MyDugsiStart learning

Surah Al-Buruj in Hausa: translation and audio

Surah 85 · البروج · The Mansions of the Stars · 22 verses

Surah Al-Buruj verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Buruj word by word in English.

Verse 1

وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلْبُرُوجِ

Transliteration wal-samāi dhāti l-burūji

Hausa Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.

Verse 2

وَٱلْيَوْمِ ٱلْمَوْعُودِ

Transliteration wal-yawmi l-mawʿūdi

Hausa Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,

Verse 3

وَشَاهِدٍ وَمَشْهُودٍ

Transliteration washāhidin wamashhūdin

Hausa Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa

Verse 4

قُتِلَ أَصْحَـٰبُ ٱلْأُخْدُودِ

Transliteration qutila aṣḥābu l-ukh'dūdi

Hausa An la'ani mutãnen rãmi.

Verse 5

ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلْوَقُودِ

Transliteration al-nāri dhāti l-waqūdi

Hausa Wato wuta wadda aka hura.

Verse 6

إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ

Transliteration idh hum ʿalayhā quʿūdun

Hausa A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.

Verse 7

وَهُمْ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ بِٱلْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ

Transliteration wahum ʿalā mā yafʿalūna bil-mu'minīna shuhūdun

Hausa Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.

Verse 8

وَمَا نَقَمُوا۟ مِنْهُمْ إِلَّآ أَن يُؤْمِنُوا۟ بِٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَمِيدِ

Transliteration wamā naqamū min'hum illā an yu'minū bil-lahi l-ʿazīzi l-ḥamīdi

Hausa Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.

Verse 9

ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدٌ

Transliteration alladhī lahu mul'ku l-samāwāti wal-arḍi wal-lahu ʿalā kulli shayin shahīdun

Hausa Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.

Verse 10

إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُوا۟ ٱلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَـٰتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا۟ فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ ٱلْحَرِيقِ

Transliteration inna alladhīna fatanū l-mu'minīna wal-mu'mināti thumma lam yatūbū falahum ʿadhābu jahannama walahum ʿadhābu l-ḥarīqi

Hausa Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.

Verse 11

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَهُمْ جَنَّـٰتٌ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْفَوْزُ ٱلْكَبِيرُ

Transliteration inna alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti lahum jannātun tajrī min taḥtihā l-anhāru dhālika l-fawzu l-kabīru

Hausa Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.

Verse 12

إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ

Transliteration inna baṭsha rabbika lashadīdun

Hausa Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.

Verse 13

إِنَّهُۥ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ

Transliteration innahu huwa yub'di-u wayuʿīdu

Hausa Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).

Verse 14

وَهُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلْوَدُودُ

Transliteration wahuwa l-ghafūru l-wadūdu

Hausa Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.

Verse 15

ذُو ٱلْعَرْشِ ٱلْمَجِيدُ

Transliteration dhū l-ʿarshi l-majīdu

Hausa Mai Al'arshi mai girma

Verse 16

فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ

Transliteration faʿʿālun limā yurīdu

Hausa Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.

Verse 17

هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْجُنُودِ

Transliteration hal atāka ḥadīthu l-junūdi

Hausa Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.

Verse 18

فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ

Transliteration fir'ʿawna wathamūda

Hausa Fir'auna da samũdãwa?

Verse 19

بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فِى تَكْذِيبٍ

Transliteration bali alladhīna kafarū fī takdhībin

Hausa Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.

Verse 20

وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطٌۢ

Transliteration wal-lahu min warāihim muḥīṭun

Hausa Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa).

Verse 21

بَلْ هُوَ قُرْءَانٌ مَّجِيدٌ

Transliteration bal huwa qur'ānun majīdun

Hausa Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.

Verse 22

فِى لَوْحٍ مَّحْفُوظٍۭ

Transliteration fī lawḥin maḥfūẓin

Hausa A cikin Allo tsararre.

Read Surah Al-Buruj in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.