MyDugsiStart learning

Surah Al-Jathiyah in Hausa: translation and audio

Surah 45 · الجاثية · The Crouching · 37 verses

Surah Al-Jathiyah verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Jathiyah word by word in English.

Verse 1

حمٓ

Transliteration hha-meem

Hausa Ḥ. M̃.

Verse 2

تَنزِيلُ ٱلْكِتَـٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَكِيمِ

Transliteration tanzīlu l-kitābi mina l-lahi l-ʿazīzi l-ḥakīmi

Hausa Saukar Littãfi daga Allah Mabuwãyi Mai hikima yake.

Verse 3

إِنَّ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ لَـَٔايَـٰتٍ لِّلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration inna fī l-samāwāti wal-arḍi laāyātin lil'mu'minīna

Hausa Lalle ne a cikin sammai da ƙasa akwai ãyõyi ga mãsu ĩmãni.

Verse 4

وَفِى خَلْقِكُمْ وَمَا يَبُثُّ مِن دَآبَّةٍ ءَايَـٰتٌ لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ

Transliteration wafī khalqikum wamā yabuthu min dābbatin āyātun liqawmin yūqinūna

Hausa Kuma a cikin halittarku da abin da ke watsuwa na dabba akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yaƙĩni.

Verse 5

وَٱخْتِلَـٰفِ ٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن رِّزْقٍ فَأَحْيَا بِهِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَتَصْرِيفِ ٱلرِّيَـٰحِ ءَايَـٰتٌ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ

Transliteration wa-ikh'tilāfi al-layli wal-nahāri wamā anzala l-lahu mina l-samāi min riz'qin fa-aḥyā bihi l-arḍa baʿda mawtihā wataṣrīfi l-riyāḥi āyātun liqawmin yaʿqilūna

Hausa Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki, akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.

Verse 6

تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱللَّهِ نَتْلُوهَا عَلَيْكَ بِٱلْحَقِّ ۖ فَبِأَىِّ حَدِيثٍۭ بَعْدَ ٱللَّهِ وَءَايَـٰتِهِۦ يُؤْمِنُونَ

Transliteration til'ka āyātu l-lahi natlūhā ʿalayka bil-ḥaqi fabi-ayyi ḥadīthin baʿda l-lahi waāyātihi yu'minūna

Hausa Waɗancan ãyõyin Allah ne, Munã karanta su gare ka da gaskiya. To, da wane lãbãri bãyan Allah da ãyõyinSa suke yin ĩmãni?

Verse 7

وَيْلٌ لِّكُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ

Transliteration waylun likulli affākin athīmin

Hausa Bone ya tabbata ga dukan mai yawan ƙiren ƙarya, mai laifi.

Verse 8

يَسْمَعُ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ثُمَّ يُصِرُّ مُسْتَكْبِرًا كَأَن لَّمْ يَسْمَعْهَا ۖ فَبَشِّرْهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Transliteration yasmaʿu āyāti l-lahi tut'lā ʿalayhi thumma yuṣirru mus'takbiran ka-an lam yasmaʿhā fabashir'hu biʿadhābin alīmin

Hausa Yanã jin ãyõyin Allah anã karanta su a kansa, sa'an nan ya dõge yanã makãngari, kamar bai jĩ su ba. To, ka yi masa bushara da azãba mai raɗaɗi.

Verse 9

وَإِذَا عَلِمَ مِنْ ءَايَـٰتِنَا شَيْـًٔا ٱتَّخَذَهَا هُزُوًا ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مُّهِينٌ

Transliteration wa-idhā ʿalima min āyātinā shayan ittakhadhahā huzuwan ulāika lahum ʿadhābun muhīnun

Hausa Kuma har idan ya san wani abu daga ãyõyin Mu, sai ya rika su da izgili. Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa (a dũniya).

Verse 10

مِّن وَرَآئِهِمْ جَهَنَّمُ ۖ وَلَا يُغْنِى عَنْهُم مَّا كَسَبُوا۟ شَيْـًٔا وَلَا مَا ٱتَّخَذُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوْلِيَآءَ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ

Transliteration min warāihim jahannamu walā yugh'nī ʿanhum mā kasabū shayan walā mā ittakhadhū min dūni l-lahi awliyāa walahum ʿadhābun ʿaẓīmun

Hausa Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma.

Verse 11

هَـٰذَا هُدًى ۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِ رَبِّهِمْ لَهُمْ عَذَابٌ مِّن رِّجْزٍ أَلِيمٌ

Transliteration hādhā hudan wa-alladhīna kafarū biāyāti rabbihim lahum ʿadhābun min rij'zin alīmun

Hausa Wannan (Alƙur'ãni) shi ne shiryuwa. Kuma waɗanda suka kãfirta game da ãyõyin Ubangijinsu, sunã da wata azãba ta wulãkanci mai raɗaɗi.

Verse 12

۞ ٱللَّهُ ٱلَّذِى سَخَّرَ لَكُمُ ٱلْبَحْرَ لِتَجْرِىَ ٱلْفُلْكُ فِيهِ بِأَمْرِهِۦ وَلِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Transliteration al-lahu alladhī sakhara lakumu l-baḥra litajriya l-ful'ku fīhi bi-amrihi walitabtaghū min faḍlihi walaʿallakum tashkurūna

Hausa Allah ne wanda Ya hõre muku tẽku dõmin jirgi ya gudãna a cikinta da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalar Sa, kuma tsammãninku zã ku gõde.

Verse 13

وَسَخَّرَ لَكُم مَّا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا مِّنْهُ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ

Transliteration wasakhara lakum mā fī l-samāwāti wamā fī l-arḍi jamīʿan min'hu inna fī dhālika laāyātin liqawmin yatafakkarūna

Hausa Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.

Verse 14

قُل لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ يَغْفِرُوا۟ لِلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ أَيَّامَ ٱللَّهِ لِيَجْزِىَ قَوْمًۢا بِمَا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ

Transliteration qul lilladhīna āmanū yaghfirū lilladhīna lā yarjūna ayyāma l-lahi liyajziya qawman bimā kānū yaksibūna

Hausa Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Verse 15

مَنْ عَمِلَ صَـٰلِحًا فَلِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَنْ أَسَآءَ فَعَلَيْهَا ۖ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمْ تُرْجَعُونَ

Transliteration man ʿamila ṣāliḥan falinafsihi waman asāa faʿalayhā thumma ilā rabbikum tur'jaʿūna

Hausa Wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, dõmin kansã, kuma wanda ya mũnana aki, to, a kansa. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku.

Verse 16

وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱلْكِتَـٰبَ وَٱلْحُكْمَ وَٱلنُّبُوَّةَ وَرَزَقْنَـٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَـٰتِ وَفَضَّلْنَـٰهُمْ عَلَى ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration walaqad ātaynā banī is'rāīla l-kitāba wal-ḥuk'ma wal-nubuwata warazaqnāhum mina l-ṭayibāti wafaḍḍalnāhum ʿalā l-ʿālamīna

Hausa Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu).

Verse 17

وَءَاتَيْنَـٰهُم بَيِّنَـٰتٍ مِّنَ ٱلْأَمْرِ ۖ فَمَا ٱخْتَلَفُوٓا۟ إِلَّا مِنۢ بَعْدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلْعِلْمُ بَغْيًۢا بَيْنَهُمْ ۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِى بَيْنَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ فِيمَا كَانُوا۟ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ

Transliteration waātaynāhum bayyinātin mina l-amri famā ikh'talafū illā min baʿdi mā jāahumu l-ʿil'mu baghyan baynahum inna rabbaka yaqḍī baynahum yawma l-qiyāmati fīmā kānū fīhi yakhtalifūna

Hausa Kuma Muka bã su hujjõji na umarni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu, sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu, a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna).

Verse 18

ثُمَّ جَعَلْنَـٰكَ عَلَىٰ شَرِيعَةٍ مِّنَ ٱلْأَمْرِ فَٱتَّبِعْهَا وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَآءَ ٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration thumma jaʿalnāka ʿalā sharīʿatin mina l-amri fa-ittabiʿ'hā walā tattabiʿ ahwāa alladhīna lā yaʿlamūna

Hausa Sa'an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ'a ta al'amarin. Sai ka bĩ ta, Kuma kada kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba.

Verse 19

إِنَّهُمْ لَن يُغْنُوا۟ عَنكَ مِنَ ٱللَّهِ شَيْـًٔا ۚ وَإِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَآءُ بَعْضٍ ۖ وَٱللَّهُ وَلِىُّ ٱلْمُتَّقِينَ

Transliteration innahum lan yugh'nū ʿanka mina l-lahi shayan wa-inna l-ẓālimīna baʿḍuhum awliyāu baʿḍin wal-lahu waliyyu l-mutaqīna

Hausa Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa.

Verse 20

هَـٰذَا بَصَـٰٓئِرُ لِلنَّاسِ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ

Transliteration hādhā baṣāiru lilnnāsi wahudan waraḥmatun liqawmin yūqinūna

Hausa wannan (Alkur'ãni) hukunce-hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni.

Verse 21

أَمْ حَسِبَ ٱلَّذِينَ ٱجْتَرَحُوا۟ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن نَّجْعَلَهُمْ كَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ سَوَآءً مَّحْيَاهُمْ وَمَمَاتُهُمْ ۚ سَآءَ مَا يَحْكُمُونَ

Transliteration am ḥasiba alladhīna ij'taraḥū l-sayiāti an najʿalahum ka-alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti sawāan maḥyāhum wamamātuhum sāa mā yaḥkumūna

Hausa Kõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã!

Verse 22

وَخَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ بِٱلْحَقِّ وَلِتُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍۭ بِمَا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ

Transliteration wakhalaqa l-lahu l-samāwāti wal-arḍa bil-ḥaqi walituj'zā kullu nafsin bimā kasabat wahum lā yuẓ'lamūna

Hausa Alhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba.

Verse 23

أَفَرَءَيْتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَـٰهَهُۥ هَوَىٰهُ وَأَضَلَّهُ ٱللَّهُ عَلَىٰ عِلْمٍ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمْعِهِۦ وَقَلْبِهِۦ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِۦ غِشَـٰوَةً فَمَن يَهْدِيهِ مِنۢ بَعْدِ ٱللَّهِ ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Transliteration afara-ayta mani ittakhadha ilāhahu hawāhu wa-aḍallahu l-lahu ʿalā ʿil'min wakhatama ʿalā samʿihi waqalbihi wajaʿala ʿalā baṣarihi ghishāwatan faman yahdīhi min baʿdi l-lahi afalā tadhakkarūna

Hausa Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi, Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba?

Verse 24

وَقَالُوا۟ مَا هِىَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنْيَا نَمُوتُ وَنَحْيَا وَمَا يُهْلِكُنَآ إِلَّا ٱلدَّهْرُ ۚ وَمَا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِنْ هُمْ إِلَّا يَظُنُّونَ

Transliteration waqālū mā hiya illā ḥayātunā l-dun'yā namūtu wanaḥyā wamā yuh'likunā illā l-dahru wamā lahum bidhālika min ʿil'min in hum illā yaẓunnūna

Hausa Kuma suka ce: "Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa (da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani." Alhãli kuwa (ko da suke faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato.

Verse 25

وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتُنَا بَيِّنَـٰتٍ مَّا كَانَ حُجَّتَهُمْ إِلَّآ أَن قَالُوا۟ ٱئْتُوا۟ بِـَٔابَآئِنَآ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ

Transliteration wa-idhā tut'lā ʿalayhim āyātunā bayyinātin mā kāna ḥujjatahum illā an qālū i'tū biābāinā in kuntum ṣādiqīna

Hausa Kuma idan anã karanta ãyõyin Mu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance hujjarsu fãce suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."

Verse 26

قُلِ ٱللَّهُ يُحْيِيكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يَجْمَعُكُمْ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ لَا رَيْبَ فِيهِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration quli l-lahu yuḥ'yīkum thumma yumītukum thumma yajmaʿukum ilā yawmi l-qiyāmati lā rayba fīhi walākinna akthara l-nāsi lā yaʿlamūna

Hausa Ka ce: "Allah ne ke rãyar da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."

Verse 27

وَلِلَّهِ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَيَوْمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوْمَئِذٍ يَخْسَرُ ٱلْمُبْطِلُونَ

Transliteration walillahi mul'ku l-samāwāti wal-arḍi wayawma taqūmu l-sāʿatu yawma-idhin yakhsaru l-mub'ṭilūna

Hausa "Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa) zã su yi hasãra."

Verse 28

وَتَرَىٰ كُلَّ أُمَّةٍ جَاثِيَةً ۚ كُلُّ أُمَّةٍ تُدْعَىٰٓ إِلَىٰ كِتَـٰبِهَا ٱلْيَوْمَ تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Transliteration watarā kulla ummatin jāthiyatan kullu ummatin tud'ʿā ilā kitābihā l-yawma tuj'zawna mā kuntum taʿmalūna

Hausa Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga littãfinta. (A ce musu) "A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Verse 29

هَـٰذَا كِتَـٰبُنَا يَنطِقُ عَلَيْكُم بِٱلْحَقِّ ۚ إِنَّا كُنَّا نَسْتَنسِخُ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Transliteration hādhā kitābunā yanṭiqu ʿalaykum bil-ḥaqi innā kunnā nastansikhu mā kuntum taʿmalūna

Hausa "Wannan littãfin Mu ne yanã yin magana a kanku da gas, kiya. Lalle Mũ, Mun kasance Muna sauya rubũtun tamkar abin dakuka kasance kunã aikãtãwa."

Verse 30

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ فَيُدْخِلُهُمْ رَبُّهُمْ فِى رَحْمَتِهِۦ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْمُبِينُ

Transliteration fa-ammā alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti fayud'khiluhum rabbuhum fī raḥmatihi dhālika huwa l-fawzu l-mubīnu

Hausa To, amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, to, Ubangijinsu zai sanya su a cikin rahamarsa. Wannan shĩ ne babban rabo bayyananne.

Verse 31

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَفَلَمْ تَكُنْ ءَايَـٰتِى تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فَٱسْتَكْبَرْتُمْ وَكُنتُمْ قَوْمًا مُّجْرِمِينَ

Transliteration wa-ammā alladhīna kafarū afalam takun āyātī tut'lā ʿalaykum fa-is'takbartum wakuntum qawman muj'rimīna

Hausa Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩ Nã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi?"

Verse 32

وَإِذَا قِيلَ إِنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّ وَٱلسَّاعَةُ لَا رَيْبَ فِيهَا قُلْتُم مَّا نَدْرِى مَا ٱلسَّاعَةُ إِن نَّظُنُّ إِلَّا ظَنًّا وَمَا نَحْنُ بِمُسْتَيْقِنِينَ

Transliteration wa-idhā qīla inna waʿda l-lahi ḥaqqun wal-sāʿatu lā rayba fīhā qul'tum mā nadrī mā l-sāʿatu in naẓunnu illā ẓannan wamā naḥnu bimus'tayqinīna

Hausa "Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba."'

Verse 33

وَبَدَا لَهُمْ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُوا۟ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ

Transliteration wabadā lahum sayyiātu mā ʿamilū waḥāqa bihim mā kānū bihi yastahziūna

Hausa Kuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.

Verse 34

وَقِيلَ ٱلْيَوْمَ نَنسَىٰكُمْ كَمَا نَسِيتُمْ لِقَآءَ يَوْمِكُمْ هَـٰذَا وَمَأْوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Transliteration waqīla l-yawma nansākum kamā nasītum liqāa yawmikum hādhā wamawākumu l-nāru wamā lakum min nāṣirīna

Hausa Kuma aka ce: "A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako.

Verse 35

ذَٰلِكُم بِأَنَّكُمُ ٱتَّخَذْتُمْ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ هُزُوًا وَغَرَّتْكُمُ ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا ۚ فَٱلْيَوْمَ لَا يُخْرَجُونَ مِنْهَا وَلَا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ

Transliteration dhālikum bi-annakumu ittakhadhtum āyāti l-lahi huzuwan wagharratkumu l-ḥayatu l-dun'yā fal-yawma lā yukh'rajūna min'hā walā hum yus'taʿtabūna

Hausa "Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba."

Verse 36

فَلِلَّهِ ٱلْحَمْدُ رَبِّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَرَبِّ ٱلْأَرْضِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration falillahi l-ḥamdu rabbi l-samāwāti warabbi l-arḍi rabbi l-ʿālamīna

Hausa Sabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã, Ubangijin halittu.

Verse 37

وَلَهُ ٱلْكِبْرِيَآءُ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ

Transliteration walahu l-kib'riyāu fī l-samāwāti wal-arḍi wahuwa l-ʿazīzu l-ḥakīmu

Hausa Kuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Hikima.

Read Surah Al-Jathiyah in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.