MyDugsiStart learning

Surah Al-Bayyinah in Hausa: translation and audio

Surah 98 · البينة · The Clear Proof · 8 verses

Surah Al-Bayyinah verse by verse: the Arabic with a recitation you can repeat, the transliteration, and the Hausa translation by Abubakar Mahmood Jummi. For the meaning of every word, see Surah Al-Bayyinah word by word in English.

Verse 1

لَمْ يَكُنِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَـٰبِ وَٱلْمُشْرِكِينَ مُنفَكِّينَ حَتَّىٰ تَأْتِيَهُمُ ٱلْبَيِّنَةُ

Transliteration lam yakuni alladhīna kafarū min ahli l-kitābi wal-mush'rikīna munfakkīna ḥattā tatiyahumu l-bayinatu

Hausa Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu.

Verse 2

رَسُولٌ مِّنَ ٱللَّهِ يَتْلُوا۟ صُحُفًا مُّطَهَّرَةً

Transliteration rasūlun mina l-lahi yatlū ṣuḥufan muṭahharatan

Hausa Wani Manzo daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki.

Verse 3

فِيهَا كُتُبٌ قَيِّمَةٌ

Transliteration fīhā kutubun qayyimatun

Hausa A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja.

Verse 4

وَمَا تَفَرَّقَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ إِلَّا مِنۢ بَعْدِ مَا جَآءَتْهُمُ ٱلْبَيِّنَةُ

Transliteration wamā tafarraqa alladhīna ūtū l-kitāba illā min baʿdi mā jāathumu l-bayinatu

Hausa Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu.

Verse 5

وَمَآ أُمِرُوٓا۟ إِلَّا لِيَعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤْتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ ۚ وَذَٰلِكَ دِينُ ٱلْقَيِّمَةِ

Transliteration wamā umirū illā liyaʿbudū l-laha mukh'liṣīna lahu l-dīna ḥunafāa wayuqīmū l-ṣalata wayu'tū l-zakata wadhālika dīnu l-qayimati

Hausa Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai.

Verse 6

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَـٰبِ وَٱلْمُشْرِكِينَ فِى نَارِ جَهَنَّمَ خَـٰلِدِينَ فِيهَآ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمْ شَرُّ ٱلْبَرِيَّةِ

Transliteration inna alladhīna kafarū min ahli l-kitābi wal-mush'rikīna fī nāri jahannama khālidīna fīhā ulāika hum sharru l-bariyati

Hausa Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai.

Verse 7

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمْ خَيْرُ ٱلْبَرِيَّةِ

Transliteration inna alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti ulāika hum khayru l-bariyati

Hausa Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta.

Verse 8

جَزَآؤُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّـٰتُ عَدْنٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ خَـٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا ۖ رَّضِىَ ٱللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا۟ عَنْهُ ۚ ذَٰلِكَ لِمَنْ خَشِىَ رَبَّهُۥ

Transliteration jazāuhum ʿinda rabbihim jannātu ʿadnin tajrī min taḥtihā l-anhāru khālidīna fīhā abadan raḍiya l-lahu ʿanhum waraḍū ʿanhu dhālika liman khashiya rabbahu

Hausa Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa.

Read Surah Al-Bayyinah in another language

All languages

All 114 surahs in Hausa: the Qur’an in Hausa.

Learn it in MyDugsi

Hausa translation: Abubakar Mahmood Jummi, from Quran.com. Transliteration: Quran.com. Recitation: Mishary Alafasy, from EveryAyah.com. MyDugsi is a learning aid, not a replacement for a qualified teacher.