Surah Al-Ma'arij in Hausa: translation and audio
Surah 70 · المعارج · The Ascending Stairways · 44 verses
Surah Al-Ma'arij verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Ma'arij word by word in English.
Verse 1
سَأَلَ سَآئِلٌۢ بِعَذَابٍ وَاقِعٍ
Transliteration sa-ala sāilun biʿadhābin wāqiʿin
Hausa Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
Verse 2
لِّلْكَـٰفِرِينَ لَيْسَ لَهُۥ دَافِعٌ
Transliteration lil'kāfirīna laysa lahu dāfiʿun
Hausa Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
Verse 3
مِّنَ ٱللَّهِ ذِى ٱلْمَعَارِجِ
Transliteration mina l-lahi dhī l-maʿāriji
Hausa Daga Allah Mai matãkala.
Verse 4
تَعْرُجُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيْهِ فِى يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُۥ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ
Transliteration taʿruju l-malāikatu wal-rūḥu ilayhi fī yawmin kāna miq'dāruhu khamsīna alfa sanatin
Hausa Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
Verse 5
فَٱصْبِرْ صَبْرًا جَمِيلًا
Transliteration fa-iṣ'bir ṣabran jamīlan
Hausa Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
Verse 6
إِنَّهُمْ يَرَوْنَهُۥ بَعِيدًا
Transliteration innahum yarawnahu baʿīdan
Hausa Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
Verse 7
وَنَرَىٰهُ قَرِيبًا
Transliteration wanarāhu qarīban
Hausa Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
Verse 8
يَوْمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلْمُهْلِ
Transliteration yawma takūnu l-samāu kal-muh'li
Hausa Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
Verse 9
وَتَكُونُ ٱلْجِبَالُ كَٱلْعِهْنِ
Transliteration watakūnu l-jibālu kal-ʿih'ni
Hausa Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
Verse 10
وَلَا يَسْـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمًا
Transliteration walā yasalu ḥamīmun ḥamīman
Hausa Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.
Verse 11
يُبَصَّرُونَهُمْ ۚ يَوَدُّ ٱلْمُجْرِمُ لَوْ يَفْتَدِى مِنْ عَذَابِ يَوْمِئِذٍۭ بِبَنِيهِ
Transliteration yubaṣṣarūnahum yawaddu l-muj'rimu law yaftadī min ʿadhābi yawmi-idhin bibanīhi
Hausa Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,
Verse 12
وَصَـٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ
Transliteration waṣāḥibatihi wa-akhīhi
Hausa Da matarsa da ɗan'uwansa.
Verse 13
وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِى تُـْٔوِيهِ
Transliteration wafaṣīlatihi allatī tu'wīhi
Hausa Da danginsa, mãsu tattarã shi.
Verse 14
وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا ثُمَّ يُنجِيهِ
Transliteration waman fī l-arḍi jamīʿan thumma yunjīhi
Hausa Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
Verse 15
كَلَّآ ۖ إِنَّهَا لَظَىٰ
Transliteration kallā innahā laẓā
Hausa A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
Verse 16
نَزَّاعَةً لِّلشَّوَىٰ
Transliteration nazzāʿatan lilshawā
Hausa Mai twãle fãtar goshi.
Verse 17
تَدْعُوا۟ مَنْ أَدْبَرَ وَتَوَلَّىٰ
Transliteration tadʿū man adbara watawallā
Hausa Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
Verse 18
وَجَمَعَ فَأَوْعَىٰٓ
Transliteration wajamaʿa fa-awʿā
Hausa Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
Verse 19
۞ إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ خُلِقَ هَلُوعًا
Transliteration inna l-insāna khuliqa halūʿan
Hausa Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
Verse 20
إِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ جَزُوعًا
Transliteration idhā massahu l-sharu jazūʿan
Hausa Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
Verse 21
وَإِذَا مَسَّهُ ٱلْخَيْرُ مَنُوعًا
Transliteration wa-idhā massahu l-khayru manūʿan
Hausa Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
Verse 22
إِلَّا ٱلْمُصَلِّينَ
Transliteration illā l-muṣalīna
Hausa Sai mãsu yin salla,
Verse 23
ٱلَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ دَآئِمُونَ
Transliteration alladhīna hum ʿalā ṣalātihim dāimūna
Hausa Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
Verse 24
وَٱلَّذِينَ فِىٓ أَمْوَٰلِهِمْ حَقٌّ مَّعْلُومٌ
Transliteration wa-alladhīna fī amwālihim ḥaqqun maʿlūmun
Hausa Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
Verse 25
لِّلسَّآئِلِ وَٱلْمَحْرُومِ
Transliteration lilssāili wal-maḥrūmi
Hausa Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
Verse 26
وَٱلَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ
Transliteration wa-alladhīna yuṣaddiqūna biyawmi l-dīni
Hausa Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
Verse 27
وَٱلَّذِينَ هُم مِّنْ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشْفِقُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum min ʿadhābi rabbihim mush'fiqūna
Hausa Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
Verse 28
إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمْ غَيْرُ مَأْمُونٍ
Transliteration inna ʿadhāba rabbihim ghayru mamūnin
Hausa Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
Verse 29
وَٱلَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَـٰفِظُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum lifurūjihim ḥāfiẓūna
Hausa Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
Verse 30
إِلَّا عَلَىٰٓ أَزْوَٰجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَـٰنُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ
Transliteration illā ʿalā azwājihim aw mā malakat aymānuhum fa-innahum ghayru malūmīna
Hausa Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
Verse 31
فَمَنِ ٱبْتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْعَادُونَ
Transliteration famani ib'taghā warāa dhālika fa-ulāika humu l-ʿādūna
Hausa To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
Verse 32
وَٱلَّذِينَ هُمْ لِأَمَـٰنَـٰتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَٰعُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum li-amānātihim waʿahdihim rāʿūna
Hausa Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
Verse 33
وَٱلَّذِينَ هُم بِشَهَـٰدَٰتِهِمْ قَآئِمُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum bishahādātihim qāimūna
Hausa Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
Verse 34
وَٱلَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum ʿalā ṣalātihim yuḥāfiẓūna
Hausa Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
Verse 35
أُو۟لَـٰٓئِكَ فِى جَنَّـٰتٍ مُّكْرَمُونَ
Transliteration ulāika fī jannātin muk'ramūna
Hausa Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
Verse 36
فَمَالِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ قِبَلَكَ مُهْطِعِينَ
Transliteration famāli alladhīna kafarū qibalaka muh'ṭiʿīna
Hausa Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
Verse 37
عَنِ ٱلْيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ عِزِينَ
Transliteration ʿani l-yamīni waʿani l-shimāli ʿizīna
Hausa Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!
Verse 38
أَيَطْمَعُ كُلُّ ٱمْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُدْخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٍ
Transliteration ayaṭmaʿu kullu im'ri-in min'hum an yud'khala jannata naʿīmin
Hausa Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?
Verse 39
كَلَّآ ۖ إِنَّا خَلَقْنَـٰهُم مِّمَّا يَعْلَمُونَ
Transliteration kallā innā khalaqnāhum mimmā yaʿlamūna
Hausa A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.
Verse 40
فَلَآ أُقْسِمُ بِرَبِّ ٱلْمَشَـٰرِقِ وَٱلْمَغَـٰرِبِ إِنَّا لَقَـٰدِرُونَ
Transliteration falā uq'simu birabbi l-mashāriqi wal-maghāribi innā laqādirūna
Hausa Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
Verse 41
عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيْرًا مِّنْهُمْ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ
Transliteration ʿalā an nubaddila khayran min'hum wamā naḥnu bimasbūqīna
Hausa Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
Verse 42
فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا۟ وَيَلْعَبُوا۟ حَتَّىٰ يُلَـٰقُوا۟ يَوْمَهُمُ ٱلَّذِى يُوعَدُونَ
Transliteration fadharhum yakhūḍū wayalʿabū ḥattā yulāqū yawmahumu alladhī yūʿadūna
Hausa Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).
Verse 43
يَوْمَ يَخْرُجُونَ مِنَ ٱلْأَجْدَاثِ سِرَاعًا كَأَنَّهُمْ إِلَىٰ نُصُبٍ يُوفِضُونَ
Transliteration yawma yakhrujūna mina l-ajdāthi sirāʿan ka-annahum ilā nuṣubin yūfiḍūna
Hausa Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
Verse 44
خَـٰشِعَةً أَبْصَـٰرُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْيَوْمُ ٱلَّذِى كَانُوا۟ يُوعَدُونَ
Transliteration khāshiʿatan abṣāruhum tarhaquhum dhillatun dhālika l-yawmu alladhī kānū yūʿadūna
Hausa Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)
Read Surah Al-Ma'arij in another language
- English (word by word)
- Albanian
- Amazigh
- Amharic
- Assamese
- Azerbaijani
- Bambara
- Bangla
- Bosnian
- Bulgarian
- Chechen
- Chinese
- Czech
- Dari
- Dhivehi
- Dutch
- Finnish
- French
- German
- Gujarati
- Hebrew
- Hindi
- Indonesian
- Italian
- Japanese
- Kannada
- Kazakh
- Khmer
- Kinyarwanda
- Korean
- Kurdish
- Luganda
- Malay
- Malayalam
- Maranao
- Marathi
- Nepali
- Norwegian
- Oromo
- Pashto
- Persian
- Polish
- Portuguese
- Romanian
- Russian
- Sindhi
- Sinhala
- Somali
- Spanish
- Swahili
- Swedish
- Tagalog
- Tajik
- Tamil
- Tatar
- Telugu
- Thai
- Turkish
- Ukrainian
- Urdu
- Uyghur
- Uzbek
- Vietnamese
- Yao
- Yoruba
All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.
Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.