MyDugsiStart learning

Surah Yunus in Hausa: translation and audio

Surah 10 · يونس · Jonah · 109 verses

Surah Yunus verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Yunus word by word in English.

Verse 1

الٓر ۚ تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ ٱلْحَكِيمِ

Transliteration alif-lam-ra til'ka āyātu l-kitābi l-ḥakīmi

Hausa A. L̃.R. Waɗancan ãyõyin littãfi ne kyautatacce.

Verse 2

أَكَانَ لِلنَّاسِ عَجَبًا أَنْ أَوْحَيْنَآ إِلَىٰ رَجُلٍ مِّنْهُمْ أَنْ أَنذِرِ ٱلنَّاسَ وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَنَّ لَهُمْ قَدَمَ صِدْقٍ عِندَ رَبِّهِمْ ۗ قَالَ ٱلْكَـٰفِرُونَ إِنَّ هَـٰذَا لَسَـٰحِرٌ مُّبِينٌ

Transliteration akāna lilnnāsi ʿajaban an awḥaynā ilā rajulin min'hum an andhiri l-nāsa wabashiri alladhīna āmanū anna lahum qadama ṣid'qin ʿinda rabbihim qāla l-kāfirūna inna hādhā lasāḥirun mubīnun

Hausa Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cẽwa, "Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cẽwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu."Kãfirai suka ce: "Lalle ne wan nan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne."

Verse 3

إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ فِى سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ ٱسْتَوَىٰ عَلَى ٱلْعَرْشِ ۖ يُدَبِّرُ ٱلْأَمْرَ ۖ مَا مِن شَفِيعٍ إِلَّا مِنۢ بَعْدِ إِذْنِهِۦ ۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمْ فَٱعْبُدُوهُ ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Transliteration inna rabbakumu l-lahu alladhī khalaqa l-samāwāti wal-arḍa fī sittati ayyāmin thumma is'tawā ʿalā l-ʿarshi yudabbiru l-amra mā min shafīʿin illā min baʿdi idh'nihi dhālikumu l-lahu rabbukum fa-uʿ'budūhu afalā tadhakkarūna

Hausa Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãna shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yanã gudãnar da al'amari. Bãbu wani macẽci fãce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunãni?

Verse 4

إِلَيْهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعًا ۖ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقًّا ۚ إِنَّهُۥ يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ لِيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ بِٱلْقِسْطِ ۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَهُمْ شَرَابٌ مِّنْ حَمِيمٍ وَعَذَابٌ أَلِيمٌۢ بِمَا كَانُوا۟ يَكْفُرُونَ

Transliteration ilayhi marjiʿukum jamīʿan waʿda l-lahi ḥaqqan innahu yabda-u l-khalqa thumma yuʿīduhu liyajziya alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti bil-qis'ṭi wa-alladhīna kafarū lahum sharābun min ḥamīmin waʿadhābun alīmun bimā kānū yakfurūna

Hausa zuwa gare Shi makõmarku take gabã ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita dõmin Ya sãka wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ãdalci, kuma waɗanda suka kãfirta sunã da abin sha daga ruwan zãfi, da azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.

Verse 5

هُوَ ٱلَّذِى جَعَلَ ٱلشَّمْسَ ضِيَآءً وَٱلْقَمَرَ نُورًا وَقَدَّرَهُۥ مَنَازِلَ لِتَعْلَمُوا۟ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلْحِسَابَ ۚ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ إِلَّا بِٱلْحَقِّ ۚ يُفَصِّلُ ٱلْـَٔايَـٰتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ

Transliteration huwa alladhī jaʿala l-shamsa ḍiyāan wal-qamara nūran waqaddarahu manāzila litaʿlamū ʿadada l-sinīna wal-ḥisāba mā khalaqa l-lahu dhālika illā bil-ḥaqi yufaṣṣilu l-āyāti liqawmin yaʿlamūna

Hausa Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, babban haske, da watã mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manzilõli, dõmin ku san ƙidãyar shẽkaru da lissãfi. Allah bai halitta wan nan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki-daki dõmin mutãne waɗan da suke sani.

Verse 6

إِنَّ فِى ٱخْتِلَـٰفِ ٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَمَا خَلَقَ ٱللَّهُ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَتَّقُونَ

Transliteration inna fī ikh'tilāfi al-layli wal-nahāri wamā khalaqa l-lahu fī l-samāwāti wal-arḍi laāyātin liqawmin yattaqūna

Hausa Lalle ne a cikin sãɓãwar dare da yini, da abin da Allah Ya halitta a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙaakwai ãyõyi ga mutãne waɗan da suke yin taƙawa.

Verse 7

إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَآءَنَا وَرَضُوا۟ بِٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَٱطْمَأَنُّوا۟ بِهَا وَٱلَّذِينَ هُمْ عَنْ ءَايَـٰتِنَا غَـٰفِلُونَ

Transliteration inna alladhīna lā yarjūna liqāanā waraḍū bil-ḥayati l-dun'yā wa-iṭ'ma-annū bihā wa-alladhīna hum ʿan āyātinā ghāfilūna

Hausa Lalle ne waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mũ, kuma suka yarda da rãyuwar dũniya kuma suka natsu da ita, da waɗanda suke gafalallu ne daga ãyõyin Mu,

Verse 8

أُو۟لَـٰٓئِكَ مَأْوَىٰهُمُ ٱلنَّارُ بِمَا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ

Transliteration ulāika mawāhumu l-nāru bimā kānū yaksibūna

Hausa Waɗannan matattãrarsu Jahannama ce sabõda abin da suka kasance sunã tsirfãtawa.

Verse 9

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ يَهْدِيهِمْ رَبُّهُم بِإِيمَـٰنِهِمْ ۖ تَجْرِى مِن تَحْتِهِمُ ٱلْأَنْهَـٰرُ فِى جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ

Transliteration inna alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti yahdīhim rabbuhum biīmānihim tajrī min taḥtihimu l-anhāru fī jannāti l-naʿīmi

Hausa Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, Ubangijinsu Yanã shiryar da su sabõda ĩmãninsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, a cikin gidãjen Aljannar ni'ima.

Verse 10

دَعْوَىٰهُمْ فِيهَا سُبْحَـٰنَكَ ٱللَّهُمَّ وَتَحِيَّتُهُمْ فِيهَا سَلَـٰمٌ ۚ وَءَاخِرُ دَعْوَىٰهُمْ أَنِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration daʿwāhum fīhā sub'ḥānaka l-lahuma wataḥiyyatuhum fīhā salāmun waākhiru daʿwāhum ani l-ḥamdu lillahi rabbi l-ʿālamīna

Hausa Kiransu a cikinta, "Tsarkin Ka yã Allah!" Kuma gaisuwarsu a cikinta,"Salãmun", kuma ƙarshen kiransu, cẽwa, "Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu."

Verse 11

۞ وَلَوْ يُعَجِّلُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ ٱلشَّرَّ ٱسْتِعْجَالَهُم بِٱلْخَيْرِ لَقُضِىَ إِلَيْهِمْ أَجَلُهُمْ ۖ فَنَذَرُ ٱلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَآءَنَا فِى طُغْيَـٰنِهِمْ يَعْمَهُونَ

Transliteration walaw yuʿajjilu l-lahu lilnnāsi l-shara is'tiʿ'jālahum bil-khayri laquḍiya ilayhim ajaluhum fanadharu alladhīna lā yarjūna liqāanā fī ṭugh'yānihim yaʿmahūna

Hausa Kuma dã Allah Yana gaggãwa ga mutãne da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da alhẽri, haƙĩƙa dã an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Sabõda haka Munã barin waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu sunã ta ɗimuwa.

Verse 12

وَإِذَا مَسَّ ٱلْإِنسَـٰنَ ٱلضُّرُّ دَعَانَا لِجَنۢبِهِۦٓ أَوْ قَاعِدًا أَوْ قَآئِمًا فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُ ضُرَّهُۥ مَرَّ كَأَن لَّمْ يَدْعُنَآ إِلَىٰ ضُرٍّ مَّسَّهُۥ ۚ كَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِلْمُسْرِفِينَ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Transliteration wa-idhā massa l-insāna l-ḍuru daʿānā lijanbihi aw qāʿidan aw qāiman falammā kashafnā ʿanhu ḍurrahu marra ka-an lam yadʿunā ilā ḍurrin massahu kadhālika zuyyina lil'mus'rifīna mā kānū yaʿmalūna

Hausa Kuma idan cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, yanã (kwance) ga sãshensa kõ kuwa zaune, kõ kuwa a tsaye. To, a lõkacin, da Muka kuranye cũtar daga gare shi, sai ya shũɗe kamar ɗai bai kirãye Mu ba zuwa ga wata cũta wadda ta shãfe shi. Kamar wannan ne aka ƙawãta ga maɓannata, abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Verse 13

وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا ٱلْقُرُونَ مِن قَبْلِكُمْ لَمَّا ظَلَمُوا۟ ۙ وَجَآءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ وَمَا كَانُوا۟ لِيُؤْمِنُوا۟ ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْقَوْمَ ٱلْمُجْرِمِينَ

Transliteration walaqad ahlaknā l-qurūna min qablikum lammā ẓalamū wajāathum rusuluhum bil-bayināti wamā kānū liyu'minū kadhālika najzī l-qawma l-muj'rimīna

Hausa Kuma, haƙĩƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabãninku, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, amma ba su kasance sunã ĩmãni ba. Kamar wannan ne, Muke sãkãwa ga mutãne mãsu laifi.

Verse 14

ثُمَّ جَعَلْنَـٰكُمْ خَلَـٰٓئِفَ فِى ٱلْأَرْضِ مِنۢ بَعْدِهِمْ لِنَنظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ

Transliteration thumma jaʿalnākum khalāifa fī l-arḍi min baʿdihim linanẓura kayfa taʿmalūna

Hausa Sa'an nan kuma Muka sanya ku mãsu mayẽwa a cikin ƙasa daga bãyansu, dõmin Mu ga yãya kuke aikatãwa.

Verse 15

وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ءَايَاتُنَا بَيِّنَـٰتٍ ۙ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَآءَنَا ٱئْتِ بِقُرْءَانٍ غَيْرِ هَـٰذَآ أَوْ بَدِّلْهُ ۚ قُلْ مَا يَكُونُ لِىٓ أَنْ أُبَدِّلَهُۥ مِن تِلْقَآئِ نَفْسِىٓ ۖ إِنْ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَىَّ ۖ إِنِّىٓ أَخَافُ إِنْ عَصَيْتُ رَبِّى عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ

Transliteration wa-idhā tut'lā ʿalayhim āyātunā bayyinātin qāla alladhīna lā yarjūna liqāanā i'ti biqur'ānin ghayri hādhā aw baddil'hu qul mā yakūnu lī an ubaddilahu min til'qāi nafsī in attabiʿu illā mā yūḥā ilayya innī akhāfu in ʿaṣaytu rabbī ʿadhāba yawmin ʿaẓīmin

Hausa Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: "Ka zo da wani Alƙur'ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã shi." Ka ce: "Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma."

Verse 16

قُل لَّوْ شَآءَ ٱللَّهُ مَا تَلَوْتُهُۥ عَلَيْكُمْ وَلَآ أَدْرَىٰكُم بِهِۦ ۖ فَقَدْ لَبِثْتُ فِيكُمْ عُمُرًا مِّن قَبْلِهِۦٓ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ

Transliteration qul law shāa l-lahu mā talawtuhu ʿalaykum walā adrākum bihi faqad labith'tu fīkum ʿumuran min qablihi afalā taʿqilūna

Hausa Ka ce: "Dã Allah Ya so dã ban karanta shi ba a kanku, kuma dã ban sanar da kũ ba gameda shi, dõmin lalle ne nã zauna a cikinku a zãmani mai tsawo daga gabãnin (fãra saukar) sa. Shin fa, bã ku hankalta?"

Verse 17

فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ ٱفْتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِـَٔايَـٰتِهِۦٓ ۚ إِنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلْمُجْرِمُونَ

Transliteration faman aẓlamu mimmani if'tarā ʿalā l-lahi kadhiban aw kadhaba biāyātihi innahu lā yuf'liḥu l-muj'rimūna

Hausa "Sabõda haka wãne ne mafi Zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata ãyõyinSa? Haƙĩƙa, mãsu laifibã su cin nasara!"

Verse 18

وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنفَعُهُمْ وَيَقُولُونَ هَـٰٓؤُلَآءِ شُفَعَـٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِ ۚ قُلْ أَتُنَبِّـُٔونَ ٱللَّهَ بِمَا لَا يَعْلَمُ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَلَا فِى ٱلْأَرْضِ ۚ سُبْحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ

Transliteration wayaʿbudūna min dūni l-lahi mā lā yaḍurruhum walā yanfaʿuhum wayaqūlūna hāulāi shufaʿāunā ʿinda l-lahi qul atunabbiūna l-laha bimā lā yaʿlamu fī l-samāwāti walā fī l-arḍi sub'ḥānahu wataʿālā ʿammā yush'rikūna

Hausa Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah."Ka ce: "Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Yã ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi."

Verse 19

وَمَا كَانَ ٱلنَّاسُ إِلَّآ أُمَّةً وَٰحِدَةً فَٱخْتَلَفُوا۟ ۚ وَلَوْلَا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ لَقُضِىَ بَيْنَهُمْ فِيمَا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ

Transliteration wamā kāna l-nāsu illā ummatan wāḥidatan fa-ikh'talafū walawlā kalimatun sabaqat min rabbika laquḍiya baynahum fīmā fīhi yakhtalifūna

Hausa Kuma mutãne ba su kasance ba fãce Al'umma guda, sa'an nan kuma suka sãɓã wa jũna, kuma ba dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijin ka, dã an yi hukunci a tsakãninsu a kan abin da yake a cikin sa suke sãɓã wa jũna.

Verse 20

وَيَقُولُونَ لَوْلَآ أُنزِلَ عَلَيْهِ ءَايَةٌ مِّن رَّبِّهِۦ ۖ فَقُلْ إِنَّمَا ٱلْغَيْبُ لِلَّهِ فَٱنتَظِرُوٓا۟ إِنِّى مَعَكُم مِّنَ ٱلْمُنتَظِرِينَ

Transliteration wayaqūlūna lawlā unzila ʿalayhi āyatun min rabbihi faqul innamā l-ghaybu lillahi fa-intaẓirū innī maʿakum mina l-muntaẓirīna

Hausa Kuma sunã cẽwa: "Don me ba a saukar da wata ãyã ba a gare shi, daga Ubangijin sa?" To, ka ce: "Abin sani kawai, gaibi ga Allah yake. Sai ku yi jira. Lalle ne nĩ, tãre da ku, inã daga mãsu jira."

Verse 21

وَإِذَآ أَذَقْنَا ٱلنَّاسَ رَحْمَةً مِّنۢ بَعْدِ ضَرَّآءَ مَسَّتْهُمْ إِذَا لَهُم مَّكْرٌ فِىٓ ءَايَاتِنَا ۚ قُلِ ٱللَّهُ أَسْرَعُ مَكْرًا ۚ إِنَّ رُسُلَنَا يَكْتُبُونَ مَا تَمْكُرُونَ

Transliteration wa-idhā adhaqnā l-nāsa raḥmatan min baʿdi ḍarrāa massathum idhā lahum makrun fī āyātinā quli l-lahu asraʿu makran inna rusulanā yaktubūna mā tamkurūna

Hausa Kuma idan Muka ɗanɗanã wa mutãne wata rahama, a bãyan wata cũta tã shãfe su, sai gã su da mãkirci a cikin ãyõyinMu. Ka ce: "Allah ne mafi gaggãwar (sakamakon) mãkirci." Lalle ne Manzannin Mu sunã rubũta abin da kuke yi na mãkirci.

Verse 22

هُوَ ٱلَّذِى يُسَيِّرُكُمْ فِى ٱلْبَرِّ وَٱلْبَحْرِ ۖ حَتَّىٰٓ إِذَا كُنتُمْ فِى ٱلْفُلْكِ وَجَرَيْنَ بِهِم بِرِيحٍ طَيِّبَةٍ وَفَرِحُوا۟ بِهَا جَآءَتْهَا رِيحٌ عَاصِفٌ وَجَآءَهُمُ ٱلْمَوْجُ مِن كُلِّ مَكَانٍ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُمْ أُحِيطَ بِهِمْ ۙ دَعَوُا۟ ٱللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ لَئِنْ أَنجَيْتَنَا مِنْ هَـٰذِهِۦ لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ

Transliteration huwa alladhī yusayyirukum fī l-bari wal-baḥri ḥattā idhā kuntum fī l-ful'ki wajarayna bihim birīḥin ṭayyibatin wafariḥū bihā jāathā rīḥun ʿāṣifun wajāahumu l-mawju min kulli makānin waẓannū annahum uḥīṭa bihim daʿawū l-laha mukh'liṣīna lahu l-dīna la-in anjaytanā min hādhihi lanakūnanna mina l-shākirīna

Hausa Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun kasance a cikin jirãge, su gudãna tãre da su da iska mai dãɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirãgen, kuma tãguwar ruwa ta jẽ musu daga kõwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirãyi Allah, sunã mãsu tsarkake addini gare Shi, (sunã cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙĩƙa munã kasancẽwa daga mãsu gõdiya.

Verse 23

فَلَمَّآ أَنجَىٰهُمْ إِذَا هُمْ يَبْغُونَ فِى ٱلْأَرْضِ بِغَيْرِ ٱلْحَقِّ ۗ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَا بَغْيُكُمْ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُم ۖ مَّتَـٰعَ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۖ ثُمَّ إِلَيْنَا مَرْجِعُكُمْ فَنُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Transliteration falammā anjāhum idhā hum yabghūna fī l-arḍi bighayri l-ḥaqi yāayyuhā l-nāsu innamā baghyukum ʿalā anfusikum matāʿa l-ḥayati l-dun'yā thumma ilaynā marjiʿukum fanunabbi-ukum bimā kuntum taʿmalūna

Hausa To, a lõkacin da Ya kuɓutar da su, sai, gã su sunã zãlunci a cikin ƙasa, bã da wanĩ hakki ba. Yã ku mutãne! Abin sani kawai, zãluncinku a kanku yake, a bisa rãyuwar dũniya. Sa'an nan kuma zuwa gare Mu makõmarku take, sa'an nan Mu bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa,

Verse 24

إِنَّمَا مَثَلُ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا كَمَآءٍ أَنزَلْنَـٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخْتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلْأَرْضِ مِمَّا يَأْكُلُ ٱلنَّاسُ وَٱلْأَنْعَـٰمُ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذَتِ ٱلْأَرْضُ زُخْرُفَهَا وَٱزَّيَّنَتْ وَظَنَّ أَهْلُهَآ أَنَّهُمْ قَـٰدِرُونَ عَلَيْهَآ أَتَىٰهَآ أَمْرُنَا لَيْلًا أَوْ نَهَارًا فَجَعَلْنَـٰهَا حَصِيدًا كَأَن لَّمْ تَغْنَ بِٱلْأَمْسِ ۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلْـَٔايَـٰتِ لِقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ

Transliteration innamā mathalu l-ḥayati l-dun'yā kamāin anzalnāhu mina l-samāi fa-ikh'talaṭa bihi nabātu l-arḍi mimmā yakulu l-nāsu wal-anʿāmu ḥattā idhā akhadhati l-arḍu zukh'rufahā wa-izzayyanat waẓanna ahluhā annahum qādirūna ʿalayhā atāhā amrunā laylan aw nahāran fajaʿalnāhā ḥaṣīdan ka-an lam taghna bil-amsi kadhālika nufaṣṣilu l-āyāti liqawmin yatafakkarūna

Hausa Abin sani kawai, misãlin rãyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutãne da dabbõbi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinãriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutãnenta suka zaci cẽwa sũ ne mãsu ĩkon yi a kanta, sai umurnin Mu ya je mata da dare kõ kuma da rãna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadãta ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki, ga mutãne waɗan da suke tunãni.

Verse 25

وَٱللَّهُ يَدْعُوٓا۟ إِلَىٰ دَارِ ٱلسَّلَـٰمِ وَيَهْدِى مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ

Transliteration wal-lahu yadʿū ilā dāri l-salāmi wayahdī man yashāu ilā ṣirāṭin mus'taqīmin

Hausa Kuma Allah Yanã kira zuwa ga gidan aminci, kuma, Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga tafarki madaidaici.

Verse 26

۞ لِّلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ ٱلْحُسْنَىٰ وَزِيَادَةٌ ۖ وَلَا يَرْهَقُ وُجُوهَهُمْ قَتَرٌ وَلَا ذِلَّةٌ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ

Transliteration lilladhīna aḥsanū l-ḥus'nā waziyādatun walā yarhaqu wujūhahum qatarun walā dhillatun ulāika aṣḥābu l-janati hum fīhā khālidūna

Hausa Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari), wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.

Verse 27

وَٱلَّذِينَ كَسَبُوا۟ ٱلسَّيِّـَٔاتِ جَزَآءُ سَيِّئَةٍۭ بِمِثْلِهَا وَتَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۖ مَّا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنْ عَاصِمٍ ۖ كَأَنَّمَآ أُغْشِيَتْ وُجُوهُهُمْ قِطَعًا مِّنَ ٱلَّيْلِ مُظْلِمًا ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ

Transliteration wa-alladhīna kasabū l-sayiāti jazāu sayyi-atin bimith'lihā watarhaquhum dhillatun mā lahum mina l-lahi min ʿāṣimin ka-annamā ugh'shiyat wujūhuhum qiṭaʿan mina al-layli muẓ'liman ulāika aṣḥābu l-nāri hum fīhā khālidūna

Hausa Kuma waɗanda suka yi tsirfar mũnanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake, kuma ƙasƙanci yanã rufe su. Bã su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe fuskokinsu da guntãyen ƙirãruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abõkan wuta, sunã madawwama a cikinta.

Verse 28

وَيَوْمَ نَحْشُرُهُمْ جَمِيعًا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ مَكَانَكُمْ أَنتُمْ وَشُرَكَآؤُكُمْ ۚ فَزَيَّلْنَا بَيْنَهُمْ ۖ وَقَالَ شُرَكَآؤُهُم مَّا كُنتُمْ إِيَّانَا تَعْبُدُونَ

Transliteration wayawma naḥshuruhum jamīʿan thumma naqūlu lilladhīna ashrakū makānakum antum washurakāukum fazayyalnā baynahum waqāla shurakāuhum mā kuntum iyyānā taʿbudūna

Hausa Kuma a rãnar da Muke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, "Ku kãma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku." Sa'an nan Mu rarrabe a tsakãninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: "Bã mũ kuka kasance kunã bauta wa ba."

Verse 29

فَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًۢا بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ إِن كُنَّا عَنْ عِبَادَتِكُمْ لَغَـٰفِلِينَ

Transliteration fakafā bil-lahi shahīdan baynanā wabaynakum in kunnā ʿan ʿibādatikum laghāfilīna

Hausa "To, kuma Allah Yã isa zama shaida a tsakãninmu da tsakãninku. Haƙĩƙa mun kasance ba mu san kõme ba na bautãwarku a gare mu!"

Verse 30

هُنَالِكَ تَبْلُوا۟ كُلُّ نَفْسٍ مَّآ أَسْلَفَتْ ۚ وَرُدُّوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ مَوْلَىٰهُمُ ٱلْحَقِّ ۖ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَفْتَرُونَ

Transliteration hunālika tablū kullu nafsin mā aslafat waruddū ilā l-lahi mawlāhumu l-ḥaqi waḍalla ʿanhum mā kānū yaftarūna

Hausa A can ne kõwane rai yake jarraba abin da ya bãyar bãshi, kuma aka mayar da su zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace musu.

Verse 31

قُلْ مَن يَرْزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ أَمَّن يَمْلِكُ ٱلسَّمْعَ وَٱلْأَبْصَـٰرَ وَمَن يُخْرِجُ ٱلْحَىَّ مِنَ ٱلْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ ٱلْمَيِّتَ مِنَ ٱلْحَىِّ وَمَن يُدَبِّرُ ٱلْأَمْرَ ۚ فَسَيَقُولُونَ ٱللَّهُ ۚ فَقُلْ أَفَلَا تَتَّقُونَ

Transliteration qul man yarzuqukum mina l-samāi wal-arḍi amman yamliku l-samʿa wal-abṣāra waman yukh'riju l-ḥaya mina l-mayiti wayukh'riju l-mayita mina l-ḥayi waman yudabbiru l-amra fasayaqūlūna l-lahu faqul afalā tattaqūna

Hausa Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?"

Verse 32

فَذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمُ ٱلْحَقُّ ۖ فَمَاذَا بَعْدَ ٱلْحَقِّ إِلَّا ٱلضَّلَـٰلُ ۖ فَأَنَّىٰ تُصْرَفُونَ

Transliteration fadhālikumu l-lahu rabbukumu l-ḥaqu famādhā baʿda l-ḥaqi illā l-ḍalālu fa-annā tuṣ'rafūna

Hausa To, Wancan ne Allah, Ubangijinku Tobbatacce. To, mẽne ne a bãyan gaskiya fãce ɓãta? To, yãya ake karkatar da ku?

Verse 33

كَذَٰلِكَ حَقَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى ٱلَّذِينَ فَسَقُوٓا۟ أَنَّهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ

Transliteration kadhālika ḥaqqat kalimatu rabbika ʿalā alladhīna fasaqū annahum lā yu'minūna

Hausa Kamar wancan ne kalmar Ubangijinka, ta tabbata a kan waɗanda suka yi fãsiƙanci, cẽwa haƙĩƙa sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.

Verse 34

قُلْ هَلْ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ۚ قُلِ ٱللَّهُ يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ۖ فَأَنَّىٰ تُؤْفَكُونَ

Transliteration qul hal min shurakāikum man yabda-u l-khalqa thumma yuʿīduhu quli l-lahu yabda-u l-khalqa thumma yuʿīduhu fa-annā tu'fakūna

Hausa Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake fãra halitta, sa'an nan kuma ya mayar da ita?" Ka ce: "Allah ne Yake fãra halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita. To, yãyã akejũyar da ku?"

Verse 35

قُلْ هَلْ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَهْدِىٓ إِلَى ٱلْحَقِّ ۚ قُلِ ٱللَّهُ يَهْدِى لِلْحَقِّ ۗ أَفَمَن يَهْدِىٓ إِلَى ٱلْحَقِّ أَحَقُّ أَن يُتَّبَعَ أَمَّن لَّا يَهِدِّىٓ إِلَّآ أَن يُهْدَىٰ ۖ فَمَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ

Transliteration qul hal min shurakāikum man yahdī ilā l-ḥaqi quli l-lahu yahdī lil'ḥaqqi afaman yahdī ilā l-ḥaqi aḥaqqu an yuttabaʿa amman lā yahiddī illā an yuh'dā famā lakum kayfa taḥkumūna

Hausa Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?" Ka ce: "Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda bã ya shiryarwa fãce dai a shiryar da shi? To, mẽne ne a gare ku? Yãya kuke yin hukunci?"

Verse 36

وَمَا يَتَّبِعُ أَكْثَرُهُمْ إِلَّا ظَنًّا ۚ إِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغْنِى مِنَ ٱلْحَقِّ شَيْـًٔا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌۢ بِمَا يَفْعَلُونَ

Transliteration wamā yattabiʿu aktharuhum illā ẓannan inna l-ẓana lā yugh'nī mina l-ḥaqi shayan inna l-laha ʿalīmun bimā yafʿalūna

Hausa Kuma mafi yawansu bã su biyar kõme fãce zato. Lalle ne zato bã ya wadãtar da kõme daga gaskiya. Lalle Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.

Verse 37

وَمَا كَانَ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانُ أَن يُفْتَرَىٰ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَـٰكِن تَصْدِيقَ ٱلَّذِى بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ ٱلْكِتَـٰبِ لَا رَيْبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration wamā kāna hādhā l-qur'ānu an yuf'tarā min dūni l-lahi walākin taṣdīqa alladhī bayna yadayhi watafṣīla l-kitābi lā rayba fīhi min rabbi l-ʿālamīna

Hausa Kuma wan nan Alƙur'ãni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabãnin sa da bayãnin hukuncin littãffan Allah, Bãbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake.

Verse 38

أَمْ يَقُولُونَ ٱفْتَرَىٰهُ ۖ قُلْ فَأْتُوا۟ بِسُورَةٍ مِّثْلِهِۦ وَٱدْعُوا۟ مَنِ ٱسْتَطَعْتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ

Transliteration am yaqūlūna if'tarāhu qul fatū bisūratin mith'lihi wa-id'ʿū mani is'taṭaʿtum min dūni l-lahi in kuntum ṣādiqīna

Hausa Kõ sunã cẽwa, "Yã ƙirƙira shi?" Ka ce: "Ku zo da sũra guda misãlinsa, kuma ku kirãyi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya."

Verse 39

بَلْ كَذَّبُوا۟ بِمَا لَمْ يُحِيطُوا۟ بِعِلْمِهِۦ وَلَمَّا يَأْتِهِمْ تَأْوِيلُهُۥ ۚ كَذَٰلِكَ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۖ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Transliteration bal kadhabū bimā lam yuḥīṭū biʿil'mihi walammā yatihim tawīluhu kadhālika kadhaba alladhīna min qablihim fa-unẓur kayfa kāna ʿāqibatu l-ẓālimīna

Hausa Ã'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassarar sa ba ta riga ta jẽ musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabãninsu. Sai ka dũba, yãya ãƙibar Azzãlumai ta kasance?

Verse 40

وَمِنْهُم مَّن يُؤْمِنُ بِهِۦ وَمِنْهُم مَّن لَّا يُؤْمِنُ بِهِۦ ۚ وَرَبُّكَ أَعْلَمُ بِٱلْمُفْسِدِينَ

Transliteration wamin'hum man yu'minu bihi wamin'hum man lā yu'minu bihi warabbuka aʿlamu bil-muf'sidīna

Hausa Kuma daga cikin su akwai wanda yake yin ĩmãni da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda bã ya yin ĩmãni da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga maɓarnata.

Verse 41

وَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل لِّى عَمَلِى وَلَكُمْ عَمَلُكُمْ ۖ أَنتُم بَرِيٓـُٔونَ مِمَّآ أَعْمَلُ وَأَنَا۠ بَرِىٓءٌ مِّمَّا تَعْمَلُونَ

Transliteration wa-in kadhabūka faqul lī ʿamalī walakum ʿamalukum antum barīūna mimmā aʿmalu wa-anā barīon mimmā taʿmalūna

Hausa Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: "Inã da aikĩna kuma kunã da aikinku, kũ kuɓutattu ne daga abin da nake aikatãwa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke aikatãwa."

Verse 42

وَمِنْهُم مَّن يَسْتَمِعُونَ إِلَيْكَ ۚ أَفَأَنتَ تُسْمِعُ ٱلصُّمَّ وَلَوْ كَانُوا۟ لَا يَعْقِلُونَ

Transliteration wamin'hum man yastamiʿūna ilayka afa-anta tus'miʿu l-ṣuma walaw kānū lā yaʿqilūna

Hausa Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke saurare zuwa gare ka. Shin fa, kai kana jiyar da kurma, kuma kõ dã sun kasance bã su hankalta?

Verse 43

وَمِنْهُم مَّن يَنظُرُ إِلَيْكَ ۚ أَفَأَنتَ تَهْدِى ٱلْعُمْىَ وَلَوْ كَانُوا۟ لَا يُبْصِرُونَ

Transliteration wamin'hum man yanẓuru ilayka afa-anta tahdī l-ʿum'ya walaw kānū lā yub'ṣirūna

Hausa Kuma daga cikinsu akwai wanda yake tsõkaci zuwa gare ka. Shin fa, kai kana shiryar da makãfi, kuma kõ dã sun kasance bã su gani?

Verse 44

إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَظْلِمُ ٱلنَّاسَ شَيْـًٔا وَلَـٰكِنَّ ٱلنَّاسَ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ

Transliteration inna l-laha lā yaẓlimu l-nāsa shayan walākinna l-nāsa anfusahum yaẓlimūna

Hausa Lalle ne Allah ba Ya zãluntar mutãne da kõme, amma mutãnen ne ke zãluntar kansu.

Verse 45

وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ كَأَن لَّمْ يَلْبَثُوٓا۟ إِلَّا سَاعَةً مِّنَ ٱلنَّهَارِ يَتَعَارَفُونَ بَيْنَهُمْ ۚ قَدْ خَسِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِلِقَآءِ ٱللَّهِ وَمَا كَانُوا۟ مُهْتَدِينَ

Transliteration wayawma yaḥshuruhum ka-an lam yalbathū illā sāʿatan mina l-nahāri yataʿārafūna baynahum qad khasira alladhīna kadhabū biliqāi l-lahi wamā kānū muh'tadīna

Hausa Kuma rãnar da Yake tãra su, kamar ba su zauna ba fãce sa'a guda daga yini. Sunã gãne jũna a tsakãninsu. Haƙĩƙa, waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasãra. Kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.

Verse 46

وَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعْضَ ٱلَّذِى نَعِدُهُمْ أَوْ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ ثُمَّ ٱللَّهُ شَهِيدٌ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ

Transliteration wa-immā nuriyannaka baʿḍa alladhī naʿiduhum aw natawaffayannaka fa-ilaynā marjiʿuhum thumma l-lahu shahīdun ʿalā mā yafʿalūna

Hausa Kuma imma dai, haƙĩƙa, Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu alkawari, kõ kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makõmarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne shaida a kan abin da suke aikatãwa.

Verse 47

وَلِكُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولٌ ۖ فَإِذَا جَآءَ رَسُولُهُمْ قُضِىَ بَيْنَهُم بِٱلْقِسْطِ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ

Transliteration walikulli ummatin rasūlun fa-idhā jāa rasūluhum quḍiya baynahum bil-qis'ṭi wahum lā yuẓ'lamūna

Hausa Kuma ga kõwace al'umma akwai Manzo. Sa'an nan idan Manzonsu ya je, sai a yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma sũ, bã a zãluntar su.

Verse 48

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَـٰذَا ٱلْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ

Transliteration wayaqūlūna matā hādhā l-waʿdu in kuntum ṣādiqīna

Hausa Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai auku, idan kun kasance mãsu gaskiya?"

Verse 49

قُل لَّآ أَمْلِكُ لِنَفْسِى ضَرًّا وَلَا نَفْعًا إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُ ۗ لِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌ ۚ إِذَا جَآءَ أَجَلُهُمْ فَلَا يَسْتَـْٔخِرُونَ سَاعَةً ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ

Transliteration qul lā amliku linafsī ḍarran walā nafʿan illā mā shāa l-lahu likulli ummatin ajalun idhā jāa ajaluhum falā yastakhirūna sāʿatan walā yastaqdimūna

Hausa Ka ce: "Ba na mallaka wa kaina wata cũta, haka kuma wani amfãni, sai abin da Allah Ya so. Ga kõwace al'umma akwai ajali, idan ajalinsu ya zo, to, bã zã su yi jinkiri daga gare shi ba, kõ dã sã'ã guda, kuma bã zã su gabãta ba."

Verse 50

قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِنْ أَتَىٰكُمْ عَذَابُهُۥ بَيَـٰتًا أَوْ نَهَارًا مَّاذَا يَسْتَعْجِلُ مِنْهُ ٱلْمُجْرِمُونَ

Transliteration qul ara-aytum in atākum ʿadhābuhu bayātan aw nahāran mādhā yastaʿjilu min'hu l-muj'rimūna

Hausa Ka ce: "Shin, kun gani, idan azãbarSa ta zo muku da dare ko da rãna? Mẽne ne daga gare shimãsu laifi suke nẽman gaggãwarsa?"

Verse 51

أَثُمَّ إِذَا مَا وَقَعَ ءَامَنتُم بِهِۦٓ ۚ ءَآلْـَٔـٰنَ وَقَدْ كُنتُم بِهِۦ تَسْتَعْجِلُونَ

Transliteration athumma idhā mā waqaʿa āmantum bihi āl'āna waqad kuntum bihi tastaʿjilūna

Hausa Shin sa'an nan kuma idan har ya auku, kun yi ĩmãni da shi? Ashe? Yanzu kuwa, alhãli kun kasance game da shi kunã nẽman gaggãwar aukuwarsa?

Verse 52

ثُمَّ قِيلَ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ ذُوقُوا۟ عَذَابَ ٱلْخُلْدِ هَلْ تُجْزَوْنَ إِلَّا بِمَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ

Transliteration thumma qīla lilladhīna ẓalamū dhūqū ʿadhāba l-khul'di hal tuj'zawna illā bimā kuntum taksibūna

Hausa Sa'an nan kuma aka ce ga waɗanda suka yi zãlunci, "Ku ɗanɗani azãbar dawwama! Shin, anã sãka muku fãce da abin da kuka kasance kuna aikatãwa?"

Verse 53

۞ وَيَسْتَنۢبِـُٔونَكَ أَحَقٌّ هُوَ ۖ قُلْ إِى وَرَبِّىٓ إِنَّهُۥ لَحَقٌّ ۖ وَمَآ أَنتُم بِمُعْجِزِينَ

Transliteration wayastanbiūnaka aḥaqqun huwa qul ī warabbī innahu laḥaqqun wamā antum bimuʿ'jizīna

Hausa Kuma sunã tambayar ka: Shin gaskiya ne? Ka ce: "Ĩ, ina rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle gaskiya ne, kuma ba ku zama mãsu buwãya ba."

Verse 54

وَلَوْ أَنَّ لِكُلِّ نَفْسٍ ظَلَمَتْ مَا فِى ٱلْأَرْضِ لَٱفْتَدَتْ بِهِۦ ۗ وَأَسَرُّوا۟ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ۖ وَقُضِىَ بَيْنَهُم بِٱلْقِسْطِ ۚ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ

Transliteration walaw anna likulli nafsin ẓalamat mā fī l-arḍi la-if'tadat bihi wa-asarrū l-nadāmata lammā ra-awū l-ʿadhāba waquḍiya baynahum bil-qis'ṭi wahum lā yuẓ'lamūna

Hausa Kuma dã kõwane rai wanda ya yi zãlunci yã mallaki duka abin da yake a cikin ƙasa, to, dã yã yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma bã zã a zãlunce su ba.

Verse 55

أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۗ أَلَآ إِنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration alā inna lillahi mā fī l-samāwāti wal-arḍi alā inna waʿda l-lahi ḥaqqun walākinna aktharahum lā yaʿlamūna

Hausa To! Haƙĩƙa Allah Ya mallaki abin da yake a cikin sammai da ƙasa. To! Haƙĩƙa wa'adin Allah gaskiya ne. Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.

Verse 56

هُوَ يُحْىِۦ وَيُمِيتُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Transliteration huwa yuḥ'yī wayumītu wa-ilayhi tur'jaʿūna

Hausa Shi ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma zuwa gare Shi ne ake mayar da ku.

Verse 57

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدْ جَآءَتْكُم مَّوْعِظَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَشِفَآءٌ لِّمَا فِى ٱلصُّدُورِ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration yāayyuhā l-nāsu qad jāatkum mawʿiẓatun min rabbikum washifāon limā fī l-ṣudūri wahudan waraḥmatun lil'mu'minīna

Hausa Ya ku mutãne! Lalle wa'azi yã jẽ muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙirãza, da shiriya da rahama ga muminai.

Verse 58

قُلْ بِفَضْلِ ٱللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِۦ فَبِذَٰلِكَ فَلْيَفْرَحُوا۟ هُوَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ

Transliteration qul bifaḍli l-lahi wabiraḥmatihi fabidhālika falyafraḥū huwa khayrun mimmā yajmaʿūna

Hausa Ka ce: "Da falalar Allah da rahamar Sa. Sai su yi farin ciki da wannan." Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa.

Verse 59

قُلْ أَرَءَيْتُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ لَكُم مِّن رِّزْقٍ فَجَعَلْتُم مِّنْهُ حَرَامًا وَحَلَـٰلًا قُلْ ءَآللَّهُ أَذِنَ لَكُمْ ۖ أَمْ عَلَى ٱللَّهِ تَفْتَرُونَ

Transliteration qul ara-aytum mā anzala l-lahu lakum min riz'qin fajaʿaltum min'hu ḥarāman waḥalālan qul āllahu adhina lakum am ʿalā l-lahi taftarūna

Hausa Ka ce: "Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar sabõda ku na arziki, sai kuka sanya hukuncin haramci da halacci a gare shi?" Ka ce: "Shin, Allah ne Ya yi muku izni, ko ga Allah kuke ƙirƙirãwar ƙarya?"

Verse 60

وَمَا ظَنُّ ٱلَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَشْكُرُونَ

Transliteration wamā ẓannu alladhīna yaftarūna ʿalā l-lahi l-kadhiba yawma l-qiyāmati inna l-laha ladhū faḍlin ʿalā l-nāsi walākinna aktharahum lā yashkurūna

Hausa Kuma mẽne ne zaton waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, a Rãnar ¡iyãma? Lalle haƙĩƙa, Allah Ma, abũcin falala ne a kan mutãne, amma kuma mafi yawansu bã su gõdẽwa.

Verse 61

وَمَا تَكُونُ فِى شَأْنٍ وَمَا تَتْلُوا۟ مِنْهُ مِن قُرْءَانٍ وَلَا تَعْمَلُونَ مِنْ عَمَلٍ إِلَّا كُنَّا عَلَيْكُمْ شُهُودًا إِذْ تُفِيضُونَ فِيهِ ۚ وَمَا يَعْزُبُ عَن رَّبِّكَ مِن مِّثْقَالِ ذَرَّةٍ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا فِى ٱلسَّمَآءِ وَلَآ أَصْغَرَ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكْبَرَ إِلَّا فِى كِتَـٰبٍ مُّبِينٍ

Transliteration wamā takūnu fī shanin wamā tatlū min'hu min qur'ānin walā taʿmalūna min ʿamalin illā kunnā ʿalaykum shuhūdan idh tufīḍūna fīhi wamā yaʿzubu ʿan rabbika min mith'qāli dharratin fī l-arḍi walā fī l-samāi walā aṣghara min dhālika walā akbara illā fī kitābin mubīnin

Hausa Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, fãce Mun kasance Halarce a lõkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bã zai yi nĩsa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma bãbu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma bãbu mafi girma, fãce yana a cikin littãfi bayyananne.

Verse 62

أَلَآ إِنَّ أَوْلِيَآءَ ٱللَّهِ لَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ

Transliteration alā inna awliyāa l-lahi lā khawfun ʿalayhim walā hum yaḥzanūna

Hausa To, Lalle ne masõyan Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba.

Verse 63

ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَكَانُوا۟ يَتَّقُونَ

Transliteration alladhīna āmanū wakānū yattaqūna

Hausa Waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa.

Verse 64

لَهُمُ ٱلْبُشْرَىٰ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَفِى ٱلْـَٔاخِرَةِ ۚ لَا تَبْدِيلَ لِكَلِمَـٰتِ ٱللَّهِ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ

Transliteration lahumu l-bush'rā fī l-ḥayati l-dun'yā wafī l-ākhirati lā tabdīla likalimāti l-lahi dhālika huwa l-fawzu l-ʿaẓīmu

Hausa Sunã da bushãra a cikin rãyuwar dũniya da ta Lãhira. Bãbu musanyãwa ga kalmõmin Allah. Wancan shi ne babban rabo mai girma,

Verse 65

وَلَا يَحْزُنكَ قَوْلُهُمْ ۘ إِنَّ ٱلْعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا ۚ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ

Transliteration walā yaḥzunka qawluhum inna l-ʿizata lillahi jamīʿan huwa l-samīʿu l-ʿalīmu

Hausa Kada maganarsu ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai jĩ, Masani.

Verse 66

أَلَآ إِنَّ لِلَّهِ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ ۗ وَمَا يَتَّبِعُ ٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ شُرَكَآءَ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُونَ

Transliteration alā inna lillahi man fī l-samāwāti waman fī l-arḍi wamā yattabiʿu alladhīna yadʿūna min dūni l-lahi shurakāa in yattabiʿūna illā l-ẓana wa-in hum illā yakhruṣūna

Hausa To! Haƙĩƙa Allah Yanã da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bã su biyar waɗansu abõkan tarẽwa (ga Allah a Mulkin Sa). Bã su biyar kõme fãce zato. Kuma ba su zama ba fãce sunã ƙiri faɗi kawai.

Verse 67

هُوَ ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيْلَ لِتَسْكُنُوا۟ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبْصِرًا ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ

Transliteration huwa alladhī jaʿala lakumu al-layla litaskunū fīhi wal-nahāra mub'ṣiran inna fī dhālika laāyātin liqawmin yasmaʿūna

Hausa Shĩ ne wanda Ya sanya muku dare, dõmin ku natsu a cikinsa, da yini mai sanya a yi gani. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda sukẽ ji.

Verse 68

قَالُوا۟ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدًا ۗ سُبْحَـٰنَهُۥ ۖ هُوَ ٱلْغَنِىُّ ۖ لَهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۚ إِنْ عِندَكُم مِّن سُلْطَـٰنٍۭ بِهَـٰذَآ ۚ أَتَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ

Transliteration qālū ittakhadha l-lahu waladan sub'ḥānahu huwa l-ghaniyu lahu mā fī l-samāwāti wamā fī l-arḍi in ʿindakum min sul'ṭānin bihādhā ataqūlūna ʿalā l-lahi mā lā taʿlamūna

Hausa Suka ce: "Allah Ya riƙi ɗa." Tsarkinsa yã tabbata! Shi ne wadãtacce Yanã da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku bãbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kunã faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah?

Verse 69

قُلْ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ لَا يُفْلِحُونَ

Transliteration qul inna alladhīna yaftarūna ʿalā l-lahi l-kadhiba lā yuf'liḥūna

Hausa Ka ce: "Haƙĩƙa waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, bã zã su ci nasara ba."

Verse 70

مَتَـٰعٌ فِى ٱلدُّنْيَا ثُمَّ إِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ ثُمَّ نُذِيقُهُمُ ٱلْعَذَابَ ٱلشَّدِيدَ بِمَا كَانُوا۟ يَكْفُرُونَ

Transliteration matāʿun fī l-dun'yā thumma ilaynā marjiʿuhum thumma nudhīquhumu l-ʿadhāba l-shadīda bimā kānū yakfurūna

Hausa Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.

Verse 71

۞ وَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ نُوحٍ إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِۦ يَـٰقَوْمِ إِن كَانَ كَبُرَ عَلَيْكُم مَّقَامِى وَتَذْكِيرِى بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ فَعَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلْتُ فَأَجْمِعُوٓا۟ أَمْرَكُمْ وَشُرَكَآءَكُمْ ثُمَّ لَا يَكُنْ أَمْرُكُمْ عَلَيْكُمْ غُمَّةً ثُمَّ ٱقْضُوٓا۟ إِلَىَّ وَلَا تُنظِرُونِ

Transliteration wa-ut'lu ʿalayhim naba-a nūḥin idh qāla liqawmihi yāqawmi in kāna kabura ʿalaykum maqāmī watadhkīrī biāyāti l-lahi faʿalā l-lahi tawakkaltu fa-ajmiʿū amrakum washurakāakum thumma lā yakun amrukum ʿalaykum ghummatan thumma iq'ḍū ilayya walā tunẓirūni

Hausa Kuma ka karanta musu lãbãrin Nũhu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ya mutãnẽna! Idan matsayĩna da tunãtarwata ameda ãyõyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dõgara. Sai ku tãra al'amarinku, kũ da abũbuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri."

Verse 72

فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَمَا سَأَلْتُكُم مِّنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ ٱلْمُسْلِمِينَ

Transliteration fa-in tawallaytum famā sa-altukum min ajrin in ajriya illā ʿalā l-lahi wa-umir'tu an akūna mina l-mus'limīna

Hausa "Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."

Verse 73

فَكَذَّبُوهُ فَنَجَّيْنَـٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِى ٱلْفُلْكِ وَجَعَلْنَـٰهُمْ خَلَـٰٓئِفَ وَأَغْرَقْنَا ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا ۖ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُنذَرِينَ

Transliteration fakadhabūhu fanajjaynāhu waman maʿahu fī l-ful'ki wajaʿalnāhum khalāifa wa-aghraqnā alladhīna kadhabū biāyātinā fa-unẓur kayfa kāna ʿāqibatu l-mundharīna

Hausa Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tãre da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su mãsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ãyõyinMu. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗan da aka yi wa gargaɗi ta kasance.

Verse 74

ثُمَّ بَعَثْنَا مِنۢ بَعْدِهِۦ رُسُلًا إِلَىٰ قَوْمِهِمْ فَجَآءُوهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَمَا كَانُوا۟ لِيُؤْمِنُوا۟ بِمَا كَذَّبُوا۟ بِهِۦ مِن قَبْلُ ۚ كَذَٰلِكَ نَطْبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلْمُعْتَدِينَ

Transliteration thumma baʿathnā min baʿdihi rusulan ilā qawmihim fajāūhum bil-bayināti famā kānū liyu'minū bimā kadhabū bihi min qablu kadhālika naṭbaʿu ʿalā qulūbi l-muʿ'tadīna

Hausa Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga bãyansa zuwa ga mutãnensu, suka jẽmusu da hujjõji bayyanannu, to, ba su kasance zã su yi ĩmãni ba sabõda sun ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufẽwa a kan zukãtan mãsu ta'addi.

Verse 75

ثُمَّ بَعَثْنَا مِنۢ بَعْدِهِم مُّوسَىٰ وَهَـٰرُونَ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِۦ بِـَٔايَـٰتِنَا فَٱسْتَكْبَرُوا۟ وَكَانُوا۟ قَوْمًا مُّجْرِمِينَ

Transliteration thumma baʿathnā min baʿdihim mūsā wahārūna ilā fir'ʿawna wamala-ihi biāyātinā fa-is'takbarū wakānū qawman muj'rimīna

Hausa Sa'an nan kuma a bãyansu Muka aika Mũsa da Hãrũna zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, tãre da ãyõyin Mu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutãne mãsu laifi.

Verse 76

فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلْحَقُّ مِنْ عِندِنَا قَالُوٓا۟ إِنَّ هَـٰذَا لَسِحْرٌ مُّبِينٌ

Transliteration falammā jāahumu l-ḥaqu min ʿindinā qālū inna hādhā lasiḥ'run mubīnun

Hausa Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga gare Mu, suka ce: "Wannan haƙĩƙa sihiri ne bayyananne."

Verse 77

قَالَ مُوسَىٰٓ أَتَقُولُونَ لِلْحَقِّ لَمَّا جَآءَكُمْ ۖ أَسِحْرٌ هَـٰذَا وَلَا يُفْلِحُ ٱلسَّـٰحِرُونَ

Transliteration qāla mūsā ataqūlūna lil'ḥaqqi lammā jāakum asiḥ'run hādhā walā yuf'liḥu l-sāḥirūna

Hausa Mũsã ya ce: " Shin, kunã cẽwa ga gaskiya a lõkacin data zo muku? Shin, sihiri ne wannan? Lalle masihirci, bã ya cin Nasara."

Verse 78

قَالُوٓا۟ أَجِئْتَنَا لِتَلْفِتَنَا عَمَّا وَجَدْنَا عَلَيْهِ ءَابَآءَنَا وَتَكُونَ لَكُمَا ٱلْكِبْرِيَآءُ فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا نَحْنُ لَكُمَا بِمُؤْمِنِينَ

Transliteration qālū aji'tanā litalfitanā ʿammā wajadnā ʿalayhi ābāanā watakūna lakumā l-kib'riyāu fī l-arḍi wamā naḥnu lakumā bimu'minīna

Hausa Suka ce: "Shin, ka zo mana ne dõmin ka jũyar da mu daga abin da muka iske ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Bã zã mu zama mãsu ĩmãni ba sabõda ku."

Verse 79

وَقَالَ فِرْعَوْنُ ٱئْتُونِى بِكُلِّ سَـٰحِرٍ عَلِيمٍ

Transliteration waqāla fir'ʿawnu i'tūnī bikulli sāḥirin ʿalīmin

Hausa Kuma Fir'auna ya ce: "Ku zo mini da dukan masihirci, masani."

Verse 80

فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلْقُوا۟ مَآ أَنتُم مُّلْقُونَ

Transliteration falammā jāa l-saḥaratu qāla lahum mūsā alqū mā antum mul'qūna

Hausa To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa."

Verse 81

فَلَمَّآ أَلْقَوْا۟ قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئْتُم بِهِ ٱلسِّحْرُ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبْطِلُهُۥٓ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصْلِحُ عَمَلَ ٱلْمُفْسِدِينَ

Transliteration falammā alqaw qāla mūsā mā ji'tum bihi l-siḥ'ru inna l-laha sayub'ṭiluhu inna l-laha lā yuṣ'liḥu ʿamala l-muf'sidīna

Hausa To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: "Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata.

Verse 82

وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلْحَقَّ بِكَلِمَـٰتِهِۦ وَلَوْ كَرِهَ ٱلْمُجْرِمُونَ

Transliteration wayuḥiqqu l-lahu l-ḥaqa bikalimātihi walaw kariha l-muj'rimūna

Hausa "Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõmin Sa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi."

Verse 83

فَمَآ ءَامَنَ لِمُوسَىٰٓ إِلَّا ذُرِّيَّةٌ مِّن قَوْمِهِۦ عَلَىٰ خَوْفٍ مِّن فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِمْ أَن يَفْتِنَهُمْ ۚ وَإِنَّ فِرْعَوْنَ لَعَالٍ فِى ٱلْأَرْضِ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلْمُسْرِفِينَ

Transliteration famā āmana limūsā illā dhurriyyatun min qawmihi ʿalā khawfin min fir'ʿawna wamala-ihim an yaftinahum wa-inna fir'ʿawna laʿālin fī l-arḍi wa-innahu lamina l-mus'rifīna

Hausa Sa'an nan bãbu wanda ya yi ĩmãni da Mũsa fãce zuriya daga mutãnensa, a kan tsõron kada Fir'auna da shũgabanninsu su fitinẽ su. Lalle, haƙĩƙa, Fir'auna marinjãyi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga mãsu ɓarna.

Verse 84

وَقَالَ مُوسَىٰ يَـٰقَوْمِ إِن كُنتُمْ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ فَعَلَيْهِ تَوَكَّلُوٓا۟ إِن كُنتُم مُّسْلِمِينَ

Transliteration waqāla mūsā yāqawmi in kuntum āmantum bil-lahi faʿalayhi tawakkalū in kuntum mus'limīna

Hausa Kuma Mũsã ya ce: "Yã kũ mutãnena! Idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah, to, a gare Shi sai ku dõgara, idan kun kasance Musulmi."

Verse 85

فَقَالُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلْنَا رَبَّنَا لَا تَجْعَلْنَا فِتْنَةً لِّلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Transliteration faqālū ʿalā l-lahi tawakkalnā rabbanā lā tajʿalnā fit'natan lil'qawmi l-ẓālimīna

Hausa Sai suka ce: "Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu fitina ga mutãne Azzãlumai.

Verse 86

وَنَجِّنَا بِرَحْمَتِكَ مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلْكَـٰفِرِينَ

Transliteration wanajjinā biraḥmatika mina l-qawmi l-kāfirīna

Hausa "Kuma Ka kuɓutar da mu dõmin RahamarKa, daga mutãne kãfirai."

Verse 87

وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰ وَأَخِيهِ أَن تَبَوَّءَا لِقَوْمِكُمَا بِمِصْرَ بُيُوتًا وَٱجْعَلُوا۟ بُيُوتَكُمْ قِبْلَةً وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ ۗ وَبَشِّرِ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration wa-awḥaynā ilā mūsā wa-akhīhi an tabawwaā liqawmikumā bimiṣ'ra buyūtan wa-ij'ʿalū buyūtakum qib'latan wa-aqīmū l-ṣalata wabashiri l-mu'minīna

Hausa Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutãnenku a Masar a cikin wasu gidãje. Kuma ku sanya gidãjenku su fuskanci Alƙibla, kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bãyar da bushãra ga mãsu ĩmãni.

Verse 88

وَقَالَ مُوسَىٰ رَبَّنَآ إِنَّكَ ءَاتَيْتَ فِرْعَوْنَ وَمَلَأَهُۥ زِينَةً وَأَمْوَٰلًا فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا رَبَّنَا لِيُضِلُّوا۟ عَن سَبِيلِكَ ۖ رَبَّنَا ٱطْمِسْ عَلَىٰٓ أَمْوَٰلِهِمْ وَٱشْدُدْ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَلَا يُؤْمِنُوا۟ حَتَّىٰ يَرَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ

Transliteration waqāla mūsā rabbanā innaka ātayta fir'ʿawna wamala-ahu zīnatan wa-amwālan fī l-ḥayati l-dun'yā rabbanā liyuḍillū ʿan sabīlika rabbanā iṭ'mis ʿalā amwālihim wa-ush'dud ʿalā qulūbihim falā yu'minū ḥattā yarawū l-ʿadhāba l-alīma

Hausa Sai MũSã ya ce: "Yã Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyõyi a cikin rãyuwar dũniya, yã Ubangijinmu, dõmin su ɓatar (damutãne) daga hanyarKa. Yã Ubangijinmu! Ka shãfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri a kan zukãtansu yadda bã zã su yi ĩmãni ba har su ga azãba mai raɗaɗi."

Verse 89

قَالَ قَدْ أُجِيبَت دَّعْوَتُكُمَا فَٱسْتَقِيمَا وَلَا تَتَّبِعَآنِّ سَبِيلَ ٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration qāla qad ujībat daʿwatukumā fa-is'taqīmā walā tattabiʿānni sabīla alladhīna lā yaʿlamūna

Hausa (Allah) Yã ce: "Lalle ne an karɓi addu'arku. Sai ku daidaitu kuma kada ku bi hanyar waɗanda ba su sani ba."

Verse 90

۞ وَجَـٰوَزْنَا بِبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱلْبَحْرَ فَأَتْبَعَهُمْ فِرْعَوْنُ وَجُنُودُهُۥ بَغْيًا وَعَدْوًا ۖ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَدْرَكَهُ ٱلْغَرَقُ قَالَ ءَامَنتُ أَنَّهُۥ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا ٱلَّذِىٓ ءَامَنَتْ بِهِۦ بَنُوٓا۟ إِسْرَٰٓءِيلَ وَأَنَا۠ مِنَ ٱلْمُسْلِمِينَ

Transliteration wajāwaznā bibanī is'rāīla l-baḥra fa-atbaʿahum fir'ʿawnu wajunūduhu baghyan waʿadwan ḥattā idhā adrakahu l-gharaqu qāla āmantu annahu lā ilāha illā alladhī āmanat bihi banū is'rāīla wa-anā mina l-mus'limīna

Hausa Kuma Muka ƙẽtãrar da Banĩ Isrã'ila tẽku sai Fir'auna da rundunarsa suka bĩ su bisa ga zãlunci da ƙẽtare haddi, har a lõkacin da nutsẽwa ta riske shi ya ce: "Nã yi ĩmãni cẽwa, haƙĩƙa, bãbu abin bautawa fãce wannan da Banũ Isrã'il suka yi ĩmãni da Shi, kumanĩ, ina daga Musulmi."

Verse 91

ءَآلْـَٔـٰنَ وَقَدْ عَصَيْتَ قَبْلُ وَكُنتَ مِنَ ٱلْمُفْسِدِينَ

Transliteration āl'āna waqad ʿaṣayta qablu wakunta mina l-muf'sidīna

Hausa Ashe! A yanzu! Alhãli kuwa, haƙĩƙa ka sãɓa a gabãni, kuma ka kasance daga mãsu ɓarna?

Verse 92

فَٱلْيَوْمَ نُنَجِّيكَ بِبَدَنِكَ لِتَكُونَ لِمَنْ خَلْفَكَ ءَايَةً ۚ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ ٱلنَّاسِ عَنْ ءَايَـٰتِنَا لَغَـٰفِلُونَ

Transliteration fal-yawma nunajjīka bibadanika litakūna liman khalfaka āyatan wa-inna kathīran mina l-nāsi ʿan āyātinā laghāfilūna

Hausa To, a yau Munã kuɓutar da kai game da jikinka, dõmin ka kasance ãyã ga waɗanda suke a bãyanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu.

Verse 93

وَلَقَدْ بَوَّأْنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ مُبَوَّأَ صِدْقٍ وَرَزَقْنَـٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَـٰتِ فَمَا ٱخْتَلَفُوا۟ حَتَّىٰ جَآءَهُمُ ٱلْعِلْمُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِى بَيْنَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ فِيمَا كَانُوا۟ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ

Transliteration walaqad bawwanā banī is'rāīla mubawwa-a ṣid'qin warazaqnāhum mina l-ṭayibāti famā ikh'talafū ḥattā jāahumu l-ʿil'mu inna rabbaka yaqḍī baynahum yawma l-qiyāmati fīmā kānū fīhi yakhtalifūna

Hausa Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun zaunar da Banĩ Isrã'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzũta su daga abũbuwa mãsu dãɗi. Sa'an nan ba su sãɓa ba har ilmi ya jẽ musu. Lalle ne Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar Kiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna.

Verse 94

فَإِن كُنتَ فِى شَكٍّ مِّمَّآ أَنزَلْنَآ إِلَيْكَ فَسْـَٔلِ ٱلَّذِينَ يَقْرَءُونَ ٱلْكِتَـٰبَ مِن قَبْلِكَ ۚ لَقَدْ جَآءَكَ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُمْتَرِينَ

Transliteration fa-in kunta fī shakkin mimmā anzalnā ilayka fasali alladhīna yaqraūna l-kitāba min qablika laqad jāaka l-ḥaqu min rabbika falā takūnanna mina l-mum'tarīna

Hausa To, idan ka kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littãfi daga gabaninka. Lalle ne, haƙĩƙa, gaskiya tã jẽ maka daga Ubangijinka dõmin haka kada ka kasance daga mãsu kõkanto.

Verse 95

وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ فَتَكُونَ مِنَ ٱلْخَـٰسِرِينَ

Transliteration walā takūnanna mina alladhīna kadhabū biāyāti l-lahi fatakūna mina l-khāsirīna

Hausa Kuma kada ka kasance daga waɗanda suke ƙaryatãwa game da ãyõyin Allah, har ka kasance daga mãsu hasãra.

Verse 96

إِنَّ ٱلَّذِينَ حَقَّتْ عَلَيْهِمْ كَلِمَتُ رَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ

Transliteration inna alladhīna ḥaqqat ʿalayhim kalimatu rabbika lā yu'minūna

Hausa Lalle ne waɗan da kalmar Ubangijinka ta wajaba a kansu, bã zã su yi ĩmãni ba.

Verse 97

وَلَوْ جَآءَتْهُمْ كُلُّ ءَايَةٍ حَتَّىٰ يَرَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ

Transliteration walaw jāathum kullu āyatin ḥattā yarawū l-ʿadhāba l-alīma

Hausa Kuma kõ dã kõwace ãyã ta jẽ musu, sai sun ga Azãba mai raɗaɗi.

Verse 98

فَلَوْلَا كَانَتْ قَرْيَةٌ ءَامَنَتْ فَنَفَعَهَآ إِيمَـٰنُهَآ إِلَّا قَوْمَ يُونُسَ لَمَّآ ءَامَنُوا۟ كَشَفْنَا عَنْهُمْ عَذَابَ ٱلْخِزْىِ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَمَتَّعْنَـٰهُمْ إِلَىٰ حِينٍ

Transliteration falawlā kānat qaryatun āmanat fanafaʿahā īmānuhā illā qawma yūnusa lammā āmanū kashafnā ʿanhum ʿadhāba l-khiz'yi fī l-ḥayati l-dun'yā wamattaʿnāhum ilā ḥīnin

Hausa To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye Azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci.

Verse 99

وَلَوْ شَآءَ رَبُّكَ لَـَٔامَنَ مَن فِى ٱلْأَرْضِ كُلُّهُمْ جَمِيعًا ۚ أَفَأَنتَ تُكْرِهُ ٱلنَّاسَ حَتَّىٰ يَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ

Transliteration walaw shāa rabbuka laāmana man fī l-arḍi kulluhum jamīʿan afa-anta tuk'rihu l-nāsa ḥattā yakūnū mu'minīna

Hausa Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã waɗanda suke a cikin ƙasa sun yi ĩmãni dukansu gabã ɗaya. Shin, kai kanã tĩlasta mutãnene har su kasance mãsu ĩmãni?

Verse 100

وَمَا كَانَ لِنَفْسٍ أَن تُؤْمِنَ إِلَّا بِإِذْنِ ٱللَّهِ ۚ وَيَجْعَلُ ٱلرِّجْسَ عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يَعْقِلُونَ

Transliteration wamā kāna linafsin an tu'mina illā bi-idh'ni l-lahi wayajʿalu l-rij'sa ʿalā alladhīna lā yaʿqilūna

Hausa Kuma ba ya kasancẽwa ga wani rai ya yi ĩmãni fãce da iznin Allah, kuma (Allah) Yanã sanya ƙazanta a kan waɗan da bã su yin hankali.

Verse 101

قُلِ ٱنظُرُوا۟ مَاذَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَمَا تُغْنِى ٱلْـَٔايَـٰتُ وَٱلنُّذُرُ عَن قَوْمٍ لَّا يُؤْمِنُونَ

Transliteration quli unẓurū mādhā fī l-samāwāti wal-arḍi wamā tugh'nī l-āyātu wal-nudhuru ʿan qawmin lā yu'minūna

Hausa Ka ce: "Ku dũbi abin da yake cikin sammai da ƙasa."Kuma ãyõyi da gargaɗi bã su wadãtarwa ga mutãne waɗanda bã su yin ĩmãni.

Verse 102

فَهَلْ يَنتَظِرُونَ إِلَّا مِثْلَ أَيَّامِ ٱلَّذِينَ خَلَوْا۟ مِن قَبْلِهِمْ ۚ قُلْ فَٱنتَظِرُوٓا۟ إِنِّى مَعَكُم مِّنَ ٱلْمُنتَظِرِينَ

Transliteration fahal yantaẓirūna illā mith'la ayyāmi alladhīna khalaw min qablihim qul fa-intaẓirū innī maʿakum mina l-muntaẓirīna

Hausa To, Shin sunã jiran wani abu fãce kamar misãlin kwãnukan waɗanda suka shũɗe daga gabãnin su? Ka ce: "Ku yi jira! Lalle nĩ tãre da ku, inã daga mãsu jira."

Verse 103

ثُمَّ نُنَجِّى رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ۚ كَذَٰلِكَ حَقًّا عَلَيْنَا نُنجِ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration thumma nunajjī rusulanā wa-alladhīna āmanū kadhālika ḥaqqan ʿalaynā nunji l-mu'minīna

Hausa Sa'an nan kuma Munã kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da mãsu ĩmãni.

Verse 104

قُلْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمْ فِى شَكٍّ مِّن دِينِى فَلَآ أَعْبُدُ ٱلَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَـٰكِنْ أَعْبُدُ ٱللَّهَ ٱلَّذِى يَتَوَفَّىٰكُمْ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Transliteration qul yāayyuhā l-nāsu in kuntum fī shakkin min dīnī falā aʿbudu alladhīna taʿbudūna min dūni l-lahi walākin aʿbudu l-laha alladhī yatawaffākum wa-umir'tu an akūna mina l-mu'minīna

Hausa Ka ce: "Yã kũ mutãne! Idan kun kasance a cikin kõkanto daga addinĩna, to bã ni bauta wa, waɗanda kuke, bautã wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rãyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu ĩmãni."

Verse 105

وَأَنْ أَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ

Transliteration wa-an aqim wajhaka lilddīni ḥanīfan walā takūnanna mina l-mush'rikīna

Hausa "Kuma (an ce mini): Ka tsayar da fuskarka ga Addini, kanã karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga mãsu shirka.

Verse 106

وَلَا تَدْعُ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَ ۖ فَإِن فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذًا مِّنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Transliteration walā tadʿu min dūni l-lahi mā lā yanfaʿuka walā yaḍurruka fa-in faʿalta fa-innaka idhan mina l-ẓālimīna

Hausa "Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci."

Verse 107

وَإِن يَمْسَسْكَ ٱللَّهُ بِضُرٍّ فَلَا كَاشِفَ لَهُۥٓ إِلَّا هُوَ ۖ وَإِن يُرِدْكَ بِخَيْرٍ فَلَا رَآدَّ لِفَضْلِهِۦ ۚ يُصِيبُ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ ۚ وَهُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration wa-in yamsaska l-lahu biḍurrin falā kāshifa lahu illā huwa wa-in yurid'ka bikhayrin falā rādda lifaḍlihi yuṣību bihi man yashāu min ʿibādihi wahuwa l-ghafūru l-raḥīmu

Hausa Kuma idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, bãbu mai yãyẽ ta fãce shi, kuma idan Yanã nufin ka da wani alhẽri, to, bãbumai mayar da falalarSa. Yanã sãmun wanda Yake so daga cikin bãyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.

Verse 108

قُلْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدْ جَآءَكُمُ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّكُمْ ۖ فَمَنِ ٱهْتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهْتَدِى لِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا ۖ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيْكُم بِوَكِيلٍ

Transliteration qul yāayyuhā l-nāsu qad jāakumu l-ḥaqu min rabbikum famani ih'tadā fa-innamā yahtadī linafsihi waman ḍalla fa-innamā yaḍillu ʿalayhā wamā anā ʿalaykum biwakīlin

Hausa Ka ce: "Yã ku mutãne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba."

Verse 109

وَٱتَّبِعْ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيْكَ وَٱصْبِرْ حَتَّىٰ يَحْكُمَ ٱللَّهُ ۚ وَهُوَ خَيْرُ ٱلْحَـٰكِمِينَ

Transliteration wa-ittabiʿ mā yūḥā ilayka wa-iṣ'bir ḥattā yaḥkuma l-lahu wahuwa khayru l-ḥākimīna

Hausa Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci.

Read Surah Yunus in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.