MyDugsiStart learning

Surah Al-Hadid in Hausa: translation and audio

Surah 57 · الحديد · The Iron · 29 verses

Surah Al-Hadid verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Hadid word by word in English.

Verse 1

سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ

Transliteration sabbaḥa lillahi mā fī l-samāwāti wal-arḍi wahuwa l-ʿazīzu l-ḥakīmu

Hausa Abin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.

Verse 2

لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ يُحْىِۦ وَيُمِيتُ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Transliteration lahu mul'ku l-samāwāti wal-arḍi yuḥ'yī wayumītu wahuwa ʿalā kulli shayin qadīrun

Hausa Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme.

Verse 3

هُوَ ٱلْأَوَّلُ وَٱلْـَٔاخِرُ وَٱلظَّـٰهِرُ وَٱلْبَاطِنُ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ

Transliteration huwa l-awalu wal-ākhiru wal-ẓāhiru wal-bāṭinu wahuwa bikulli shayin ʿalīmun

Hausa Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme.

Verse 4

هُوَ ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ فِى سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ ٱسْتَوَىٰ عَلَى ٱلْعَرْشِ ۚ يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا ۖ وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ ۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

Transliteration huwa alladhī khalaqa l-samāwāti wal-arḍa fī sittati ayyāmin thumma is'tawā ʿalā l-ʿarshi yaʿlamu mā yaliju fī l-arḍi wamā yakhruju min'hā wamā yanzilu mina l-samāi wamā yaʿruju fīhā wahuwa maʿakum ayna mā kuntum wal-lahu bimā taʿmalūna baṣīrun

Hausa Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi, Yanã sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta, kuma Shĩ yanã tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.

Verse 5

لَّهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرْجَعُ ٱلْأُمُورُ

Transliteration lahu mul'ku l-samāwāti wal-arḍi wa-ilā l-lahi tur'jaʿu l-umūru

Hausa Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma zuwa gare Shĩ (Allah) kawai ake mayar da al'amura.

Verse 6

يُولِجُ ٱلَّيْلَ فِى ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِى ٱلَّيْلِ ۚ وَهُوَ عَلِيمٌۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Transliteration yūliju al-layla fī l-nahāri wayūliju l-nahāra fī al-layli wahuwa ʿalīmun bidhāti l-ṣudūri

Hausa Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãza.

Verse 7

ءَامِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَأَنفِقُوا۟ مِمَّا جَعَلَكُم مُّسْتَخْلَفِينَ فِيهِ ۖ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مِنكُمْ وَأَنفَقُوا۟ لَهُمْ أَجْرٌ كَبِيرٌ

Transliteration āminū bil-lahi warasūlihi wa-anfiqū mimmā jaʿalakum mus'takhlafīna fīhi fa-alladhīna āmanū minkum wa-anfaqū lahum ajrun kabīrun

Hausa Ku yi ĩmãni da Allah da Manzon Sa, kuma ku ciyar daga abin da Allah Ya wakilta ku a cikinsa (na dũkiya). To, waɗannan da suka yi ĩmãni daga cikinku, kuma suka ciyar, sunã da wani sakamako mai girma.

Verse 8

وَمَا لَكُمْ لَا تُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ ۙ وَٱلرَّسُولُ يَدْعُوكُمْ لِتُؤْمِنُوا۟ بِرَبِّكُمْ وَقَدْ أَخَذَ مِيثَـٰقَكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ

Transliteration wamā lakum lā tu'minūna bil-lahi wal-rasūlu yadʿūkum litu'minū birabbikum waqad akhadha mīthāqakum in kuntum mu'minīna

Hausa kuma me ya same ku, bã zã ku yi ĩmãni ba da Allah, alhãli kuwa manzon Sa na kiran ku dõmin ku yi ĩmãni da Ubangijinku, kuma lalle Allah Ya karɓi alkawarinku (cẽwa zã ku bauta Masa)? (Ku bauta Masa) idan kun kasance mãsu ĩmãni.

Verse 9

هُوَ ٱلَّذِى يُنَزِّلُ عَلَىٰ عَبْدِهِۦٓ ءَايَـٰتٍۭ بَيِّنَـٰتٍ لِّيُخْرِجَكُم مِّنَ ٱلظُّلُمَـٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ ۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ بِكُمْ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ

Transliteration huwa alladhī yunazzilu ʿalā ʿabdihi āyātin bayyinātin liyukh'rijakum mina l-ẓulumāti ilā l-nūri wa-inna l-laha bikum laraūfun raḥīmun

Hausa Shĩ ne wanda ke sassaukar da ãyõyi bayyanannu ga Bãwan Sa, dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai tausayi ne gare ku, Mai jin ƙai.

Verse 10

وَمَا لَكُمْ أَلَّا تُنفِقُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلِلَّهِ مِيرَٰثُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ لَا يَسْتَوِى مِنكُم مَّنْ أَنفَقَ مِن قَبْلِ ٱلْفَتْحِ وَقَـٰتَلَ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَعْظَمُ دَرَجَةً مِّنَ ٱلَّذِينَ أَنفَقُوا۟ مِنۢ بَعْدُ وَقَـٰتَلُوا۟ ۚ وَكُلًّا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلْحُسْنَىٰ ۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ

Transliteration wamā lakum allā tunfiqū fī sabīli l-lahi walillahi mīrāthu l-samāwāti wal-arḍi lā yastawī minkum man anfaqa min qabli l-fatḥi waqātala ulāika aʿẓamu darajatan mina alladhīna anfaqū min baʿdu waqātalū wakullan waʿada l-lahu l-ḥus'nā wal-lahu bimā taʿmalūna khabīrun

Hausa Kuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafĩfĩta girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.

Verse 11

مَّن ذَا ٱلَّذِى يُقْرِضُ ٱللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا فَيُضَـٰعِفَهُۥ لَهُۥ وَلَهُۥٓ أَجْرٌ كَرِيمٌ

Transliteration man dhā alladhī yuq'riḍu l-laha qarḍan ḥasanan fayuḍāʿifahu lahu walahu ajrun karīmun

Hausa Wãne ne wanda zai ranta wa Allah rance mai kyau dõmin Allah Ya ninka masa shi (a dũniya) kuma Yanã da wani sakamako na karimci (a Lãhira)?

Verse 12

يَوْمَ تَرَى ٱلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَـٰتِ يَسْعَىٰ نُورُهُم بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَـٰنِهِم بُشْرَىٰكُمُ ٱلْيَوْمَ جَنَّـٰتٌ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ

Transliteration yawma tarā l-mu'minīna wal-mu'mināti yasʿā nūruhum bayna aydīhim wabi-aymānihim bush'rākumu l-yawma jannātun tajrī min taḥtihā l-anhāru khālidīna fīhā dhālika huwa l-fawzu l-ʿaẓīmu

Hausa Rãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo mai girma.

Verse 13

يَوْمَ يَقُولُ ٱلْمُنَـٰفِقُونَ وَٱلْمُنَـٰفِقَـٰتُ لِلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱنظُرُونَا نَقْتَبِسْ مِن نُّورِكُمْ قِيلَ ٱرْجِعُوا۟ وَرَآءَكُمْ فَٱلْتَمِسُوا۟ نُورًا فَضُرِبَ بَيْنَهُم بِسُورٍ لَّهُۥ بَابٌۢ بَاطِنُهُۥ فِيهِ ٱلرَّحْمَةُ وَظَـٰهِرُهُۥ مِن قِبَلِهِ ٱلْعَذَابُ

Transliteration yawma yaqūlu l-munāfiqūna wal-munāfiqātu lilladhīna āmanū unẓurūnā naqtabis min nūrikum qīla ir'jiʿū warāakum fal-tamisū nūran faḍuriba baynahum bisūrin lahu bābun bāṭinuhu fīhi l-raḥmatu waẓāhiruhu min qibalihi l-ʿadhābu

Hausa Rãnar da munafikai maza da munãfikai mãtã ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmãni: "Ku dũbẽ mu, mu yi makãmashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku kõma a bãyanku, dõmin ku nẽmo wani haske." Sai a danne a tsakãninsu da wani gãru yanã da wani ƙyaure, a cikinsa nan rahama take, kuma a bãyansa daga wajensa azaba take.

Verse 14

يُنَادُونَهُمْ أَلَمْ نَكُن مَّعَكُمْ ۖ قَالُوا۟ بَلَىٰ وَلَـٰكِنَّكُمْ فَتَنتُمْ أَنفُسَكُمْ وَتَرَبَّصْتُمْ وَٱرْتَبْتُمْ وَغَرَّتْكُمُ ٱلْأَمَانِىُّ حَتَّىٰ جَآءَ أَمْرُ ٱللَّهِ وَغَرَّكُم بِٱللَّهِ ٱلْغَرُورُ

Transliteration yunādūnahum alam nakun maʿakum qālū balā walākinnakum fatantum anfusakum watarabbaṣtum wa-ir'tabtum wagharratkumu l-amāniyu ḥattā jāa amru l-lahi wagharrakum bil-lahi l-gharūru

Hausa Sunã kiran su, "Ashe, bã tãre muke da ku ba?" Su ce: "Ĩ, amma kũ, kun fitini kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku game da Allah."

Verse 15

فَٱلْيَوْمَ لَا يُؤْخَذُ مِنكُمْ فِدْيَةٌ وَلَا مِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ۚ مَأْوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ ۖ هِىَ مَوْلَىٰكُمْ ۖ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ

Transliteration fal-yawma lā yu'khadhu minkum fid'yatun walā mina alladhīna kafarū mawākumu l-nāru hiya mawlākum wabi'sa l-maṣīru

Hausa "To, a yau bã zã a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bã zã a karɓa daga waɗanda suka kãfirta ba. Makõmarku wutã ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makõmarku ɗin nan tã mũnana."

Verse 16

۞ أَلَمْ يَأْنِ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَن تَخْشَعَ قُلُوبُهُمْ لِذِكْرِ ٱللَّهِ وَمَا نَزَلَ مِنَ ٱلْحَقِّ وَلَا يَكُونُوا۟ كَٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ مِن قَبْلُ فَطَالَ عَلَيْهِمُ ٱلْأَمَدُ فَقَسَتْ قُلُوبُهُمْ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ فَـٰسِقُونَ

Transliteration alam yani lilladhīna āmanū an takhshaʿa qulūbuhum lidhik'ri l-lahi wamā nazala mina l-ḥaqi walā yakūnū ka-alladhīna ūtū l-kitāba min qablu faṭāla ʿalayhimu l-amadu faqasat qulūbuhum wakathīrun min'hum fāsiqūna

Hausa Shin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ zukãtansu su yi tawãlu'i ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.

Verse 17

ٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ يُحْىِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ قَدْ بَيَّنَّا لَكُمُ ٱلْـَٔايَـٰتِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ

Transliteration iʿ'lamū anna l-laha yuḥ'yī l-arḍa baʿda mawtihā qad bayyannā lakumu l-āyāti laʿallakum taʿqilūna

Hausa Ku sani cẽwa Allah Yanã rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle Mun bayyanamuku ãyõyi da fatan zã ku yi hankali.

Verse 18

إِنَّ ٱلْمُصَّدِّقِينَ وَٱلْمُصَّدِّقَـٰتِ وَأَقْرَضُوا۟ ٱللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا يُضَـٰعَفُ لَهُمْ وَلَهُمْ أَجْرٌ كَرِيمٌ

Transliteration inna l-muṣadiqīna wal-muṣadiqāti wa-aqraḍū l-laha qarḍan ḥasanan yuḍāʿafu lahum walahum ajrun karīmun

Hausa Lalle mãsu gaskatãwa maza da mãsu gaskatãwa mãtã, kuma suka ranta wa Allah rance mai kyau, anã riɓanya musu, kuma suna da wani sakamako na karimci.

Verse 19

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦٓ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلصِّدِّيقُونَ ۖ وَٱلشُّهَدَآءُ عِندَ رَبِّهِمْ لَهُمْ أَجْرُهُمْ وَنُورُهُمْ ۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَآ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلْجَحِيمِ

Transliteration wa-alladhīna āmanū bil-lahi warusulihi ulāika humu l-ṣidīqūna wal-shuhadāu ʿinda rabbihim lahum ajruhum wanūruhum wa-alladhīna kafarū wakadhabū biāyātinā ulāika aṣḥābu l-jaḥīmi

Hausa Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da Mazannin Sa waɗannan sũ ne kamãlar gaskatãwa kuma su ne mãsu shahãda awurin Ubangjinsu. sunã da sakamakonsu da haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, waɗannan su ne'yan Jahĩm.

Verse 20

ٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّمَا ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا لَعِبٌ وَلَهْوٌ وَزِينَةٌ وَتَفَاخُرٌۢ بَيْنَكُمْ وَتَكَاثُرٌ فِى ٱلْأَمْوَٰلِ وَٱلْأَوْلَـٰدِ ۖ كَمَثَلِ غَيْثٍ أَعْجَبَ ٱلْكُفَّارَ نَبَاتُهُۥ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَىٰهُ مُصْفَرًّا ثُمَّ يَكُونُ حُطَـٰمًا ۖ وَفِى ٱلْـَٔاخِرَةِ عَذَابٌ شَدِيدٌ وَمَغْفِرَةٌ مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضْوَٰنٌ ۚ وَمَا ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَآ إِلَّا مَتَـٰعُ ٱلْغُرُورِ

Transliteration iʿ'lamū annamā l-ḥayatu l-dun'yā laʿibun walahwun wazīnatun watafākhurun baynakum watakāthurun fī l-amwāli wal-awlādi kamathali ghaythin aʿjaba l-kufāra nabātuhu thumma yahīju fatarāhu muṣ'farran thumma yakūnu ḥuṭāman wafī l-ākhirati ʿadhābun shadīdun wamaghfiratun mina l-lahi wariḍ'wānun wamā l-ḥayatu l-dun'yā illā matāʿu l-ghurūri

Hausa Ku sani cẽwa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai.

Verse 21

سَابِقُوٓا۟ إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا كَعَرْضِ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ أُعِدَّتْ لِلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ ۚ ذَٰلِكَ فَضْلُ ٱللَّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَآءُ ۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلْفَضْلِ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration sābiqū ilā maghfiratin min rabbikum wajannatin ʿarḍuhā kaʿarḍi l-samāi wal-arḍi uʿiddat lilladhīna āmanū bil-lahi warusulihi dhālika faḍlu l-lahi yu'tīhi man yashāu wal-lahu dhū l-faḍli l-ʿaẓīmi

Hausa Ku yi tsẽre zuwa ga (nẽman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna fãɗinta kamar fãɗin samã da ƙasã ne, an yi tattalinta dõmin waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da Manzannin Sa. Wannan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma.

Verse 22

مَآ أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٍ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا فِىٓ أَنفُسِكُمْ إِلَّا فِى كِتَـٰبٍ مِّن قَبْلِ أَن نَّبْرَأَهَآ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٌ

Transliteration mā aṣāba min muṣībatin fī l-arḍi walā fī anfusikum illā fī kitābin min qabli an nabra-ahā inna dhālika ʿalā l-lahi yasīrun

Hausa Wata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne.

Verse 23

لِّكَيْلَا تَأْسَوْا۟ عَلَىٰ مَا فَاتَكُمْ وَلَا تَفْرَحُوا۟ بِمَآ ءَاتَىٰكُمْ ۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخْتَالٍ فَخُورٍ

Transliteration likaylā tasaw ʿalā mā fātakum walā tafraḥū bimā ātākum wal-lahu lā yuḥibbu kulla mukh'tālin fakhūrin

Hausa Dõmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar alfahari da abin da Ya bã ku. Kuma Allah bã Ya son dukkan mai tãƙama, mai alfahari.

Verse 24

ٱلَّذِينَ يَبْخَلُونَ وَيَأْمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلْبُخْلِ ۗ وَمَن يَتَوَلَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْغَنِىُّ ٱلْحَمِيدُ

Transliteration alladhīna yabkhalūna wayamurūna l-nāsa bil-bukh'li waman yatawalla fa-inna l-laha huwa l-ghaniyu l-ḥamīdu

Hausa Watau, waɗanda ke yin rõwa, kuma sunã umumin mutãne da yin rõwa. Kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne kaɗai Mawadãci, Gõdadde.

Verse 25

لَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلَنَا بِٱلْبَيِّنَـٰتِ وَأَنزَلْنَا مَعَهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ وَٱلْمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلْقِسْطِ ۖ وَأَنزَلْنَا ٱلْحَدِيدَ فِيهِ بَأْسٌ شَدِيدٌ وَمَنَـٰفِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعْلَمَ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥ وَرُسُلَهُۥ بِٱلْغَيْبِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِىٌّ عَزِيزٌ

Transliteration laqad arsalnā rusulanā bil-bayināti wa-anzalnā maʿahumu l-kitāba wal-mīzāna liyaqūma l-nāsu bil-qis'ṭi wa-anzalnā l-ḥadīda fīhi basun shadīdun wamanāfiʿu lilnnāsi waliyaʿlama l-lahu man yanṣuruhu warusulahu bil-ghaybi inna l-laha qawiyyun ʿazīzun

Hausa Haƙĩƙa, lalle Mun aiko Manzannin Mu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin Allah Ya san mai taimakon Sa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.

Verse 26

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا وَإِبْرَٰهِيمَ وَجَعَلْنَا فِى ذُرِّيَّتِهِمَا ٱلنُّبُوَّةَ وَٱلْكِتَـٰبَ ۖ فَمِنْهُم مُّهْتَدٍ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ فَـٰسِقُونَ

Transliteration walaqad arsalnā nūḥan wa-ib'rāhīma wajaʿalnā fī dhurriyyatihimā l-nubuwata wal-kitāba famin'hum muh'tadin wakathīrun min'hum fāsiqūna

Hausa Kuma haƙĩƙa, lalle, Mun aiki Nũhu da Ibrahĩm, kuma Muka sanya Annabci da Littĩfi a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai nẽman shiryuwa, kuma mãsu yawa daga cikinsu fasiƙai ne.

Verse 27

ثُمَّ قَفَّيْنَا عَلَىٰٓ ءَاثَـٰرِهِم بِرُسُلِنَا وَقَفَّيْنَا بِعِيسَى ٱبْنِ مَرْيَمَ وَءَاتَيْنَـٰهُ ٱلْإِنجِيلَ وَجَعَلْنَا فِى قُلُوبِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ رَأْفَةً وَرَحْمَةً وَرَهْبَانِيَّةً ٱبْتَدَعُوهَا مَا كَتَبْنَـٰهَا عَلَيْهِمْ إِلَّا ٱبْتِغَآءَ رِضْوَٰنِ ٱللَّهِ فَمَا رَعَوْهَا حَقَّ رِعَايَتِهَا ۖ فَـَٔاتَيْنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مِنْهُمْ أَجْرَهُمْ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ فَـٰسِقُونَ

Transliteration thumma qaffaynā ʿalā āthārihim birusulinā waqaffaynā biʿīsā ib'ni maryama waātaynāhu l-injīla wajaʿalnā fī qulūbi alladhīna ittabaʿūhu rafatan waraḥmatan warahbāniyyatan ib'tadaʿūhā mā katabnāhā ʿalayhim illā ib'tighāa riḍ'wāni l-lahi famā raʿawhā ḥaqqa riʿāyatihā faātaynā alladhīna āmanū min'hum ajrahum wakathīrun min'hum fāsiqūna

Hausa Sa'an nan Muka biyar a bãyansu da Manzannin Mu; kuma Muka biyar da ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin zukãtan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbãnanci wanda suka ƙãga, shi, ba Mu rubũta shi ba a kansu, fãce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabõda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinsu sakamakonsu kuma mãsu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.

Verse 28

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَءَامِنُوا۟ بِرَسُولِهِۦ يُؤْتِكُمْ كِفْلَيْنِ مِن رَّحْمَتِهِۦ وَيَجْعَل لَّكُمْ نُورًا تَمْشُونَ بِهِۦ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ۚ وَٱللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ

Transliteration yāayyuhā alladhīna āmanū ittaqū l-laha waāminū birasūlihi yu'tikum kif'layni min raḥmatihi wayajʿal lakum nūran tamshūna bihi wayaghfir lakum wal-lahu ghafūrun raḥīmun

Hausa Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da Manzon Sa Ya bã ku rabo biyu daga rahamar Sa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama.

Verse 29

لِّئَلَّا يَعْلَمَ أَهْلُ ٱلْكِتَـٰبِ أَلَّا يَقْدِرُونَ عَلَىٰ شَىْءٍ مِّن فَضْلِ ٱللَّهِ ۙ وَأَنَّ ٱلْفَضْلَ بِيَدِ ٱللَّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَآءُ ۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلْفَضْلِ ٱلْعَظِيمِ

Transliteration li-allā yaʿlama ahlu l-kitābi allā yaqdirūna ʿalā shayin min faḍli l-lahi wa-anna l-faḍla biyadi l-lahi yu'tīhi man yashāu wal-lahu dhū l-faḍli l-ʿaẓīmi

Hausa Dõmin kada mutãnen Littãfi su san cẽwa lalle bã su da ikon yi ga kõme na falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so (wannan jãhilci yã hana su ĩmani). Kuma Alah Mai falala ne mai girma.

Read Surah Al-Hadid in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.