Surah An-Nahl in Hausa: translation and audio
Surah 16 · النحل · The Bee · 128 verses
Surah An-Nahl verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah An-Nahl word by word in English.
Verse 1
أَتَىٰٓ أَمْرُ ٱللَّهِ فَلَا تَسْتَعْجِلُوهُ ۚ سُبْحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Transliteration atā amru l-lahi falā tastaʿjilūhu sub'ḥānahu wataʿālā ʿammā yush'rikūna
Hausa Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
Verse 2
يُنَزِّلُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ بِٱلرُّوحِ مِنْ أَمْرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦٓ أَنْ أَنذِرُوٓا۟ أَنَّهُۥ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱتَّقُونِ
Transliteration yunazzilu l-malāikata bil-rūḥi min amrihi ʿalā man yashāu min ʿibādihi an andhirū annahu lā ilāha illā anā fa-ittaqūni
Hausa Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.
Verse 3
خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ بِٱلْحَقِّ ۚ تَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Transliteration khalaqa l-samāwāti wal-arḍa bil-ḥaqi taʿālā ʿammā yush'rikūna
Hausa Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.
Verse 4
خَلَقَ ٱلْإِنسَـٰنَ مِن نُّطْفَةٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٌ مُّبِينٌ
Transliteration khalaqa l-insāna min nuṭ'fatin fa-idhā huwa khaṣīmun mubīnun
Hausa Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya.
Verse 5
وَٱلْأَنْعَـٰمَ خَلَقَهَا ۗ لَكُمْ فِيهَا دِفْءٌ وَمَنَـٰفِعُ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ
Transliteration wal-anʿāma khalaqahā lakum fīhā dif'on wamanāfiʿu wamin'hā takulūna
Hausa Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci.
Verse 6
وَلَكُمْ فِيهَا جَمَالٌ حِينَ تُرِيحُونَ وَحِينَ تَسْرَحُونَ
Transliteration walakum fīhā jamālun ḥīna turīḥūna waḥīna tasraḥūna
Hausa Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã.
Verse 7
وَتَحْمِلُ أَثْقَالَكُمْ إِلَىٰ بَلَدٍ لَّمْ تَكُونُوا۟ بَـٰلِغِيهِ إِلَّا بِشِقِّ ٱلْأَنفُسِ ۚ إِنَّ رَبَّكُمْ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ
Transliteration wataḥmilu athqālakum ilā baladin lam takūnū bālighīhi illā bishiqqi l-anfusi inna rabbakum laraūfun raḥīmun
Hausa Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai.
Verse 8
وَٱلْخَيْلَ وَٱلْبِغَالَ وَٱلْحَمِيرَ لِتَرْكَبُوهَا وَزِينَةً ۚ وَيَخْلُقُ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Transliteration wal-khayla wal-bighāla wal-ḥamīra litarkabūhā wazīnatan wayakhluqu mā lā taʿlamūna
Hausa Kuma da dawãki da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba.
Verse 9
وَعَلَى ٱللَّهِ قَصْدُ ٱلسَّبِيلِ وَمِنْهَا جَآئِرٌ ۚ وَلَوْ شَآءَ لَهَدَىٰكُمْ أَجْمَعِينَ
Transliteration waʿalā l-lahi qaṣdu l-sabīli wamin'hā jāirun walaw shāa lahadākum ajmaʿīna
Hausa Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacẽwa. Kuma da Yã so, dã Ya shiryar da ku gabã ɗaya.
Verse 10
هُوَ ٱلَّذِىٓ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً ۖ لَّكُم مِّنْهُ شَرَابٌ وَمِنْهُ شَجَرٌ فِيهِ تُسِيمُونَ
Transliteration huwa alladhī anzala mina l-samāi māan lakum min'hu sharābun wamin'hu shajarun fīhi tusīmūna
Hausa Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dõminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itãce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo.
Verse 11
يُنۢبِتُ لَكُم بِهِ ٱلزَّرْعَ وَٱلزَّيْتُونَ وَٱلنَّخِيلَ وَٱلْأَعْنَـٰبَ وَمِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
Transliteration yunbitu lakum bihi l-zarʿa wal-zaytūna wal-nakhīla wal-aʿnāba wamin kulli l-thamarāti inna fī dhālika laāyatan liqawmin yatafakkarūna
Hausa Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
Verse 12
وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمْسَ وَٱلْقَمَرَ ۖ وَٱلنُّجُومُ مُسَخَّرَٰتٌۢ بِأَمْرِهِۦٓ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Transliteration wasakhara lakumu al-layla wal-nahāra wal-shamsa wal-qamara wal-nujūmu musakharātun bi-amrihi inna fī dhālika laāyātin liqawmin yaʿqilūna
Hausa Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta.
Verse 13
وَمَا ذَرَأَ لَكُمْ فِى ٱلْأَرْضِ مُخْتَلِفًا أَلْوَٰنُهُۥٓ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَذَّكَّرُونَ
Transliteration wamā dhara-a lakum fī l-arḍi mukh'talifan alwānuhu inna fī dhālika laāyatan liqawmin yadhakkarūna
Hausa Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai sãɓãnin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke tunãwa.
Verse 14
وَهُوَ ٱلَّذِى سَخَّرَ ٱلْبَحْرَ لِتَأْكُلُوا۟ مِنْهُ لَحْمًا طَرِيًّا وَتَسْتَخْرِجُوا۟ مِنْهُ حِلْيَةً تَلْبَسُونَهَا وَتَرَى ٱلْفُلْكَ مَوَاخِرَ فِيهِ وَلِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Transliteration wahuwa alladhī sakhara l-baḥra litakulū min'hu laḥman ṭariyyan watastakhrijū min'hu ḥil'yatan talbasūnahā watarā l-ful'ka mawākhira fīhi walitabtaghū min faḍlihi walaʿallakum tashkurūna
Hausa Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa.
Verse 15
وَأَلْقَىٰ فِى ٱلْأَرْضِ رَوَٰسِىَ أَن تَمِيدَ بِكُمْ وَأَنْهَـٰرًا وَسُبُلًا لَّعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ
Transliteration wa-alqā fī l-arḍi rawāsiya an tamīda bikum wa-anhāran wasubulan laʿallakum tahtadūna
Hausa Kuma Ya jẽfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dõmin kada ta karkata da ku, da kõguna da hanyõyi, ɗammãnin ku kunã shiryuwa.
Verse 16
وَعَلَـٰمَـٰتٍ ۚ وَبِٱلنَّجْمِ هُمْ يَهْتَدُونَ
Transliteration waʿalāmātin wabil-najmi hum yahtadūna
Hausa Kuma da waɗan su alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci).
Verse 17
أَفَمَن يَخْلُقُ كَمَن لَّا يَخْلُقُ ۗ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Transliteration afaman yakhluqu kaman lā yakhluqu afalā tadhakkarūna
Hausa Shin, wanda Yake yin halitta yanã yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bã ku tunãwa?
Verse 18
وَإِن تَعُدُّوا۟ نِعْمَةَ ٱللَّهِ لَا تُحْصُوهَآ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Transliteration wa-in taʿuddū niʿ'mata l-lahi lā tuḥ'ṣūhā inna l-laha laghafūrun raḥīmun
Hausa Kuma idan kun ƙidãya ni'imar Allah, bã ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Verse 19
وَٱللَّهُ يَعْلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعْلِنُونَ
Transliteration wal-lahu yaʿlamu mā tusirrūna wamā tuʿ'linūna
Hausa Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke asirtãwa da abin da kuke bayyanãwa.
Verse 20
وَٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَخْلُقُونَ شَيْـًٔا وَهُمْ يُخْلَقُونَ
Transliteration wa-alladhīna yadʿūna min dūni l-lahi lā yakhluqūna shayan wahum yukh'laqūna
Hausa Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kõme ba, kuma sũ ne ake halittawa.
Verse 21
أَمْوَٰتٌ غَيْرُ أَحْيَآءٍ ۖ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ
Transliteration amwātun ghayru aḥyāin wamā yashʿurūna ayyāna yub'ʿathūna
Hausa Matattũ ne, bã su da rai, kuma ba su san a wane lõkaci ake tãyar da su ba.
Verse 22
إِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌ وَٰحِدٌ ۚ فَٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ قُلُوبُهُم مُّنكِرَةٌ وَهُم مُّسْتَكْبِرُونَ
Transliteration ilāhukum ilāhun wāḥidun fa-alladhīna lā yu'minūna bil-ākhirati qulūbuhum munkiratun wahum mus'takbirūna
Hausa Abin bautawarku, abin bautãwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, zukãtansu mãsu musu ne, kuma su makangara ne.
Verse 23
لَا جَرَمَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ ۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلْمُسْتَكْبِرِينَ
Transliteration lā jarama anna l-laha yaʿlamu mā yusirrūna wamā yuʿ'linūna innahu lā yuḥibbu l-mus'takbirīna
Hausa Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yanã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. Lalle ne Shi, bã Ya Son mãsu girman kai.
Verse 24
وَإِذَا قِيلَ لَهُم مَّاذَآ أَنزَلَ رَبُّكُمْ ۙ قَالُوٓا۟ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ
Transliteration wa-idhā qīla lahum mādhā anzala rabbukum qālū asāṭīru l-awalīna
Hausa Idan aka ce musu: "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Sai su ce: "Tãtsũniyõyin mutãnen farko."
Verse 25
لِيَحْمِلُوٓا۟ أَوْزَارَهُمْ كَامِلَةً يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۙ وَمِنْ أَوْزَارِ ٱلَّذِينَ يُضِلُّونَهُم بِغَيْرِ عِلْمٍ ۗ أَلَا سَآءَ مَا يَزِرُونَ
Transliteration liyaḥmilū awzārahum kāmilatan yawma l-qiyāmati wamin awzāri alladhīna yuḍillūnahum bighayri ʿil'min alā sāa mā yazirūna
Hausa Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar ¡iyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana.
Verse 26
قَدْ مَكَرَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَأَتَى ٱللَّهُ بُنْيَـٰنَهُم مِّنَ ٱلْقَوَاعِدِ فَخَرَّ عَلَيْهِمُ ٱلسَّقْفُ مِن فَوْقِهِمْ وَأَتَىٰهُمُ ٱلْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لَا يَشْعُرُونَ
Transliteration qad makara alladhīna min qablihim fa-atā l-lahu bun'yānahum mina l-qawāʿidi fakharra ʿalayhimu l-saqfu min fawqihim wa-atāhumu l-ʿadhābu min ḥaythu lā yashʿurūna
Hausa Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa, sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba.
Verse 27
ثُمَّ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ يُخْزِيهِمْ وَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ كُنتُمْ تُشَـٰٓقُّونَ فِيهِمْ ۚ قَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ إِنَّ ٱلْخِزْىَ ٱلْيَوْمَ وَٱلسُّوٓءَ عَلَى ٱلْكَـٰفِرِينَ
Transliteration thumma yawma l-qiyāmati yukh'zīhim wayaqūlu ayna shurakāiya alladhīna kuntum tushāqqūna fīhim qāla alladhīna ūtū l-ʿil'ma inna l-khiz'ya l-yawma wal-sūa ʿalā l-kāfirīna
Hausa Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kãfirai."
Verse 28
ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ ظَالِمِىٓ أَنفُسِهِمْ ۖ فَأَلْقَوُا۟ ٱلسَّلَمَ مَا كُنَّا نَعْمَلُ مِن سُوٓءٍۭ ۚ بَلَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌۢ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Transliteration alladhīna tatawaffāhumu l-malāikatu ẓālimī anfusihim fa-alqawū l-salama mā kunnā naʿmalu min sūin balā inna l-laha ʿalīmun bimā kuntum taʿmalūna
Hausa Waɗanda malãiku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu zãluntar kansu. Sai suka jẽfa nẽman sulhu (suka ce) "Ba mu kasance muna aikata wani mummũnan aiki ba." Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Verse 29
فَٱدْخُلُوٓا۟ أَبْوَٰبَ جَهَنَّمَ خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۖ فَلَبِئْسَ مَثْوَى ٱلْمُتَكَبِّرِينَ
Transliteration fa-ud'khulū abwāba jahannama khālidīna fīhā falabi'sa mathwā l-mutakabirīna
Hausa Sai ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kunã madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin mãsu girman kai.
Verse 30
۞ وَقِيلَ لِلَّذِينَ ٱتَّقَوْا۟ مَاذَآ أَنزَلَ رَبُّكُمْ ۚ قَالُوا۟ خَيْرًا ۗ لِّلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ فِى هَـٰذِهِ ٱلدُّنْيَا حَسَنَةٌ ۚ وَلَدَارُ ٱلْـَٔاخِرَةِ خَيْرٌ ۚ وَلَنِعْمَ دَارُ ٱلْمُتَّقِينَ
Transliteration waqīla lilladhīna ittaqaw mādhā anzala rabbukum qālū khayran lilladhīna aḥsanū fī hādhihi l-dun'yā ḥasanatun waladāru l-ākhirati khayrun walaniʿ'ma dāru l-mutaqīna
Hausa Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan mãsu taƙawa.
Verse 31
جَنَّـٰتُ عَدْنٍ يَدْخُلُونَهَا تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۖ لَهُمْ فِيهَا مَا يَشَآءُونَ ۚ كَذَٰلِكَ يَجْزِى ٱللَّهُ ٱلْمُتَّقِينَ
Transliteration jannātu ʿadnin yadkhulūnahā tajrī min taḥtihā l-anhāru lahum fīhā mā yashāūna kadhālika yajzī l-lahu l-mutaqīna
Hausa Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke sãkã wa mãsu taƙawa.
Verse 32
ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ طَيِّبِينَ ۙ يَقُولُونَ سَلَـٰمٌ عَلَيْكُمُ ٱدْخُلُوا۟ ٱلْجَنَّةَ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Transliteration alladhīna tatawaffāhumu l-malāikatu ṭayyibīna yaqūlūna salāmun ʿalaykumu ud'khulū l-janata bimā kuntum taʿmalūna
Hausa Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
Verse 33
هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن تَأْتِيَهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ أَوْ يَأْتِىَ أَمْرُ رَبِّكَ ۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ وَمَا ظَلَمَهُمُ ٱللَّهُ وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Transliteration hal yanẓurūna illā an tatiyahumu l-malāikatu aw yatiya amru rabbika kadhālika faʿala alladhīna min qablihim wamā ẓalamahumu l-lahu walākin kānū anfusahum yaẓlimūna
Hausa Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
Verse 34
فَأَصَابَهُمْ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُوا۟ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ
Transliteration fa-aṣābahum sayyiātu mā ʿamilū waḥāqa bihim mā kānū bihi yastahziūna
Hausa Sai mũnãnan abũbuwan da suka aikata ya sãme su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.
Verse 35
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ لَوْ شَآءَ ٱللَّهُ مَا عَبَدْنَا مِن دُونِهِۦ مِن شَىْءٍ نَّحْنُ وَلَآ ءَابَآؤُنَا وَلَا حَرَّمْنَا مِن دُونِهِۦ مِن شَىْءٍ ۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ فَهَلْ عَلَى ٱلرُّسُلِ إِلَّا ٱلْبَلَـٰغُ ٱلْمُبِينُ
Transliteration waqāla alladhīna ashrakū law shāa l-lahu mā ʿabadnā min dūnihi min shayin naḥnu walā ābāunā walā ḥarramnā min dūnihi min shayin kadhālika faʿala alladhīna min qablihim fahal ʿalā l-rusuli illā l-balāghu l-mubīnu
Hausa Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã?
Verse 36
وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِى كُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولًا أَنِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱجْتَنِبُوا۟ ٱلطَّـٰغُوتَ ۖ فَمِنْهُم مَّنْ هَدَى ٱللَّهُ وَمِنْهُم مَّنْ حَقَّتْ عَلَيْهِ ٱلضَّلَـٰلَةُ ۚ فَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَٱنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُكَذِّبِينَ
Transliteration walaqad baʿathnā fī kulli ummatin rasūlan ani uʿ'budū l-laha wa-ij'tanibū l-ṭāghūta famin'hum man hadā l-lahu wamin'hum man ḥaqqat ʿalayhi l-ḍalālatu fasīrū fī l-arḍi fa-unẓurū kayfa kāna ʿāqibatu l-mukadhibīna
Hausa Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance.
Verse 37
إِن تَحْرِصْ عَلَىٰ هُدَىٰهُمْ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى مَن يُضِلُّ ۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ
Transliteration in taḥriṣ ʿalā hudāhum fa-inna l-laha lā yahdī man yuḍillu wamā lahum min nāṣirīna
Hausa Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah bã Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma bã su da waɗansu mataimaka.
Verse 38
وَأَقْسَمُوا۟ بِٱللَّهِ جَهْدَ أَيْمَـٰنِهِمْ ۙ لَا يَبْعَثُ ٱللَّهُ مَن يَمُوتُ ۚ بَلَىٰ وَعْدًا عَلَيْهِ حَقًّا وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
Transliteration wa-aqsamū bil-lahi jahda aymānihim lā yabʿathu l-lahu man yamūtu balā waʿdan ʿalayhi ḥaqqan walākinna akthara l-nāsi lā yaʿlamūna
Hausa Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bã ya tãyar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
Verse 39
لِيُبَيِّنَ لَهُمُ ٱلَّذِى يَخْتَلِفُونَ فِيهِ وَلِيَعْلَمَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَنَّهُمْ كَانُوا۟ كَـٰذِبِينَ
Transliteration liyubayyina lahumu alladhī yakhtalifūna fīhi waliyaʿlama alladhīna kafarū annahum kānū kādhibīna
Hausa Dõmin Ya bayyana musu abin da suke sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin waɗan da suka kãfirta su sani cẽwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryatã.
Verse 40
إِنَّمَا قَوْلُنَا لِشَىْءٍ إِذَآ أَرَدْنَـٰهُ أَن نَّقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Transliteration innamā qawlunā lishayin idhā aradnāhu an naqūla lahu kun fayakūnu
Hausa Abin sani kawai, Maganar Mu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, "Ka kasance; sai yanã kasancẽwa.
Verse 41
وَٱلَّذِينَ هَاجَرُوا۟ فِى ٱللَّهِ مِنۢ بَعْدِ مَا ظُلِمُوا۟ لَنُبَوِّئَنَّهُمْ فِى ٱلدُّنْيَا حَسَنَةً ۖ وَلَأَجْرُ ٱلْـَٔاخِرَةِ أَكْبَرُ ۚ لَوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ
Transliteration wa-alladhīna hājarū fī l-lahi min baʿdi mā ẓulimū lanubawwi-annahum fī l-dun'yā ḥasanatan wala-ajru l-ākhirati akbaru law kānū yaʿlamūna
Hausa Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su, haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi girmã, dã sun kasance sunã sani.
Verse 42
ٱلَّذِينَ صَبَرُوا۟ وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Transliteration alladhīna ṣabarū waʿalā rabbihim yatawakkalūna
Hausa Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.
Verse 43
وَمَآ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ إِلَّا رِجَالًا نُّوحِىٓ إِلَيْهِمْ ۚ فَسْـَٔلُوٓا۟ أَهْلَ ٱلذِّكْرِ إِن كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
Transliteration wamā arsalnā min qablika illā rijālan nūḥī ilayhim fasalū ahla l-dhik'ri in kuntum lā taʿlamūna
Hausa Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, fãce waɗansu mazãje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutãnen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba.
Verse 44
بِٱلْبَيِّنَـٰتِ وَٱلزُّبُرِ ۗ وَأَنزَلْنَآ إِلَيْكَ ٱلذِّكْرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيْهِمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ
Transliteration bil-bayināti wal-zuburi wa-anzalnā ilayka l-dhik'ra litubayyina lilnnāsi mā nuzzila ilayhim walaʿallahum yatafakkarūna
Hausa Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãnin hisu su yi tunãni.
Verse 45
أَفَأَمِنَ ٱلَّذِينَ مَكَرُوا۟ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن يَخْسِفَ ٱللَّهُ بِهِمُ ٱلْأَرْضَ أَوْ يَأْتِيَهُمُ ٱلْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لَا يَشْعُرُونَ
Transliteration afa-amina alladhīna makarū l-sayiāti an yakhsifa l-lahu bihimu l-arḍa aw yatiyahumu l-ʿadhābu min ḥaythu lā yashʿurūna
Hausa Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba?
Verse 46
أَوْ يَأْخُذَهُمْ فِى تَقَلُّبِهِمْ فَمَا هُم بِمُعْجِزِينَ
Transliteration aw yakhudhahum fī taqallubihim famā hum bimuʿ'jizīna
Hausa Ko kuwa Ya kama su a cikin jujjuyawarsu? Sabõda haka ba su zama masu buwãya ba.
Verse 47
أَوْ يَأْخُذَهُمْ عَلَىٰ تَخَوُّفٍ فَإِنَّ رَبَّكُمْ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ
Transliteration aw yakhudhahum ʿalā takhawwufin fa-inna rabbakum laraūfun raḥīmun
Hausa Ko kuwa Ya kama su a kan naƙasa? To, lalle ne Ubangijinka haƙĩƙa Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
Verse 48
أَوَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَىٰ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ مِن شَىْءٍ يَتَفَيَّؤُا۟ ظِلَـٰلُهُۥ عَنِ ٱلْيَمِينِ وَٱلشَّمَآئِلِ سُجَّدًا لِّلَّهِ وَهُمْ دَٰخِرُونَ
Transliteration awalam yaraw ilā mā khalaqa l-lahu min shayin yatafayya-u ẓilāluhu ʿani l-yamīni wal-shamāili sujjadan lillahi wahum dākhirūna
Hausa Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu ƙasƙantar da kai?
Verse 49
وَلِلَّهِ يَسْجُدُ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ مِن دَآبَّةٍ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ وَهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ
Transliteration walillahi yasjudu mā fī l-samāwāti wamā fī l-arḍi min dābbatin wal-malāikatu wahum lā yastakbirūna
Hausa Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma bã su kangara.
Verse 50
يَخَافُونَ رَبَّهُم مِّن فَوْقِهِمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ ۩
Transliteration yakhāfūna rabbahum min fawqihim wayafʿalūna mā yu'marūna
Hausa Suna tsõron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umuruin su.
Verse 51
۞ وَقَالَ ٱللَّهُ لَا تَتَّخِذُوٓا۟ إِلَـٰهَيْنِ ٱثْنَيْنِ ۖ إِنَّمَا هُوَ إِلَـٰهٌ وَٰحِدٌ ۖ فَإِيَّـٰىَ فَٱرْهَبُونِ
Transliteration waqāla l-lahu lā tattakhidhū ilāhayni ith'nayni innamā huwa ilāhun wāḥidun fa-iyyāya fa-ir'habūni
Hausa Kuma Allah Ya ce: "Kada ku riƙi abũbuwan bautãwa biyu. Abin sani kawai, wanda ake bautãwa guda ne, sa'an nan sai kuji tsõro Na, Ni kawai."
Verse 52
وَلَهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَلَهُ ٱلدِّينُ وَاصِبًا ۚ أَفَغَيْرَ ٱللَّهِ تَتَّقُونَ
Transliteration walahu mā fī l-samāwāti wal-arḍi walahu l-dīnu wāṣiban afaghayra l-lahi tattaqūna
Hausa Kuma Yana da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, kuma Yana da addini wanda yake dawwamamme. Shin fa, wanin Allah kuke bĩ da taƙãwa?
Verse 53
وَمَا بِكُم مِّن نِّعْمَةٍ فَمِنَ ٱللَّهِ ۖ ثُمَّ إِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فَإِلَيْهِ تَجْـَٔرُونَ
Transliteration wamā bikum min niʿ'matin famina l-lahi thumma idhā massakumu l-ḍuru fa-ilayhi tajarūna
Hausa Kuma abin da yake a gare ku na ni'ima, to, daga Allah ne. Sa'an nan kuma idan cũta ta shãfeku, to, zuwa gare Shi kuke hargõwa.
Verse 54
ثُمَّ إِذَا كَشَفَ ٱلضُّرَّ عَنكُمْ إِذَا فَرِيقٌ مِّنكُم بِرَبِّهِمْ يُشْرِكُونَ
Transliteration thumma idhā kashafa l-ḍura ʿankum idhā farīqun minkum birabbihim yush'rikūna
Hausa sa'an nan idan Ya kuranye cũtar daga gare ku, sai gã wani ɓangare daga gare ku game da Ubangijin su sunã shirki.
Verse 55
لِيَكْفُرُوا۟ بِمَآ ءَاتَيْنَـٰهُمْ ۚ فَتَمَتَّعُوا۟ ۖ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ
Transliteration liyakfurū bimā ātaynāhum fatamattaʿū fasawfa taʿlamūna
Hausa Dõmin su kãfirta da abin da Muka bã su. To, ku ji dãɗi, sa'an nan da sannu zã ku sani.
Verse 56
وَيَجْعَلُونَ لِمَا لَا يَعْلَمُونَ نَصِيبًا مِّمَّا رَزَقْنَـٰهُمْ ۗ تَٱللَّهِ لَتُسْـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمْ تَفْتَرُونَ
Transliteration wayajʿalūna limā lā yaʿlamūna naṣīban mimmā razaqnāhum tal-lahi latus'alunna ʿammā kuntum taftarūna
Hausa Kuma sunã sanya rabõ ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa.
Verse 57
وَيَجْعَلُونَ لِلَّهِ ٱلْبَنَـٰتِ سُبْحَـٰنَهُۥ ۙ وَلَهُم مَّا يَشْتَهُونَ
Transliteration wayajʿalūna lillahi l-banāti sub'ḥānahu walahum mā yashtahūna
Hausa Kuma sunã danganta 'ya'ya mãta ga Allah. Tsarkinsa yã tabbata! Kuma sũ ne da abin da suke sha'awa.
Verse 58
وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِٱلْأُنثَىٰ ظَلَّ وَجْهُهُۥ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظِيمٌ
Transliteration wa-idhā bushira aḥaduhum bil-unthā ẓalla wajhuhu mus'waddan wahuwa kaẓīmun
Hausa Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki.
Verse 59
يَتَوَٰرَىٰ مِنَ ٱلْقَوْمِ مِن سُوٓءِ مَا بُشِّرَ بِهِۦٓ ۚ أَيُمْسِكُهُۥ عَلَىٰ هُونٍ أَمْ يَدُسُّهُۥ فِى ٱلتُّرَابِ ۗ أَلَا سَآءَ مَا يَحْكُمُونَ
Transliteration yatawārā mina l-qawmi min sūi mā bushira bihi ayum'sikuhu ʿalā hūnin am yadussuhu fī l-turābi alā sāa mā yaḥkumūna
Hausa Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana.
Verse 60
لِلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ مَثَلُ ٱلسَّوْءِ ۖ وَلِلَّهِ ٱلْمَثَلُ ٱلْأَعْلَىٰ ۚ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ
Transliteration lilladhīna lā yu'minūna bil-ākhirati mathalu l-sawi walillahi l-mathalu l-aʿlā wahuwa l-ʿazīzu l-ḥakīmu
Hausa Ga waɗan da ba su yi ĩmãni da Lãhira ba akwai sifar cũta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwãyi, Mai hikima.
Verse 61
وَلَوْ يُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِظُلْمِهِم مَّا تَرَكَ عَلَيْهَا مِن دَآبَّةٍ وَلَـٰكِن يُؤَخِّرُهُمْ إِلَىٰٓ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمْ لَا يَسْتَـْٔخِرُونَ سَاعَةً ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ
Transliteration walaw yuākhidhu l-lahu l-nāsa biẓul'mihim mā taraka ʿalayhā min dābbatin walākin yu-akhiruhum ilā ajalin musamman fa-idhā jāa ajaluhum lā yastakhirūna sāʿatan walā yastaqdimūna
Hausa Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu, dã bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta ba.
Verse 62
وَيَجْعَلُونَ لِلَّهِ مَا يَكْرَهُونَ وَتَصِفُ أَلْسِنَتُهُمُ ٱلْكَذِبَ أَنَّ لَهُمُ ٱلْحُسْنَىٰ ۖ لَا جَرَمَ أَنَّ لَهُمُ ٱلنَّارَ وَأَنَّهُم مُّفْرَطُونَ
Transliteration wayajʿalūna lillahi mā yakrahūna wataṣifu alsinatuhumu l-kadhiba anna lahumu l-ḥus'nā lā jarama anna lahumu l-nāra wa-annahum muf'raṭūna
Hausa Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlẽwa ne (a cikinta).
Verse 63
تَٱللَّهِ لَقَدْ أَرْسَلْنَآ إِلَىٰٓ أُمَمٍ مِّن قَبْلِكَ فَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ أَعْمَـٰلَهُمْ فَهُوَ وَلِيُّهُمُ ٱلْيَوْمَ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Transliteration tal-lahi laqad arsalnā ilā umamin min qablika fazayyana lahumu l-shayṭānu aʿmālahum fahuwa waliyyuhumu l-yawma walahum ʿadhābun alīmun
Hausa Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabãninka, sai Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
Verse 64
وَمَآ أَنزَلْنَا عَلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ إِلَّا لِتُبَيِّنَ لَهُمُ ٱلَّذِى ٱخْتَلَفُوا۟ فِيهِ ۙ وَهُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Transliteration wamā anzalnā ʿalayka l-kitāba illā litubayyina lahumu alladhī ikh'talafū fīhi wahudan waraḥmatan liqawmin yu'minūna
Hausa Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
Verse 65
وَٱللَّهُ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَحْيَا بِهِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَآ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ
Transliteration wal-lahu anzala mina l-samāi māan fa-aḥyā bihi l-arḍa baʿda mawtihā inna fī dhālika laāyatan liqawmin yasmaʿūna
Hausa Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre.
Verse 66
وَإِنَّ لَكُمْ فِى ٱلْأَنْعَـٰمِ لَعِبْرَةً ۖ نُّسْقِيكُم مِّمَّا فِى بُطُونِهِۦ مِنۢ بَيْنِ فَرْثٍ وَدَمٍ لَّبَنًا خَالِصًا سَآئِغًا لِّلشَّـٰرِبِينَ
Transliteration wa-inna lakum fī l-anʿāmi laʿib'ratan nus'qīkum mimmā fī buṭūnihi min bayni farthin wadamin labanan khāliṣan sāighan lilshāribīna
Hausa Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima; Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã.
Verse 67
وَمِن ثَمَرَٰتِ ٱلنَّخِيلِ وَٱلْأَعْنَـٰبِ تَتَّخِذُونَ مِنْهُ سَكَرًا وَرِزْقًا حَسَنًا ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
Transliteration wamin thamarāti l-nakhīli wal-aʿnābi tattakhidhūna min'hu sakaran wariz'qan ḥasanan inna fī dhālika laāyatan liqawmin yaʿqilūna
Hausa Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.
Verse 68
وَأَوْحَىٰ رَبُّكَ إِلَى ٱلنَّحْلِ أَنِ ٱتَّخِذِى مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا وَمِنَ ٱلشَّجَرِ وَمِمَّا يَعْرِشُونَ
Transliteration wa-awḥā rabbuka ilā l-naḥli ani ittakhidhī mina l-jibāli buyūtan wamina l-shajari wamimmā yaʿrishūna
Hausa Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa."
Verse 69
ثُمَّ كُلِى مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ فَٱسْلُكِى سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلًا ۚ يَخْرُجُ مِنۢ بُطُونِهَا شَرَابٌ مُّخْتَلِفٌ أَلْوَٰنُهُۥ فِيهِ شِفَآءٌ لِّلنَّاسِ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
Transliteration thumma kulī min kulli l-thamarāti fa-us'lukī subula rabbiki dhululan yakhruju min buṭūnihā sharābun mukh'talifun alwānuhu fīhi shifāon lilnnāsi inna fī dhālika laāyatan liqawmin yatafakkarūna
Hausa "Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
Verse 70
وَٱللَّهُ خَلَقَكُمْ ثُمَّ يَتَوَفَّىٰكُمْ ۚ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرْذَلِ ٱلْعُمُرِ لِكَىْ لَا يَعْلَمَ بَعْدَ عِلْمٍ شَيْـًٔا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ قَدِيرٌ
Transliteration wal-lahu khalaqakum thumma yatawaffākum waminkum man yuraddu ilā ardhali l-ʿumuri likay lā yaʿlama baʿda ʿil'min shayan inna l-laha ʿalīmun qadīrun
Hausa Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi.
Verse 71
وَٱللَّهُ فَضَّلَ بَعْضَكُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ فِى ٱلرِّزْقِ ۚ فَمَا ٱلَّذِينَ فُضِّلُوا۟ بِرَآدِّى رِزْقِهِمْ عَلَىٰ مَا مَلَكَتْ أَيْمَـٰنُهُمْ فَهُمْ فِيهِ سَوَآءٌ ۚ أَفَبِنِعْمَةِ ٱللَّهِ يَجْحَدُونَ
Transliteration wal-lahu faḍḍala baʿḍakum ʿalā baʿḍin fī l-riz'qi famā alladhīna fuḍḍilū birāddī riz'qihim ʿalā mā malakat aymānuhum fahum fīhi sawāon afabiniʿ'mati l-lahi yajḥadūna
Hausa Kuma Allah Ya fifita sãshenku a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu?
Verse 72
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَٰجًا وَجَعَلَ لَكُم مِّنْ أَزْوَٰجِكُم بَنِينَ وَحَفَدَةً وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَـٰتِ ۚ أَفَبِٱلْبَـٰطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَتِ ٱللَّهِ هُمْ يَكْفُرُونَ
Transliteration wal-lahu jaʿala lakum min anfusikum azwājan wajaʿala lakum min azwājikum banīna waḥafadatan warazaqakum mina l-ṭayibāti afabil-bāṭili yu'minūna wabiniʿ'mati l-lahi hum yakfurūna
Hausa Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta?
Verse 73
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَمْلِكُ لَهُمْ رِزْقًا مِّنَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ شَيْـًٔا وَلَا يَسْتَطِيعُونَ
Transliteration wayaʿbudūna min dūni l-lahi mā lā yamliku lahum riz'qan mina l-samāwāti wal-arḍi shayan walā yastaṭīʿūna
Hausa Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa (ga aikata kõme).
Verse 74
فَلَا تَضْرِبُوا۟ لِلَّهِ ٱلْأَمْثَالَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
Transliteration falā taḍribū lillahi l-amthāla inna l-laha yaʿlamu wa-antum lā taʿlamūna
Hausa Sa'an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba.
Verse 75
۞ ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا عَبْدًا مَّمْلُوكًا لَّا يَقْدِرُ عَلَىٰ شَىْءٍ وَمَن رَّزَقْنَـٰهُ مِنَّا رِزْقًا حَسَنًا فَهُوَ يُنفِقُ مِنْهُ سِرًّا وَجَهْرًا ۖ هَلْ يَسْتَوُۥنَ ۚ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Transliteration ḍaraba l-lahu mathalan ʿabdan mamlūkan lā yaqdiru ʿalā shayin waman razaqnāhu minnā riz'qan ḥasanan fahuwa yunfiqu min'hu sirran wajahran hal yastawūna l-ḥamdu lillahi bal aktharuhum lā yaʿlamūna
Hausa Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme, da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba.
Verse 76
وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا رَّجُلَيْنِ أَحَدُهُمَآ أَبْكَمُ لَا يَقْدِرُ عَلَىٰ شَىْءٍ وَهُوَ كَلٌّ عَلَىٰ مَوْلَىٰهُ أَيْنَمَا يُوَجِّههُّ لَا يَأْتِ بِخَيْرٍ ۖ هَلْ يَسْتَوِى هُوَ وَمَن يَأْمُرُ بِٱلْعَدْلِ ۙ وَهُوَ عَلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Transliteration waḍaraba l-lahu mathalan rajulayni aḥaduhumā abkamu lā yaqdiru ʿalā shayin wahuwa kallun ʿalā mawlāhu aynamā yuwajjihhu lā yati bikhayrin hal yastawī huwa waman yamuru bil-ʿadli wahuwa ʿalā ṣirāṭin mus'taqīmin
Hausa Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici?
Verse 77
وَلِلَّهِ غَيْبُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَمَآ أَمْرُ ٱلسَّاعَةِ إِلَّا كَلَمْحِ ٱلْبَصَرِ أَوْ هُوَ أَقْرَبُ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ
Transliteration walillahi ghaybu l-samāwāti wal-arḍi wamā amru l-sāʿati illā kalamḥi l-baṣari aw huwa aqrabu inna l-laha ʿalā kulli shayin qadīrun
Hausa Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne.
Verse 78
وَٱللَّهُ أَخْرَجَكُم مِّنۢ بُطُونِ أُمَّهَـٰتِكُمْ لَا تَعْلَمُونَ شَيْـًٔا وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمْعَ وَٱلْأَبْصَـٰرَ وَٱلْأَفْـِٔدَةَ ۙ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Transliteration wal-lahu akhrajakum min buṭūni ummahātikum lā taʿlamūna shayan wajaʿala lakumu l-samʿa wal-abṣāra wal-afidata laʿallakum tashkurūna
Hausa Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde.
Verse 79
أَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَى ٱلطَّيْرِ مُسَخَّرَٰتٍ فِى جَوِّ ٱلسَّمَآءِ مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا ٱللَّهُ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
Transliteration alam yaraw ilā l-ṭayri musakharātin fī jawwi l-samāi mā yum'sikuhunna illā l-lahu inna fī dhālika laāyātin liqawmin yu'minūna
Hausa Shin ba su ga tsuntsãye ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
Verse 80
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنۢ بُيُوتِكُمْ سَكَنًا وَجَعَلَ لَكُم مِّن جُلُودِ ٱلْأَنْعَـٰمِ بُيُوتًا تَسْتَخِفُّونَهَا يَوْمَ ظَعْنِكُمْ وَيَوْمَ إِقَامَتِكُمْ ۙ وَمِنْ أَصْوَافِهَا وَأَوْبَارِهَا وَأَشْعَارِهَآ أَثَـٰثًا وَمَتَـٰعًا إِلَىٰ حِينٍ
Transliteration wal-lahu jaʿala lakum min buyūtikum sakanan wajaʿala lakum min julūdi l-anʿāmi buyūtan tastakhiffūnahā yawma ẓaʿnikum wayawma iqāmatikum wamin aṣwāfihā wa-awbārihā wa-ashʿārihā athāthan wamatāʿan ilā ḥīnin
Hausa Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci.
Verse 81
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّمَّا خَلَقَ ظِلَـٰلًا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلْجِبَالِ أَكْنَـٰنًا وَجَعَلَ لَكُمْ سَرَٰبِيلَ تَقِيكُمُ ٱلْحَرَّ وَسَرَٰبِيلَ تَقِيكُم بَأْسَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُتِمُّ نِعْمَتَهُۥ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تُسْلِمُونَ
Transliteration wal-lahu jaʿala lakum mimmā khalaqa ẓilālan wajaʿala lakum mina l-jibāli aknānan wajaʿala lakum sarābīla taqīkumu l-ḥara wasarābīla taqīkum basakum kadhālika yutimmu niʿ'matahu ʿalaykum laʿallakum tus'limūna
Hausa Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa.
Verse 82
فَإِن تَوَلَّوْا۟ فَإِنَّمَا عَلَيْكَ ٱلْبَلَـٰغُ ٱلْمُبِينُ
Transliteration fa-in tawallaw fa-innamā ʿalayka l-balāghu l-mubīnu
Hausa To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã.
Verse 83
يَعْرِفُونَ نِعْمَتَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُنكِرُونَهَا وَأَكْثَرُهُمُ ٱلْكَـٰفِرُونَ
Transliteration yaʿrifūna niʿ'mata l-lahi thumma yunkirūnahā wa-aktharuhumu l-kāfirūna
Hausa Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne.
Verse 84
وَيَوْمَ نَبْعَثُ مِن كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا ثُمَّ لَا يُؤْذَنُ لِلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَلَا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ
Transliteration wayawma nabʿathu min kulli ummatin shahīdan thumma lā yu'dhanu lilladhīna kafarū walā hum yus'taʿtabūna
Hausa Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba.
Verse 85
وَإِذَا رَءَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ ٱلْعَذَابَ فَلَا يُخَفَّفُ عَنْهُمْ وَلَا هُمْ يُنظَرُونَ
Transliteration wa-idhā raā alladhīna ẓalamū l-ʿadhāba falā yukhaffafu ʿanhum walā hum yunẓarūna
Hausa Kuma idan waɗanda suka yi zãlunci suka ga azãba, sa'an nan bã za a saukake ta daga gare su ba, kuma bã su zama anã yi musu jinkiri ba.
Verse 86
وَإِذَا رَءَا ٱلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ شُرَكَآءَهُمْ قَالُوا۟ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ شُرَكَآؤُنَا ٱلَّذِينَ كُنَّا نَدْعُوا۟ مِن دُونِكَ ۖ فَأَلْقَوْا۟ إِلَيْهِمُ ٱلْقَوْلَ إِنَّكُمْ لَكَـٰذِبُونَ
Transliteration wa-idhā raā alladhīna ashrakū shurakāahum qālū rabbanā hāulāi shurakāunā alladhīna kunnā nadʿū min dūnika fa-alqaw ilayhimu l-qawla innakum lakādhibūna
Hausa Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne."
Verse 87
وَأَلْقَوْا۟ إِلَى ٱللَّهِ يَوْمَئِذٍ ٱلسَّلَمَ ۖ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَفْتَرُونَ
Transliteration wa-alqaw ilā l-lahi yawma-idhin l-salama waḍalla ʿanhum mā kānū yaftarūna
Hausa Kuma su shiga nẽman sulhu zuwa ga Allah a rãnar nan, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace daga gare su.
Verse 88
ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ زِدْنَـٰهُمْ عَذَابًا فَوْقَ ٱلْعَذَابِ بِمَا كَانُوا۟ يُفْسِدُونَ
Transliteration alladhīna kafarū waṣaddū ʿan sabīli l-lahi zid'nāhum ʿadhāban fawqa l-ʿadhābi bimā kānū yuf'sidūna
Hausa Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange daga hanyar, Allah, Mun ƙãra musu wata azãba bisa ga azãbar, sabõda abin da suka kasance sunã yi na fasãdi.
Verse 89
وَيَوْمَ نَبْعَثُ فِى كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا عَلَيْهِم مِّنْ أَنفُسِهِمْ ۖ وَجِئْنَا بِكَ شَهِيدًا عَلَىٰ هَـٰٓؤُلَآءِ ۚ وَنَزَّلْنَا عَلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ تِبْيَـٰنًا لِّكُلِّ شَىْءٍ وَهُدًى وَرَحْمَةً وَبُشْرَىٰ لِلْمُسْلِمِينَ
Transliteration wayawma nabʿathu fī kulli ummatin shahīdan ʿalayhim min anfusihim waji'nā bika shahīdan ʿalā hāulāi wanazzalnā ʿalayka l-kitāba tib'yānan likulli shayin wahudan waraḥmatan wabush'rā lil'mus'limīna
Hausa Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al'umma a kansu daga kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littãli a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi).
Verse 90
۞ إِنَّ ٱللَّهَ يَأْمُرُ بِٱلْعَدْلِ وَٱلْإِحْسَـٰنِ وَإِيتَآئِ ذِى ٱلْقُرْبَىٰ وَيَنْهَىٰ عَنِ ٱلْفَحْشَآءِ وَٱلْمُنكَرِ وَٱلْبَغْىِ ۚ يَعِظُكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Transliteration inna l-laha yamuru bil-ʿadli wal-iḥ'sāni waītāi dhī l-qur'bā wayanhā ʿani l-faḥshāi wal-munkari wal-baghyi yaʿiẓukum laʿallakum tadhakkarūna
Hausa Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa.
Verse 91
وَأَوْفُوا۟ بِعَهْدِ ٱللَّهِ إِذَا عَـٰهَدتُّمْ وَلَا تَنقُضُوا۟ ٱلْأَيْمَـٰنَ بَعْدَ تَوْكِيدِهَا وَقَدْ جَعَلْتُمُ ٱللَّهَ عَلَيْكُمْ كَفِيلًا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا تَفْعَلُونَ
Transliteration wa-awfū biʿahdi l-lahi idhā ʿāhadttum walā tanquḍū l-aymāna baʿda tawkīdihā waqad jaʿaltumu l-laha ʿalaykum kafīlan inna l-laha yaʿlamu mā tafʿalūna
Hausa Kuma ku cika da alkãwarin Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa.
Verse 92
وَلَا تَكُونُوا۟ كَٱلَّتِى نَقَضَتْ غَزْلَهَا مِنۢ بَعْدِ قُوَّةٍ أَنكَـٰثًا تَتَّخِذُونَ أَيْمَـٰنَكُمْ دَخَلًۢا بَيْنَكُمْ أَن تَكُونَ أُمَّةٌ هِىَ أَرْبَىٰ مِنْ أُمَّةٍ ۚ إِنَّمَا يَبْلُوكُمُ ٱللَّهُ بِهِۦ ۚ وَلَيُبَيِّنَنَّ لَكُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ مَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ
Transliteration walā takūnū ka-allatī naqaḍat ghazlahā min baʿdi quwwatin ankāthan tattakhidhūna aymānakum dakhalan baynakum an takūna ummatun hiya arbā min ummatin innamā yablūkumu l-lahu bihi walayubayyinanna lakum yawma l-qiyāmati mā kuntum fīhi takhtalifūna
Hausa Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bãyan tukka, ya zama warwararku, kunã riƙon rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, dõmin kasancẽwar wata al'umma tãfi rĩba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yanã jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yanã bayyana muku a Rãnar ¡iyãma, abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wajũna.
Verse 93
وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمْ أُمَّةً وَٰحِدَةً وَلَـٰكِن يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهْدِى مَن يَشَآءُ ۚ وَلَتُسْـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Transliteration walaw shāa l-lahu lajaʿalakum ummatan wāḥidatan walākin yuḍillu man yashāu wayahdī man yashāu walatus'alunna ʿammā kuntum taʿmalūna
Hausa Kuma dã Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dã Ya sanya ku al'umma gudã, kuma Yanã ɓatar da wanda Ya so. kuma Yanã shiryar da wanda Ya so. Lalle ne anã tambayarku abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Verse 94
وَلَا تَتَّخِذُوٓا۟ أَيْمَـٰنَكُمْ دَخَلًۢا بَيْنَكُمْ فَتَزِلَّ قَدَمٌۢ بَعْدَ ثُبُوتِهَا وَتَذُوقُوا۟ ٱلسُّوٓءَ بِمَا صَدَدتُّمْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ۖ وَلَكُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Transliteration walā tattakhidhū aymānakum dakhalan baynakum fatazilla qadamun baʿda thubūtihā watadhūqū l-sūa bimā ṣadadttum ʿan sabīli l-lahi walakum ʿadhābun ʿaẓīmun
Hausa Kada ku riƙi rantsuwõyin ku dõmin yaudara a tsakãnin ku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma.
Verse 95
وَلَا تَشْتَرُوا۟ بِعَهْدِ ٱللَّهِ ثَمَنًا قَلِيلًا ۚ إِنَّمَا عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Transliteration walā tashtarū biʿahdi l-lahi thamanan qalīlan innamā ʿinda l-lahi huwa khayrun lakum in kuntum taʿlamūna
Hausa Kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.
Verse 96
مَا عِندَكُمْ يَنفَدُ ۖ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ بَاقٍ ۗ وَلَنَجْزِيَنَّ ٱلَّذِينَ صَبَرُوٓا۟ أَجْرَهُم بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
Transliteration mā ʿindakum yanfadu wamā ʿinda l-lahi bāqin walanajziyanna alladhīna ṣabarū ajrahum bi-aḥsani mā kānū yaʿmalūna
Hausa Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Verse 97
مَنْ عَمِلَ صَـٰلِحًا مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةً طَيِّبَةً ۖ وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُم بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
Transliteration man ʿamila ṣāliḥan min dhakarin aw unthā wahuwa mu'minun falanuḥ'yiyannahu ḥayatan ṭayyibatan walanajziyannahum ajrahum bi-aḥsani mā kānū yaʿmalūna
Hausa Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Verse 98
فَإِذَا قَرَأْتَ ٱلْقُرْءَانَ فَٱسْتَعِذْ بِٱللَّهِ مِنَ ٱلشَّيْطَـٰنِ ٱلرَّجِيمِ
Transliteration fa-idhā qarata l-qur'āna fa-is'taʿidh bil-lahi mina l-shayṭāni l-rajīmi
Hausa Sa'an nan idan ka karantã Alƙur'ãni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe.
Verse 99
إِنَّهُۥ لَيْسَ لَهُۥ سُلْطَـٰنٌ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
Transliteration innahu laysa lahu sul'ṭānun ʿalā alladhīna āmanū waʿalā rabbihim yatawakkalūna
Hausa Lalle ne shi, bã shi da wani ƙarfi a kan waɗan da suka yi ĩmãni, kuma sunã dõgara ga Ubangijin su.
Verse 100
إِنَّمَا سُلْطَـٰنُهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ يَتَوَلَّوْنَهُۥ وَٱلَّذِينَ هُم بِهِۦ مُشْرِكُونَ
Transliteration innamā sul'ṭānuhu ʿalā alladhīna yatawallawnahu wa-alladhīna hum bihi mush'rikūna
Hausa Abin sani kawai ƙarfinsa yanã a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, mãsu shirki ne.
Verse 101
وَإِذَا بَدَّلْنَآ ءَايَةً مَّكَانَ ءَايَةٍ ۙ وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُنَزِّلُ قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مُفْتَرٍۭ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Transliteration wa-idhā baddalnā āyatan makāna āyatin wal-lahu aʿlamu bimā yunazzilu qālū innamā anta muf'tarin bal aktharuhum lā yaʿlamūna
Hausa Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne." Ã'a, mafi yawansu bã swa sani.
Verse 102
قُلْ نَزَّلَهُۥ رُوحُ ٱلْقُدُسِ مِن رَّبِّكَ بِٱلْحَقِّ لِيُثَبِّتَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَهُدًى وَبُشْرَىٰ لِلْمُسْلِمِينَ
Transliteration qul nazzalahu rūḥu l-qudusi min rabbika bil-ḥaqi liyuthabbita alladhīna āmanū wahudan wabush'rā lil'mus'limīna
Hausa Ka ce: "Rũhul ¡udusi ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma (dõmin) shiriya da bushãra ga Musulmi."
Verse 103
وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّهُمْ يَقُولُونَ إِنَّمَا يُعَلِّمُهُۥ بَشَرٌ ۗ لِّسَانُ ٱلَّذِى يُلْحِدُونَ إِلَيْهِ أَعْجَمِىٌّ وَهَـٰذَا لِسَانٌ عَرَبِىٌّ مُّبِينٌ
Transliteration walaqad naʿlamu annahum yaqūlūna innamā yuʿallimuhu basharun lisānu alladhī yul'ḥidūna ilayhi aʿjamiyyun wahādhā lisānun ʿarabiyyun mubīnun
Hausa Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin (cẽwa) lalle ne sũ, sunã cẽwa, "Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi." Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan (Alƙur'ãni) harshe ne Balãrabe bayyanan ne.
Verse 104
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ لَا يَهْدِيهِمُ ٱللَّهُ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Transliteration inna alladhīna lā yu'minūna biāyāti l-lahi lā yahdīhimu l-lahu walahum ʿadhābun alīmun
Hausa Lalle ne waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, Allahbã zai shiryar da su ba, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.
Verse 105
إِنَّمَا يَفْتَرِى ٱلْكَذِبَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْكَـٰذِبُونَ
Transliteration innamā yaftarī l-kadhiba alladhīna lā yu'minūna biāyāti l-lahi wa-ulāika humu l-kādhibūna
Hausa Abin sani kawai waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata.
Verse 106
مَن كَفَرَ بِٱللَّهِ مِنۢ بَعْدِ إِيمَـٰنِهِۦٓ إِلَّا مَنْ أُكْرِهَ وَقَلْبُهُۥ مُطْمَئِنٌّۢ بِٱلْإِيمَـٰنِ وَلَـٰكِن مَّن شَرَحَ بِٱلْكُفْرِ صَدْرًا فَعَلَيْهِمْ غَضَبٌ مِّنَ ٱللَّهِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Transliteration man kafara bil-lahi min baʿdi īmānihi illā man uk'riha waqalbuhu muṭ'ma-innun bil-īmāni walākin man sharaḥa bil-kuf'ri ṣadran faʿalayhim ghaḍabun mina l-lahi walahum ʿadhābun ʿaẓīmun
Hausa Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma.
Verse 107
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱسْتَحَبُّوا۟ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا عَلَى ٱلْـَٔاخِرَةِ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلْكَـٰفِرِينَ
Transliteration dhālika bi-annahumu is'taḥabbū l-ḥayata l-dun'yā ʿalā l-ākhirati wa-anna l-laha lā yahdī l-qawma l-kāfirīna
Hausa Waɗancan ne kãfirai dõmin sun fĩfĩta son dũniya a kan Lãhira, kuma lalle ne Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.
Verse 108
أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ وَسَمْعِهِمْ وَأَبْصَـٰرِهِمْ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْغَـٰفِلُونَ
Transliteration ulāika alladhīna ṭabaʿa l-lahu ʿalā qulūbihim wasamʿihim wa-abṣārihim wa-ulāika humu l-ghāfilūna
Hausa Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukãtansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗan can sũ ne gafalallu.
Verse 109
لَا جَرَمَ أَنَّهُمْ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ
Transliteration lā jarama annahum fī l-ākhirati humu l-khāsirūna
Hausa Bãbu shakka lalle ne a Lãhira sũ ne mãsu hasãra.
Verse 110
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ هَاجَرُوا۟ مِنۢ بَعْدِ مَا فُتِنُوا۟ ثُمَّ جَـٰهَدُوا۟ وَصَبَرُوٓا۟ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Transliteration thumma inna rabbaka lilladhīna hājarū min baʿdi mā futinū thumma jāhadū waṣabarū inna rabbaka min baʿdihā laghafūrun raḥīmun
Hausa Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Verse 111
۞ يَوْمَ تَأْتِى كُلُّ نَفْسٍ تُجَـٰدِلُ عَن نَّفْسِهَا وَتُوَفَّىٰ كُلُّ نَفْسٍ مَّا عَمِلَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Transliteration yawma tatī kullu nafsin tujādilu ʿan nafsihā watuwaffā kullu nafsin mā ʿamilat wahum lā yuẓ'lamūna
Hausa A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba.
Verse 112
وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا قَرْيَةً كَانَتْ ءَامِنَةً مُّطْمَئِنَّةً يَأْتِيهَا رِزْقُهَا رَغَدًا مِّن كُلِّ مَكَانٍ فَكَفَرَتْ بِأَنْعُمِ ٱللَّهِ فَأَذَٰقَهَا ٱللَّهُ لِبَاسَ ٱلْجُوعِ وَٱلْخَوْفِ بِمَا كَانُوا۟ يَصْنَعُونَ
Transliteration waḍaraba l-lahu mathalan qaryatan kānat āminatan muṭ'ma-innatan yatīhā riz'quhā raghadan min kulli makānin fakafarat bi-anʿumi l-lahi fa-adhāqahā l-lahu libāsa l-jūʿi wal-khawfi bimā kānū yaṣnaʿūna
Hausa Kuma Allah Ya buga misãli, wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.
Verse 113
وَلَقَدْ جَآءَهُمْ رَسُولٌ مِّنْهُمْ فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمُ ٱلْعَذَابُ وَهُمْ ظَـٰلِمُونَ
Transliteration walaqad jāahum rasūlun min'hum fakadhabūhu fa-akhadhahumu l-ʿadhābu wahum ẓālimūna
Hausa Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci.
Verse 114
فَكُلُوا۟ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَـٰلًا طَيِّبًا وَٱشْكُرُوا۟ نِعْمَتَ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ
Transliteration fakulū mimmā razaqakumu l-lahu ḥalālan ṭayyiban wa-ush'kurū niʿ'mata l-lahi in kuntum iyyāhu taʿbudūna
Hausa Sa'an nan ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa.
Verse 115
إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمُ ٱلْمَيْتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحْمَ ٱلْخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيْرِ ٱللَّهِ بِهِۦ ۖ فَمَنِ ٱضْطُرَّ غَيْرَ بَاغٍ وَلَا عَادٍ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Transliteration innamā ḥarrama ʿalaykumu l-maytata wal-dama walaḥma l-khinzīri wamā uhilla lighayri l-lahi bihi famani uḍ'ṭurra ghayra bāghin walā ʿādin fa-inna l-laha ghafūrun raḥīmun
Hausa Abin sani kawai (Allah) Ya haramta muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
Verse 116
وَلَا تَقُولُوا۟ لِمَا تَصِفُ أَلْسِنَتُكُمُ ٱلْكَذِبَ هَـٰذَا حَلَـٰلٌ وَهَـٰذَا حَرَامٌ لِّتَفْتَرُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ ۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ لَا يُفْلِحُونَ
Transliteration walā taqūlū limā taṣifu alsinatukumu l-kadhiba hādhā ḥalālun wahādhā ḥarāmun litaftarū ʿalā l-lahi l-kadhiba inna alladhīna yaftarūna ʿalā l-lahi l-kadhiba lā yuf'liḥūna
Hausa Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba.
Verse 117
مَتَـٰعٌ قَلِيلٌ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Transliteration matāʿun qalīlun walahum ʿadhābun alīmun
Hausa Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi.
Verse 118
وَعَلَى ٱلَّذِينَ هَادُوا۟ حَرَّمْنَا مَا قَصَصْنَا عَلَيْكَ مِن قَبْلُ ۖ وَمَا ظَلَمْنَـٰهُمْ وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Transliteration waʿalā alladhīna hādū ḥarramnā mā qaṣaṣnā ʿalayka min qablu wamā ẓalamnāhum walākin kānū anfusahum yaẓlimūna
Hausa Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni, kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta.
Verse 119
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ عَمِلُوا۟ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَـٰلَةٍ ثُمَّ تَابُوا۟ مِنۢ بَعْدِ ذَٰلِكَ وَأَصْلَحُوٓا۟ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Transliteration thumma inna rabbaka lilladhīna ʿamilū l-sūa bijahālatin thumma tābū min baʿdi dhālika wa-aṣlaḥū inna rabbaka min baʿdihā laghafūrun raḥīmun
Hausa Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Verse 120
إِنَّ إِبْرَٰهِيمَ كَانَ أُمَّةً قَانِتًا لِّلَّهِ حَنِيفًا وَلَمْ يَكُ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ
Transliteration inna ib'rāhīma kāna ummatan qānitan lillahi ḥanīfan walam yaku mina l-mush'rikīna
Hausa Lalle ne Ibrãhĩm ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.
Verse 121
شَاكِرًا لِّأَنْعُمِهِ ۚ ٱجْتَبَىٰهُ وَهَدَىٰهُ إِلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Transliteration shākiran li-anʿumihi ij'tabāhu wahadāhu ilā ṣirāṭin mus'taqīmin
Hausa Mai gõdiya ga ni'imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici.
Verse 122
وَءَاتَيْنَـٰهُ فِى ٱلدُّنْيَا حَسَنَةً ۖ وَإِنَّهُۥ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Transliteration waātaynāhu fī l-dun'yā ḥasanatan wa-innahu fī l-ākhirati lamina l-ṣāliḥīna
Hausa Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai.
Verse 123
ثُمَّ أَوْحَيْنَآ إِلَيْكَ أَنِ ٱتَّبِعْ مِلَّةَ إِبْرَٰهِيمَ حَنِيفًا ۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ
Transliteration thumma awḥaynā ilayka ani ittabiʿ millata ib'rāhīma ḥanīfan wamā kāna mina l-mush'rikīna
Hausa Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cẽwa), "Ka bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirka ba.'
Verse 124
إِنَّمَا جُعِلَ ٱلسَّبْتُ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱخْتَلَفُوا۟ فِيهِ ۚ وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَحْكُمُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ فِيمَا كَانُوا۟ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ
Transliteration innamā juʿila l-sabtu ʿalā alladhīna ikh'talafū fīhi wa-inna rabbaka layaḥkumu baynahum yawma l-qiyāmati fīmā kānū fīhi yakhtalifūna
Hausa Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã.
Verse 125
ٱدْعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلْحِكْمَةِ وَٱلْمَوْعِظَةِ ٱلْحَسَنَةِ ۖ وَجَـٰدِلْهُم بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ ۖ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ
Transliteration ud'ʿu ilā sabīli rabbika bil-ḥik'mati wal-mawʿiẓati l-ḥasanati wajādil'hum bi-allatī hiya aḥsanu inna rabbaka huwa aʿlamu biman ḍalla ʿan sabīlihi wahuwa aʿlamu bil-muh'tadīna
Hausa Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
Verse 126
وَإِنْ عَاقَبْتُمْ فَعَاقِبُوا۟ بِمِثْلِ مَا عُوقِبْتُم بِهِۦ ۖ وَلَئِن صَبَرْتُمْ لَهُوَ خَيْرٌ لِّلصَّـٰبِرِينَ
Transliteration wa-in ʿāqabtum faʿāqibū bimith'li mā ʿūqib'tum bihi wala-in ṣabartum lahuwa khayrun lilṣṣābirīna
Hausa Kuma idan kuka sãka wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri.
Verse 127
وَٱصْبِرْ وَمَا صَبْرُكَ إِلَّا بِٱللَّهِ ۚ وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُ فِى ضَيْقٍ مِّمَّا يَمْكُرُونَ
Transliteration wa-iṣ'bir wamā ṣabruka illā bil-lahi walā taḥzan ʿalayhim walā taku fī ḍayqin mimmā yamkurūna
Hausa Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci.
Verse 128
إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوا۟ وَّٱلَّذِينَ هُم مُّحْسِنُونَ
Transliteration inna l-laha maʿa alladhīna ittaqaw wa-alladhīna hum muḥ'sinūna
Hausa Lalle Allah Yanã tãre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ mãsu kyautatãwa ne.
Read Surah An-Nahl in another language
- English (word by word)
- Albanian
- Amazigh
- Amharic
- Assamese
- Azerbaijani
- Bambara
- Bangla
- Bosnian
- Bulgarian
- Chechen
- Chinese
- Czech
- Dari
- Dhivehi
- Dutch
- Finnish
- French
- German
- Gujarati
- Hebrew
- Hindi
- Indonesian
- Italian
- Japanese
- Kannada
- Kazakh
- Khmer
- Kinyarwanda
- Korean
- Kurdish
- Luganda
- Malay
- Malayalam
- Maranao
- Marathi
- Nepali
- Norwegian
- Oromo
- Pashto
- Persian
- Polish
- Portuguese
- Romanian
- Russian
- Sindhi
- Sinhala
- Somali
- Spanish
- Swahili
- Swedish
- Tagalog
- Tajik
- Tamil
- Tatar
- Telugu
- Thai
- Turkish
- Ukrainian
- Urdu
- Uyghur
- Uzbek
- Vietnamese
- Yao
- Yoruba
All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.
Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.