Surah Al-Mu'minun in Hausa: translation and audio
Surah 23 · المؤمنون · The Believers · 118 verses
Surah Al-Mu'minun verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Mu'minun word by word in English.
Verse 1
قَدْ أَفْلَحَ ٱلْمُؤْمِنُونَ
Transliteration qad aflaḥa l-mu'minūna
Hausa Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ.
Verse 2
ٱلَّذِينَ هُمْ فِى صَلَاتِهِمْ خَـٰشِعُونَ
Transliteration alladhīna hum fī ṣalātihim khāshiʿūna
Hausa Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne.
Verse 3
وَٱلَّذِينَ هُمْ عَنِ ٱللَّغْوِ مُعْرِضُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum ʿani l-laghwi muʿ'riḍūna
Hausa Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne.
Verse 4
وَٱلَّذِينَ هُمْ لِلزَّكَوٰةِ فَـٰعِلُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum lilzzakati fāʿilūna
Hausa Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne.
Verse 5
وَٱلَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَـٰفِظُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum lifurūjihim ḥāfiẓūna
Hausa Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne.
Verse 6
إِلَّا عَلَىٰٓ أَزْوَٰجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَـٰنُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ
Transliteration illā ʿalā azwājihim aw mā malakat aymānuhum fa-innahum ghayru malūmīna
Hausa Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne.
Verse 7
فَمَنِ ٱبْتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْعَادُونَ
Transliteration famani ib'taghā warāa dhālika fa-ulāika humu l-ʿādūna
Hausa Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi.
Verse 8
وَٱلَّذِينَ هُمْ لِأَمَـٰنَـٰتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَٰعُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum li-amānātihim waʿahdihim rāʿūna
Hausa Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
Verse 9
وَٱلَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَوَٰتِهِمْ يُحَافِظُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum ʿalā ṣalawātihim yuḥāfiẓūna
Hausa Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa.
Verse 10
أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْوَٰرِثُونَ
Transliteration ulāika humu l-wārithūna
Hausa Waɗannan, sũ ne magãda.
Verse 11
ٱلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلْفِرْدَوْسَ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ
Transliteration alladhīna yarithūna l-fir'dawsa hum fīhā khālidūna
Hausa Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne.
Verse 12
وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ مِن سُلَـٰلَةٍ مِّن طِينٍ
Transliteration walaqad khalaqnā l-insāna min sulālatin min ṭīnin
Hausa Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka.
Verse 13
ثُمَّ جَعَلْنَـٰهُ نُطْفَةً فِى قَرَارٍ مَّكِينٍ
Transliteration thumma jaʿalnāhu nuṭ'fatan fī qarārin makīnin
Hausa Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.
Verse 14
ثُمَّ خَلَقْنَا ٱلنُّطْفَةَ عَلَقَةً فَخَلَقْنَا ٱلْعَلَقَةَ مُضْغَةً فَخَلَقْنَا ٱلْمُضْغَةَ عِظَـٰمًا فَكَسَوْنَا ٱلْعِظَـٰمَ لَحْمًا ثُمَّ أَنشَأْنَـٰهُ خَلْقًا ءَاخَرَ ۚ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ أَحْسَنُ ٱلْخَـٰلِقِينَ
Transliteration thumma khalaqnā l-nuṭ'fata ʿalaqatan fakhalaqnā l-ʿalaqata muḍ'ghatan fakhalaqnā l-muḍ'ghata ʿiẓāman fakasawnā l-ʿiẓāma laḥman thumma anshanāhu khalqan ākhara fatabāraka l-lahu aḥsanu l-khāliqīna
Hausa Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyawun mãsu halittawa.
Verse 15
ثُمَّ إِنَّكُم بَعْدَ ذَٰلِكَ لَمَيِّتُونَ
Transliteration thumma innakum baʿda dhālika lamayyitūna
Hausa Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.
Verse 16
ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ تُبْعَثُونَ
Transliteration thumma innakum yawma l-qiyāmati tub'ʿathūna
Hausa Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar alkiyãma, za a iãyar da ku,
Verse 17
وَلَقَدْ خَلَقْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعَ طَرَآئِقَ وَمَا كُنَّا عَنِ ٱلْخَلْقِ غَـٰفِلِينَ
Transliteration walaqad khalaqnā fawqakum sabʿa ṭarāiqa wamā kunnā ʿani l-khalqi ghāfilīna
Hausa Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba.
Verse 18
وَأَنزَلْنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءًۢ بِقَدَرٍ فَأَسْكَنَّـٰهُ فِى ٱلْأَرْضِ ۖ وَإِنَّا عَلَىٰ ذَهَابٍۭ بِهِۦ لَقَـٰدِرُونَ
Transliteration wa-anzalnā mina l-samāi māan biqadarin fa-askannāhu fī l-arḍi wa-innā ʿalā dhahābin bihi laqādirūna
Hausa Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne.
Verse 19
فَأَنشَأْنَا لَكُم بِهِۦ جَنَّـٰتٍ مِّن نَّخِيلٍ وَأَعْنَـٰبٍ لَّكُمْ فِيهَا فَوَٰكِهُ كَثِيرَةٌ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ
Transliteration fa-anshanā lakum bihi jannātin min nakhīlin wa-aʿnābin lakum fīhā fawākihu kathīratun wamin'hā takulūna
Hausa Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci.
Verse 20
وَشَجَرَةً تَخْرُجُ مِن طُورِ سَيْنَآءَ تَنۢبُتُ بِٱلدُّهْنِ وَصِبْغٍ لِّلْـَٔاكِلِينَ
Transliteration washajaratan takhruju min ṭūri saynāa tanbutu bil-duh'ni waṣib'ghin lil'ākilīna
Hausa Da wata itãciya, tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ.
Verse 21
وَإِنَّ لَكُمْ فِى ٱلْأَنْعَـٰمِ لَعِبْرَةً ۖ نُّسْقِيكُم مِّمَّا فِى بُطُونِهَا وَلَكُمْ فِيهَا مَنَـٰفِعُ كَثِيرَةٌ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ
Transliteration wa-inna lakum fī l-anʿāmi laʿib'ratan nus'qīkum mimmā fī buṭūnihā walakum fīhā manāfiʿu kathīratun wamin'hā takulūna
Hausa Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ
Verse 22
وَعَلَيْهَا وَعَلَى ٱلْفُلْكِ تُحْمَلُونَ
Transliteration waʿalayhā waʿalā l-ful'ki tuḥ'malūna
Hausa Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku.
Verse 23
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِۦ فَقَالَ يَـٰقَوْمِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـٰهٍ غَيْرُهُۥٓ ۖ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Transliteration walaqad arsalnā nūḥan ilā qawmihi faqāla yāqawmi uʿ'budū l-laha mā lakum min ilāhin ghayruhu afalā tattaqūna
Hausa Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba?"
Verse 24
فَقَالَ ٱلْمَلَؤُا۟ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِن قَوْمِهِۦ مَا هَـٰذَآ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ يُرِيدُ أَن يَتَفَضَّلَ عَلَيْكُمْ وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ لَأَنزَلَ مَلَـٰٓئِكَةً مَّا سَمِعْنَا بِهَـٰذَا فِىٓ ءَابَآئِنَا ٱلْأَوَّلِينَ
Transliteration faqāla l-mala-u alladhīna kafarū min qawmihi mā hādhā illā basharun mith'lukum yurīdu an yatafaḍḍala ʿalaykum walaw shāa l-lahu la-anzala malāikatan mā samiʿ'nā bihādhā fī ābāinā l-awalīna
Hausa Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko."
Verse 25
إِنْ هُوَ إِلَّا رَجُلٌۢ بِهِۦ جِنَّةٌ فَتَرَبَّصُوا۟ بِهِۦ حَتَّىٰ حِينٍ
Transliteration in huwa illā rajulun bihi jinnatun fatarabbaṣū bihi ḥattā ḥīnin
Hausa "Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci."
Verse 26
قَالَ رَبِّ ٱنصُرْنِى بِمَا كَذَّبُونِ
Transliteration qāla rabbi unṣur'nī bimā kadhabūni
Hausa Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka taimakeni Saboda mutãnena sun ƙaryatã ni."
Verse 27
فَأَوْحَيْنَآ إِلَيْهِ أَنِ ٱصْنَعِ ٱلْفُلْكَ بِأَعْيُنِنَا وَوَحْيِنَا فَإِذَا جَآءَ أَمْرُنَا وَفَارَ ٱلتَّنُّورُ ۙ فَٱسْلُكْ فِيهَا مِن كُلٍّ زَوْجَيْنِ ٱثْنَيْنِ وَأَهْلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيْهِ ٱلْقَوْلُ مِنْهُمْ ۖ وَلَا تُخَـٰطِبْنِى فِى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓا۟ ۖ إِنَّهُم مُّغْرَقُونَ
Transliteration fa-awḥaynā ilayhi ani iṣ'naʿi l-ful'ka bi-aʿyuninā wawaḥyinā fa-idhā jāa amrunā wafāra l-tanūru fa-us'luk fīhā min kullin zawjayni ith'nayni wa-ahlaka illā man sabaqa ʿalayhi l-qawlu min'hum walā tukhāṭib'nī fī alladhīna ẓalamū innahum mugh'raqūna
Hausa Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idon Mu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne.
Verse 28
فَإِذَا ٱسْتَوَيْتَ أَنتَ وَمَن مَّعَكَ عَلَى ٱلْفُلْكِ فَقُلِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ٱلَّذِى نَجَّىٰنَا مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Transliteration fa-idhā is'tawayta anta waman maʿaka ʿalā l-ful'ki faquli l-ḥamdu lillahi alladhī najjānā mina l-qawmi l-ẓālimīna
Hausa "Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai."
Verse 29
وَقُل رَّبِّ أَنزِلْنِى مُنزَلًا مُّبَارَكًا وَأَنتَ خَيْرُ ٱلْمُنزِلِينَ
Transliteration waqul rabbi anzil'nī munzalan mubārakan wa-anta khayru l-munzilīna
Hausa "Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.'"
Verse 30
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ وَإِن كُنَّا لَمُبْتَلِينَ
Transliteration inna fī dhālika laāyātin wa-in kunnā lamub'talīna
Hausa Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙiƙa' Mãsu jarrabãwa.
Verse 31
ثُمَّ أَنشَأْنَا مِنۢ بَعْدِهِمْ قَرْنًا ءَاخَرِينَ
Transliteration thumma anshanā min baʿdihim qarnan ākharīna
Hausa Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu.
Verse 32
فَأَرْسَلْنَا فِيهِمْ رَسُولًا مِّنْهُمْ أَنِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـٰهٍ غَيْرُهُۥٓ ۖ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Transliteration fa-arsalnā fīhim rasūlan min'hum ani uʿ'budū l-laha mā lakum min ilāhin ghayruhu afalā tattaqūna
Hausa Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba?"
Verse 33
وَقَالَ ٱلْمَلَأُ مِن قَوْمِهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَكَذَّبُوا۟ بِلِقَآءِ ٱلْـَٔاخِرَةِ وَأَتْرَفْنَـٰهُمْ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا مَا هَـٰذَآ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ يَأْكُلُ مِمَّا تَأْكُلُونَ مِنْهُ وَيَشْرَبُ مِمَّا تَشْرَبُونَ
Transliteration waqāla l-mala-u min qawmihi alladhīna kafarū wakadhabū biliqāi l-ākhirati wa-atrafnāhum fī l-ḥayati l-dun'yā mā hādhā illā basharun mith'lukum yakulu mimmā takulūna min'hu wayashrabu mimmā tashrabūna
Hausa Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã."
Verse 34
وَلَئِنْ أَطَعْتُم بَشَرًا مِّثْلَكُمْ إِنَّكُمْ إِذًا لَّخَـٰسِرُونَ
Transliteration wala-in aṭaʿtum basharan mith'lakum innakum idhan lakhāsirūna
Hausa "Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne."
Verse 35
أَيَعِدُكُمْ أَنَّكُمْ إِذَا مِتُّمْ وَكُنتُمْ تُرَابًا وَعِظَـٰمًا أَنَّكُم مُّخْرَجُونَ
Transliteration ayaʿidukum annakum idhā mittum wakuntum turāban waʿiẓāman annakum mukh'rajūna
Hausa "Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da kasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne?"
Verse 36
۞ هَيْهَاتَ هَيْهَاتَ لِمَا تُوعَدُونَ
Transliteration hayhāta hayhāta limā tūʿadūna
Hausa "Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi."
Verse 37
إِنْ هِىَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنْيَا نَمُوتُ وَنَحْيَا وَمَا نَحْنُ بِمَبْعُوثِينَ
Transliteration in hiya illā ḥayātunā l-dun'yā namūtu wanaḥyā wamā naḥnu bimabʿūthīna
Hausa "Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
Verse 38
إِنْ هُوَ إِلَّا رَجُلٌ ٱفْتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا وَمَا نَحْنُ لَهُۥ بِمُؤْمِنِينَ
Transliteration in huwa illā rajulun if'tarā ʿalā l-lahi kadhiban wamā naḥnu lahu bimu'minīna
Hausa "Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba."
Verse 39
قَالَ رَبِّ ٱنصُرْنِى بِمَا كَذَّبُونِ
Transliteration qāla rabbi unṣur'nī bimā kadhabūni
Hausa Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni."
Verse 40
قَالَ عَمَّا قَلِيلٍ لَّيُصْبِحُنَّ نَـٰدِمِينَ
Transliteration qāla ʿammā qalīlin layuṣ'biḥunna nādimīna
Hausa Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma."
Verse 41
فَأَخَذَتْهُمُ ٱلصَّيْحَةُ بِٱلْحَقِّ فَجَعَلْنَـٰهُمْ غُثَآءً ۚ فَبُعْدًا لِّلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Transliteration fa-akhadhathumu l-ṣayḥatu bil-ḥaqi fajaʿalnāhum ghuthāan fabuʿ'dan lil'qawmi l-ẓālimīna
Hausa Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai!
Verse 42
ثُمَّ أَنشَأْنَا مِنۢ بَعْدِهِمْ قُرُونًا ءَاخَرِينَ
Transliteration thumma anshanā min baʿdihim qurūnan ākharīna
Hausa Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu.
Verse 43
مَا تَسْبِقُ مِنْ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسْتَـْٔخِرُونَ
Transliteration mā tasbiqu min ummatin ajalahā wamā yastakhirūna
Hausa Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
Verse 44
ثُمَّ أَرْسَلْنَا رُسُلَنَا تَتْرَا ۖ كُلَّ مَا جَآءَ أُمَّةً رَّسُولُهَا كَذَّبُوهُ ۚ فَأَتْبَعْنَا بَعْضَهُم بَعْضًا وَجَعَلْنَـٰهُمْ أَحَادِيثَ ۚ فَبُعْدًا لِّقَوْمٍ لَّا يُؤْمِنُونَ
Transliteration thumma arsalnā rusulanā tatrā kulla mā jāa ummatan rasūluhā kadhabūhu fa-atbaʿnā baʿḍahum baʿḍan wajaʿalnāhum aḥādītha fabuʿ'dan liqawmin lā yu'minūna
Hausa Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni!
Verse 45
ثُمَّ أَرْسَلْنَا مُوسَىٰ وَأَخَاهُ هَـٰرُونَ بِـَٔايَـٰتِنَا وَسُلْطَـٰنٍ مُّبِينٍ
Transliteration thumma arsalnā mūsā wa-akhāhu hārūna biāyātinā wasul'ṭānin mubīnin
Hausa Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyin Mu da, dalĩli bayyananne.
Verse 46
إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِۦ فَٱسْتَكْبَرُوا۟ وَكَانُوا۟ قَوْمًا عَالِينَ
Transliteration ilā fir'ʿawna wamala-ihi fa-is'takbarū wakānū qawman ʿālīna
Hausa Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya.
Verse 47
فَقَالُوٓا۟ أَنُؤْمِنُ لِبَشَرَيْنِ مِثْلِنَا وَقَوْمُهُمَا لَنَا عَـٰبِدُونَ
Transliteration faqālū anu'minu libasharayni mith'linā waqawmuhumā lanā ʿābidūna
Hausa Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne."
Verse 48
فَكَذَّبُوهُمَا فَكَانُوا۟ مِنَ ٱلْمُهْلَكِينَ
Transliteration fakadhabūhumā fakānū mina l-muh'lakīna
Hausa Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku.
Verse 49
وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْكِتَـٰبَ لَعَلَّهُمْ يَهْتَدُونَ
Transliteration walaqad ātaynā mūsā l-kitāba laʿallahum yahtadūna
Hausa Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu zã su shiryu.
Verse 50
وَجَعَلْنَا ٱبْنَ مَرْيَمَ وَأُمَّهُۥٓ ءَايَةً وَءَاوَيْنَـٰهُمَآ إِلَىٰ رَبْوَةٍ ذَاتِ قَرَارٍ وَمَعِينٍ
Transliteration wajaʿalnā ib'na maryama wa-ummahu āyatan waāwaynāhumā ilā rabwatin dhāti qarārin wamaʿīnin
Hausa Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari.
Verse 51
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلرُّسُلُ كُلُوا۟ مِنَ ٱلطَّيِّبَـٰتِ وَٱعْمَلُوا۟ صَـٰلِحًا ۖ إِنِّى بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ
Transliteration yāayyuhā l-rusulu kulū mina l-ṭayibāti wa-iʿ'malū ṣāliḥan innī bimā taʿmalūna ʿalīmun
Hausa Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
Verse 52
وَإِنَّ هَـٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمْ أُمَّةً وَٰحِدَةً وَأَنَا۠ رَبُّكُمْ فَٱتَّقُونِ
Transliteration wa-inna hādhihi ummatukum ummatan wāḥidatan wa-anā rabbukum fa-ittaqūni
Hausa Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa.
Verse 53
فَتَقَطَّعُوٓا۟ أَمْرَهُم بَيْنَهُمْ زُبُرًا ۖ كُلُّ حِزْبٍۭ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ
Transliteration fataqaṭṭaʿū amrahum baynahum zuburan kullu ḥiz'bin bimā ladayhim fariḥūna
Hausa Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.
Verse 54
فَذَرْهُمْ فِى غَمْرَتِهِمْ حَتَّىٰ حِينٍ
Transliteration fadharhum fī ghamratihim ḥattā ḥīnin
Hausa To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci.
Verse 55
أَيَحْسَبُونَ أَنَّمَا نُمِدُّهُم بِهِۦ مِن مَّالٍ وَبَنِينَ
Transliteration ayaḥsabūna annamā numidduhum bihi min mālin wabanīna
Hausa Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya,
Verse 56
نُسَارِعُ لَهُمْ فِى ٱلْخَيْرَٰتِ ۚ بَل لَّا يَشْعُرُونَ
Transliteration nusāriʿu lahum fī l-khayrāti bal lā yashʿurūna
Hausa Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri?
Verse 57
إِنَّ ٱلَّذِينَ هُم مِّنْ خَشْيَةِ رَبِّهِم مُّشْفِقُونَ
Transliteration inna alladhīna hum min khashyati rabbihim mush'fiqūna
Hausa Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu,
Verse 58
وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَـٰتِ رَبِّهِمْ يُؤْمِنُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum biāyāti rabbihim yu'minūna
Hausa Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni,
Verse 59
وَٱلَّذِينَ هُم بِرَبِّهِمْ لَا يُشْرِكُونَ
Transliteration wa-alladhīna hum birabbihim lā yush'rikūna
Hausa Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki,
Verse 60
وَٱلَّذِينَ يُؤْتُونَ مَآ ءَاتَوا۟ وَّقُلُوبُهُمْ وَجِلَةٌ أَنَّهُمْ إِلَىٰ رَبِّهِمْ رَٰجِعُونَ
Transliteration wa-alladhīna yu'tūna mā ātaw waqulūbuhum wajilatun annahum ilā rabbihim rājiʿūna
Hausa Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu,
Verse 61
أُو۟لَـٰٓئِكَ يُسَـٰرِعُونَ فِى ٱلْخَيْرَٰتِ وَهُمْ لَهَا سَـٰبِقُونَ
Transliteration ulāika yusāriʿūna fī l-khayrāti wahum lahā sābiqūna
Hausa Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri).
Verse 62
وَلَا نُكَلِّفُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا ۖ وَلَدَيْنَا كِتَـٰبٌ يَنطِقُ بِٱلْحَقِّ ۚ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Transliteration walā nukallifu nafsan illā wus'ʿahā waladaynā kitābun yanṭiqu bil-ḥaqi wahum lā yuẓ'lamūna
Hausa Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su.
Verse 63
بَلْ قُلُوبُهُمْ فِى غَمْرَةٍ مِّنْ هَـٰذَا وَلَهُمْ أَعْمَـٰلٌ مِّن دُونِ ذَٰلِكَ هُمْ لَهَا عَـٰمِلُونَ
Transliteration bal qulūbuhum fī ghamratin min hādhā walahum aʿmālun min dūni dhālika hum lahā ʿāmilūna
Hausa Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su, mãsu aikatãwa ne.
Verse 64
حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذْنَا مُتْرَفِيهِم بِٱلْعَذَابِ إِذَا هُمْ يَجْـَٔرُونَ
Transliteration ḥattā idhā akhadhnā mut'rafīhim bil-ʿadhābi idhā hum yajarūna
Hausa Har idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa.
Verse 65
لَا تَجْـَٔرُوا۟ ٱلْيَوْمَ ۖ إِنَّكُم مِّنَّا لَا تُنصَرُونَ
Transliteration lā tajarū l-yawma innakum minnā lā tunṣarūna
Hausa Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku.
Verse 66
قَدْ كَانَتْ ءَايَـٰتِى تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فَكُنتُمْ عَلَىٰٓ أَعْقَـٰبِكُمْ تَنكِصُونَ
Transliteration qad kānat āyātī tut'lā ʿalaykum fakuntum ʿalā aʿqābikum tankiṣūna
Hausa Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya.
Verse 67
مُسْتَكْبِرِينَ بِهِۦ سَـٰمِرًا تَهْجُرُونَ
Transliteration mus'takbirīna bihi sāmiran tahjurūna
Hausa Kunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha.
Verse 68
أَفَلَمْ يَدَّبَّرُوا۟ ٱلْقَوْلَ أَمْ جَآءَهُم مَّا لَمْ يَأْتِ ءَابَآءَهُمُ ٱلْأَوَّلِينَ
Transliteration afalam yaddabbarū l-qawla am jāahum mā lam yati ābāahumu l-awalīna
Hausa Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu?
Verse 69
أَمْ لَمْ يَعْرِفُوا۟ رَسُولَهُمْ فَهُمْ لَهُۥ مُنكِرُونَ
Transliteration am lam yaʿrifū rasūlahum fahum lahu munkirūna
Hausa Kõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi?
Verse 70
أَمْ يَقُولُونَ بِهِۦ جِنَّةٌۢ ۚ بَلْ جَآءَهُم بِٱلْحَقِّ وَأَكْثَرُهُمْ لِلْحَقِّ كَـٰرِهُونَ
Transliteration am yaqūlūna bihi jinnatun bal jāahum bil-ḥaqi wa-aktharuhum lil'ḥaqqi kārihūna
Hausa Kõ sunã cẽwa, "Akwai hauka gare shi?" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne.
Verse 71
وَلَوِ ٱتَّبَعَ ٱلْحَقُّ أَهْوَآءَهُمْ لَفَسَدَتِ ٱلسَّمَـٰوَٰتُ وَٱلْأَرْضُ وَمَن فِيهِنَّ ۚ بَلْ أَتَيْنَـٰهُم بِذِكْرِهِمْ فَهُمْ عَن ذِكْرِهِم مُّعْرِضُونَ
Transliteration walawi ittabaʿa l-ḥaqu ahwāahum lafasadati l-samāwātu wal-arḍu waman fīhinna bal ataynāhum bidhik'rihim fahum ʿan dhik'rihim muʿ'riḍūna
Hausa Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa.
Verse 72
أَمْ تَسْـَٔلُهُمْ خَرْجًا فَخَرَاجُ رَبِّكَ خَيْرٌ ۖ وَهُوَ خَيْرُ ٱلرَّٰزِقِينَ
Transliteration am tasaluhum kharjan fakharāju rabbika khayrun wahuwa khayru l-rāziqīna
Hausa Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa.
Verse 73
وَإِنَّكَ لَتَدْعُوهُمْ إِلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ
Transliteration wa-innaka latadʿūhum ilā ṣirāṭin mus'taqīmin
Hausa Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya.
Verse 74
وَإِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ عَنِ ٱلصِّرَٰطِ لَنَـٰكِبُونَ
Transliteration wa-inna alladhīna lā yu'minūna bil-ākhirati ʿani l-ṣirāṭi lanākibūna
Hausa Kuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne.
Verse 75
۞ وَلَوْ رَحِمْنَـٰهُمْ وَكَشَفْنَا مَا بِهِم مِّن ضُرٍّ لَّلَجُّوا۟ فِى طُغْيَـٰنِهِمْ يَعْمَهُونَ
Transliteration walaw raḥim'nāhum wakashafnā mā bihim min ḍurrin lalajjū fī ṭugh'yānihim yaʿmahūna
Hausa Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa.
Verse 76
وَلَقَدْ أَخَذْنَـٰهُم بِٱلْعَذَابِ فَمَا ٱسْتَكَانُوا۟ لِرَبِّهِمْ وَمَا يَتَضَرَّعُونَ
Transliteration walaqad akhadhnāhum bil-ʿadhābi famā is'takānū lirabbihim wamā yataḍarraʿūna
Hausa Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u.
Verse 77
حَتَّىٰٓ إِذَا فَتَحْنَا عَلَيْهِم بَابًا ذَا عَذَابٍ شَدِيدٍ إِذَا هُمْ فِيهِ مُبْلِسُونَ
Transliteration ḥattā idhā fataḥnā ʿalayhim bāban dhā ʿadhābin shadīdin idhā hum fīhi mub'lisūna
Hausa Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi.
Verse 78
وَهُوَ ٱلَّذِىٓ أَنشَأَ لَكُمُ ٱلسَّمْعَ وَٱلْأَبْصَـٰرَ وَٱلْأَفْـِٔدَةَ ۚ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ
Transliteration wahuwa alladhī ansha-a lakumu l-samʿa wal-abṣāra wal-afidata qalīlan mā tashkurūna
Hausa Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa.
Verse 79
وَهُوَ ٱلَّذِى ذَرَأَكُمْ فِى ٱلْأَرْضِ وَإِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
Transliteration wahuwa alladhī dhara-akum fī l-arḍi wa-ilayhi tuḥ'sharūna
Hausa Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku.
Verse 80
وَهُوَ ٱلَّذِى يُحْىِۦ وَيُمِيتُ وَلَهُ ٱخْتِلَـٰفُ ٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Transliteration wahuwa alladhī yuḥ'yī wayumītu walahu ikh'tilāfu al-layli wal-nahāri afalā taʿqilūna
Hausa Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba?
Verse 81
بَلْ قَالُوا۟ مِثْلَ مَا قَالَ ٱلْأَوَّلُونَ
Transliteration bal qālū mith'la mā qāla l-awalūna
Hausa Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa.
Verse 82
قَالُوٓا۟ أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَـٰمًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ
Transliteration qālū a-idhā mit'nā wakunnā turāban waʿiẓāman a-innā lamabʿūthūna
Hausa Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lale ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne?
Verse 83
لَقَدْ وُعِدْنَا نَحْنُ وَءَابَآؤُنَا هَـٰذَا مِن قَبْلُ إِنْ هَـٰذَآ إِلَّآ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ
Transliteration laqad wuʿid'nā naḥnu waābāunā hādhā min qablu in hādhā illā asāṭīru l-awalīna
Hausa "Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko."
Verse 84
قُل لِّمَنِ ٱلْأَرْضُ وَمَن فِيهَآ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Transliteration qul limani l-arḍu waman fīhā in kuntum taʿlamūna
Hausa Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani?"
Verse 85
سَيَقُولُونَ لِلَّهِ ۚ قُلْ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Transliteration sayaqūlūna lillahi qul afalā tadhakkarūna
Hausa Zã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba?"
Verse 86
قُلْ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ ٱلسَّبْعِ وَرَبُّ ٱلْعَرْشِ ٱلْعَظِيمِ
Transliteration qul man rabbu l-samāwāti l-sabʿi warabbu l-ʿarshi l-ʿaẓīmi
Hausa Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma?"
Verse 87
سَيَقُولُونَ لِلَّهِ ۚ قُلْ أَفَلَا تَتَّقُونَ
Transliteration sayaqūlūna lillahi qul afalā tattaqūna
Hausa Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba?"
Verse 88
قُلْ مَنۢ بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَىْءٍ وَهُوَ يُجِيرُ وَلَا يُجَارُ عَلَيْهِ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Transliteration qul man biyadihi malakūtu kulli shayin wahuwa yujīru walā yujāru ʿalayhi in kuntum taʿlamūna
Hausa Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani?"
Verse 89
سَيَقُولُونَ لِلَّهِ ۚ قُلْ فَأَنَّىٰ تُسْحَرُونَ
Transliteration sayaqūlūna lillahi qul fa-annā tus'ḥarūna
Hausa Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku?"
Verse 90
بَلْ أَتَيْنَـٰهُم بِٱلْحَقِّ وَإِنَّهُمْ لَكَـٰذِبُونَ
Transliteration bal ataynāhum bil-ḥaqi wa-innahum lakādhibūna
Hausa Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
Verse 91
مَا ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ مِن وَلَدٍ وَمَا كَانَ مَعَهُۥ مِنْ إِلَـٰهٍ ۚ إِذًا لَّذَهَبَ كُلُّ إِلَـٰهٍۭ بِمَا خَلَقَ وَلَعَلَا بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ ۚ سُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
Transliteration mā ittakhadha l-lahu min waladin wamā kāna maʿahu min ilāhin idhan ladhahaba kullu ilāhin bimā khalaqa walaʿalā baʿḍuhum ʿalā baʿḍin sub'ḥāna l-lahi ʿammā yaṣifūna
Hausa Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa.
Verse 92
عَـٰلِمِ ٱلْغَيْبِ وَٱلشَّهَـٰدَةِ فَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Transliteration ʿālimi l-ghaybi wal-shahādati fataʿālā ʿammā yush'rikūna
Hausa Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.
Verse 93
قُل رَّبِّ إِمَّا تُرِيَنِّى مَا يُوعَدُونَ
Transliteration qul rabbi immā turiyannī mā yūʿadūna
Hausa Ka ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi."
Verse 94
رَبِّ فَلَا تَجْعَلْنِى فِى ٱلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Transliteration rabbi falā tajʿalnī fī l-qawmi l-ẓālimīna
Hausa "Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai."
Verse 95
وَإِنَّا عَلَىٰٓ أَن نُّرِيَكَ مَا نَعِدُهُمْ لَقَـٰدِرُونَ
Transliteration wa-innā ʿalā an nuriyaka mā naʿiduhum laqādirūna
Hausa Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi.
Verse 96
ٱدْفَعْ بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ ٱلسَّيِّئَةَ ۚ نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَصِفُونَ
Transliteration id'faʿ bi-allatī hiya aḥsanu l-sayi-ata naḥnu aʿlamu bimā yaṣifūna
Hausa Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ ne Mafi sani game da abin da suke siffantãwa.
Verse 97
وَقُل رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ هَمَزَٰتِ ٱلشَّيَـٰطِينِ
Transliteration waqul rabbi aʿūdhu bika min hamazāti l-shayāṭīni
Hausa Ka ce: "Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu."
Verse 98
وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن يَحْضُرُونِ
Transliteration wa-aʿūdhu bika rabbi an yaḥḍurūni
Hausa "Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni, "
Verse 99
حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَهُمُ ٱلْمَوْتُ قَالَ رَبِّ ٱرْجِعُونِ
Transliteration ḥattā idhā jāa aḥadahumu l-mawtu qāla rabbi ir'jiʿūni
Hausa Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: "Yã Ubangijina, Ku mayar da ni (dũniya)."
Verse 100
لَعَلِّىٓ أَعْمَلُ صَـٰلِحًا فِيمَا تَرَكْتُ ۚ كَلَّآ ۚ إِنَّهَا كَلِمَةٌ هُوَ قَآئِلُهَا ۖ وَمِن وَرَآئِهِم بَرْزَخٌ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Transliteration laʿallī aʿmalu ṣāliḥan fīmā taraktu kallā innahā kalimatun huwa qāiluhā wamin warāihim barzakhun ilā yawmi yub'ʿathūna
Hausa "Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su.
Verse 101
فَإِذَا نُفِخَ فِى ٱلصُّورِ فَلَآ أَنسَابَ بَيْنَهُمْ يَوْمَئِذٍ وَلَا يَتَسَآءَلُونَ
Transliteration fa-idhā nufikha fī l-ṣūri falā ansāba baynahum yawma-idhin walā yatasāalūna
Hausa Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba.
Verse 102
فَمَن ثَقُلَتْ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ
Transliteration faman thaqulat mawāzīnuhu fa-ulāika humu l-muf'liḥūna
Hausa To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
Verse 103
وَمَنْ خَفَّتْ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ فِى جَهَنَّمَ خَـٰلِدُونَ
Transliteration waman khaffat mawāzīnuhu fa-ulāika alladhīna khasirū anfusahum fī jahannama khālidūna
Hausa Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama.
Verse 104
تَلْفَحُ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ وَهُمْ فِيهَا كَـٰلِحُونَ
Transliteration talfaḥu wujūhahumu l-nāru wahum fīhā kāliḥūna
Hausa Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne.
Verse 105
أَلَمْ تَكُنْ ءَايَـٰتِى تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فَكُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
Transliteration alam takun āyātī tut'lā ʿalaykum fakuntum bihā tukadhibūna
Hausa "Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa?"
Verse 106
قَالُوا۟ رَبَّنَا غَلَبَتْ عَلَيْنَا شِقْوَتُنَا وَكُنَّا قَوْمًا ضَآلِّينَ
Transliteration qālū rabbanā ghalabat ʿalaynā shiq'watunā wakunnā qawman ḍāllīna
Hausa Suka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwace ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu."
Verse 107
رَبَّنَآ أَخْرِجْنَا مِنْهَا فَإِنْ عُدْنَا فَإِنَّا ظَـٰلِمُونَ
Transliteration rabbanā akhrij'nā min'hā fa-in ʿud'nā fa-innā ẓālimūna
Hausa "Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci."
Verse 108
قَالَ ٱخْسَـُٔوا۟ فِيهَا وَلَا تُكَلِّمُونِ
Transliteration qāla ikh'saū fīhā walā tukallimūni
Hausa Ya ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana."
Verse 109
إِنَّهُۥ كَانَ فَرِيقٌ مِّنْ عِبَادِى يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱغْفِرْ لَنَا وَٱرْحَمْنَا وَأَنتَ خَيْرُ ٱلرَّٰحِمِينَ
Transliteration innahu kāna farīqun min ʿibādī yaqūlūna rabbanā āmannā fa-igh'fir lanā wa-ir'ḥamnā wa-anta khayru l-rāḥimīna
Hausa Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi."
Verse 110
فَٱتَّخَذْتُمُوهُمْ سِخْرِيًّا حَتَّىٰٓ أَنسَوْكُمْ ذِكْرِى وَكُنتُم مِّنْهُمْ تَضْحَكُونَ
Transliteration fa-ittakhadhtumūhum sikh'riyyan ḥattā ansawkum dhik'rī wakuntum min'hum taḍḥakūna
Hausa Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõ Na kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya.
Verse 111
إِنِّى جَزَيْتُهُمُ ٱلْيَوْمَ بِمَا صَبَرُوٓا۟ أَنَّهُمْ هُمُ ٱلْفَآئِزُونَ
Transliteration innī jazaytuhumu l-yawma bimā ṣabarū annahum humu l-fāizūna
Hausa Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
Verse 112
قَـٰلَ كَمْ لَبِثْتُمْ فِى ٱلْأَرْضِ عَدَدَ سِنِينَ
Transliteration qāla kam labith'tum fī l-arḍi ʿadada sinīna
Hausa Ya ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru?"
Verse 113
قَالُوا۟ لَبِثْنَا يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ فَسْـَٔلِ ٱلْعَآدِّينَ
Transliteration qālū labith'nā yawman aw baʿḍa yawmin fasali l-ʿādīna
Hausa Suka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa."
Verse 114
قَـٰلَ إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا قَلِيلًا ۖ لَّوْ أَنَّكُمْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Transliteration qāla in labith'tum illā qalīlan law annakum kuntum taʿlamūna
Hausa Ya ce: "Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani."
Verse 115
أَفَحَسِبْتُمْ أَنَّمَا خَلَقْنَـٰكُمْ عَبَثًا وَأَنَّكُمْ إِلَيْنَا لَا تُرْجَعُونَ
Transliteration afaḥasib'tum annamā khalaqnākum ʿabathan wa-annakum ilaynā lā tur'jaʿūna
Hausa "Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba?"
Verse 116
فَتَعَـٰلَى ٱللَّهُ ٱلْمَلِكُ ٱلْحَقُّ ۖ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلْعَرْشِ ٱلْكَرِيمِ
Transliteration fataʿālā l-lahu l-maliku l-ḥaqu lā ilāha illā huwa rabbu l-ʿarshi l-karīmi
Hausa Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja.
Verse 117
وَمَن يَدْعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ لَا بُرْهَـٰنَ لَهُۥ بِهِۦ فَإِنَّمَا حِسَابُهُۥ عِندَ رَبِّهِۦٓ ۚ إِنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلْكَـٰفِرُونَ
Transliteration waman yadʿu maʿa l-lahi ilāhan ākhara lā bur'hāna lahu bihi fa-innamā ḥisābuhu ʿinda rabbihi innahu lā yuf'liḥu l-kāfirūna
Hausa Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara.
Verse 118
وَقُل رَّبِّ ٱغْفِرْ وَٱرْحَمْ وَأَنتَ خَيْرُ ٱلرَّٰحِمِينَ
Transliteration waqul rabbi igh'fir wa-ir'ḥam wa-anta khayru l-rāḥimīna
Hausa Kuma ka ce: "Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama."
Read Surah Al-Mu'minun in another language
- English (word by word)
- Albanian
- Amazigh
- Amharic
- Assamese
- Azerbaijani
- Bambara
- Bangla
- Bosnian
- Bulgarian
- Chechen
- Chinese
- Czech
- Dari
- Dhivehi
- Dutch
- Finnish
- French
- German
- Gujarati
- Hebrew
- Hindi
- Indonesian
- Italian
- Japanese
- Kannada
- Kazakh
- Khmer
- Kinyarwanda
- Korean
- Kurdish
- Luganda
- Malay
- Malayalam
- Maranao
- Marathi
- Nepali
- Norwegian
- Oromo
- Pashto
- Persian
- Polish
- Portuguese
- Romanian
- Russian
- Sindhi
- Sinhala
- Somali
- Spanish
- Swahili
- Swedish
- Tagalog
- Tajik
- Tamil
- Tatar
- Telugu
- Thai
- Turkish
- Ukrainian
- Urdu
- Uyghur
- Uzbek
- Vietnamese
- Yao
- Yoruba
All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.
Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.