MyDugsiStart learning

Surah Al-Jinn in Hausa: translation and audio

Surah 72 · الجن · The Jinn · 28 verses

Surah Al-Jinn verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Jinn word by word in English.

Verse 1

قُلْ أُوحِىَ إِلَىَّ أَنَّهُ ٱسْتَمَعَ نَفَرٌ مِّنَ ٱلْجِنِّ فَقَالُوٓا۟ إِنَّا سَمِعْنَا قُرْءَانًا عَجَبًا

Transliteration qul ūḥiya ilayya annahu is'tamaʿa nafarun mina l-jini faqālū innā samiʿ'nā qur'ānan ʿajaban

Hausa Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui'ãni), mai ban mãmãki."

Verse 2

يَهْدِىٓ إِلَى ٱلرُّشْدِ فَـَٔامَنَّا بِهِۦ ۖ وَلَن نُّشْرِكَ بِرَبِّنَآ أَحَدًا

Transliteration yahdī ilā l-rush'di faāmannā bihi walan nush'rika birabbinā aḥadan

Hausa "Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba."

Verse 3

وَأَنَّهُۥ تَعَـٰلَىٰ جَدُّ رَبِّنَا مَا ٱتَّخَذَ صَـٰحِبَةً وَلَا وَلَدًا

Transliteration wa-annahu taʿālā jaddu rabbinā mā ittakhadha ṣāḥibatan walā waladan

Hausa "Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba."

Verse 4

وَأَنَّهُۥ كَانَ يَقُولُ سَفِيهُنَا عَلَى ٱللَّهِ شَطَطًا

Transliteration wa-annahu kāna yaqūlu safīhunā ʿalā l-lahi shaṭaṭan

Hausa "Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah."

Verse 5

وَأَنَّا ظَنَنَّآ أَن لَّن تَقُولَ ٱلْإِنسُ وَٱلْجِنُّ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا

Transliteration wa-annā ẓanannā an lan taqūla l-insu wal-jinu ʿalā l-lahi kadhiban

Hausa "Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah."

Verse 6

وَأَنَّهُۥ كَانَ رِجَالٌ مِّنَ ٱلْإِنسِ يَعُوذُونَ بِرِجَالٍ مِّنَ ٱلْجِنِّ فَزَادُوهُمْ رَهَقًا

Transliteration wa-annahu kāna rijālun mina l-insi yaʿūdhūna birijālin mina l-jini fazādūhum rahaqan

Hausa "Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai."

Verse 7

وَأَنَّهُمْ ظَنُّوا۟ كَمَا ظَنَنتُمْ أَن لَّن يَبْعَثَ ٱللَّهُ أَحَدًا

Transliteration wa-annahum ẓannū kamā ẓanantum an lan yabʿatha l-lahu aḥadan

Hausa "Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba."

Verse 8

وَأَنَّا لَمَسْنَا ٱلسَّمَآءَ فَوَجَدْنَـٰهَا مُلِئَتْ حَرَسًا شَدِيدًا وَشُهُبًا

Transliteration wa-annā lamasnā l-samāa fawajadnāhā muli-at ḥarasan shadīdan washuhuban

Hausa "Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye."

Verse 9

وَأَنَّا كُنَّا نَقْعُدُ مِنْهَا مَقَـٰعِدَ لِلسَّمْعِ ۖ فَمَن يَسْتَمِعِ ٱلْـَٔانَ يَجِدْ لَهُۥ شِهَابًا رَّصَدًا

Transliteration wa-annā kunnā naqʿudu min'hā maqāʿida lilssamʿi faman yastamiʿi l-āna yajid lahu shihāban raṣadan

Hausa "Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa."

Verse 10

وَأَنَّا لَا نَدْرِىٓ أَشَرٌّ أُرِيدَ بِمَن فِى ٱلْأَرْضِ أَمْ أَرَادَ بِهِمْ رَبُّهُمْ رَشَدًا

Transliteration wa-annā lā nadrī asharrun urīda biman fī l-arḍi am arāda bihim rabbuhum rashadan

Hausa "Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?"

Verse 11

وَأَنَّا مِنَّا ٱلصَّـٰلِحُونَ وَمِنَّا دُونَ ذَٰلِكَ ۖ كُنَّا طَرَآئِقَ قِدَدًا

Transliteration wa-annā minnā l-ṣāliḥūna waminnā dūna dhālika kunnā ṭarāiqa qidadan

Hausa "Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam."

Verse 12

وَأَنَّا ظَنَنَّآ أَن لَّن نُّعْجِزَ ٱللَّهَ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَن نُّعْجِزَهُۥ هَرَبًا

Transliteration wa-annā ẓanannā an lan nuʿ'jiza l-laha fī l-arḍi walan nuʿ'jizahu haraban

Hausa "Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba."

Verse 13

وَأَنَّا لَمَّا سَمِعْنَا ٱلْهُدَىٰٓ ءَامَنَّا بِهِۦ ۖ فَمَن يُؤْمِنۢ بِرَبِّهِۦ فَلَا يَخَافُ بَخْسًا وَلَا رَهَقًا

Transliteration wa-annā lammā samiʿ'nā l-hudā āmannā bihi faman yu'min birabbihi falā yakhāfu bakhsan walā rahaqan

Hausa "Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba."

Verse 14

وَأَنَّا مِنَّا ٱلْمُسْلِمُونَ وَمِنَّا ٱلْقَـٰسِطُونَ ۖ فَمَنْ أَسْلَمَ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ تَحَرَّوْا۟ رَشَدًا

Transliteration wa-annā minnā l-mus'limūna waminnā l-qāsiṭūna faman aslama fa-ulāika taḥarraw rashadan

Hausa "Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa."

Verse 15

وَأَمَّا ٱلْقَـٰسِطُونَ فَكَانُوا۟ لِجَهَنَّمَ حَطَبًا

Transliteration wa-ammā l-qāsiṭūna fakānū lijahannama ḥaṭaban

Hausa "Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama."

Verse 16

وَأَلَّوِ ٱسْتَقَـٰمُوا۟ عَلَى ٱلطَّرِيقَةِ لَأَسْقَيْنَـٰهُم مَّآءً غَدَقًا

Transliteration wa-allawi is'taqāmū ʿalā l-ṭarīqati la-asqaynāhum māan ghadaqan

Hausa "Kuma dã sun tsayu sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa."

Verse 17

لِّنَفْتِنَهُمْ فِيهِ ۚ وَمَن يُعْرِضْ عَن ذِكْرِ رَبِّهِۦ يَسْلُكْهُ عَذَابًا صَعَدًا

Transliteration linaftinahum fīhi waman yuʿ'riḍ ʿan dhik'ri rabbihi yasluk'hu ʿadhāban ṣaʿadan

Hausa "Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa."

Verse 18

وَأَنَّ ٱلْمَسَـٰجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدْعُوا۟ مَعَ ٱللَّهِ أَحَدًا

Transliteration wa-anna l-masājida lillahi falā tadʿū maʿa l-lahi aḥadan

Hausa "Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)."

Verse 19

وَأَنَّهُۥ لَمَّا قَامَ عَبْدُ ٱللَّهِ يَدْعُوهُ كَادُوا۟ يَكُونُونَ عَلَيْهِ لِبَدًا

Transliteration wa-annahu lammā qāma ʿabdu l-lahi yadʿūhu kādū yakūnūna ʿalayhi libadan

Hausa "Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa."

Verse 20

قُلْ إِنَّمَآ أَدْعُوا۟ رَبِّى وَلَآ أُشْرِكُ بِهِۦٓ أَحَدًا

Transliteration qul innamā adʿū rabbī walā ush'riku bihi aḥadan

Hausa Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba."

Verse 21

قُلْ إِنِّى لَآ أَمْلِكُ لَكُمْ ضَرًّا وَلَا رَشَدًا

Transliteration qul innī lā amliku lakum ḍarran walā rashadan

Hausa Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri."

Verse 22

قُلْ إِنِّى لَن يُجِيرَنِى مِنَ ٱللَّهِ أَحَدٌ وَلَنْ أَجِدَ مِن دُونِهِۦ مُلْتَحَدًا

Transliteration qul innī lan yujīranī mina l-lahi aḥadun walan ajida min dūnihi mul'taḥadan

Hausa Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi."

Verse 23

إِلَّا بَلَـٰغًا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِسَـٰلَـٰتِهِۦ ۚ وَمَن يَعْصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ لَهُۥ نَارَ جَهَنَّمَ خَـٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا

Transliteration illā balāghan mina l-lahi warisālātihi waman yaʿṣi l-laha warasūlahu fa-inna lahu nāra jahannama khālidīna fīhā abadan

Hausa "Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da Manzon Sa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada."

Verse 24

حَتَّىٰٓ إِذَا رَأَوْا۟ مَا يُوعَدُونَ فَسَيَعْلَمُونَ مَنْ أَضْعَفُ نَاصِرًا وَأَقَلُّ عَدَدًا

Transliteration ḥattā idhā ra-aw mā yūʿadūna fasayaʿlamūna man aḍʿafu nāṣiran wa-aqallu ʿadadan

Hausa Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi.

Verse 25

قُلْ إِنْ أَدْرِىٓ أَقَرِيبٌ مَّا تُوعَدُونَ أَمْ يَجْعَلُ لَهُۥ رَبِّىٓ أَمَدًا

Transliteration qul in adrī aqarībun mā tūʿadūna am yajʿalu lahu rabbī amadan

Hausa Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya masa dõgon ajali!"

Verse 26

عَـٰلِمُ ٱلْغَيْبِ فَلَا يُظْهِرُ عَلَىٰ غَيْبِهِۦٓ أَحَدًا

Transliteration ʿālimu l-ghaybi falā yuẓ'hiru ʿalā ghaybihi aḥadan

Hausa "Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinsa ga kowa."

Verse 27

إِلَّا مَنِ ٱرْتَضَىٰ مِن رَّسُولٍ فَإِنَّهُۥ يَسْلُكُ مِنۢ بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِۦ رَصَدًا

Transliteration illā mani ir'taḍā min rasūlin fa-innahu yasluku min bayni yadayhi wamin khalfihi raṣadan

Hausa "Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi."

Verse 28

لِّيَعْلَمَ أَن قَدْ أَبْلَغُوا۟ رِسَـٰلَـٰتِ رَبِّهِمْ وَأَحَاطَ بِمَا لَدَيْهِمْ وَأَحْصَىٰ كُلَّ شَىْءٍ عَدَدًۢا

Transliteration liyaʿlama an qad ablaghū risālāti rabbihim wa-aḥāṭa bimā ladayhim wa-aḥṣā kulla shayin ʿadadan

Hausa "Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga."

Read Surah Al-Jinn in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.