَكْثَرُهُم مُّشْرِكِينَ

Transliteration qul sīrū fī l-arḍi fa-unẓurū kayfa kāna ʿāqibatu alladhīna min qablu kāna aktharuhum mush'rikīna

Hausa Ka ce: "Ku tafi a cikin ƙasã sa'an nan ku dũbi yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninku ta kasance. Mafi yawansu sun kasance mãsu yin shirka."

Verse 43

فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ ٱلْقَيِّمِ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِىَ يَوْمٌ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِ ۖ يَوْمَئِذٍ يَصَّدَّعُونَ

Transliteration fa-aqim wajhaka lilddīni l-qayimi min qabli an yatiya yawmun lā maradda lahu mina l-lahi yawma-idhin yaṣṣaddaʿūna

Hausa Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgẽwa (su rabu biyu).

Verse 44

مَن كَفَرَ فَعَلَيْهِ كُفْرُهُۥ ۖ وَمَنْ عَمِلَ صَـٰلِحًا فَلِأَنفُسِهِمْ يَمْهَدُونَ

Transliteration man kafara faʿalayhi kuf'ruhu waman ʿamila ṣāliḥan fali-anfusihim yamhadūna

Hausa Wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, sabõda kansu suke yin shimfiɗa.

Verse 45

لِيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ مِن فَضْلِهِۦٓ ۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلْكَـٰفِرِينَ

Transliteration liyajziya alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti min faḍlihi innahu lā yuḥibbu l-kāfirīna

Hausa Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai.

Verse 46

وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦٓ أَن يُرْسِلَ ٱلرِّيَاحَ مُبَشِّرَٰتٍ وَلِيُذِيقَكُم مِّن رَّحْمَتِهِۦ وَلِتَجْرِىَ ٱلْفُلْكُ بِأَمْرِهِۦ وَلِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Transliteration wamin āyātihi an yur'sila l-riyāḥa mubashirātin waliyudhīqakum min raḥmatihi walitajriya l-ful'ku bi-amrihi walitabtaghū min faḍlihi walaʿallakum tashkurūna

Hausa Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra kuma dõmin Ya ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma dõmin jirãgen ruwa su gudãna da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalar Sa, fãtanku zã ku gode.

Verse 47

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ رُسُلًا إِلَىٰ قَوْمِهِمْ فَجَآءُوهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَٱنتَقَمْنَا مِنَ ٱلَّذِينَ أَجْرَمُوا۟ ۖ وَكَانَ حَقًّا عَلَيْنَا نَصْرُ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration walaqad arsalnā min qablika rusulan ilā qawmihim fajāūhum bil-bayināti fa-intaqamnā mina alladhīna ajramū wakāna ḥaqqan ʿalaynā naṣru l-mu'minīna

Hausa Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabãninka, zuwa ga mutãnensu sai suka je musu da hujjõji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi, kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu.

Verse 48

ٱللَّهُ ٱلَّذِى يُرْسِلُ ٱلرِّيَـٰحَ فَتُثِيرُ سَحَابًا فَيَبْسُطُهُۥ فِى ٱلسَّمَآءِ كَيْفَ يَشَآءُ وَيَجْعَلُهُۥ كِسَفًا فَتَرَى ٱلْوَدْقَ يَخْرُجُ مِنْ خِلَـٰلِهِۦ ۖ فَإِذَآ أَصَابَ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦٓ إِذَا هُمْ يَسْتَبْشِرُونَ

Transliteration al-lahu alladhī yur'silu l-riyāḥa fatuthīru saḥāban fayabsuṭuhu fī l-samāi kayfa yashāu wayajʿaluhu kisafan fatarā l-wadqa yakhruju min khilālihi fa-idhā aṣāba bihi man yashāu min ʿibādihi idhā hum yastabshirūna

Hausa Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi.

Verse 49

وَإِن كَانُوا۟ مِن قَبْلِ أَن يُنَزَّلَ عَلَيْهِم مِّن قَبْلِهِۦ لَمُبْلِسِينَ

Transliteration wa-in kānū min qabli an yunazzala ʿalayhim min qablihi lamub'lisīna

Hausa Kuma kõ da sun kasance a gabãnin a saukar da shi a kansu, kusa-kusa, sunã baƙin ciki hai bã su iya magana.

Verse 50

فَٱنظُرْ إِلَىٰٓ ءَاثَـٰرِ رَحْمَتِ ٱللَّهِ كَيْفَ يُحْىِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَآ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحْىِ ٱلْمَوْتَىٰ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Transliteration fa-unẓur ilā āthāri raḥmati l-lahi kayfa yuḥ'yī l-arḍa baʿda mawtihā inna dhālika lamuḥ'yī l-mawtā wahuwa ʿalā kulli shayin qadīrun

Hausa Sai ka dũbi alãmõmin rahamar Allah yadda Yake rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas, Mai rãyar da halitta ne, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan kõme.

Verse 51

وَلَئِنْ أَرْسَلْنَا رِيحًا فَرَأَوْهُ مُصْفَرًّا لَّظَلُّوا۟ مِنۢ بَعْدِهِۦ يَكْفُرُونَ

Transliteration wala-in arsalnā rīḥan fara-awhu muṣ'farran laẓallū min baʿdihi yakfurūna

Hausa Kuma lalle idan Mun aika wata iska, suka ganta fatsifatsi, lalle zã su yini a bãyansa sunã kãfirta.

Verse 52

فَإِنَّكَ لَا تُسْمِعُ ٱلْمَوْتَىٰ وَلَا تُسْمِعُ ٱلصُّمَّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا وَلَّوْا۟ مُدْبِرِينَ

Transliteration fa-innaka lā tus'miʿu l-mawtā walā tus'miʿu l-ṣuma l-duʿāa idhā wallaw mud'birīna

Hausa Sabõda haka, kai, bã ka jiyar da matattu kira, kuma bã ka jiyar da kurãme kira idan sun jũya bãya sunã gudu.

Verse 53

وَمَآ أَنتَ بِهَـٰدِ ٱلْعُمْىِ عَن ضَلَـٰلَتِهِمْ ۖ إِن تُسْمِعُ إِلَّا مَن يُؤْمِنُ بِـَٔايَـٰتِنَا فَهُم مُّسْلِمُونَ

Transliteration wamā anta bihādi l-ʿum'yi ʿan ḍalālatihim in tus'miʿu illā man yu'minu biāyātinā fahum mus'limūna

Hausa Kuma ba ka zamo mai shiryar da makãfi ba daga ɓatarsu, bã ka jiyarwa fãce wanda ke yin ĩmãni da ãyõyin Mu, watau sũ ne mãsu mĩƙa wuya, su sallama.

Verse 54

۞ ٱللَّهُ ٱلَّذِى خَلَقَكُم مِّن ضَعْفٍ ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعْدِ ضَعْفٍ قُوَّةً ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعْدِ قُوَّةٍ ضَعْفًا وَشَيْبَةً ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ ۖ وَهُوَ ٱلْعَلِيمُ ٱلْقَدِيرُ

Transliteration al-lahu alladhī khalaqakum min ḍaʿfin thumma jaʿala min baʿdi ḍaʿfin quwwatan thumma jaʿala min baʿdi quwwatin ḍaʿfan washaybatan yakhluqu mā yashāu wahuwa l-ʿalīmu l-qadīru

Hausa Allah ne Ya halitta ku daga rauni, sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Mai ilmi, Mai ĩkon yi,

Verse 55

وَيَوْمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُقْسِمُ ٱلْمُجْرِمُونَ مَا لَبِثُوا۟ غَيْرَ سَاعَةٍ ۚ كَذَٰلِكَ كَانُوا۟ يُؤْفَكُونَ

Transliteration wayawma taqūmu l-sāʿatu yuq'simu l-muj'rimūna mā labithū ghayra sāʿatin kadhālika kānū yu'fakūna

Hausa Kuma a rãnar da Sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi na rantsuwã: Ba su zauna a cikin kabari ba fãce sã'a guda. Kamar haka suka kasance anã karkatar da su.

Verse 56

وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ وَٱلْإِيمَـٰنَ لَقَدْ لَبِثْتُمْ فِى كِتَـٰبِ ٱللَّهِ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْبَعْثِ ۖ فَهَـٰذَا يَوْمُ ٱلْبَعْثِ وَلَـٰكِنَّكُمْ كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ

Transliteration waqāla alladhīna ūtū l-ʿil'ma wal-īmāna laqad labith'tum fī kitābi l-lahi ilā yawmi l-baʿthi fahādhā yawmu l-baʿthi walākinnakum kuntum lā taʿlamūna

Hausa Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da ĩmãni suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kun zauna a cikin Littãfin Allah, har zuwa rãnar tãyarwa, to, kuma wannan ita ce rãnar tãyarwar, kuma amma kũ, kun kasance ba ku sani ba."

Verse 57

فَيَوْمَئِذٍ لَّا يَنفَعُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مَعْذِرَتُهُمْ وَلَا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ

Transliteration fayawma-idhin lā yanfaʿu alladhīna ẓalamū maʿdhiratuhum walā hum yus'taʿtabūna

Hausa To, a rãnar da uzurin waɗanda suka yi zãlunci bã ya amfaninsu, kuma bã a neman yardarsu.

Verse 58

وَلَقَدْ ضَرَبْنَا لِلنَّاسِ فِى هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٍ ۚ وَلَئِن جِئْتَهُم بِـَٔايَةٍ لَّيَقُولَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا مُبْطِلُونَ

Transliteration walaqad ḍarabnā lilnnāsi fī hādhā l-qur'āni min kulli mathalin wala-in ji'tahum biāyatin layaqūlanna alladhīna kafarū in antum illā mub'ṭilūna

Hausa Kuma lalle tabbas Mun buga kõwane irin misãli ga mutãne a cikin wannan Alƙur'ãni, kuma lalle idan kã je musu da kõwace ãyã, lalle, waɗanda suka kãfirta zã su ce "Kũ, bã kõme kuke ba fãce mãsu barua."

Verse 59

كَذَٰلِكَ يَطْبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration kadhālika yaṭbaʿu l-lahu ʿalā qulūbi alladhīna lā yaʿlamūna

Hausa Kamar haka Allah Yake shãfe haske a kan zukãtan waɗanda ba su sani ba.

Verse 60

فَٱصْبِرْ إِنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّ ۖ وَلَا يَسْتَخِفَّنَّكَ ٱلَّذِينَ لَا يُوقِنُونَ

Transliteration fa-iṣ'bir inna waʿda l-lahi ḥaqqun walā yastakhiffannaka alladhīna lā yūqinūna

Hausa Sabõda haka ka yi haƙuri lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma kada waɗanda bã su da yaƙĩni su sassance maka hankali.

Read Surah Ar-Rum in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.