MyDugsiStart learning

Surah Ad-Dukhan in Hausa: translation and audio

Surah 44 · الدخان · The Smoke · 59 verses

Surah Ad-Dukhan verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Ad-Dukhan word by word in English.

Verse 1

حمٓ

Transliteration hha-meem

Hausa Ḥ. M̃.

Verse 2

وَٱلْكِتَـٰبِ ٱلْمُبِينِ

Transliteration wal-kitābi l-mubīni

Hausa Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.

Verse 3

إِنَّآ أَنزَلْنَـٰهُ فِى لَيْلَةٍ مُّبَـٰرَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ

Transliteration innā anzalnāhu fī laylatin mubārakatin innā kunnā mundhirīna

Hausa Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.

Verse 4

فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ

Transliteration fīhā yuf'raqu kullu amrin ḥakīmin

Hausa A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.

Verse 5

أَمْرًا مِّنْ عِندِنَآ ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ

Transliteration amran min ʿindinā innā kunnā mur'silīna

Hausa Umurni na daga wurin Mu. Lalle Mũ ne Muka kasance Mãsu aikãwã.

Verse 6

رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ

Transliteration raḥmatan min rabbika innahu huwa l-samīʿu l-ʿalīmu

Hausa Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.

Verse 7

رَبِّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَآ ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ

Transliteration rabbi l-samāwāti wal-arḍi wamā baynahumā in kuntum mūqinīna

Hausa (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).

Verse 8

لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْىِۦ وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ

Transliteration lā ilāha illā huwa yuḥ'yī wayumītu rabbukum warabbu ābāikumu l-awalīna

Hausa Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.

Verse 9

بَلْ هُمْ فِى شَكٍّ يَلْعَبُونَ

Transliteration bal hum fī shakkin yalʿabūna

Hausa A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.

Verse 10

فَٱرْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِى ٱلسَّمَآءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍ

Transliteration fa-ir'taqib yawma tatī l-samāu bidukhānin mubīnin

Hausa Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.

Verse 11

يَغْشَى ٱلنَّاسَ ۖ هَـٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ

Transliteration yaghshā l-nāsa hādhā ʿadhābun alīmun

Hausa Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.

Verse 12

رَّبَّنَا ٱكْشِفْ عَنَّا ٱلْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ

Transliteration rabbanā ik'shif ʿannā l-ʿadhāba innā mu'minūna

Hausa Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.

Verse 13

أَنَّىٰ لَهُمُ ٱلذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَآءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌ

Transliteration annā lahumu l-dhik'rā waqad jāahum rasūlun mubīnun

Hausa Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?

Verse 14

ثُمَّ تَوَلَّوْا۟ عَنْهُ وَقَالُوا۟ مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌ

Transliteration thumma tawallaw ʿanhu waqālū muʿallamun majnūnun

Hausa Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."

Verse 15

إِنَّا كَاشِفُوا۟ ٱلْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَآئِدُونَ

Transliteration innā kāshifū l-ʿadhābi qalīlan innakum ʿāidūna

Hausa Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).

Verse 16

يَوْمَ نَبْطِشُ ٱلْبَطْشَةَ ٱلْكُبْرَىٰٓ إِنَّا مُنتَقِمُونَ

Transliteration yawma nabṭishu l-baṭshata l-kub'rā innā muntaqimūna

Hausa Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.

Verse 17

۞ وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَآءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ

Transliteration walaqad fatannā qablahum qawma fir'ʿawna wajāahum rasūlun karīmun

Hausa Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.

Verse 18

أَنْ أَدُّوٓا۟ إِلَىَّ عِبَادَ ٱللَّهِ ۖ إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ

Transliteration an addū ilayya ʿibāda l-lahi innī lakum rasūlun amīnun

Hausa (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."

Verse 19

وَأَن لَّا تَعْلُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ ۖ إِنِّىٓ ءَاتِيكُم بِسُلْطَـٰنٍ مُّبِينٍ

Transliteration wa-an lā taʿlū ʿalā l-lahi innī ātīkum bisul'ṭānin mubīnin

Hausa "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."

Verse 20

وَإِنِّى عُذْتُ بِرَبِّى وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ

Transliteration wa-innī ʿudh'tu birabbī warabbikum an tarjumūni

Hausa "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."

Verse 21

وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا۟ لِى فَٱعْتَزِلُونِ

Transliteration wa-in lam tu'minū lī fa-iʿ'tazilūni

Hausa "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."

Verse 22

فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَ

Transliteration fadaʿā rabbahu anna hāulāi qawmun muj'rimūna

Hausa Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.

Verse 23

فَأَسْرِ بِعِبَادِى لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ

Transliteration fa-asri biʿibādī laylan innakum muttabaʿūna

Hausa (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"

Verse 24

وَٱتْرُكِ ٱلْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ

Transliteration wa-ut'ruki l-baḥra rahwan innahum jundun mugh'raqūna

Hausa "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."

Verse 25

كَمْ تَرَكُوا۟ مِن جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ

Transliteration kam tarakū min jannātin waʿuyūnin

Hausa Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.

Verse 26

وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ

Transliteration wazurūʿin wamaqāmin karīmin

Hausa Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.

Verse 27

وَنَعْمَةٍ كَانُوا۟ فِيهَا فَـٰكِهِينَ

Transliteration wanaʿmatin kānū fīhā fākihīna

Hausa Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.

Verse 28

كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَـٰهَا قَوْمًا ءَاخَرِينَ

Transliteration kadhālika wa-awrathnāhā qawman ākharīna

Hausa Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.

Verse 29

فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ ٱلسَّمَآءُ وَٱلْأَرْضُ وَمَا كَانُوا۟ مُنظَرِينَ

Transliteration famā bakat ʿalayhimu l-samāu wal-arḍu wamā kānū munẓarīna

Hausa Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.

Verse 30

وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ مِنَ ٱلْعَذَابِ ٱلْمُهِينِ

Transliteration walaqad najjaynā banī is'rāīla mina l-ʿadhābi l-muhīni

Hausa Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.

Verse 31

مِن فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَالِيًا مِّنَ ٱلْمُسْرِفِينَ

Transliteration min fir'ʿawna innahu kāna ʿāliyan mina l-mus'rifīna

Hausa Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.

Verse 32

وَلَقَدِ ٱخْتَرْنَـٰهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى ٱلْعَـٰلَمِينَ

Transliteration walaqadi ikh'tarnāhum ʿalā ʿil'min ʿalā l-ʿālamīna

Hausa Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.

Verse 33

وَءَاتَيْنَـٰهُم مِّنَ ٱلْـَٔايَـٰتِ مَا فِيهِ بَلَـٰٓؤٌا۟ مُّبِينٌ

Transliteration waātaynāhum mina l-āyāti mā fīhi balāon mubīnun

Hausa Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna

Verse 34

إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَيَقُولُونَ

Transliteration inna hāulāi layaqūlūna

Hausa Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,

Verse 35

إِنْ هِىَ إِلَّا مَوْتَتُنَا ٱلْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ

Transliteration in hiya illā mawtatunā l-ūlā wamā naḥnu bimunsharīna

Hausa "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."

Verse 36

فَأْتُوا۟ بِـَٔابَآئِنَآ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ

Transliteration fatū biābāinā in kuntum ṣādiqīna

Hausa "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."

Verse 37

أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَـٰهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ مُجْرِمِينَ

Transliteration ahum khayrun am qawmu tubbaʿin wa-alladhīna min qablihim ahlaknāhum innahum kānū muj'rimīna

Hausa shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.

Verse 38

وَمَا خَلَقْنَا ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَـٰعِبِينَ

Transliteration wamā khalaqnā l-samāwāti wal-arḍa wamā baynahumā lāʿibīna

Hausa Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.

Verse 39

مَا خَلَقْنَـٰهُمَآ إِلَّا بِٱلْحَقِّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Transliteration mā khalaqnāhumā illā bil-ḥaqi walākinna aktharahum lā yaʿlamūna

Hausa Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.

Verse 40

إِنَّ يَوْمَ ٱلْفَصْلِ مِيقَـٰتُهُمْ أَجْمَعِينَ

Transliteration inna yawma l-faṣli mīqātuhum ajmaʿīna

Hausa Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.

Verse 41

يَوْمَ لَا يُغْنِى مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْـًٔا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ

Transliteration yawma lā yugh'nī mawlan ʿan mawlan shayan walā hum yunṣarūna

Hausa Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.

Verse 42

إِلَّا مَن رَّحِمَ ٱللَّهُ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Transliteration illā man raḥima l-lahu innahu huwa l-ʿazīzu l-raḥīmu

Hausa fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Verse 43

إِنَّ شَجَرَتَ ٱلزَّقُّومِ

Transliteration inna shajarata l-zaqūmi

Hausa Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),

Verse 44

طَعَامُ ٱلْأَثِيمِ

Transliteration ṭaʿāmu l-athīmi

Hausa Ita ce abincin mai laifi.

Verse 45

كَٱلْمُهْلِ يَغْلِى فِى ٱلْبُطُونِ

Transliteration kal-muh'li yaghlī fī l-buṭūni

Hausa Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.

Verse 46

كَغَلْىِ ٱلْحَمِيمِ

Transliteration kaghalyi l-ḥamīmi

Hausa Kamar tafasar ruwan zãfi.

Verse 47

خُذُوهُ فَٱعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلْجَحِيمِ

Transliteration khudhūhu fa-iʿ'tilūhu ilā sawāi l-jaḥīmi

Hausa (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."

Verse 48

ثُمَّ صُبُّوا۟ فَوْقَ رَأْسِهِۦ مِنْ عَذَابِ ٱلْحَمِيمِ

Transliteration thumma ṣubbū fawqa rasihi min ʿadhābi l-ḥamīmi

Hausa "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."

Verse 49

ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْكَرِيمُ

Transliteration dhuq innaka anta l-ʿazīzu l-karīmu

Hausa (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"

Verse 50

إِنَّ هَـٰذَا مَا كُنتُم بِهِۦ تَمْتَرُونَ

Transliteration inna hādhā mā kuntum bihi tamtarūna

Hausa "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."

Verse 51

إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى مَقَامٍ أَمِينٍ

Transliteration inna l-mutaqīna fī maqāmin amīnin

Hausa Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.

Verse 52

فِى جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ

Transliteration fī jannātin waʿuyūnin

Hausa A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.

Verse 53

يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَـٰبِلِينَ

Transliteration yalbasūna min sundusin wa-is'tabraqin mutaqābilīna

Hausa Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.

Verse 54

كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَـٰهُم بِحُورٍ عِينٍ

Transliteration kadhālika wazawwajnāhum biḥūrin ʿīnin

Hausa Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyawun idãnu, mãsu girmansu.

Verse 55

يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَـٰكِهَةٍ ءَامِنِينَ

Transliteration yadʿūna fīhā bikulli fākihatin āminīna

Hausa Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).

Verse 56

لَا يَذُوقُونَ فِيهَا ٱلْمَوْتَ إِلَّا ٱلْمَوْتَةَ ٱلْأُولَىٰ ۖ وَوَقَىٰهُمْ عَذَابَ ٱلْجَحِيمِ

Transliteration lā yadhūqūna fīhā l-mawta illā l-mawtata l-ūlā wawaqāhum ʿadhāba l-jaḥīmi

Hausa Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.

Verse 57

فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ

Transliteration faḍlan min rabbika dhālika huwa l-fawzu l-ʿaẓīmu

Hausa Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.

Verse 58

فَإِنَّمَا يَسَّرْنَـٰهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ

Transliteration fa-innamā yassarnāhu bilisānika laʿallahum yatadhakkarūna

Hausa Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.

Verse 59

فَٱرْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَ

Transliteration fa-ir'taqib innahum mur'taqibūna

Hausa Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.

Read Surah Ad-Dukhan in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.